Showing 285001 words to 288000 words out of 325075 words
daga baya ta ?ago ta kalli Nu'aymah sannan suka gaisa dasu Yoohan.
Nu'aymah dai bata sake bi takantaba itama ta juya ta gaida Dawood da Miemaa data amsa mata da fara'a da kulawa, dan itama ta taimaka mata ta zauna a kujera. Daga haka ta gaida Jay da a kallonsa sai da gabanta ya fa?i. Duk da ba tsananin kamanni suke da Yoohan ba dolene kaga yanayin gittawar jini tattare a tsakaninsu. Duk da ba mutum bane shi mai yawan wasa saida ya tsokaneta ka?an. Har hakan ya bama su Yoohan mamaki. Dan su dai ba ta?a ganin dariyarsa sukaiba tunda suke mu'amula da shi.
Sai da aka lafa da gaishe-gaiahe Jay ya fara magana.
"So ba shirita ne ya taramu ananba. Inason ku bani hankulanku nan gaba ?aya. Da farko dai kece bakisan dalilin zamanmu ananba duk da mijinki ya tabbatar mana ta hanyarki yasan wasu abubuwan. Sai ko Afrah da sanin nata baida muhimmanci daga tushe duk da itama da taimakonta ne muka samu bayanan sirri game da gidanku. So yanzu little zata miki sabon bayani, ke kuma Afrah jeki waje ki jiramu".
Sosai Afrah ta ?ata fuska kamar zatayi kuka. Cikin magiya tace, "Abie Please ka barni dan ALLAH, wlhy nima zan taimaka muku da wani abun kaimafa ka sani. Duk da ba aikin nan nakeba so nawa ina muku aiki ta ?ar?ashin ?asa".
Fuska ya ha?e zai mata magana Aymah da duk kwarjininsa ya cika mata idanu tace, "Abie dan ALLAH, indai hakan ba laifi bane ka barmin Aunty zanfi samun ?warin gwiwa nima".
Kasa cewa komai Jay yayi, ya kai dubansa ga little. Da wani style na ?warewar aiki taima mahaifin nasu alamar ro?on yabar Afrah ?in. Dan itama tana hasashen tasirin zamanta a wajen.
?auke kansa kawai yayi ya maida ga Yoohan dake ta kallonsa kamar ya samu television. Sai kuma ya ?auke ya sake maidawa ga little bee alamar ya bata damar yima Aymah bayani.
Tsaf ta gama yima Nu'aymah bayanin komai. Dan haka taketa duban Yoohan da Umar cike da mamaki. Da damuwa a harshenta tace, "Amma Yah Yoohan baka gudun Abbana kar yaga ba'a ?yauta masaba. Sam baya son laifin jama'ar gidan nan namu, shiyyasa yake ?o?arin maida laifukansu kuskure dan gudun lalacewar zuminci".
"Zeeynab inhar muka cigaba da bama Uncle goyan baya akan hakan tabbas sai an salwantar da ran ?aya daga cikinsu ko ke ko Muhammad a wannan gidan naku. Dan ni nasan mina ganarma idona a Austria da wasu maban-banta wajaje dangane da ke".
Bata iya tace komaiba dan tasan gaskiya Yoohan ya fa?a. Bandama ALLAH yasa tanada sauran kwana a duniya ai da tun tana jinjira an aikata barzahu ?in. Sannan shima Muhammad ?in ai ansha gwada rayuwarsa a mabanbanta lokuta Abba na ?oyewane kawai........
Cikin katse mata tunani Jay yace, "Karki damu akan Sheikh, ni zan masa bayanin dazai gamsu akan hakan. Yanzu zamu tafine kai tsaye akan abinda ya taramu anan tunda kin gama jin bayanan farko. Dan dama munsa mijinki ya dawo dake ?asarnan ne dan zamu ?anaki a gidanku ne matsayin tarko. Dawood minene bayani akan binciken wayar matar nan da aka sakeyi?". Ya ?are maganar da maida hankalinsa ga Dawood.
