Showing 132001 words to 135000 words out of 325075 words
ta faru? A ina kuma? Yaushe kuma?".
Kan baba malam a ?asa, muryarsa a matu?ar cinkushe da tashin hankali yace, "Inna bazamuyi saurin ?in gaskatawaba, tunda kinga ai aikinsane hakan".
"Duk da aikin nasa ne ban yardaba. Sai an nemo wani likitan ya sake dubata tukunna. Kokuma muje asibiti da safe idan ALLAH ya kaimu".
Basu iya mata musu akan hakanba da ga shi har Umm da bata iya furta komai ba har yanzun.
WASHE GARI
Da safe Doctor Sale ya dawo gidan zuwa 8:30 kamar yanda yay al?awari. A lokacin Hajjo ta gyara Nu'aymah da kanta. Yayinda Rabi ta sake tsaftace ?akin ita kuma.
Ya dubata yanda ya kamata, ya kuma tabbatar musu komai Alhmdllh dan UBANGIJI ya sau?a?a al'amarin. Ita dai Nu'aymah ba wani fahimtarsu take ba, dan batasan ainahin abinda ya sameta ba bayan ciwon cikin da zata iya tuna tayi kafin gushewar hankalinta.
Ya bada magungunan da zatay amfani da su, da wa?anda bashi da su za'aje a sayo. Daga haka yay musu sallama akan da yamma zai dawo ya sake dubata idan ya taso aiki. Godiya baba malam yay masa. Hajjo da Nu'aymah dai basuce komai ba. Hakama Umm da tun daren jiya da hankalinta yabar jikinta har zuwa yanzun bai gama dawowa ba.
Baba malam baiso maida hankali akan maganar hajjo na nemo wani likitanba. Amma ganin ta matsa sai ya bi umarninta suka kira wani Doctor Faisal abokin Ahmad. Wajen ?arfe goma na safen shima ya iso, a lokacin an maida Nu'aymah sashen hajjo.
Shima dai sun bashi dama yayi aikinsa yanda ya kamata. Kafin daga bisani yay zaman basu bayanin daya matu?ar tada musu hankali akan result ?in shima. Ya tabbatar musu da gaske Nu'aymah ?arin ciki tayi ?an sati shidda da wasu kwanaki, amma babu wata matsala tattare da ita, magunguna kawai zataita sha jikinta zai koma normal.
Har ya kai karshen bayaninsa babu wanda ya iya motsawa a falon, sai hajjo ce tai ?arfin halin masa godiya.
Bayan wucewar Doctor hajjo ta sake tabbatar musu shima bata yarda da nashi aikinba. Duk yanda baba malam yaso fahimtar da ita tace bata yarda ba. A yanzu sai su ?auki Nu'aymah suje asibiti kawai, kuma na gwamnati take so.
?ari bisa ?ari su Abba Musbahu sun yarda da maganar hajjo, dan suma zukatansu sam basu aminta da maganar ?arin cikin Nu'aymah ba sam. Sunfi baba malam yawa, dan haka dole yay shiru ya barsu. Amma a ?asan zuciyarsa bai son sake fitar maganar kuma dan hakan tamkar tonama kansu asirine sukeyi, tunda yasan ba duka likitocinne zasu iya barin maganar a cikinsu ba duk da yasan basusan Nu'aymah bata da aure ba.
_____________________
Bisa matsawar hajjo suka ?auki Nu'aymah da sam jikinta babu ?arfi zuwa asibiti. Kasancewar su manyan mutane da ake girmamawa basu wani sha wahalar ganin likita ba, a yanzu kam mace ce ma Doctor Halima. Itama ?in dai ta gunar da aikinta cike da ?warewa. Bayan kamar awa biyu ta basu samako dai-dai dana su Doctor Sale. Dan ta sake tabbatar musu da Nu'aymah tayi ?arin ciki ?an sati shida da wasu kwanaki dai, harma ta ?ora da fa?in Nu'aymahr na bu?atar hutu sosai da yawaita cin abinci mai inganci saboda jinin data zubar.
