Showing 315001 words to 318000 words out of 325075 words

Chapter 106 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29090

abu mai amfani. Duk kuwa da a raina ina addu'a da fatan tarkon dana ?ana musu ya zama sanadin tafiyarsu har abadan. Komai na gansa, dan haka na tattare tsaf na hada a jikka, na fito falo inda yaron ke barci na ajiye tare da zaman jiran sakamako".
"Mintuna talatin kuwa ban rufa da zamaba saiga babban labarin da nake jiran gani daga television. ?an jaridan dake bada rahoto ne ke magana cikin tsantsar sar?ewar harshe, akan samun nasarar kama mutane biyu da suka shigo daga ?asar Italy da hodar ibilis. An samu nasarar cafke ?aya a airport, ?aya kuma daidai traffic light tare da matarsa. Sai dai bisa kuskuren guduwa da sukayi na gardamar su basusan komaiba ?an sanda suka harbesu, wanda bisa tsautsayi suka matu har lahira. Sai ga gawar ?an uwana an nuno tare da matarsa kwance cikin jini. Hannayensu ri?e dana juna. Ga ?an sanda na lalube wallet din dana saka masa tare da wayata anata faman bincike. Ko ?ar banji a raina na nadamar yin hakanba, dan koba komai asirina ya rufu, zan fara sabuwar rayuwa. A take na ?arasa ha?a duk wani abu mai muhimmanci dake gidan, tare da kayan yaron na shiga mota na fice a gidan. Na tabbatar yanzu bazan fuskanci kowacce irin matsalaba, musamman daya kasance hankalin jami'an tsaron ya koma gaba daya akan nasarar cafke masu laifi. Aiko banci karo da kowace matsalaba wajen barin ?asar ta mota. Duk da naci uwar wahala ga yaro nata zubamin kuka ban damuba. Haka nai nasarar fita a ?asar zuwa ?asar dake ma?waftaka da su, acan kuma nabi jirgin ruwa, inda anan ne na ha?u da Chioma, itama tsagerace ta kanta, dan kuwa kusan duk irin harkokina shi takeyi, sai dai ita oganta a Nigeria take. A dai takaice na samu nasarar komawa Italy tare da jariri da ?unbin dukiya da takardun kaddarori da taimakon Chioma. Ogana yayi farin cikin ganina dajin labarin ta hanyar dana ku?uta, dan haka yaymin al?awarin taimakona ta hanyar tabbatar duk wa?annan kaddarori na ?an uwana a tafin hannuna. Yanda Chioma ke taimakona da rainon jariri dana canjama suna da John ne yay sanadin ?ulluwar soyayya mai ?arfi a tsakaninmu har mukaima juna al?awarin aure. Ta matsa matu?a muyi aure sannan mu koma 9ja dan haka na amince mata saboda nima ina sonta. Bayan aurenmu muka nufi ?asar haihuwarmu cikin danginmu. Wanda zuwa yanzu labari ya gama zuwa kunnen danginmu na rasu ta hanyar kamani ina safarar hodar ibilis ni da wata, dan a haka labarin keta yawo. Kowa kuma yana ?auka ni aka kashe, saboda kowa yasan halina. ni kuma nine ?an uwana. Munzo Nigeria ne dama da shirin hutu mai dogon zango, dan ogana ya tabbatarmin dolene inyi nesa da shiga kowacce ?asa. Inba hakaba kuwa babu makawa sai an banka?o ainahin gaskiyar nine mai laifi ba ?an uwanaba. Nayi amfani da wannan shawara kuwa, dan haka na yada zango a Lagos gidan da ya sanarmin ya saya ta hanyar abokinsa. A labarin nanfa da nake baku kowa ya ?auka dama nine aka kashe, dan ansan nine tsagera, ?an uwana kuma shine ni. Dan haka na canja sosai wajen ?aukar ?yawawan halayyar ?an uwana na yafama kaina akan dole. halena kuma na ?oyesu, dagani sai matata muka sansu. Ban wani cika burin ?an uwana ba na mallakama mamana da ?annenmu dukiya ba, sai dai naja ?an uwan nawa a jiki wajen sakasu cikin har?allolina. Bansan yaya akai Godwin ya fahimci banine twin bro ?ina ba, sai kawai rana tsaka ya fuskanceni da wannan zance shi da Mike. Na matu?ar tsorata da firgita, amma sai Chioma ta bani dabarun maidasu a hankalinsu ta hanyar ?ara jansu jikina da rufe bakunansu da dukiya mai tsoka da ku?a?enta. Danni a lokacin bawani kudine da niba. Sunko bi sun tsuke bakunansu kuma, tun daga nan suka zama sunsan kowacce irin har?allata, sun kuma san John ba ?ana baneba".