Takardun gabansa ya ?auka ya fara bayani. "Sir bayanan sununa tabbas ana amfani da wayarta batare data saniba. Kamar maganar yin waya da mai aiki da aka turoma matar Yoohan anan Abuja, sam ba Rabi bace ke waya da Uwaliya. Mun tabbatar da hakane ta hanyar binciken ainahin muryar da aka samu a voice recording ?in nan. Ha?ine ta hanyar makirci babba na masu ilimin sani akan na'ura mai ?wa?walwa. Suna amfani da wani app... Ne da aka saka cikin wayar matar, dama kowacce waya idan ta sake sai suke sarrafa wayar tata daga wajensu batare da ita ta saniba, suna barin mata bayanan abinda sukai da tasu wayar, dan ko an tashi bincke ita za'a zarga kai tsaye. Hakan yana nufin kenan tun fil azal da aka kawota gidan dama akwai manufa a ciki, kokuma daga baya aka fara amfni da ita. Wa?anan sune tatattun bayanai akan ainahin contact dake a wayar Rabi wanda suke aiki da saninta. Wa?anan kuma sune ainahin wa?anda ake amfani da ita ta wayar batare data saniba. Kuma insha ALLAHU zasu taimaka mana mu za?ulo kosu wanene masu aikata hakan kamar yanda Abdurrahman Sameer Saifudden ya bamu tabbaci, dan shine yay wannan bincike gaba ?aya tun daga ?asar india. Ya kuma tabbatar mana idan ana bu?atarsa zai iya zuwa koshi ko abokan aikinsa yan uwan tagwaicinsa kenan".
Cikin jinjina kai Jay ya amshi takardun yana duban little bee. "Bilkisu! Minene bayanan wajenki akan zaman Afrah gidan?".
Juyowa Little bee tayi da kujerar da take a kai tana fuskantarsu. Yoohan ta sake kallo kamar yanda dama tuni shi take kallon a sace bisa ?ya?y?yawan nazari datakeyi akansa tun farkon fara ganinta da shi.
"Sir! Bayanan dake anan sun nuna wasu sunaye da Afrah ta rubuta akan zarginta, saboda wasu al'amura da suke aiwatarwa a gidan na marasa gaskiya. Akwai Rabi. Mai aikinsu, a yanzu tana a hannunmu. Sai Mai aikin sashen Addah, sai ita kanta Addah da tafi kowa kusanci da Umm a gidan. Sai Nasir wanda asali shi bama ?an gidan bane yana zuwane lokaci-lokaci. da wasu sunaye a jerin ?aliban Uncle Soorajidden ?in. Ta tattara wa?an nan sunayen ne bisa dalilai mabanbanta da suka faru akan idonta da kuma yanda labarin yazo garemu. Zamu iya jin bayani daga bakinta gata nan idan da bu?atar hakan".
A yanzu kam bily ce tai wani gutun murmushi tana kallon Jay. Cike da nuna ?warewar aiki tace, "Boss niko kaga a duk jerin sunayen nan mutum uku kawai naba ayar tambaya. Sauran kuma inaji a jikina basa zaune a cikin gidan. Abinda yasa nai wannan maganar shine duk lokacin da za'a cutar da ita Nu'aymah akan yine lokacin wani taro a gidan. Hakan na nufin akwai mazauna gidan dake zaune a waje cikin tafiyar. Amma ?asurgumin azzalumin yana nan cikin gidan tare da su ko akasin haka.
Murmushi Jay yayi a karo na farko. Ya sauke numfashi da ?an buga pen ?insa akan takardar gabansa. "Tabbas komai zai iya kasancewa. Dan suma sauran ai hasahe mukeyi, tunda ga Rabi a hashe muka samota kuma sai gashi babu laifinta".
"Hakane kuma boss. suspect ?inmu na gaba sune, Nasir, Ameer, Hamisu, Kubrah, Abdallah. Da iyayen su Abdallah n".
Da sauri Aymah tace, "momy!" cikin zaro idanu. sai kuma ta shiga girgiza kanta da sauri-sauri tana cigaba da fa?in, "Bazai kasance hakaba Momy. Uncles ?ina suna matu?ar son Abbana. Hakama Yah Abdallah na matu?ar sona. Bazasu cutar damu ba sai dai idan Nasir ne".
