Showing 126001 words to 129000 words out of 325075 words

Chapter 43 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29099

dan tasan nanne wajen zaman su Naser ?in musamman da daddare.
Duk kuma wannan abun dake faruwa Adawiya bata nan, dan kwanansu biyu da zuwa sukai tafiya biki ita dasu Hajarah dangin kakarsu maman su Addah. Da Addah ta ?arrafa ayi tafiyar da Nu'aymah ma. Sai dai yanayin jikinta yasa Hajjo hanawa. Shiyyasa suka tafi su uku harda Kubrah sai Addahn da sauran ?a?anta na ma'auri.

Da farko rikicin nasu Naser nisha?i yake saka Nu'aymah, amma ganin al'amarin na sake ?aukar zafi sai hankalinta ya fara tashi. Dan neman birkita mata tunani sukeyi har takan rasa wanene yafi cancanta ta mallakama kan nata?.
Al'amarin bai sake tada hankalin kowaba a gidan sai randa Hajjo take cema Abdallah dama ya ha?ura ya barma Naser Nu'aymah. Tunda shi a yanzu gashi yana auren su Yusrah. A fusace yace, "Indai su Yusrah ne zasu masa katanga da mallakar Nu'aymah to lallai zai rusa katangar".
Babu wanda ya ?auki furucin nasa da muhimmanci a lokacin da yayisa. Sai dai ga mamakinsu bayan sallar isha'i sai gashi da zungureriyar takarda har guda biyu yazo ya dire gaban hajjo.
Kallonsa tayi fuska a yatsine. "Kai wannan takardun kuma na miye ka ajiyemin kamar wani ?an sa?on kotu?". Fuska a tur?une yace, "Hajjo sakamakon katangar da kika tabbatar min zata shiga tsakanina da Nu'aymah ne a ciki. Kinga yanzu sai ki daina min baki ko".
Sam hajjo bata fahimci zancen nasa ba, amma sai ta saka Omar dake zaune tare da ita ya duba mata. ?aukar ?aya yay yana murmushin diramar kakar tasu da yayansu. Da sauri ya fesar da ruwan da ya ke sha yana fa?in, "What!?" saboda abinda yaci karo da shi a rubuce.
A rikice hajjo tace, "Miya faru Umaru?". Jikin Omar na ?ari ya ajiye kofin ruwan tare da ?aukar ?ayarma ya bu?e. Nanma dai abinda ke cikin ta farkon ce a ta biyu, ai baima san lokacin daya furta, "Hajjo wlhy Yah Abdallah ya haukace! ko kuma ya fara shaye-shaye ku bincika!. Hajjo sakin Yusrah da Adawiya fa ya yi....."
"Saki kuma?!!" Hajjo ta fa?a itama tana mi?ewa zumbur.
"Wlhy kuwa Hajjo gashi a rubuce saki ?ai-?ai".
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Abdullahi!!. A wlhy gaskiyarka kuwa Umaru Abdullahi ya haukace. Ni Zainabu na shiga uku. Kaga kiramin ?an malam duk inda yake yazo gida".
?an jimm Omar yayi alamar tunani, sai kuma ya dubi Hajjo da ranta ke a matu?ar ?ace. Cikin lallashi yace, "Amma Hajjo inaga kamar dai kiyi ha?uri har ya dawo gida. Kinga yanzu bamusan wane uziri yake kan yiba, kiran da za'ai masa zai iya dagula masa tunani, amma idan kince a kirasan dai sai na kirasa ?in".
"Hakane Umaru! Kaima kayi maganar hankali, amma lallai sai na sa?ama Abdullahi fiye da zato a gidan nan. Wane irin wawancine wannan? Ashe hankalin da ake ganinsa da shi da girma bashi da shi ?in?".
"Kiyi ha?uri Hajjo, ALLAH ya huci zuciyarki. Ni kaina ban ta?a zaton hakan daga garesa ba. Kinga wannan ai tushen ?ata zuminci ne, idan iyayen namu basu kai zuciya nesa ba sai kiga al'amarin ya kawo ?acin rai. Sannan su kansu yaran an saka wani abu a zuciyarsu gur?ataccen. Dan zasu iya tsanar Nu'aymahr da yace dominta yayi, hakan kuma bashi da amfani".
?wafa kawai hajjo tayi ranta da zuciyarta na ?ara mata suya da ?aci. Omar dai yayta lallashinta har sai da yaga ta ?an kwantar da hankalinta sannan ya fice cike da jimami. Sashensu ya nufa, yaje ya fa?ama Momy duk abinda ya faru.
Sosai itama ta rikice hankalinta ya tashi. Dan ta tabbata Abbansu dama wasu a mutanen gidan bazata fita da ga zarginsu ba, musamman ma da akasan taso ya auri ?iyar ?anwarta. Waya ta ?auka ta shiga neman Abdallah. Sai dai harta tsinke bai ?agaba. Bata gajiya ba wajen cigaba da jera masa kira, amma ya?i ya ?aga.

