Showing 15001 words to 18000 words out of 325075 words

Chapter 6 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29092

zama cikin masoya masu mana SARAN ?OYE akan kasuwancinmu????, muna alfahari daku aduk inda kuke. Muna godiya kuma da ?aunar da kuke nuna mana irin trillions ?in nan. Idan nace ku na dabanne ina nufin na daban har cikin raina????????_.


*_Masu bu?atar mu saka musu tallar kayan sana'arsu zasu iya zuwa suyi magana damu domin tayasu tallata hajojinsu a yanar gizo??????_*.


No. 5

................."Indai har a yau dole sai an ?aura auren Abdallah da wata kamar yanda Yaya Malam ya fa?a, to kuwa sai dai a ?aura masa da ?iyar ?ar uwata Nusaiba!!".
Abban Abdallah dake shirin fita wajen ?aurin aure ya tsaya cak daga ?o?arin saka ma?allin rigar farar shaddarsa ?ar ciki yana kallon Momy ta mirror. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya cigaba da abinda ya keyi.
?arasa shigowa cikin ?akin tayi ta tsaya a bayansa cike da damuwa. Sai da ya gama saka ma?allin guda uku sannan ya ?auki babbar rigar itama ya warware zai saka. Saurin ri?e rigar Momy tayi hawaye na zubo mata saman fuska. Yanzu kam kallonta yayi da ?yau yana ?o?arin ha?iye damuwarsa. "Na zata mun gama wannan maganar tun shekaru uku da suka shu?e Khadija".
Sosai ta fashe masa da kuka yanzun kam tana kallonsa cikin ido, "Abban Abdallah dan ALLAH ka fahimcen......". "An?i a fahimcekin Khadijah!!". Ya fa?a a tsananin tsawace jikinsa har yana rawa. Ya fisge rigarsa dake a hannunta tare da nuna mata hanya alamar ta fice masa a ?aki.
"Abban Abdal......." "Khadija!!!". Ya kira sunanta da tsawa fiye dana farko. Baya taja a firgice ta manne da bango, sai kuma ta fashe da kuka bakinta na rawa alamar tanason yin magana amma tana shakka.
Tsaki Abba yay ya jefa babbar rigar saman gado yay ficewarsa ya barta a ?akin. Can bayan ?akunansu ya zagaya yanata huci. (nace, "Ashe ba Baba malam bane kawai mai zuciya a gidan??).