"Relax Nu'aymah. Muma bamun tabbatar bane hashene kawai. Dan dolene mu ala?anta laifin nan da mafiya kusanci da iyayenki dake kanki, shiyyasa zamuyi amfani da wannan lokacin da mukasan duk ahalinki zasu taru a gida saboda bikin aure da saukar yaran gidan marayunku mu ?ana musu ke a matsayin tarko wajen dam?esu batare da sun fargaba....."
Yoohan ya katse Bily da cewar, "Humm tabbas Momy bana tantama akan hakan. Musamman akan Abdallah. Dan ta dalilinsa na sakama sauran ayar tambaya. Abdallah yayi fushi yabar Nigeria saboda ba'a aura masa itaba. Amma kuma a bayan fage yana a cikin ?asar, dan yana yawan shigowa akai-akai. Sannan kuma yana bibiyar al'amarinta dani kaina. Dalilina na biyu a kansa shine wani business da yakeyi a ?oye batare da sanin iyayen nasaba. Dalili na uku akwai har?alla akan aurensa da yara biyu na gidan da aka aura masa dalilin sace Zeeynab da akai ranar wancan auren nasu. Ya saki yaran batare da ?aya ta tare ba. Wadda ta tare ?in bincikena ya tabbatar min da tasha wahalar zama da shi. Zargi na uku. Akan hotona da aka kai gidansu ni da ita. A yanda labarin yazo kakarsu bata bari su Abdallah sunga hotunanba a waccan ranar, amma daga baya sai hotunan suka zo hannun Abdallah harya kaisu office ?ina. Hakan na nufin bayan na hannunsu akwai wasu kenan dama a wajensu komi? Zargi na biyar, Abdallah yafi kowa ?aukar zafi akan hotunan a gidan, duk da kuwa nasan Uncle da Umm sai sunfi kowa jin ra?a?i da zafin hakan game da tilon ?arsu. Amma sai ya nuna za?ewa akan hakan harda kawomin abokinsa wai yay Arresting ?ina. Zargi na ?arshe, miyasa a duk lokacin da akai tunanin ?ulla aurensu sai wani dalili ya ruguza shi?......"
"Please Yah Yoohan ya isa haka mana. Miyasa dukanin zarge-zargenka zai ?are akan Yah Abdallah? Kana kishi da shi ba shike nufin komai ka yaya ka aza a kansaba".
Sosai zantukan Aymah suka zafi zuciyar Yoohan, dan gani yake matar tasa tana goyen bayan tsohon saurayin natane kawai. Sai dai kuma uffan baice akan hakanba, yama ?auke kansa daga gareta kawai.
Karan farko little bee ta saki murmushi tana kallonsu. Sai kuma ta ta?e baki da fa?in, "Wannan fa?ane da ya shafeku a gidanku Mrs and Mr".
Hararta Yoohan yayi, dan dama tunba yauba yana jin haushin yanda take zaman yimasa kallon ?urilla a fakaice. Yana nuna bai gani bane kawai saboda kunyar iyayenta.
"A'a bar hararata malami, ni yanzu saina sassafa ka a gaban sahibar taka babu ruwana".
"Ashe kuwa mijinki ma zai sassafu a hannuna tare da wannan miskilar fuskar taki mai ?inyima mutane dariya".
Harara itama little ta zuba masa tana tsuke fuska. "Oh kace dama kullum cikin takaicina kake bana maka murmushi, to ?walelen kare da hantar kura".
Baki Yoohan ?in ya ta?e da ?auke kansa gefe yana cije lip. Dan saiya saita yarinyarnan akan layi kafin a gama case ?in nan. shi babu ruwansa da wani ?ar-sandancin ta ehe. (Kuji ?arfin hali irin na Yoohan. Da alama mafa little bee ?in zata bashi shekara ?aya a duniya, amma wai yarinya??lol)
Babu wanda drama ?intasu baisa dariyaba. Sai Jay da Bily basu dara ?inba a fili sai a zuciya. Sundaita kallonsu cike da nazarin su?utar harsunan nasu.