"Abinda ya faru baisa na daina har?allataba, sai harkokine suka sake bu?ewa sabbi dan yanzun dukiyar Chioma muke juyawa, nazama jan wuya anan Nigeria, ta hanyar turomin da kaya da ogana yakeyi. Cikin shekara hu?u kacal na shahara, na kuma sakeyin kutse cikin addini har saida na zama Pastor a wata ?aramar church duk da babu wani ilimi da nake da shi. Zuwa lokacin John ya fara wayo, yanada shekara hu?u, dan ko ina zuwa yake, ga surutu a bakinsa ba'a magana. Yanda yaron ya shiga ranmu muke tarairayarsa bazaka ta?a kawowa a ranka ba d?anmu bane, dan soyayya ta gaske Chioma ke nuna masa. hakan yasa na ?ara sonta a raina, dukda kaf dangina basa sonta dan ta rainasu, su kuma gani suke ta ?waceni ta hanani taimaka musu bayan kuma dukiyarsuce tunda dai kallona suke a matsayin twin bro ?ina. Dukiyar ?an uwana tazo hannuna, sai dai ba dukantaba, dan wata an tabbatar da dolene sai John ya girma sannan nasoba kuwa dole na ha?ura, na cigaba da juya abinda ke hannuna ta hanyar har?alla daban-daban. A wannan lokacin ne naje ?asar France yin wani couse na watanni tara, dan rashin yawan ilimi nason min tangar?a akan zamana pastor. inda acanne muka ha?u da Sooraj Hashim Jibiya. Bayan korarsa da akai a makaranta sanadin dukan da yaymin nai jiyya kusan ta watanni uku, da ?yarma na kammala abinda ya kaini na dawo gida cike da alwashi kala-kala akan Sooraj dama yankin daya fito gaba ?aya. Dan nayi al?awarin sanadin abinda ya aikata mani saina tarwatsa duk danginsa da jama'ar yankinsa. Wannan shine dalilin farkon fara sato yara daga yankinsu ana kawomin ina cinikinsu. Sai dai na gaza lalubo a ina Sooraj yake? Dan ko'a wancan karon dama bansan taka-maimai shi ?an ina bane, nadai san musilmine ?an arewa. a zahiri kuma na lullu?e True color dina da rigar addini, babu mai cewa ni shege ne. Cikin kan?anin lokaci na shahara, dukiya da girma suka zauna saina tattaro na dawo Abuja. Wani halaye da John ya fara nuna mana na ?yamar addini da wasu abubuwan namu duk da ?an?antar shekarunsa yasa hankalina tashi. Dan da alama yaron yanada wata baiwa dake nuna ya fahimci kamar mu?in ba iyayensa bane. Mike ne ya bani shawarar zuwa gidan boka a kulle tunanin Yoohan gaba ?aya, koda ya girma bazai ta?a kawo a ransa mu?in ba iyayensa bane koda yaga rashin kamansa da Chioma. Naji da?in wannan shawara, nakumayi amfani da ita. Bayan munje wajen boka ya amsa zai mana aiki, sai dai aikin zai zama sanadin saka ciwon rashin barci ga John lokaci-lokaci. A take kuwa muka amince, akai asiri John ya koma tafin hannunmu sosai. Duk abinda muka sakashi babu tantama yake mana, sai dai ban ta?a yarda yasan ?oyayyar har?allataba Mamana ma da sauran ?an uwana nasa akai musu asirin da bazasu ta?a tunanin ko kawowa a ransu ni?in ba ?an uwana bane. Ana haka Chioma ta haihu twins itama, Gebrail da Joy. Nayi farin ciki sosai da samuwar nawa ?a?an, amma samun nawa baisa naji tsanar Yoohan ba. Bayan su Joy Chioma bata sake yarda ta haihuba sai da John ya shiga jami'a ta sake haihuwar Victoria. Ta sake Abraham wanda cikinsa yazo mata babu shirin hakan, dan tace daga ya?a uku ta gama. To ashe da rabon zuwan Abraham. Abinda yasa nasaka Solomon kullum yake tare da John tun bayan gama karatunsa, saboda tsoron kar wajen yawon ?asashensa da aiki ya tilasta masa yin gamo da wani dangin mahaifiyarsa ?wa?ata tayi ruwa. Shiyyasa dukkan motsinsa sai na sani ta hanyar Solomon".