Zubewa ?asa Momy tayi tana kuka abin tausayi, kusan mintuna hu?u da fitar Abba akai Knocking ?ofar dayin sallama. Saurin share hawayenta tayi ta mi?e tsaye jin muryar Abdallah. Sai da ta kalla kanta a mirror ta sake cirar tissue ta gyara fuskar da ?yau sannan ta amsa masa sallamar da bashi izinin shigowa.
Jikinsa a sanyaye ya shigo, ya ?araso cikin ?akin sosai idanunsa akan mahaifiyarsa da itama kallonsa take cike da tausayawa. Matsowa tai da sauri kafin ya ?araso, ta kama hannunsa ta zaunar a bakin gadon tana fa?in, "Abdallah kana lafiya dai ko?".
"Momy bana a lafiya wlhy". Ya fa?a tamkar zai fashe da kuka. Murmushin ?arfin hali Momy tayi, kusa da shi ta zauna tana ?o?arin ha?iye tata damuwar. Ta kamo hanunsa cikin nata ta rumtse. "Abdallah nasan dole ka tsinta kanka a cikin ru?ani game da wannan al'amarin, sai dai dan ALLAH ka kwantar da hankalinka kaji, kasa a ranka haka shine mafi alkairi shiyyasa ALLAH ya ?addara hakan. Nu'aymah ba ita bace autar mata, bakuma dama an halicceka domin ita kawai bane ba........"
"Momy karkice haka, wlhy ina son Nu'aymah sosai, da sonta na rayu tun ban gama sanin ciwon kaina ba. Amma dan ALLAH Momy ki fa?amin inada wani haline mara ?yau da zaisa Nu'aymah ta ?ini?".
Murmushi Momy tayi, takai hannu saman kumatunsa ta shafa. "Baka da wani aibu Abdallah na, babu wata mace da zaka tunkara da kalmar so ace ta gujeka. Itama ?uruciya ce da rashin sanin ciwon kai ke ?awainiya da ita. Shawara ?aya zan baka shine ka kwantar da hankalinka, ka cigaba da addu'a kuma, inhar Nu'aymah alkairi ce a gareka, ALLAH kuma ya ?addara zata kasance cikin matanka ALLAH ya dawo da hankalinta gareka. Idan kuma ba alkairi bane aurenta ALLAH ya cire maka ita a zuciyarka kaji. Zan tayaka da addu'ar nan nima insha ALLAH".
Kansa ya ?aga mata hawaye na sulalo masa a ido ?aya. Momy ta saka babban yatsanta ta ?auke masa shi tana murmushi. "Banason ganin wannan hawayen Sweetheart kaji". Nanma kai kawai ya jinjina mata yana ha?iye tsantsar damuwarsa.
"To amma Momy ni banason a auramin kowa, a bari kawai zan jira Nu'aymah. Na ro?i Baba Malam hakan amma ya?i saurarena, nasa Abba ma bazai saurareniba tunda basa tsallake maganar Baba malam".
Shiru Momy tai kamar wadda ta tafi tunani, sai da Abdallah ya ?an ta?ata da kiran sunanta sannan ta sauke gajeren numfashi da kallonsa. "Abdallah kaima ka sani babu wanda ya isa canja abinda Yaya Malam ya fa?a a gidan nan, ko Hajjo goyama duk abinda ya shar?anta baya takeyi. Babbar damuwata kar ace za'a aura maka cikin ?ananun yarannan Yusrah ko Adawiya, dan kaga dai Hajarah da Kubrah duk sunada samarinsu kuma kowa yasani a gidan nan, tunda har an tsaida magana, jira kawai ake su kammala karatunsu a ?aura musu aure. Abdallah kullum shekaru kake ?arawa ba ?uruciya ba, ka kai minzalin da ya kamata ace ka ajiye iyali tuni, da ace baka zauna jiran gawon shanu ba da yanzu ?anka ko ?arka zai kai shekara biyar koma fiye da haka Abdallah. Abdallah dubeni tsufa fa nakeyi, ina bu?atar jikokina kamar yanda nasan kaima kana bu?atar mace tare da kai. Ya kamata ace ka auri yarinyar da zata iya kula da duka ?awainiyarka ba wadda zakai tunanin zaman raino ba Abdallah. Kayi nazari akan maganata ka ?aurata a mizanin fahimta. Aysha, Sumayya, Badariyya, Maryam duk ?annanka ne a gidan nan, amma ka duba shekarunsu nawa da yin aure?, dukansu sunada ?a?ansu abin sha'awa, duk da matane ba kamar kai namiji ba".
"Momy duka na fahimci maganarki, to amma kinga nima ai bansan wadda zasu aura mani ?inba, amma nasan Abbah ya sani, ki tambayesa kozai sanar miki?".
"Bazai sanar mini ba Abdallah, sai dai kaine nakeson ka kawoma kanka mafita". "Mafita kuma Momy? Tami?".
Numfashi ta sauke tana sake kallonsa da ?yau. "Abdallah kaje ka samu Baba malam ka sanar masa ka yarda su aura maka duk wadda sukaga ta dace, amma su ha?a maka da Nusaiban Fatima {Gwaggonka}".
"Momy Nusaiba kuma? Momy baki ha?ura da zancen nanba dama? ALLAH ni banta?a jin Nusaiba a rainaba Momy, ina mata sone na ?anwa kamar yanda nakema su Aysha".
"Abdallah basai kaso Nusaiba ba yanzun, idan kukai aure tana gidanka a hankali zaka fara sonta. Yarinyarnan ?ya?y?yawa ce itama, sannan tanada tarbiyya da hankali kaima ka sani ai".
Shiru Abdallah yay kawai yana kallon Momy, a cikin ransa sai faman fa?in, 'Nu'aymah kina inane? Dan ALLAH ki dawo gareni, ki taimakeni ki ceci zuciyar da bata ta?a fashi a ?aunarki ba, ki taimaki numfashin da ke burin rayuwa da naki har abada. Nu'aymah miyasa kika kasancemin mai SARAN ?OYE ne.........?'
"Abdallah!". Momy ta fa?a tana girgiza shi. Kallonta yay da sauri dan baiji mitace ba. Zaiyi magana Abba ya shigo ?akin. Duk da ya gansu sai ya ?auke kansa kamar baisan da suba, rigarsa ya nufa ya ?auka yana ?o?arin sakawa. Tashi Abdallah yay ya tako zuwa gabansa, taimaka masa yay ya saka rigar sannan ya kallesa. Zaiyi magana Abbah ya ?aga masa hannu. "Banason jin komai Abdallah, kaje ka shirya ka fita massallaci, dan da an idar da sallar Juma'a za'a ?aura maka aure kamar yanda Yayah ya fa?a".
?asa Abdallah yay da kansa yana ha?iye zuciya da sauri-sauri, baice komaiba ya juya ya fita idanunsa cike da ?walla.
?auke kai Abba yay ya maida ga mirror inda yake hidimar cigaba da shiryawa. Momy kuwa tabi ?an nata da kallo tamkar zata fasa kuka.