Hajjo, Omar, Momy sun yi yinin yau ne cikin tashin hankali da damuwar ?arnar da Abdallah ya tafka. Duk da sun ?agara Baba malam ya dawo gidan ransu cike yake da fargabar sakamakon da zai biyo baya kuma.
Sai bayan sallar la'asar baba malam da Abban Abdallah suka dawo gidan. Dan dama tare suka fita. Sunje wani ?auyene akan maganar wata katafariyar gona da zasu saya. Sunason gyarata su maidata gidan gona a zuba dabbobi kala-kala na kiwo a ciki. Wannan ma ne dalilin da yasa har yanzu shi da Abba Musbahu basu koma ba. Suna son sai komai ya kammala sannan su ?auka iyalansu su koma inda suka fito sai kuma biki.
Kamar yanda al'adarsu take ta fara shiga sashen mahaifiyarsu yau ma hakan suna fitowa daga mota can suka nufa. Yanda suke tafe suna firarsu kowanne fuska ?auke da fara'a dolene su matu?ar burgeka. Dan a kallo ?aya zaka fahimci ?unbin sha?uwa da ?aunar juna dake a tsakaninsu.
Sai da sukai sallama Hajjo da ke zaune cikin ?acin rai har yanzu ta amsa musu da basu izinin sannan suka shiga. Kallo ?aya sukai mata suka fahimci tana cikin damuwa. Kusan da sassarfa duk suka ?arasa gareta kowanne na tambayarta tana lafiya?.
Batai magana ba, sai wajen zama data nuna musu. Sai dai maimakon su zauna a kujerun sai suka zauna ?asa tamkar yanda suka saba. Gaisheta sukayi, sannan suka sake jero mata tambayoyi akan yanayin nata.
?wallar da suka cika mata idanu tasa bakin ?an kwalinta ta share. Hakan sai ya sake tada musu hankali.
"Inna dan ALLAH ki fa?a mana minene ke damunki? Mune mukai muki laifi? Ko matan mu? Kokuwa a cikin yaran nan ne wani yay miki wani abu?".
Sake share hawayen data matso tayi da cewar, "Ni babu abinda kukai min ?an malam, Abdullahi ne kawai keson watsa mana gida".
Hankali a tashe baba malam da Abban su Abdallah suka kalli juna. Cikin ?arfin hali baba malam yace, "Innah mi Abdallahn ya aikata?".
Takardun da Abdallah ya rubuta ta ?akko ta mi?a musu. Amsa sukayi kowanne ya bu?e guda ?aya gabansa na fa?uwa. A tare suka ?ago a razane suka kalli juna da ambaton sunan ALLAH. Baba malam har yana tsallaken kalma wajen fa?in, "Innah shi Abdallah ?inne ya rubuta wannan takardar?".
"Shine ?an malam, shine da kansa ya rubutasu ya kuma kawo mani. Wai dan kawai jiya na bashi shawarar cewar yay ha?uri ya barma Nasiru Zainabu tunda shi yanzu yana da matansa har biyu. Shine fa yau ya kawomin takardar sakinsu Adawiya wai gashinan ya rushe katangar dana ce masa tana tsakaninsa da Zainabu".
Abba da ya gaza cewa komai tun ?azun yace, "Innalillahi..., wai inna kina nufin su duka biyun ya saka?".
"Eh mana Lurwanu, baga takardun nan ba duka biyu na baku".
Da sauri baba malam ya amshi ta hannun Abba, shima ya kar?a ta hannunsa. Da gaske kuwa su duka biyun ya saki. A take tsananin ?acin rai ya sake bayyana a kan fuskokinsu. Abba ya mi?e a fusace zai fice. Kiransa baba malam ya shigayi amma ina zuciyar gadon ta motsa. Dan ha?uri kawai ya bashi batare da ya juyoba ya fice.

