Showing 324001 words to 325075 words out of 325075 words

Chapter 109 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29164

kansa a ciki ya tashi zaune, kallon yanda yaran duk suka zuba tagumi yay, ya kuma dubi yanda Nu'aymah tai bala'in tsare gida. Sai shima kawai yay tagumi kamar yanda yaran sukayi ya zuba mata ido. Hararsu tayi su duka ta ida shigowa cikin ?akin. Da sauri Ibrahim dake da shekaru shida ya matsa jikin Yoohan ya lafe, sai itama Anum dake da uku ta matsa ta lafe. Duk yanda Yoohan yaso daurewa sai ya kasa ya saki ?aramar dariya yana kama kunnuwansu yaja ka?an.
"Wato ku?innan fa nagama ni kuka raina a gidan nan, ita Mie-mie kuna tsoronta, amma ni kunma maidani Uncle Jay kakanku ko?".
Yanda yay maganarne ya saka Nu'aymah yin dariya itama, ta yamutsa fuska da fa?in, "Dan ALLAH ka tattarasu ni kama kaisu gidan Miemaa, abar min Deen kawai anan".
Cikin ?age gira Yoohan yace, "Oh, saboda kinga yarona mai hakuri kina samin shi aiki ko. To na?i wayon, wa?anan tom and jerry ?in zan bar miki anan, Abbana kuwa kano ma zan kaisa yayma Umm Hutu da Uncle Muhammad. Inama yake?".
"Haba Yah Maleek dan ALLAH kar muyi haka da kai, wa?anan mi suka iya banda takurama mutane".
"Hhhh kunfi kusa ai. Kai mai jan kunne ina Abbana yake?". Yoohan ya fa?a dajan kunnen Ibrahim.
?wa?e fuska yaron yayi yana tashi daga jikinsa ya koma wajen Nu'aymah. "Mie-mie ALLAH nama fasa sayama Dada birthday gift ?in da nace miki tunda bazai daina cemin maijan kunne ba. Gashi nan har Wannan Anum ?in ta kama bayan itama jajayen kunnen ne da ita".
Sosai Yoohan da Nu'aymah suka kwashe da dariya. Cikin dariya Yoohan yace, "A to indai hakane bazan sakeba Abban Mie-mie. Zomu shirya kaji".
?an jimm yaron yayi, sai kuma ya kalli Aymah. "Mie-mie kin yarda na shirya da shi?".
"Hhhh haba Abbana wake fushi da babansa dama inba shashasha ba".
"Ai dama nima bana fushi da shi ko Dada?".
Yay maganar da matsawa jikin Yoohan dake kallonsu da murmushi. Rungumesa yayi sannan ya dubi Aymah da wani narkakken kallo. "Wai ina Abbana?".
Mi?ewa tai tana bashi amsa. "Yana ?akinsufa yana gyarawa, dukansa nai shiyyasa ya?i fitowa, yana can yana faman ha?iyar zuciya uwa budiddigin ?wa?o".
Sakkowa Yoohan yay daga gadon ?auke da Anuma yana fa?in, Ayyah Mie-Mie mi mukayi haka ne harda ta?a mana lafiyarmu?".
"Miskilancin da kuka saba mana. Yaron nan a gabansa na gama gohon gyara musu ?aki wai dan wula?anci yana zaune a ?akin su Anum suka sake hargitsashi bai hanasuba shi shugaban miskilawan Najeriya. Shiyyasa na dakesa dan gobe idan sunyi ai ya hanasu ko".
"Aiko a kansu zansa ya rama. Abbana kana ina?".
Kafin Aymah ta bashi amsa Deen ya fito daga ?akinsu baki cike da iska. Yana ganin Yoohan sai gashi da gudu yazo ya rungume Dadan sa.
Cike da so da ?auna Yoohan yace, "Oh my sweetheart so sorry yeah. Bar Mie-mie anayin hutu Kano zan kaika wajen Umm da Uncle. Aiko cike da jin da?i yaron ya hau murna. Yayinda su Ibrahim suka koma jikin Aymah suka lafe wai sunan jealous ya motsa. Dariya Yoohan yayi suma ya mi?a musu ?ayan hannunsa. Da gudu kuwa suka ?araso ya ha?asu ya rungume yana maijin farin ciki a ransa da samuwarsu a garesa matsayin ?a?a. Wa?anda suka fito daga tsatson Nu'aymahrsa mai rigima da tsiwa. Shikam babu abinda zaicema ALLAH sai godiya kuma, dan ya gama masa dukkan rahama. Ko a musilinci n daya tsunta kansa a ciki bayan dulmiyar da shi da su papa sukayi ai ya gamacin ribar rayuwa. Balle kuma da?in da?awa ga ?yautar mace ta gari da ?a?a nutsatstsu da ALLAH ya bashi. Wanda ya tabbatar tarbiyyar mahaifiyarsu ma tana taka rawar gani wajen samuwar tasu. Shiyyasa akace ka nemawa ?a?anka uwa ta gari, matama su nemawa ?a?ansu uba na gari. Fatansa ALLAH ya raya masa su da baiwar ilimin addini tamkar mahaifiyarsu. Duk da shima zuwa yanzun Alhmdllh, ya sauke alkur'ani mai girma haryayi nisama a hadda. Yasan littatafai masu yawa na addini, bai kuma tsaya a hakaba yana cigaba da neman ilimi babu dare babu rana. Dolene ya kasance mai yawan ambaton Alhamdulillahi ala kulli halin a kowanne daki?a na rayuwarsa, suka kalli juna shida matarsa suna murmushi, hannu ya mi?a mata itama tazo ta ha?asu ta rungume cike da godiyar UBANGIJI mai rahama mai jin?ai.?????????.

To nima bilyn ku dolene na kasance mai yawaita ambaton ALHAMDULILLAHI ALA LULLIHALIN a kowacce da?i?a ta rayuwata.

*_ALLAH na gode maka da dama daka bani da iko kammala wannan littafi, abinda na rubuta dai-dai ALLAH ya bamu ladar amfanuwa da shi da ikonsa. Wanda nayi kuskure ALLAH ya yafe mana ni da ku masu karantawa. Ina fatan zakuyi watsi da duk abinda bai kasance mai amfaniba sai dan ?ayatar da jin da?in karatunku. Duk wanda na ?atama rai a lokacin rubuta wannan littafi ya gafarceni. ALLAH ya ha?amu a gaba da alkairi??????????._*

*_ZAFAFA BIYAR na sake mi?a ?umbin godiyarsu a gareku. Mun gode da ?auna da kuka nuna mana, ALLAH ya bar zuminci ya cigaba da bamu ikon sauke ha??in junanmu. Muna fatan zaku sake kasancewa cikin shirin zuwan ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL insha ALLAH anan gaba ka?an. Mun gode, mun gode, mun gode??????????????????_*

Harna fara kewarku silly guys????????????¡â?????¡â?????¡â???????


*_Bilyn Abdull ce??????_*




__________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________


Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login