Showing 168001 words to 171000 words out of 325075 words

Chapter 57 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29183

dan bayason yayi wani ?an sakaci da Aymah zata birkice masa a wajen nan. A haka suka shiga cikin hall ?in daya ha?u harya gaji, decoration ?in wajen ma komai fari ne da kwalliyar pitch ka?an-ka?an. Gashi komai a tsare babu wani hayaniya ko shirme, ga uban haske tako ina tamkar rana. Ko allura ka yadda zaka ?auka abarka. Kowa yana zaune a inda ya dace da shi. Ita dai kanta na a ?asa ne bata yarda ta kalli kowa ba duk da uban tafi da ake musu, ga wata wa?ar na tashi a hankali cikin hall ?in. Bayan an musu rakkiya inda ya dace su zauna kowa ya nema wajen zama. Papa ya gudanar da addu'a a wajen da kansa, shidai Yoohan yayi tasa a cikin rai. Nu'aymah ma sunayi tanayin tata cike da takaici. Ita abinda yafi birkitata shine su baba malam basu san Yoohan arne bane suka aura mata kenan? (Kusanfa ita batasan Yoohan ya musulinta ba) wannan bahagon tunanin ne yake neman zauta mata ?walwar kai. Shiyyasa tai shiru bata sake koda wani ?wa?w?waran motsi ba har aka fara gudanar da abinda ya tara mutane. Ita dai komai a shirme ma take kallonsa, sai dai ta ?anji sanyi a ranta lokacin data ?aga kai idonta ya sauka akan ahalinta su aunty hibbah da sukazo wajen daga baya. Amma saboda girmamawa a garesu sai aka kawosu gaba inda aka tanadar musu tebiri biyu dama. A yanzunma bataga Adawiya ba tare da su.
Lokacin da akace su yanka cake tasha uban takaici. Dan ?in basa tayi. Idanunsa ya?an lumshe ya bu?e a kanta ganin yanda hall ?in yay tsit kowa ya zuba musu idanu. "Kinason muji kunya wajen wa?an nan ?unbin mutanen da suka taru saboda mu ko? To idanfa kin?i yin yanda akace ALLAH saina miki abinda sai kin kasa fita hall ?innan da kafafunkin nan".
Gabantane ya fa?i. dan tasan zai iya aikatawar. Tunda har baiji nauyi ko shakkar mata kiss a gidansu ba. Sai da ta?an hararesa ta gefen ido sannan ta ciri cake ?in da suka yanka ?in, batare da ta yarda ta kallesa ba takai hannunta bakinsa. Hannun ya kama da nasa hannun ya ?arasa da cake ?in cikin bakinsa. ?an ka?an ma ya gutsira ya juya hannun nata dake ri?e a cikin nasa wajen nata bakin. Badan ta so ba ta bu?e ka?an itama danta ?an gutsirar sai ya tura mata shi gaba ?aya tsabar neman rigima. Saurin ?agowa tai a ?an zabure, hakan yasata gullewa tai gefe zata fa?i yay azamar ri?o ?ugunta ta dawo kan ?irjinsa. Tuni tsiwar mutuniyar taku ta motsa, ta ?ago birkitattun idanun nan nata da suka sake girma ruwan hawayen da suka taru a ciki suka sasu wani kala ta musamman. Cikin nasa manyan idanun suka shige caraf, ya sar?eta da su yanda ya hanata koda motsi suka cigaba da tsaiwa a haka tana a jikinsa idanunsu sar?e cikin na juna. Gaba ?aya tama rasa wane kalar bore zatai masa yasan halin da take ciki akan ganinsa matsayin wai miji a gareta. A hankali ta motsa la??anta zatai magana. Yatsansa ya ?aura saman la??ansa. a hankali yace, "Shiiii!!!". Kasa yin maganar kuwa tayi batare da tasan dalilin hakan ba. Sai ma wata iriyar kasala data saukar mata da bala'in kwarjininsa da bata ta?a ganiba cikin idanunsa.
Kusan a tare hall ?in ya ?auki dariya, sai uban hasken camaras kake gani nata walwala su. Dan yanda suke a tsayen dolene su birge mai kallo, musamman ma'abota son soyayya.
Saurin yin ?asa da kai Madam Chioma tayi tare da saka handkerchief ta share hawayen da suka cika mata idanu, badan shirin da suka ?ulla akan yarinyar nan ba ita da ?awarta da tun a wajen nan saita halakata ta huta akan yaronta da takejin tsananin kishi. Miracle ma tsaki tayi ta mi?e ta fice daga cikin hall ?in tana kuka, daga nan sai gidan barasa, dan tana bu?atar she?e wasu kwalabe ko zata sami nutsuwa. Hakama sauran ?ammatansa da baisan da zamansu ba abun yamusu takaici, ko joy da take ?anwarsa sai da ranta ya sosu duk da kuwa sun birgeta itama.
Da sauri Nu'aymah data dawo hayyacinta saboda maganar mc tai saurin saka hannayenta ta ?an turasa. Sakinta yay badan yaji turawar datai masa ba, sai dan kawai muguntar da tazo masa a cikin rai. Baya ta sakeyi zata fa?i ya ri?o hannunta da sauri ta kuma dawowa jikin nasa. Ya ?an tsuke fuska ka?an yana fa?in, "Silly girl". Sannan ya saketa a hankali. Baki ta murgu?a masa ka?an tana gyara tsaiwarta zuciyarta na wani irin harbawa da sauri-sauri. Kallo ?aya taima sashen dasu Ananah suke ta maida idonta ?asa ta du?ar saboda tsananin jin kunyarsu data lullu?e ta.