Ba ?aramin tashin hankali suka sake tsintar kansu ba a wannan karon kam. Dan ko masu tatsuniya sunce ?urun ?us, anzo ?arshe. Hajjo mai gardamar bata yardanba a yanzu sai bata iya cewa komai ba. Haka suka tattaro suka taho, dama ita da Ahmad da Naser da Abban su Abdallah da Addah ne suka je.
Ganin Hajjo na sharar hawaye Nu'aymah da ke magana da ?yar saboda rashin ?arfin jiki ta matsa da son jin mike damun kakar tasu?. Banza tai mata, hakan yasa tunanin Nu'aymah ko hajjo bataji ba ne sai ta sake maimaitawa.
Tsawar data sakata ?inke bakinta Hajjo tai mata, ta kuma ja mata dogon garga?i akan ta barta taji da abinda ya dameta. Shiru kawai Nu'aymah tai tana kallon hajjon, a ?asan ranta ko fal tambayoyin mike faruwa ne?.
Koda suka iso gida Addah ce ta taimakama Nu'aymah zuwa sashen hajjo, inda suka iske Abdallah da ya dawo gidan tare da sauran samarin gidan suna zaman jiran tsammanin dawowarsu.
Kowa ransa babu da?i ya shiga yima Nu'aymah sannu, yayinda Yah Ab ya kafeta da idanu kawai yana kallo. Itama dai kallon nasa takeyi. a ?asan ranta kuma tanajin da?in dawowarsa gidan.
Basuyi zaman mintuna biyar ba baba malam da sauran ?an uwansa suka shishshigo harda Umm ma da sauran matan gidan dan Hajjo ce ta aika kiran kowa. Sai dai babu yaran gidan da ?ammata. Yaseer ma dake falon zaune tun ?azun korashi waje akayi, Abba Musbahu yace yaje ya tattara yaran su wuce islamiyya.
Shiru falon yayi kowa na jiran mi hajjo zata fa?a, Nu'aymah da ganin ita ba'ace ta tashi ta fitaba taita binsu da kallo a ?asan ido tana mamakin yanda fuskar kowa ke ?auke da ru?ani da tashin hankali........
Maganar Hajjo ce ta katsema Nu'aymah tunani.
"Alhamdulillahi, kamar yanda na bu?aci zuwa asibiti dan tabbatar da abinda zuciyata ta kasa gaskatawa ga shi munje mun kuma dawo. Sai dai abin razanin da tashin hankalin shine babu banbancin magana tsakanin likitocin farko da wadda ta duba Zainabu a yanzu. Itama ta sake tabbatar mana cewar Zainabu ?arin ciki tayi ?an sati shidda........"
"What?!!!".
Nu'aymah ta katse hajjo a zabure tana mi?ewa zaune zumbur tamkar ba itace kejin kamar iska zata ?auketa ta fa?i ba yanzun. Jikinta na matu?ar rawa tace, "Hajjo ban ganeba dan ALLAH! Wace Zainabu kike magana badai ni Zainab ?inba?".
Matsananciyar tsawa baba malam ya daka mata, ai bama tasan ta koma ?asa rib ba ta zube a carpet sa?anin kujera da take kwance a kai ?azun. Baba malam ya nunata da yatsa yana fa?in, "Zainab!! Wlhy tallahi kinji na rantse, inhar na sakejin bakinki batare da an baki izinin magana ba sai kinyi nadama".
Babu wanda ya iya ko motsi, dan jin ainahin sunan Nu'aymah a bakin baba malam ya tabbatar musu da lallai magana tazo iyaka. Ita kanta jin sunan daya kiratan ya saka zuciyarta ?ara gudu da tsitstsinkewa lokaci guda, wani bahagon tsoro da ru?ani suka da ?a mamaye dukanin ga??anta.
Hajjo data juyo tana kallonta tace, "Zainabu bama bu?atar wani ja'inja ko rantse-rantse, nan gurin duk zuri'armune babu wani bare a ciki. ki daure ki fa?a mana wanda ya aikata miki wannan ?arna. Shin da ganganci ne kokuwa fin ?arfinki aka y? Wanene uban cikin nan da ya salwanta jiya?".