"Abu mafi ?agamin hankali daya faru shine tarayyarsa da Sheikh Sooraj. Lokacin dana san wannan ala?a hankalina yayi ?ololuwar tashi, na kumayi murna dan sanadin John ma?iyina dana ?auki shekaru ina bulayin nema ya bayyana. har ?auye naje mukai zaman meeting da sauran mutanena, dan saboda gudun irin haka yasa na cusa masa ?iyayyarsu tun yana yaro, amma daga ?arshe sai gashi abinda nake gudun ya auku. John ya xama musulmi kamar mahaifinsa. Ranar nayi tamkar mahaukaciya a gidan nan, harma na yanke hukuncin kashesa kawai na huta bayan na sakashi ya sakamin hannu a takardun da naketa a jiya tsahon shekaru, dan company ?in yanata ha?aka zuwa yanzun, sai dai ina mamakin ta hanyar wa hakan ke faruwa?. Su Mike ne suka ha?u wajen bani shawarar mizaisa na damu da musilincinsa. Sun san dai babu ta yanda za'ai ya iya gano shi?in wanene saboda asirin da ke a kansa. Sooraj kuwa amfani zamuyi da kusancinsa da John ?in mu yashe masa asusunsa tsaf mubarsa da ?imautar ?wa?walwa da bugawar zuciya. Amma wai koda na tuntu?i John akan mike ala?arsu sai ya nunamin wani aiki yakeyi akan Sooraj ?in. Nafa yarda da shi har cikin raina. Saboda nasan irin horon danai masa tun yana yaro akan wannan yanki. Har raina da?i nakeji zai ?aukamin fansa akan abinda Sooraj yaymin tsahon shekaru, dan duk da korar da akai masa a makaranta wancan karon baisa na huceba, na kuma da?e ina addu'ar ha?uwarmu amma hakan bai yuwuba sai yanzun. Ban fahimci John folani yake a kwalayeba sai akan aurensa da ?iyar Sooraj, idan nace zan bayyana muku halin dana shiga ni da matata dasu Mike a wannan tsakanin ?ata lokacine, da ?yar Godwin ya kwantar min da hankali akan na amince da auren, bayan anyi mu kashe yarinyar yanda Sooraj zaiji ciwo sosai a ransa kafin kuma mu yashe masa asusunsa. Wannan shawarace ta kwantarmin da hankali na amince akai aure batare dana yarda na nunama Yoohan nasan ya musulintaba, sanann matata ma ban ta?a fa?a mata ya zama mai salla ba dan nasan tana son John sosai fiyema da ?a?anta, kodan shita fara samu matsayin ?a ne kafin ta haifi nata oho. Shigowar ?iyar Sooraj cikinmu ta sake ruguza komai na shirinmu, dan yarinyace hatsabibiya. takai ko ganinta nai sai naji matsanancin tsoro na shigata. Bala'in kwarjini takemin kamar ubanta, gata bata da tsoro. Ban sake tabbatar da yarinyarnan abar tsoro bace sai randa ta shigar min ?aki, ta kuma nuna ba ita bace. Da gaske nima ?in na yarda ba ita ?in bace a lokacin, sai daga baya na gane itace ta hanyar cctv dake a falona wadda ko matata batasan da zamanta ba duk da kuwa har?alla ?aya mukeyi, kai hasalima na sakatane domin ita dan haka harkarmu take a kullum bama yarda da juna. Bawai ina tunanin itama zata cutar dani bane, dan ina tsananin ?aunarta, na kuma yarda da ita. Ina tsoron kar dai cikin abokan har?alla wani yay amfani da ita ya cutar dani ne dai. Sosai hankalina ya tashi da lamarin yarinyar, da kuma tunanin mahaifintane ya turota le?en asirina. Sai kawai na shirya yanda Doctor ?in da zasu mata aiki zasu kashe min ita ta cikin sau?i kafin na dawo kan John ?in shima. Naji da?in abinda Gebrail yay mata, dan nasan nesa tazo kusa akan aiwatar da aikina a kanta, sai dai kash Dr Mateo ya lalatamin burina. Naji takaici, naji ciwo, na kuma yanke shawarar halaka John