Momy na zaune cikin damuwa da fargabar jiran dawowar mijinta Abba ya shiga. Jiki a sanyaye ta dubesa dan ko sallama baiyi ba
Takardun guda biyu ya watsa mata a jiki. "Da saninki ?anki yay wannan aika-aikar ko?".
Gaban Momy na fa?uwa ta ?auki takardun ta karanta, hawayen da taketa faman dannewa tun ?azun suka zubo mata a saman kumatu. "Wlhy Abban Abdallah ban sani ba. Nima ina zaune Omar yazo yake sanarmin. na kirashi yafi sau hamsin amma ya ?i ?agamin waya ma, kai........"
Baki ya bu?e zai daka mata tsawa Omar da ya shigo basu sani ba yace, "Abba wlhy babu ruwan Momy, hasalima batasan komaiba akan al'amarin nan sai da nazo na sanar mata. Abba ko kasan dama tunda Yah Abdallah ya dawo gidannan baiyi zaman minti biyar da Momy ba. Da ya shigo ya gaidata da safe bazata sake ganinsa ba sai washe gari. Fushi yake da ita babu gaira babu dalili. Ta sakani na tambayesa amma yacemin idan na sake zuwa masa da zancen Momy sai ya ?atamin rai. Ita kanta nace zan sanar maka abinda ke faruwa amma ta hanani, wai mu bashi lokaci kozata fahimci abinda ke damunsa".
Jikin Abba ne yay sanyi, dan tabbas kuwa ya kula tunda Abdallah ya dawo ?asar nan bai ta?a ganinsa zaune da Momy ba, da farko yaso tambayarta sai kuma yayi tunanin ?ila sai ya fita suke zaman. Wannan ya sakashi yin shiru duk da kuwa yasan yanda matar tashi take da ?ulafucin ?a?a musamman Abdallah.
Nannauyan numfashi ya sauke tare da zama yana cire hular kansa ya ajiya.....

