Showing 96001 words to 99000 words out of 325075 words

Chapter 33 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29141

amsa mata da "Lafiya lau ?anwarmu, kinyi salla lafiya?". Kai ta gya?a masa kawai, dan duk sai taji kuma ta takura da kallon da yake mata. Ganin bata gaida Yoohan ba ya saka Malam ?arami hararta, yace, "Shi kuma fa?".
Yanzun kam baki ta kumbura sosai, ta kalli Yoohan ?in da yay tamkar baisan da zaman kowaba a falon tace, "Good evening.
Sarai yajita, amma sai ya share baiko motsaba. Sai da Hamza ya ?an ta?asa da fa?a masa ana gaishesa sannan ya ?ago manyan idanunsa farare tas ya sauke a cikin nata. Karan farko da sukaima juna kallon ido cikin ido. Kusan lokaci guda kowanne gabansa ya fa?i. Nu'aymah tai saurin fara janye nata da ?o?arin juyawa daga saitinsa.
Shima ?an lumshe nasa yay ya bu?e (dan hakan ya zame masa kamar wata ?abi'a) cikin muryarsa mai amo ?in nan yace, "Kina lafiya?".
A mugun razane Nu'aymah ta sake waigowa inda yake, har taune harshenta take wajen fa?in, "What?! Dama kanajin hausa?".
Yanda tayi tambayar sai da ya saka su hajjo yin dariya. Hakan sai ya ?arama Nu'aymah takaici, musamman ganin yanda Yoohan ?in ya wani yamutse fuska, tare da mi?ewa saboda wayarsa da aka kira, dama shi baiyi dariyarba. Sai da yazo daf da ita a hankali yace, "Yeyye girl".
Kafin wani ya sake magana a cikinsu, ko ita ta bashi amsa Abban su Adawiya da Abban Musbahu suka shigo falon da sallama. Shi kuma ya fice yana amsa wayar.
Daurewa tai ta shiga gaishesu tana ?an harar ?ofar da Yoohan yabi ya fice ta gefen ido, a ranta kuwa sai cewa take, 'Oh ALLAH, amma dai gayen nan akwai munafurci, dama yanajin hausa amma duk sanda suka ha?u yake nuna mata bayaji, jibesa da wani shegen aski kamar kan zakara, sai kuwa yaga yeyye kafin yabar gidan nan yau'.
Duk kallon harar Yoohan da take Manager yana kallonta ne ta gefen ido shima, sai da Abban Musbahu ya kira sunansa ne sannan ya maida hankalinsa garesa, a ransa yana mamakin yanda alamu suka nuna akwai sanayya tsakanin Yoohan da wannan Zu?e?iyar budurwar data gama tafiya da dukkan imaninsa a kallo ?aya.
Ita kam Nu'aymah da batasan yanayi ba sai ta lalla?a ta fice dan jitai tama fasa cin wainar, yau duk yanda za'ai sai taji dalilin shigowar wannan kahirin cikin gidansu, harma falon kakarsu...........?

??Kina ruwa Aymah??.



______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________


Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[5/18, 3:08 PM] Ummuanwar??: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta_*.