da yarinyar gaba ?aya da zarar sun dawo ?asar nan. Zan fara halakata ita da duka danginsu da ubanta kafin shi ma na juyo kansa. Amma taurin kai irin na John da bani da tantama wajen ubansa ya gada sai ya sake ruguzamin shirina. Ya koro Solomon, ya kuma ?auketa daga Austria ya canja mata ?asar da bani da damar shiga, dan tuni aka hanani lasisin shiga ?asar U.S. Wamnan shine dalilin yimin katanga a garesu, na zauna dakon jiran dawowarsu ko zuwansu ?asar a tare. A randa John ya dakarmin yaro wai ya shigar masa ?aki naji kamar shima na halakashi da hannuna. Amma na taushi zuciyata dan nasan a tafin hannuna yake. Shina ?an?anin lokacine ya rage masa ai. Na tattara komai na ajiyeshine ban masa magana a kaiba dan banason ya zargi komai a kaina har sai randa ya sakamin hannu a wa?annan takardun, ya kuma kawomin shegiyar matarsa ?asarnan. Dan nagama shiryawa tsaf akan yanda zan yashe asusun ubanta kaf na maidashi sifili. Wai kawai kwatsam rana tsaka saiga yarannan da ciki sunzomin gida. Lallai naga ba?ar rana kuwa, dan da gaske ranar susucewa nasoyi gaba ?aya. Randa na gama shirya ?udirin aikata lahira suka baro Abuja batare da ko John ya sanar minba da yake shima tantirin ?wallon shege ne. Nasa a biyota kanon, a daren da zasuzo bisa jagorancin Solomon kuma ?an sanda suka ritsamin yaro a hanyarsa ta kawomin kaya daga ?asar Cameroon. Da ?yar yasha zuwa abuja, duk sun fasa masa jiki da bullets, amma sai yayi ?o?arin zuwa ya isarmin da sa?on na gudu, dan da gaske wanann tarkone babba aka ?ulla a kaina tsahon lokaci. wannan shine sanadin tserema ?an sanda da nayi, sai da na bada ?afa ta watanni biyu na dawo da baya saboda jin matar John ta haihu ta hanyar wani ?an le?en asirina. Na fahimci lokaci yayi da zai sakamin hannu a takardu, daga haka na kama gabana bayan na kasheaa shi da ?an da matar tasa. Sooraj kuwa zan dawo masa da nasa shirin bayan ?ura ta kuma kwanciya......."
Kallonsa kawai kowa keyi a falon kamar sun sami television. Dan shi kansa Jay makircin na Goshpower ya matu?ar rikitashi. Ashe shine sanadin halakar ?anwarsa da mijinta. Iya bincike sunyi bayan faruwan wancan al'amarin amma suka gagara sanin gaskiya, dan sudai basusan mijin Anum da wani twin Brother ba. Ba komai yaja hakaba sai sakacin rashin bincike danginsa koda a ?oyene, duk da dai shi yaso yayi binciken a lokacin mahaifin Anum ?in yace a barsa darajar gaskiyar yaron, a bashi dama har ya bayyana mana danginsa suma ya bayyana musu mu. Tunda dai shi sun gwadashi ta hanyoyi da dama basu samesa da wani mummunan hali ba. A lokacin haushi shi Jay yaji yace ya cire hannunsa akan batun, dan ya rasa wane irin so sukema mijin Anum ?in. Ganin yanda ya dage da harkar nema da neman ilimin addini yasa shima Jay din ?aga masa ?afa ya bashi lokaci zuwa sanda Anum zata haihu, dan yayi al?awarin da zarar ta haihu kosu Ummu sun yarda ko basu yardaba dolene yasan dangin mijin Anum ta hanyar tasa ?eyarsu har Nigeria aje tare da shi. Sai gashi a dai-dai ga?ar da take shirin kawo musu ribar auren nata su gani su kuma je ga dangin mijin nata wannan al'amari ya bayyana. Wanda ta sanadin haka suka rasa ?ar uwarsu da mijinta da ?anta. Suka kuma rasa ainahin gaskiyar zance akan zargin da akema mijin nata. Haka suka ha?ura badan zukatansu