Kai jay ya girgiza kawai yana katse little dake son ?ara magana. "Kunga ku aje wannan shirmen naku sai kun fita can sai kuyi, idan kunso ku sassafa kawunan naku munada likita a kusa da zai duba ku. Yanzu dai Yoohan dole a yau ?in nan Nu'aymah ta wuce kano. Dan aikin nan banason ya shige satin nan bamu kammalashi ba. Maganar Abdallah kuwa na tabbatar jin Nu'aymah na Nigeria zaizo shima koda a ?oyen daya saba ne. Yanzu zan baza jami'ai da zasu fara bibiyar lamarin motsin kowa na gidan idan ya fito. Shima Nasir ina bu?atar a jawomin hankalinsa yazo kano. Babu sanya a aikinmu, duk wanda mukaci karo da rashin gaskiyarsa zamu kamasane mu tuhumesa kamar Rabi. Za kuma mu maida Rabi itama dan wayarta zata taimaka mana sosai wajen za?ulo abubuwa".
Cike da gamsuwa kowa ya amsa masa. Duk da kuwa Yoohan dai da alama baiso yin nisa da matarsaba. Amma ya fahimci hakan zai taimakesa gameda ?udirin papa kuma a kanta. duk da kuwa a kanon ma wasu kurayen zata tarar. amma gara can akwai jami'ai masu sanya ido a lamarinta.
________¡ï
Koda su Aymah suka dawo gida bata ga Blessing ba. Hakama Madam Chioma da papa da alama basa gidan ma. Yara kawai suka tarar da Mama debora. Joy ta wuce makaranta, Miracle kuwa mama debora ke basu labarin wai ta ha?a kayanta ta koma gida.
Ko a jikin Yoohan. Aymah kuwa yar dariyar sha?iyanci tayi abinta ta wuce sama cike da tunanin ina Blessing ta shiga. ?akinta ta nufa direct, ta fara zame kayanta zuciyarta taf damuwa akan maganar hoton nan. Agogonta data cire ne ya fa?i ?asa. ta ?an matsa baya tana dubawa ta tillesa da ?afa yay ?ar?ashin gado. Abin ya bata haushi, dan harta barsa akan yayta zama sai kuma taji tanason ?akko kayanta dan Yoohan ya batashi matsayin ?yauta a ranar da suka cika shekara ?aya da aure. Fita tai ta ?akko mopping stick dan Yoohan bai shigoba har yanzu yanacan tare da mama debora. Dur?usawa tai gaban gadon batare da damuwa da cikin dake gabantaba saboda wauta. Ta kunna fitilar wayarta ta haska. Da ?yar ta iya hango agogon ta saka mopping stick ?innan ta turosa a hankali. Sai da yazo dab da ita ta fahimci harda wani abu take jawowa. Hannu ta mi?a danta jawosu duka ta kasa. Dole ta sake zungurowa da iccen mofa ?in sannan suka fito. Jikinta har rawa yake wajen fara ?aukar envelope ?in ta bu?e. Tai wani irin waro ido na al'ajabi da mamaki. Batama san sanda ta ?wa?ume hoton a ?irjiba saboda murna. Jin an ta?a ?ofar za'a bu?e tai saurin sakin hoton ?asa, kafin Yoohan daya shigo ya ?araso ta tura hoton ciki yanda bazai ganiba.
Duk da ta masa alamun rashin gaskiya sai bai nuna yama fahimcetaba. Yay baya da fi?in, "Oh ashe kina nan, bara na watsa ruwa saiki shirya kema zuwa biyar na yamma zamu wuce kano. Amma mi kikeyi ma a dur?ushe anan? Bayan kinsan bake ka?ai bace?".
Mi?ewa tai tana nuna masa agogon data ?akko. "Kaga abinda na yadda nan na ?akko".
"Ki kulafa, dan na fahimci har yanzu wautanki na nan".