Haka dai taro ya tashi lafiya bayan anci an sha kamar ba'asan ciwon ku?i ba. li?i kam sai kace basu sa zafin nema ba. Dan ?an dubu-dubu ne sabbi ?al keta farfar a ?asa. Musamman lokacin da ango da amarya suka fito filin rawa. Sai dai sunyi tsayene babu wanda ya motsa, dama can kowa yasan Yoohan baya rawa, to bare Aymah da basa samun wannan sakewar a nasu gidan dama.
Su Osin abokan ango dai dasu Gebrail ?annen ango an cashe gwargwadon iko. Mawa?an da sukayi wasa a wajen sun kwashi ku?i kam gwargwadon iko. ?arfe ?aya dai-dai aka tashi.
Wasu sun nufi gidajensu ne, wasu kuma anan hotel ?in, sai masu komawa gidansu Yoohan da amarya. Su Amal dai binsu Aunty Ananah sukayi suka koma gidan Abbah kamar yanda Omar ya tasasu a gaba............?



ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 46
__________

_INA MA'ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA... DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._

_LITTAFIN *UNCLE NE...* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._

_"Wait... Dakata hafsat Rano, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?.."_

_"Kede bari Billyn Abdul.. Tsaya kiji kanun labarin a tak'aice..*NIMCYLUV* Tace book din a ta'kaice labarin *UNCLE NE* ne yana tafe:_

_Da farko yana mata kallon uwa wacce ta haife shi kuma jigon rayuwarsa, ashe itace silar rushewar rayuwarsa??yarinyar da yakewa kallon ?anwa uwa ?aya Uba ?aya ita aka wayi gari ta zama MATAR SA?????¡â? ?addara ta ha?ashi da (Ahlil kitab) kiristan ya bata farin ciki, kulawa, soyayya, harya samu ta musulunta, Dalilinta sbd al'?awarin aure da yyi mata,ashe ba sonta yake ba??yaje birnin NUFAR domin kai masu tayin Muslunci, sun amince da hakan amma shara?in dole ya kwanta da ?arsu,?????¡â?gashi bashi da cikakkiyar lfy mazantakarsa bata aiki?? ashe mahaukaciya ce ta haife shi.._

"_Kai lalle akwai runguntsumi acikin wannan littafi.. Ba za'ayi babu ni ba, Domin Za'a sha lagwadar romon dadi. shin tayaya ake biya Hansatu?_"

_"Ai ta Abdul..LITTAFIN *UNCLE NE* Naira 300 ne, Idan kuma kana son vip inda za'a ake posting sau biyu a rana kuma za'a baku littafan data rubuta na ku?i sai ka bada 600 mai ma kon 1k.. number asusu wato bank account details: 0116886423 : account name sulaiman Na'ima S. Bank name: unioun bank: Sai a tura shedar biya ta 08119237616... A nuna mata ?auna ta hanyar turowa ta account????kamar yadda Za'a faranta maku a littafin UNCLE NE_
_(Best romantic love story of the year//Had'adden labarin kauna na shekarar 2021)_


____________


No. 46

.............Washe gari ?an biki duk suka kama gabansu. Ciki kuwa harda ?an kano su aunty hibba. Dan cikin sa'a sun sami jirgin safe. Sun tafi kuma da ?unbin alkairi daga Yoohan. Sai dai kuma zukatansu cike da tausayin Nu'aymah da ?addarar aure ta kawo tsakkiyar wa?an nan mutane. Amma zasu cigaba da tayata da addu'ar zama mai nasara a cikinsu.