Sake rikicewa Nu'aymah tayi, jikinta na rawa tace, "Wlhy hajjo, na rantse da UBANGIJIN al'arshi ban ta?a aikata abinda kuke tuhumata da shi ba. ALLAH shine shaidata ni banda ciki........."
Wu?a shar?e?iya Abba Musbahu ya fiddo ya nunama Nu'aymah, sai ?yalli take da ?aukar ido, mai kallo daya ganta yasan ta cancanci a kirata da suna GAYAWA JINI NA WUCE.
"Nu'aymah kinga wannan wu?ar ko?".
Kai ta ?aga masa da sauri jikinta na cigaba da rawa.
Ya jinjina kansa da cigaba da fa?in, "Inhar kikace zaki mana wasa da hankali to nan tsakkiyar falon nan zansa su Abdallah su kwantar min dake na yankaki kamar yanda ake yanka ragon layya. Ke dawa kuke aikata wannan shai?ancin anan gidan.....?"
Kai Nu'aymah ta shiga girgizawa tana kuka tamkar ranta zai fita. Bakinta kuwa sai wani irin karkarwa yakeyi kamar la??anta zasu zubo ?asa. Ta bu?e baki zatai magana sai kuma ta sake rushewa da wani sabon kuka.
Kamar daga sama sukaji a bayansu ance, "Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan ita ta gaza baku.........."?
????To wane majanunun ne kuma wannan?.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.No. 36
*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.
_KAWATA INA KIKA KOYO HADADDUN CAKES DA GIRKUNA NE HAKA? KINGA ABINCIN NAN NAKI DA NAYI TAKE AWAY BABAN AMEER BAKIGA YADDA YAKE SANTIN SABA, KWANA BIYU INA GIRKI AMMAN NAKI DAI YAKE TA SANTI, YACE LALLAI KAFATA KAFARKI KI RAKANI INDA KIKA KOYO_
_TAB! LALLE MAMAN SUDEIS AN BARKI A BAYA, AI WAJEN *UMMU AYMAAN'S KITCHEN*!NA KOYO HADADDUN BIRTHDAY CAKES, SNACKS, DA ABINCIN YAN GAYU KE HARDA NA NAHIYAR KETARE.. BIKIN ADAMA KANWATA MA ITA NA BAWA ORDER TAYI MANA NA MUTANE DARI BIYAR.._
_LALLE AN BARNI A BAYA, WAI.. YANZU YA ZANYI NA KOYA DAN ALLAH?_
_SHA KURUMIN KI MATAR MIJIN TA.. UMMU AYMAANS KITCHEN TA SAKE DAWOWA DA KOYAR DA BIRTHDAYS CAKES AND DECORATIONS WANDA ZATAYI A KWANAKI 2, PRACTICAL CLASS , AMMA IDAN KINASON KOYA TA ONLINE NANMA ZATA KOYA MIKI._
_WAYYO ALLAH NA DADI..! YANZU YAUSHE ZAAI WANNAN BONANZA? KUMA NAWANE KUDIN?_
_NAIRA DUBU 6 KACAL WALLAHI, DUK ABUNDA YA SHAFI HARKAR BIRTHDAY CAKES AND DECORATIONS ZATA KOYAR_
_BA'ANAN TA TSAYA BA, AKWAI_ CAKE PARFAIT,
CUPCAKES
SAMOSAS
SPRING ROLLS
MEAT PIE DA DOUGHNUTS.