Baki ta kumbura da iska batare datace masa komaiba. Shima sai ya juya abinsa ya fice kawai ya barta batare daya sake maganaba. Sai dai bai rufe ?ofaba. Da wannan damar ya samu zarafin la?ewa kozaiga mitakeyi. Aiko tana ganin ya fita ta sake du?awa ta ?akko hoton tana ambaton 'Alhmdllh ya ALLAH. Da banga hoton nanba da bazan ta?a yafema duk wanda ya ?aukesaba. Dolene nasan wacece wannan mai kama da mijina ?in insha ALLAHU'.
Dukkan maganganun Aymah a cikin kunnen Yoohan ne. Hakan yasa zancen tsaya masa a rai tare da son jin ganin hoton nan shima. Yayi kamar zai dawo sai kuma ya fasa. Akan idonsa ta maida hoton a Wadrobe. Tafiya yay ?akinsa tunda yaga inda ta ajiye. Sai dai kamar tasan yana kallonta. Yana barin wajen ta ?auke hoton ta sakashi a ?ar jikkar data ha?a kayan tafiya kano wai dan kar wani ya sake shigo ya sace mata. Tana shiga wanka Yoohan ya dawo duba hoton. Sai dai kuma komai kama da shi bai ganima. sai ma kamashi da Aymah taso yi ALLAH dai ya taimakesa ya gudu.
Haka suka kammala shirin wucewa kano mamakin atsabibancin Aymah na damun Yoohan, shi ganima yake ta gansa shiyyasa ta canjama hoton waje.
Itako Aymah ranta fal ba?in cikin rashin ganin Blessing da Yoohan yasa tabar gidan har sai sun wuce dan bayason ta sanamar Nu'aymah abinda ya faru tsakaninsa da Momynsa.
*_KANO TA DABO_*
?arfe bakwai dai-dai jirgin su Aymah ya sauka a kano. Batare da sanin kowa daga ahalintaba har su baba malam. Sai da Yoohan yasa suka fara biyawa sukai shopping na tsarabar da zata kaimusu sannan suka wuce gidan.
Ganin Aymah da Yoohan ya saka mai gadi bu?e musu gate mai taxi ya shiga har ciki. Nu'aymah zata fita da kwakwazo Yoohan ya ri?ota yana girgiza mata kai. "Please kibi a hankali, a ganinama ba gara ki shige babu wanda ya san da zuwanki ba da safe sai kiyi musu surprise".
Baki ta ?an tura gaba. Sai kuma tai saurin sakin dariya da cewa, "Yes Yah Yoohan kayi gaskiya kuma".
Murmushi yay mata da bata sumba a gefen kumatu. Daga haka suka fito a motar. Gidan shiru kowa yana a sashensa, hakan yasa Yoohan taya maigadi kaima Aymah kayanta bakin ?ofa. Sannan ya turata ciki ya sulale ya koma taxi ?in suka fice. Dan hotel yake son guduwa kafin baba malam su fito massallaci su ritsashi.
Umm na zaune a bedroom tana karatu da jiran lokacin sallar isha'i sai ji kawai tai an rungumeta. A firgice ta juyo dan harga ALLAH ta tsorata. Ta waro idanu sabida mamakin ganin wadda batayi zatoba.
"Nu'aymah wai kece da gaske?".
Kukan murnar ganin Umm ?inta ta saki tana fa?in, "Nice Ummna, I miss you so much".
Rungumeta Umm tayi da ?yau a jikinta itama ?walla na cika mata idanu. Kai ?a dabanne gaskiya. Sanin ba ita ka?ai bace yasa Umm tadata daga dur?uson da tayi a ?asa ta zaunar da ita a bakin gado. Gaba ?aya Aymah sai kuma taji kunyar Umm ta mamayeta, sai ta du?ar da kai ?asa tana ?ara lullu?e cikinta da gyale. Dariya abin ya bama Umm sosai. Sai dai bataiba. Saima tambayarta tai ina mijin nata?.
Kan Aymah a ?asa tace waje ta barsa ita dai suna kwaso kaya shi da maigadi. Jin haka yasa Umm fita ta le?a. Sai dai babu Yoohan babu dalilinsa sai maigadi kawai dake shigo da kayan ?an barandar falonsu. Shine ke sanar mata Yoohan ?in ya juya tare da mai taxi akan da safe zai dawo insha ALLAH.
Kai kawai Umm