__________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
______________________

Masu posting a facebook dan ALLAH wannan ro?onane a gareku dama na WhatsApp da ko ina.. Nasan duk masoyin ?warai nason cigaban masoyinsa. Tabbas soyayyace ta sakaku kai littafina can, kuma inajin da?in hakan da alfahari da wannan soyayya. To amma dan ALLAH ina ro?onku ku tausaya mana banda littatafan mu na ?u?i. Kamar wannan SARAN ?OYE na ku?i ne, yana cikin ZAFAFA BIYAR 2021. daga yau kuma free pages sun ?are, gamai bu?ata yazo ya biya naira 300 kacal sai ya cigaba da samu dan girman ALLAH Masoya amana adalci????????.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

____________________________

Hankalin Umm a tashe yake matu?a gaya, ta?i yarda ta fita wajen ?an uwanta balle ta sanar musu halin da ake ciki. Tunda Baba Malam da ya?i saurarenta itama ya fita bayan yayi shiri taketa kai kawo a ?akinsa. Lokaci zuwa lokaci tana share ?wallar dake ziraro mata.
Sam zuciyarta ta kasa yarda Nu'aymah guduwa tayi da kanta. Tasan wacece ?arta, tasan tarbiyyar data bata. To amma a yanda al'amarin ya zone babu ta inda ita kanta zata iya bama Nu'aymah kariya koda a wajen mahaifinta ne. Balle kuma sauran jama'ar gidan. 'Shin miya samu yarinyarta ne? Ta yaya tabar gida?' tai maganar a fili tana fashewa da kuka maiban tausayi.

"ALLAH sarki Umm kiyi ha?uri ALLAH na nan??????".

___________________________________

Gaba ?aya yanayin shagalin bikin a cikin gida ya canja, mazane kawai a waje da basusan mike faruwaba keta walwalarsu. Hakama abokan Abdallah sai faman fantamawa suke cikin farar shadda datai bala'in musu ?yau.
Sai da aka fara gabatar da sallar juma'a kafin a ?ora da ?aura auren da yazoma mutane da sa?anin abinda suka gani a jikin invitation card.
Ba mutanen waje kawai ba, hatta ?annen Baba Malam su Abba sai da sukasha mamaki matu?a da yanda ?aurin auren yazo. Dan kuwa ?aurin auren yazo musu ne a yanda basuyi tunani ko tsammani ba.
An ?aura auren Abdallah Rudwan Hashim Jibiya da Yusrah Musbahu Hashim Jibiya akan sadaki naira dubu ?ari. Sai aka sake ?aurawa da Adawiya Mustapha Hashim jibiya, da Abdallah Rudwan Hashim Jibiya shima akan sadaki naira dubu ?ari. Aka ?ora da doguwar addu'ar fatan zaman lafiya ga ma'auratan daga ?arshe.