sunsoba, suka ?auka wannan itace ?addararta kuma. Tare da mahaifinta sukaje suka amshi gawarsu wajen ?an sanda bayan ansha gwagwamaya suka sallacesu aka kaisu makwancinsu. Sai dai basuga gawar yaronba, sai suka ?auka wani ya ?auke gawar a cikin wannan rubibi. Sai dai a binda ya ?aure musu kai rasa muhimman takardun mijin Anum a gidansa. Bayan wasu watanni kuma akazo musu da batun an ?wace duka kaddarorin nasa dake a ?asar ta Syria. Basu da ikon nuna rashin yarda tunda sunsan hakan shine dokar ?asar ga duk wanda aka kama da irin wannan laifin. Badan zukatansu sunso ba daga haka suka rufe babin Anum da duk abinda ya shafeta. Sai kuma gashi kwatsam bayan tsahon shekaru sunci karo da mai tsananin kamanni da ita a Nigeria, tare kuma da mai tsananin kamanni da mijinta matsayin ubansa. Wannan abu ya rikita Jay matu?a, harma yaji a aransa inama Ummu da mahaifin Anum na raye su tayasa wannan al'ajabi.....
Ta ?asan da Jabeer yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa daga tunanin daya tafi, Jabeer ya nuna masa agogo da fa?in, "Boss asuba fa na gab da shiga, muyi abinda ya dace kafin masu ?arfin fa?a aji suce wani abu"..............?
[7/9, 5:05 PM] +234 901 860 0202: No. 77

............Kai Jay ya jinjina masa zuciyarsa a matu?ar raunane ya dubi Yoohan da kansa ke a du?e yana hawaye. Nu'aymah kanta kuka take hakama Umar. Cikin ?acin murya da soyewar zuciya Jay yace, "Goshpower nama rasa abin fa?a a gareka. Dan kaine mutum na biyu da bazan ta?a yafemawa ba da mantawa da shi, bayan gagarumin zalincin da akaima rayuwata da barmin tabo a shekarun baya. Ka cika azzalumi na gasken gaske. Ni nan da kake ganina nine yayan wannan mata ta ?an uwanka Anum. Mune mukaje har Italy muka taho da ita, tabbas inaji a raina UBANGIJI ya lullu?e idanunmu daga garekane saboda wannan shine rubutacciyar ?addarar Yoohan, wannan wata hikimace daga hikimomin UBANGIJI, ya kuma fimu sanin dalilin yin hakan, kamar yanda ban isa goge abinda aka zana daga zuciya ba, haka ma ban isa canja abinda ya zama rubutacciyar ?addara ba domin ALLAH shine ka?ai masanin gaibu, sai yaso mu sani, sai yaso mu gani, sai yaso muji".
A kallo ?aya zaka fahimci a tsananin firgice Papa yake, dan jikinsa har ?ari yake ya dubi Jay, bakinsa ma rawa yake amma ya kasa cewa komai. Hakama Yoohan da Nu'aymah wani irin kallo mai firgitarwa sukema Jay ?in. Ya furzar da huci mai azabar zafi da ?auke kansa. Dan ji yake kamar yay fata fata da goshpower kawai kozai samu sassauci a ransa. Lallai yanaji a ransa idan ya cigaba da zama a gidan nan babu abinda zai hanashi huhhuda jikin Goshpower da bullets, dan haka ya mi?e da sauri ya fice hawaye na ziraro masa a saman kumatu. Komai dawo masa yake sabo a rai da zuciya. Gawar Anum da mijinta ne ke dawo masa cikin ido tamkar yanzu komai ya faru. Zafi da ra??i da ru?anin da suka shiga da mutincin mahaifin Anum da ya ta?u a idon danginsa da al'umarsa a wancan karon na dawo masa a zuciya. A?idar larabawa ce wannan gudun zubewar mutuncin dangi. Idan kuwa aka samu kuskure wani abu ya auku na zubewar mutunci ga ?ayanku sai ya shafi kusan duk zuri'arku. To hakance ta faru ga zuri'ar Anum, dan sanadin wannan al'amarin mahaifinta yabar duniya, ?an


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login