No. 26

..............Cike da jin haushin Yoohan Nu'aymah ta fito daga sashen hajjo. Hakan yayi dai-dai da shikuma Yoohan ?in zai koma dan ya kammala wayar.
Karo sukayi, goshin Nu'aymah ya bugu da sar?ar Cross ?insa. Da sauri tai baya saboda azaba. Shima bayan yaja ka?an yana wani yamutsa fuska idonsa a kanta. Kasancewar Nu'aymah bata taka ?an step ?in ?ofar falon hajjon dai-dai ba lokacin da tai baya sai ta sake yo gaba zata fa?i.
Yoohan ya tabbatar idan ya barta ta fa?i zataji mugun ciwo ne, dan haka da saurinsa kuwa ya tarota ta fa?o jikinsa. Sai kuma ta firgice saboda tsoratar da tai najinta kwance a ?irjinsa, ta wage baki zata tsala ihu yay azamar ?ora lallausan tafin hannunsa saman bakin nata ya rufe ruf.
Cikin tashin hankali Nu'aymah ta fara mutsu-mutsun kwatar kanta, jikinta sai rawa ya ke yi. Shikuma ya?i sakinta dan ya tabbatar yana sakin nata fa?uwar daya gudar mata a farko sai tayi wadda ta fita a yanzu, cike dajin haushi ya daka mata tsawa, dan jiyayma kamar ya saketa ta fa?in ma yaga ?arshen rashin kunya.
Duk da tsawan da yay mata bata nutsuba, sai ma cigaba dayin mutsu-mutsunta nason ?wacewa takeyi, tuni hawaye kuwa sun fara bimata kumatu, dan a rayuwarta da hankalin kanta kuma hakan bai ta?a faruwa da itaba. Ko hannu bata yarda samarin gidansu wani ya ri?e mata balle akai ga runguma irin haka. Sai gata yau kwance a ?irjin ?aton kahiri, da ko yayunta basu ta?a aikata haka a gareta ba. gashi ya rufe mata baki babu damar magana. Kuma ?arfi ba ?aya ba.........
Jin ya manneta da bango sai tashin hankalinta ya ?aru, dan ta zata wani abun kuma zai aikata mata, ta kasa nutsuwa ta fahimci taimakonta yayi. hannayenta duka biyu ta saka tare da dukan ?arfinta tana ?o?arin ture masa hannunsa daya rufe mata baki da shi. Ko gezau baiyiba, saima wani shegen kallo da yake binta da shi tamkar ya manta a inda suke, ga fuskarsa a matu?ar ?aure balle kai tunanin da biyu yay hakan, sai dai shima zuciyarsa wani irin harbawa take da sauri-sauri.
"Ouch!!" ya fa?a da sauri yana janye hannunsa da ya toshe mata baki da shi, dan kuwa daddagewa tayi ta gasa masa cizo a tafin hannun. Yaja da baya yana yarfe hannun nasa da fa?in, "Are you mad?!".
Nu'aymah da har yanzu jikinta bai bar rawa ba ta galla masa harara tana share hawayenta. "Eh banda shi. ALLAH ya isana kuma, wlhy ka sake gigin ta?ani saina fasa maka kai, danni ba ?ar iska baceba!".
"Silly girl! Waye ?an iskan?" ya fa?a da turanci kamar yanda ta fa?a itama yana galla mata harara tare da cafkota, iya ?arfinsa ya fisgota tayo baya ta sake fa?awa jikinsa. Mannata jikin bangon ya sakeyi, ya toshe mata baki da ?ayan hannunsa. kafin ya ?ago ?ayan hannun ya kalli inda ta cije sa, yamutse fuska yay ganin yanda shatin ha?oranta suka fito masa, ba wajen data ciza ?in kawaiba, tafin hannun gaba ?aya yayi jaa abinka da ba'asan wahala ba...
Nu'aymah ta rikice iyakar rikicewa yanzun kam, dan ta yarda a ranta da gaske Yoohan son cutar da ita yake. ?ilama abinda ya kawosa gidan kenan. Sake kaima ?ayan hannun cizo tayi. Yayi saurin janyewa ya maye gurbin hannun nasa da bakinsa. Shi kansa baisan yaya akai hakan ta faru ba, ya tsinci kansa ne kawai da ha?e bakin nasa da nata ya shiga kissing ?inta.
Yanda take kuka da turesa da yakushinsa ne ya sashi janyewa daga gareta da sauri. Duk da halin daya ganta na ?ololuwar shiga ru?ani da tashin hankali hakan bai hanashi kallonta ba, tare da zazzaro mata manyan idanunsa da suka sauya kala zuwa ja.
Harga ALLAH Nu'aymah ta tsorata yau kam, dan ta tabbatar tunda har ya iya mata wannan abun a cikin gidansu to lallai zai mata duk abinda yazo masa rai. Tunda tasan su basu ?auki keta mutuncin mace a komai ba. Amma tsabar ?arfin hali irin na mutuniyar taku ana sakar mata baki sai ko ta murgu?a masa bakin da sake zuba masa harara. iya ?arfinta ta turashi dan har yanzun yana manne da ita ne a bangon, amma ko gezau baiyiba balle tasa ran samun hanyar ku?uta. Waige-waige take gudun kar wani ya fito ya gansu a haka, tana kuma hawaye, cike da tsiwa cikin harshen turancin data san yafi fahimta sosai tace,
*_"Dama ku babu abinda kuka iya sai son ta?a mata da ?ata musu rayuwa, ALLAH ya isana ?an iska kawai. shiyyasa wanda baya salla an haramta ma sa jin da?in duniya. Sannan zai gamu da wahalhalu a wurare guda hu?u: A nan duniya, da ranar mutuwa, da cikin ?abari da ranar hisabi. A duniya ana ?ebe ma sa albarka, a cire ma sa kwarjini daga fuska, a sa ma jama'a ?yamar sa. A ranar mutuwa zai mutu da wula?anci da yunwa da ?ishirwa. A cikin kabari ALLAH zai ?untata ma sa, a hura ma sa wuta a cikin sa, a aika ma sa kumurci a tsakanin fatar jikinsa da namansa. A ranar hisabi za a ba?anta fuskarsa, a yi masa hisabi dalla-dalla, sannan a ha?a shi da zabaniyawa da za su wurga shi cikin wuta. Lallai, sallah ita ce ginshi?in addini. Idan ka?i gaskiya zaka fa?a ?ata. Idan ba ka ji nasiha ba, zaka yi da-na-sani. Wanda baiji bari ba ya ji hoho!......"_*
Ta ?are maganar da sake turashi da ?arfi. Yanzun kam da kansa ma ya matsa ya bata hanya, da gudu tabar wajen kuwa tana kukanta har yanzun.
Cike da takaicin kansa ya rumtse idanusa da ?arfi, tare da ?ora hannunsa a goshi yana murzawa da abaton "Oh lord!, mina aikata?!".