Babu wanda ya iya magana a cikin su Abbah, dan kuwa su duk abinda Baba Malam ya zartar akansu bama ?a?ansu ba basu da ja. Sun gama bashi darajar Uba tun tuni, sunsan bazai cutar da suba balle kuma ?a?ansu. Fatansu kawai ALLAH yasa hakan shine mafi alkairi, ALLAH ya basu zaman lafiya kuma. Itama Nu'aymah ALLAH ya dawo musu da ita gida lafiya.

Kan Abdallah neman kwancewa yay dajin wannan al'amari, ko kammala ?aura auren ba'ayiba ya sulale ya koma cikin gida kansa na wani kalar mahaukacin sara masa, ?akin Abubakar cikin ?annensa samarin gidan ya shige ya kulle kansa batare da kowa ya saniba.

Abokansa kansu cikin ru?ani da mamaki suke, sai dai kafin su sami damar tambayarsa suka nemesa suka rasa a wajen. Dole sai tambayar juna lafiya? suka komayi. Amma babu mai bada amsa.

¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï¡ï

Hakama cikin gidan tunda sakamakon ?aurin aure ya iso kunnuwansu kowa ya kasa motsi, sai kallon kallo kawai akeyi da idanu baki ya gaza furta komai.
Momyn Abdallah jitai kamar an ?aura mata dutsen dala bisa kai. Tayayama za'a aurama Abdallah aure da yara ?anana irin wa?an nan har guda biyu?.
Haka taketa ayyanawa a zuciyarta, a fili kam sai la??anta ke motsi maganar ta kasa furtuwa. Sai danginta ne keta ?ananun magana musamman ma Umman Nusaiba.

Yusrah ma tunda zancen ya isa garesu ta yanke jiki ta fa?i a sume, sai da aka yayyafa mata ruwa ta farfa?o. Kuka take tamkar ranta zai fita. Ta yayama zata auri Yah Abdallah da tasan duk duniya babu wadda yake so sama da Nu'aymah. Sannan Nu'aymah ma na bala'in sonsa da ?aunarsa. Tunda aka wayi gari da ?atan Nu'aymah sam bata yarda guduwa tayiba, dan kuwa a daren jiya ana wajen walima ta dawo gida tanason shiga toilet. Motsin mutum taji a ?akin, amma tana shigowa aka ?uya bataga ko waneneba. Kashin daya matseta ne yasa batabi takan sanin wanene ba ta shige toilet. Bayan ta shiga ta fito taji motsin fitar koma wanene daga ?akin. Bataga kowayeba, hakan yasata fita da sauri ta zagaya ta bayan Windows ?in saboda ?arar jan akwati da taji kamar anayi tacan. Dan ko ina na gidan Interlock ne. Tana ?ullowa ana barin wajen, sai dai zuciyarta ta zargi mutum ?aya a lokacin, amma bata da tabbas ?in da zata fito tace ga abinda ta gani kokuma ga wanda ta gani. Dan babu wata ?wa?waran shaida a hannunta.
Abu na biyu Nu'aymah abokiyar firartace sosai, dan ko suna Lagos takanyi dogon Charting da Nu'aymah fiye da Amal da Adawiya, sannan kusan kullum sai sunyi waya, mafi yawan hirar da Nu'aymah ke mata kuma akan Yah Abdallah ne, dan komai na Nu'aymah da sunan Abdallah a ciki.
Ta sake fashewa da kuka tana ?an?ame Aminta da itama cikin ru?anin take. Bawai auren ?arta da Abdallah ne matsalarta ba, matsalarta yanda al'amarin yazo. Tana ganin kamar Mazansu sunyi gaggawa akan yanke wannan hukuncin. Kamar ya dace ace sun zauna sunyi dogon nazari da bincike akan al'amarin Nu'aymah. To amma ita bata da wani ?arfin iko akan sakawa ko hanawa a gidan, sai dai kawai ta shiga jerin shiga sahun masu addu'ar ALLAH ya warware al'amarin cikin sau?i, duk inda Nu'aymah take kuma ALLAH ya kareta ya tsareta, ALLAH ya maido hankalinta gida.