_DUKA TANAYIN NA SHAGULAN BUKUKUWA, TARON SUNA, DANA CI A GIDA DAN MOTSA BAKI, KE HARDA GIRKUNAN DA KIKESON KI KOYA NA NAHIYAR KETARE DANA NAMU GIDA NIGERIA._
_KAI NAGODE KAWATA, AWANE GARI TAKE NE?_
_FARKO DAI GA NUMBER WAYAR TA :08032964266_
_SANNAN TANA NAN KANO, UNGUWA UKU, LAYIN MAI FATA, ZARIA ROAD KANO._
_CLASSES DIN ASABAR DA LAHADI NE KAWATA WATO 5 DA 6 GA WATAN JUNE DINNAN. MAZA FADAWA SU UMMI DAKE KADUNA KICE ZATA KOYAR A ONLINE MA.._
_KAI AIKO NAGODE DA SANARWARKI KAWATA. SHIN TANA INSTAGRAM?_
_Eh SUNANTA:_
@Ummu_aymaan_kitchen.
_TANA TURA KAYANTA A KOINA A FADIN KASAR NAN, INGANCI, KYAU, RAHUSA, LAGWADA GA CIKA CIKI DON DADI SAI UMMU AYMAANS KITCHEN AND CATERING SERVICES_
No. 36
............."Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan ita ta gaza baku. Amma kuyimin afuwa idan ya kasance na shiga hurumin da ba nawa ba".
Gaba ?aya suka juya suna kallon bakin ?ofar har Nu'aymah data fara ganin dishi-dishi cikin idanunta.
Ba kowa bane mai maganar face ?aya daga cikin amintattun almajiran baba malam mai suna Hamisu. Hamisu ?an anguwar su Nu'aymah ne, hasalima ma?waftan junane. Mahaifin su baba malam yayi zaman mutunci da girmama juna da kakansu Hamisu, dan takai harda ?aukar nauyin karatun mahaifin Hamisun a wancan lokwcin. Sai dai ALLAH bai masa tsahon rai ba, dan ya rasu tun su Hamisu suna ?anana sosai. Wannan dalilin ne ya saka zuri'ar gidan su Hamisu ta dawo ?ar?ashin kulawar zuri'ar ?an Jibiya bisa wasulcin da ya barma ?a?ansu su baba malam.
Tabbas baba malam ya cika wannan wasiyya, dan babu irin ?awainiyar da bayayi da gidan su Hamisun, har takai Hamisu yana ?aya daga cikin amintattun almajiransa da sukasan abubuwa masu yawan gaske da ya shafesa, kuma Hamisu har cikin gidan yakan shigo bisa yarjewarsa musamman akan aiko da wani abu cikin gidan idan babu ?aya daga yaran gidan a tare da shi...
A fusace Yah Ab ya mi?e yana nunasa da yatsa. Har tdallaken kalma yake wajen fa?in, "Amma kasan wannan matsalace ta family da bata shafekaba ko malam. To ta yayama akai kai kasan cewar ana wannan zancen a gidan nan? da har zaka wani shigoma mutane tsulum batare da neman izini ba sai kace wasu sa'anninka. Wannan ma ai raini ne da keta haddin mutane".
Nasir da shima ba?in ciki ya lullu?e ya mi?e a fusacen yana cewa, "Tabbas maganarka gaskiyace Abdallah, mi zaisa ya........."
"Kunga ya isa haka" baba malam yay saurin dakatar dasu ganin yanda Hamisu duk ya muzanta abin tausayi. Ya cigaba da cewa, "Tabbas yayi kuskuren shigowa kai tsaye, amma ina ganin mu bashi dama ?ila mu sami bakin zaren matsalar tamu. Hamisu ya akai kasan da wannan issue ?in?".
"ALLAH ya gafaeta malam ka gafarceni, tabbas nima a yanzu na fahimci nayi kuskuren shigowa babu izininku. Ba komai ya jawo hakanba kuma sai ?unbin ru?anin dana tsinci kaina a ciki. Abinda yasa kukaji zancen nan a gareni jiya da daddare na dawo daga inda ka turani kai sa?o. Duk da dare yayi sai naga ya dace nazo na kawo maka sa?on koda ban samu damar maka bayani ba. Da ?yar ma na samu maigadi ya barni na shigo, to a lokacin dana shigone na samu duk jama'ar gidan a sashenka, na iskeku cikin tashin hankali shine na juya da sa?on gidanmu, sai da safe na dawo kawowa nakejin abinda ke faruwa bisa fahimtar da nai daga maganganun ku. Har fitarsu asibiti akan idonane, wlhy da farko naso ?oyewa nima, sai dai tashin hankalin danaganka a ciki ne naga ya cancanci na bayyana abinda na sani kodan ka samu nutsuwar warware al'amarin yanda ya dace, ku fita daga ru?ani kuma".