¡ï¡ï¡ï¡ï

A wani ?an lungun sashensu Nu'aymah ta ma?ale tana sauke tagwayen shashshekar kuka, har zuwa yanzu jikinta baibar rawa ba, sai faman waige-waige take tamjar ance mata Yoohan ?in biyota yayi.
Ta ?an?ame jikinta lokacin da abinda ya farun ya sake dawo mata a rai, yanda gashin jikinta ke wani mimmi?ewa zai tabbatar maka da tsigar jikinta tashi takeyi.
Da sauri ta saka hannu tana share hawayenta saboda jin tahowar mutum. 'Na shiga uku ya biyo ni' ta fa?a a fili zuciyarta na wani irin zallo tamkar zata faso ?irjinta ta fito........
"Nu'aymah lafiya na ganki anan? Mi kikeyi ne haka?".
Duk da ganin Aunty Kubrah ce ba Yoohan ?inba hakan bai hana Nu'aymah sake rikicewa ba, ta shiga inda-inda jikinta na tsuma. "A..Aunty babu ko.. Komai".
Kubrah data kafeta da ido ta?an murmusa, sai kuma ta juya bayanta tana fa?in, "Ki kwantar da hankalinki ai ba biyoki yayi ba, na tabbatar kuma babu wanda ya ganku a gidan nan".
Wani muguwar fa?uwa gaban Nu'aymah ya sakeyi daboda jin furicin Aunty Kubrah. Cikin rawar harshe Nu'aymah tace, "Aunty Kubrah wlhy ni......."
"Kinga kwantar da hankalinki Nu'aymah babu maiji, indai nice ko Hajarah baza taji wannan zancenba balle wani a gidan nan. Amma inason ki fa?amin gaskiya, yaushe kuka fara wannan abun ke da shi?".
"Innalillahi! Aunty wlhy bamu ta?a yiba, yau ma na rantse shin......"
"Kinga ya isa. Share wa?an nan hawayen idan baso kike ki tonama kanki asiri ba da kanki".
Nu'aymah duk ta sake rikicewa, tama rasa fahimtar inda maganganun Aunty Kubrah suka dosa saboda tashin hankali. Duk da ta share hawayen sun gaza tsayawa. Hannunta Kubrah ta kama har lokacin fuskarta da murmushin da Nu'aymah ta gaza fahimtar na minene. "Kinga muje sashenmu, idan ba hakaba Umm sai ta fahimci abinda ya faru, ko kinfi bu?atar hakan?".
Da sauri Nu'aymah ta shiga girgiza mata kai, "A'a wlhy Aunty, banason Umm ta sani dan zata kasheni, dan ALLAH karki fa?a mata, wlhy kuskurene ba kuma laifina bane ba, na rantse da ALLAH Aunty ban ta?a yiba, ko hannuna Namiji bai ta?a ri?ewa ba". Ta ?are maganar da rushewa da wani irin kuka maiban tausayi.
Komai Kubrah bata sake cewaba ta kama hannun Nu'aymah suka nufi sashensu. Ta ?ofar baya tabi da ita, dan ?annen Addah su Aunty Basira suna falo zaune dasu Addah suna hira. Batare data bari sun gansu ba ta shige da Nu'aymah bedroom ?insu. Zaunar da ita tayi sannan itama ta zauna a kusa da ita. Har lokacin kuma Nu'aymah kuka takeyi, zuciyarta na ?arajin tsanar Yoohan matu?a........
"Ko shine Ameer ?in Saurayinki?".
Da sauri Nu'aymah ta ?ago tana kallon Kubrah, sai kuma ta shiga girgiza mata kai, "Aunty dan ALLAH ki yarda dani, wlhy Ameer ba saurayina bane. Wannan kuma bama musulmi bane ba, ba?one yau na fara ganinsa".
Ha?e fusaka Kubrah tayi tamau tana kallon Nu'aymah ?in. "Karkimin ?arya Nu'aymah, inba hakaba wlhy na fasa rufa miki asirin, a yau da daddare zan sanarma Hajjo da Baba malam da Umm komai. Ki fa?amin tun yaushe kuke tare? Sau nawa kuma yay amfani da ke?".
Duk sai Nu'aymah ta sake daburcewa, dan tama rasa wace amsa zata bama Aunty Kubrah, gaba ?aya ta kasa fahimtar manufar Kubrah.......