A ?angaren baba malam kuwa Abba na fita waya ya zaro ya shiga neman layin Abdallah. Sai dai kuma abin mamaki switch off. Ajiye wayar yayi ya maida hankali ga Hajjo da ke sharar hawaye har yanzun. Kwantar mata da hankali ya shigayi da bata ha?uri. Yace, "Inna ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, insha ALLAHU mu dai wannan bazai kawo mana rabuwar kawuna ba. Duk inda Abdallah ya shiga kuma na tabbata zuwa dare dole ne ya dawo gida ya kwana ai, insha ALLAHU a daren nan sai ya maidasu su duka biyun".
"?an malam bazaka gane abinda nake nufi ba, amma duk yanda kake tunanin sau?i a al'amarin nan da wahala ya kasance hakan. akwai abinda na sani wanda kai da sauran ?an uwanka baku san da shi ba a gidan nan. Ina barin masu aikatawar ne kawai kafin ranar da zan masu banka?a da tonon silili a gaban kowa. Ni dai abinda zan sanar maka yanzu shine da ga Abdullahi har Nasiru ka zaunar da Zainabu ta za?i wanda tafi so tunda abin ya zama haka. Kokuma ta auri wani bare can a zauna lafiya. Sannan inason ka nutsu kayi tsai da hankalinka a wannan karon game da kowa a gidannan, koda baka fahimci duka abinda na fahimtaba zaka fahimci wasu daga ciki. Dan kai ne uba a gidan nan, duk da dama nauyi da girman ya rataya a wuyankane tunbayan rasuwar mahaifinku, ina kuma alfahari da yanda ka ri?e hakan, amma sai randa ?asa ta rufe idanuna zaka sake tabbatar da girman dake bisa kanka da tarin fituntunun da ke kwance a cikin gidannan wanda ALLAH ne kawai hanasu fallasuwa saboda rahamarsa da ikonsa da kuma ?arfin addu'ar mahaifinku da har yanzu take biye da ku. Kai dai ALLAH ya ?ara maka ha?uri da juriya kawai. Tashi kaje ka huta, ka kumayi ?o?arin tausar sauran ?an uwanka akan duk ma abinda zai iya biyo baya game da wannan gagarumar fitinar da Abdullahi ya ?a??ago mana".
Kasa cewa komai baba malam yayi. Cike da ru?anin maganganun Hajjo ya jinjina mata kansa kawai da mi?ewa ya fice zuwa nasa sashen. Bai iske kowa a falon ba sai Muhammad dake karatun Al-Qur'ani na haddar da aka basu a islamiyya. Yaron bai dakata daga karatun da yakeyi ba, shima kuma bai masa magana ba ya wuce ?akinsa.
Komai tsaf a gyare kamar yanda ya saba zuwa ya iske, ga ?amshi mai da?i. A ?aya daga kujerun ya zube hankalinsa har yanzu baya tare da shi. Dan ransa da zuciyarsa cike suke da tarin ru?anin kalaman mahaifiyar tasu. Shi kansa yasan akwai abubuwan dake kwance a gidan nan ?warai da gaske. Wa?anda da yawansu shi da iyalinsa sun cutu matu?a a cikinsu. Koma yace suna kan cutuwa. Ya kumayi imani da ALLAH babu wani ba?on ido daga waje da zasuce yana aikata su, dolene mai aikatawar a cikin zuri'arsu yake. Yasha yin tunanin tsananta bincike, amma sai zuciyarsa ta garga?e sa da yin ha?uri, sannan yana mai tsananin jin tsoron wanda sakamakon ?arnar zata tabbata a garesa. A ganinsa gara kawai a cigaba da tafiya a lullu?en dan UBANGIJI mai ji ne kuma mai ganine akan kowa da komai..........
Ta?a shin da akayi ne ya saka tunaninsa katsewa. Duban Umm da tun ?azun take masa magana yay. Fuskarta cike da damuwa tace, "Malam lafiya kuwa? Wane irin zurfafa tunanine haka? lna fatan dai lafiya ko?".
"Humm! Jannat lafiyar nan da dau?i".
Saurin zama tayi hannunta ri?e da kofin data zuba masa ruwa tana fa?in, "Miya faru?".
Ruwan ya fara kar?a ya sha, ta sake ?ara masa ya shanye sannan ya ajiye kofin ya labarta mata duk abinda ya faru, harma da zancen da Hajjo tai masa.
Duk da itama ta jima da ji a ranta duk abinda Hajjo ke zargi a kwaishi a gidan hakan bai hanata jin tashin hankali ba. Ita kanta tanason sanin mai aikata musu SARAN ?OYE a lokuta da dama. Sai dai tsoron wanda zata gani yana aikatawar ke sakata sama ranta ha?uri da barin komai hannun UBANGIJI.