¡ï¡ï¡ï¡ï

Adawiya da ko wanka ta kasayi saboda fargabar wadda za'a mayema Abdallah gurbin Nu'aymah da ita ta mi?e zumbur sanda labarin ya iso kunnenta. Dama a sashensu take tun bayan gama dambarwar guduwar Nu'aymah. Ta daka wani uban tsalle zata ?wala ihun farin ciki Hajarah yayarta wadda takebi data shigo yanzun tai azamar rufe mata baki.
"Innalillahi, Adawiya minene haka kikeyi? Kefa nagama tamkar murna kikeyi ne ko mi?".
Janye hanun Aunty Hajarah Adawiya tai daga kan bakinta tana hura hanci, kamar zatai magana cikin masifa kuma saita fasa. Canja yanayinta tayi zuwa damuwa ?walla na taruwar mata a idanu. "Aunty Hajarah ki barni nayi ihu ko zanji sanyi a raina, ta yaya za'ace ni Adawiya nice matar Yah Abdallah yau?". A mamakin Hajarah sai taga Adawiya kuma ta fashe da dariya.
Baki Hajarah ta saki tana kallonta dan al'ajabi. Zatai magana sai ga Addah ta shigo ?akin.
"K! Wane kalar iskancine wannan?!!". Ta fa?a da matsananciyar tsawa tana kallon Adawiya data fara taka rawa. Da?ar ta zauna a bakin gado tana ?ata fuska.
Addah ta ?araso cikin ?akin jikinta har rawa yakeyi, jikake "Tasss!!" ta ?auke fuskar Adawiya da wani bahagon mari haggu da damanta. Kifff Adawiya ta kifo ?asa dan azaba da gushewar numfashi na wucin gadi.
Cikin tsananin firgici da tashin hankali Hajarah tai tsalle gefe jikinta itama na rawa, tai masifar ware idanu akan mahaifiyar tasu da akan da?e ba'aga fushintaba a gidan.
Addah tasa hannu ta ?ago Adawiya ta cigaba da bata maruka, sai da tai mata shidda ?warara sannan ta hanka?ata kan hado. Sosai wahala ma ta hana Adawiya kuka, sai sauke numfarfashi take tamkar zata shi?e. Kallon Hajarah Addah tayi, batare da tayi magana na ta nuna mata hanyar fita.
Zabira Hajarah tai ta nufi ?ofar da bala'in sassarfa, sai da taje gab da fita sannan ta tsaya cak saboda tsawar da Addah ta daka mata. "Idan kin fita ki sanar da kowa kinji ko?". Saurin ha?iye kukan dake neman kufce mata Hajarah tayi, ta kalli mahaifiyar tasu tana mai girgiza kanta. "K....k...kiyi ha?uri dan ALLAH Addah". Hanya ta sake nuna mata alamar ta wuce. Hajarah bata sake magana ba tabi umarnin Addah ta fice.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ?OYE na ku?ine, yana ?aya daga zafafa biyar, idan kana bu?ata kaima wa?anan numbers ?in magana ka biya ku?insa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka ya?a dan ALLAH idan ka gani??????.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

____________________________

Juyawa Addah ta sakeyi ga Adawiya dake kwance tamkar wadda sha?ar iskar numfashi taima ?aranci. "Tashi dan Ubanki!!". Da sauri Adawiya ta tashi tanaja baya daga farkon gadon zuwa ?arshe, jikinta sai rawa yake tana kallon Addah, amma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login