Kamar Kubrah tasan tunanun da Nu'aymahn keyi, sai ta sassauta fuskarta tana gyara zama. Ta ?an rage kaushin muryarta kuma ta koma magana cikin lallashi. "Nu'aymah kinsan dai yaya nake a gareki, duk abinda zan iya gani gasu Hajarah raina ya ?aci idan nagani daga gareki dolene naji zafi, ?iyar ?ar uwar mahaifiyata ce kuma ke, dan kuwa Umm tamkar ?ar uwar Adda take, tamafi min wasu ?an uwan Addan. Yanzu Nu'aymah da wani ya ganki a gidannan ?aton banza yana lalubeki mikike tunanin zai faru?, idan ma iskancin zakiyi ai gara kuyisa can a waje wani bai gankiba ko, amma a cikin gidanku? Babban gida mai daraja irin wannan? Wane kallo kikeson aima iyayenki maza damu kanmu Nu'aymah?".
"Dan ALLAH kiyi ha?uri Aunty Kubrah, wlhy bazan sakeba wannan ma ?addara ce da kuma kuskure".
"ALLAH yasa hakane to". Kubrah ta fa?a tana wani ?auke fuska da ?ya?e baki.
Nu'aymah na kuka tace, "Wlhy da gaske nake Aunty. Dan ALLAH ki yarda dani".
"Nu'aymah idan ban yarda da ke ba minene amfanin musawar to?, tunda idan kunbar gabanmu ALLAH ka?ai yasan mi kuke aikatawa, masu iya magana fa kance rana dubu ta barawo, ?aya tak ta mai kaya. Yau ?inma ai bakiyi tunanin zan ganku ba".
?asa Nu'aymah ta zube tana kuka tamkar ranta zai fita, 'Ita mizata fa?ama Aunty Kubrah ta fahimceta ne wai? Wane rantsuwa zatai mata danta yarda ba da yardarta kafirin nan ya aikata hakanba a gareta?'.
Sai da taci kuka sosai, Kubrah na zaune na kallonta kafin ta ?agota ta rungumeta, "Kukan ya isa haka, aina yarda ba laifinki bane. Na miki hakane kawai dan kisan baki dai-dai ba".
"Na gode da kika fahimceni Aunty, kuma namiki al?awarin hakan bazata sake faruwa ba insha ALLAHU".
?agota Kubrah tayi ta share mata hawayen tana murmushi, "Shikenan naji, kuma na miki al?awarin babu maijin zancen nan a gidan nan kinji, kije bayi ki wanke fuskarki kizo ki sake shafa hoda dan karma wani ya zargi wani abun kuma kinji ko. Ki kuma saki jikinki inba hakaba Umm zata gane, kuma kinsan halinta. Zatabi duk hanyar data dace dan tasan gaskiyar abinda ya sakaki kukan".
"Insha ALLAHU bazan bari ta gane ba Aunty, bara ma na wanke". Ta ?are maganar tana mi?ewa da sauri ta nufi bayin su dake cikin ?akin. Tana wanke fuska tana kallon bakinta a mirror. Wasu hawayen sai sake ?o?arin zubowa suke tana dannesu da ?yar. A fili tace, 'Na tsaneka mugu ?an iska mai suffar samudawa, bazan ta?a yafe makaba wlhy". Ta ?are maganar da fashewa da kuka.
Taja kusan mintuna biyu tana kukan kafin ta wanke fuskar ta fito. Fitowar tata tayi dai-dai da shigowar Hajarah da wayar Kubrah a hannu. Da mamaki Hajarah take kallon Nu'aymahn, dan ita dai bataga shigowarta sashen ba.
"Nu'aymah yaushe kika shigo ne? Gashi kamar kinyi kuka?". Da sauri Nu'aymah ta girgiza mata kai, sai kuma ta kalli Inda tabar Aunty Kubrah dan tana zaune a wajen, tana jinsu kuma amma ko kallonsu ta?i tayi balle ta nuna alamar tasan mi sukeyi ma. "Babu komai Aunty Hajarah, kaina ne kawai ke ?an ciwo".
?arasawa inda Nu'aymahn take Hajarahn tayi, ta ?ago fuskarta cike da nazari........
"Wai miye hakane? Tace miki babu komai kanta ke mata ciwo miye na damunta ne kuma?".
Baya Hajarahn taja kanta a ?asa tace, "Kiyi ha?uri Aunty Kubrah, ga wayarki dama Alhaji ne ya kiraki". Ta matsa inda take cike da girmamawa ta bata wayar.
Tana amsa ta nuna mata ?ofa da ido. Da sauri kuwa Hajarahn ta fice.
Kubrah ta maida dubanta ga Nu'aymah dake a tsaye har yanzu. "K kuma ki bada himmar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login