¡ï¡ï¡ï¡ï

A yau dai har dare Abdallah bai dawo gidanba duk jiran da su baba malam sukai zaman yi masa. Dole suka ha?ura suka kwanta al'amarin nacin ransu da zuciya.
Washe gari bayan fitowa sallar asuba baba malam da sauran ?an uwansa suka hallara gaba ?aya a sashen mahaifiyarsu. Bayan sun gaisheta suka sake ha?uwa gaba ?aya wajen bata ha?uri akan abinda Abdallah yayi, suka kuma tabbatar mata insha ALLAH zasu dai-daita komai ba sai yayi tsamari ba.
Batace da su komaiba dai, sai dai ta musu addu'ar nasara da nemawa Abdallah dama sauran yaran shiriya gaba ?aya.

A wannan yinin maganar sakin ta shiga kunnen kowa dake a gidan ciki harda Addah da yaranta dake can suna shan biki. Aiko ba ?aramin rikita musu lissafi Adawiya tayi ba. Dole babu shiri suka tattaro suka nufo kano zuciyar kowa babu da?i.

Tunda sa?on saki ya isa kunnen Yusrah kuwa sai wani tarin farin ciki ya kamata. Bama tasan lokacin data shiga dirga tsalle akan gadon ?akinsu ba. Kafin ta sakko da sauri ta shiga bayi ta ?auro alwala. Salla tayi raka'a biyu na godiya ga ALLAH daya kawo ?arewar wannan aure da ko tarewa batayi ba a cikinsa. Dama tunda su Adawiya suka diro ?asar bata da wani sukuni. Shiyyasa ta koma yinin makarantar Tahfiz ?in gidansu dan kawai ta gujema ganinsa. Hakan kuwa akayi, dan tunda suka iso sau biyu ta ha?u da shi. ?aya da daddare ya shigo sashensu wajen Abba. Na biyu kuma a sashen hajjo taje kai mata abinci. Duka a ha?uwar tasu gaisuwa ce kawai ta shiga tsakaninsu. Yanda baya sakar mata fuska itama bata shiga sabgarsa sam, dan baya wani nuna alamar akwai ko ?igon ha??inta daya rataya a kansa ma. Hakan kuma bai dameta ba, to gashi cikin amincin ALLAH komai ya zama yanda taketa fata a kullum. Ba ?aramin azumi da ?iyamullaili tayi ba akan auren nan a cikin watannin nan. Dan ita ka?ai tasan dalilin rashin son auren.

Duk wannan rugu?ai da akeyi Nu'aymah batasan anai ba ita kam, dan Umm da baba malam babu wanda ya sanar mata. Sashen Hajjo kuma yanzu ba wani shigarsa takeba sosai saboda takurawar Nasir da Abdallah da suka maida sashen hajjo wajen zamansu. Ta gwammaci taita zama a sashensu, idan Muhammad na gidan susha shirmensu, idan kuma ya fita makaranta tayi kallo idan akwai wuta ko su zauna hira da Umm. Wani lokacin kuma tai barcinta dan Doctor ya ce ta dinga yawan barci, shiyyasa ma ya saka mata maganin barci a magungunanta.
Yauma tana a ?aki tasha barcin rana har su Adawiya suka dawo bata saniba. Ta fito wanka tai sallar la'asar, shiri ta farayi da ?udirin zuwa islamiyya yau dan tanajinta Alhmdllh. Tana tsaka da saka kaya ta jiyo kururuwar kuka kamar muryar Adawiya kuma. Saurin ?arasa saka kayan tayi ta fito, a mamakinta duk ma sai ta iske ?an gidan a tsakar gida kowa ya fito an rufu kan Adawiya. Gabantane ya fa?i da tunanin ko Accident sukayi a hanya. Da sauri ta shiga bin kowa da kallo sai taga kowa ma yana nan, harsu Aunty Aysha ma basu wuce gidajensu ba nan sukayo.
Kallon Jafar dake kusa da ita tayi tace, "Jafar miya faru wai?".
"Aunty Nu'aymah ban saniba nima. Kawai dai naga Aunty Adawiya na kuka tana cewa wai indai aka rabata da Yah Ab zata mutu".
Kafesa da kallo Nu'aymah tai tana son fassara kalaman nasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login