Duk da sun gamsu da jawabinsa Naser da Abdallah sai zabga masa harara sukeyi. Baba malam ya bashi izinin ?arasowa ciki. Da ga ?an gefe ya dur?usa, ya mi?ama Abban Adawiya dake kusa da inda yake Envelope ?in dake a hannunsa.
Amsa Abban su Adawiya yayi, batare da ya bu?e ba ya mi?ama baba malam. Nuni baba malam ?in yay masa daya bu?e kawai. Abban su Adawiya ya bu?e Envelope ?in ya ciro hotuna dake a ciki guda uku. Ba ?aramin razana yayi ba matu?a, har ta kai yana dubawa hannunsa na rawa.
Hoton Nu'aymah ne da Yoohan, a ranar farko da tsautsayi ya saka shi taimaka mata lokacin da zata fa?i a ranar salla, har ta kaisa ga kissing ?inta saboda baki data wage zata masa ihu. Sai rana ta biyu itama ranar daya musulunta. Saina ukun shima dai a ranar farko ne, ya ran?wafa a kanta suna kallon juna.
Yanda baba malam yaga ?an uwan nasa ya shiga wani haline ya sakashi zare hotunan daga hannunsa. A take jinsa ya ?auracema kunnensa. Hakama ganinsa neman ku?ucema idanunsa yake neman yi. Saurin fara ambaton UBANGIJI yayi yana ?o?arin ajiye hotunan Abban Abdallah ya amsa. Shi kam ma na farko kawai ya iya kallo ya mi?ama hajjo. Itakam ta jima tana kallon hotunan ko ?yaftawa batayi, ta haka ne Nu'aymah da ke gani dishi-dishi ta samu damar ganin hotunan gaba ?ayansu a hannun hajjo.
Babu wanda ya lura da ita. Sai ganinta kawai sukai kwance ?asa wanwar. A take falon ya sake rikicewa gaba ?aya. Duk suka rufu a kanta banda Baba malam da Umm da ko motsi basuyi ba da ga inda suke. Hajjo ma da bata tashiba sai ta maida hotunan a Envelope ?in batare da ta sake bama kowa ba. Sai ma mi?ewa tai ta shiga bedroom ?inta da su. Babu jimawa ta fito lokacin anata ?o?arin zubama Nu'aymah ruwa dan son aga ta farfa?o. Sai dai kuma ko motsi batai ba balle suyi tunanin dacewa.
Gidan ya sake caku?ewa fiye da farko, sai da baba malam ya musu magana sannan suka ?an nutsu. Tamkar bai damu da halin da Nu'aymah ke a ciki ba ya kalli Hamisu dake zaune tsuru-tsuru yana zare idanu. "Hamisu su wa?anan hotunan ina ka samesu ne haka?".
Kansa a ?asa yace, "Baba malam nine na ?aukesu da waya gaba ?aya".
"Hakan na nufin komai ka gani kenan Hamisu? Ina nufin duk abinda ke a cikin hotunan nan a gaban idonka aka yisa?".
"Eh wlhy duk na gani".
"To miyasa baka ta?a sanar minba kuma?".
Jimmm Hamisu yayi kafin yace, "Wlhy ina tsoron ?aga maka hankaline, tare da gudun abinda zai iya zuwa ya dawo malam. Amma ka gafarceni nayi kuskure ".
Nannauyan numfashin baba malam ya sauke. kafin a sanyaye yace, "Shike nan jeka abinka. na gode sosai".
Godiya shima Hamisu yayi ya tashi ya fita.
Hajjo da duk kejin komai na