Nu'aymah kam bama tasan wainar da ake toyawaba a cikin gidan. Babu wanda ya nemeta a jama'ar gidan, itama kuma bata damu da son ganin kowa ba ma. Dan kukan data raba dare tanayi jiya ne ya ja mata komawa barci mai nauyi yau da safe. Bata farka ba sai wajen sha ?aya. Haka ta tashi jikinta zau da zazza?i. Cikin dauriya tai wanka da ruwa mai zafin gaske. Tana fitowa anayin knocking ?ofar. Sai da ?irjinta ya ?an harba ka?an, dan zatonta ko Yoohan ?in ne. Jin an sake knocking ?in ya sakata rumtse idanunta da sukai mata nauyi, hijjab ta ?auka ta zira, sannan tazo ta bu?e ?ofar tana faman cin magani.
Victoria ce tsaye da tray a hannu, Destiny a bayanta ?auke da flask ?in shayi madaidaici. Ganin yanda yaran keta washe mata fuska ya sata sassauta fuskarta data ?aure. Baki suka ha?a wajen fa?in, "Good morning Aunty!".
A ta?aice Nu'aymah tace musu, "How are you?".
"Fine Aunty, dama Aunty Blessing ce tace mu kawo miki breakfast". (Kukun gidan).
Matsa musu tayi suka shiga cikin ?akin batare data sake cewa komai ba. ?akin sukebi da kallo cike da sha'awar yanda ya ha?u. Bayan sun ajiye Destiny da bakinta baya iya yin shiru tace, "Aunty ?akinki yayi ?yau".
"Thanks you". Aymah ta sake fa?a a ta?aice. Dan ta kula shegen surutu yaran zasu dameta da shi idan ta basu fuska. Ilai kuwa sai Victoria ma ta bu?e baki zatai magana aka turo ?ofar ?akin. Basai an fa?a ba, ?amshin turarensa ma kawai ya isa amsa garesu. Da sauri suka mi?e daga zaman da sukayi akan sofa. Cikin ?an rawar baki suke gaishesa. Janye idanunsa yayi akan Nu'aymah data ?auke kanta bayan ta masa kallo ?aya ya maida garesu. A ta?aice ya amsa musu yana cigaba da takowa cikin ?akin. Saurin nufar ?ofa sukai suka fice.
Duk abinda sukeyi Nu'aymah na kallonsu ta cikin mirror, sai dai ta basar tanata shafa mai a ?afarta kamar batasan da zamasu ba. Sai dai a ranta ji take kamar taje ta sha?esa. Amma zata daure taga iya gudun ruwansa na yinin yau kawai......
Yanda bata tanka masa ba shima bai tanka matanba. Wayar dake a hannunsa yana latsawa ya matsa ya ajiye mata saman mirror ?in, batare da yace komaiba ya juya zai fice. Cike da jin haushi Aymah ta bisa da kallo, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta murgu?a baki da harar bayansa.
Shiko haushin ?in gaidashin da batayi bane ya sakashi ?inyi mata magana. Duk da daman dai yau ya tashi ne da rashin ?an son maganar saboda barci dake cike da idanunsa.
Yana ficewa Aymah ta maida dubanta ga wayar tasa mai azabar ?yau, baki ta ta?e, harta ?auke kanta sai kuma ta sake duban wayar. ba komaine yazo mata a rai ba sai kiran su Umm. Kwana ?aya kawai har taji kewarsu, ji take kamar ta shekara babu su tare da ita. Sannan koba komai tanason sanar musu abinda take ganin basu sani ba, dan ta tabbata akan rashin sani iyayenta sukai wannan gamin gambizar. Ita dai tasan mutumin nan da aka aura mata kafiri ne, kuma tana da tabbacin iyayenta bazasu aura mata arne ba tunda sunsan haramunne a musulinci. Shin ko dai ya ?oye musu ainahin kansa ne? Tabbas Aunty Kubrah ta cutar da ita, tunda har ta ?auki hoton abinda ya faru a kuskure ta bama Hamisu ya kawo gidansu, (dan harga ALLAH tasan Kubrah ce ta saka hamisu yin hakan, sai dai shi tarasa miyasa ya amince ya aikata?) gashi nan ta silar hakan taja an aura mata kafirin da baisan ALLAH ba, danginsa mushiri kai. Dolene a yau tai gaggawar sanarma baba malam abinda ke faruwa..
Hawayene masu zafi suka sake gangaro mata, harga ALLAH ta gwammaci zaman gidansu akan wannan gidan da babu komai sai shirka a cikinsa. Gashi bazata ?oyeba tana son Yah Ab har gobe a cikin zuciyarta. Tana danne soyayyarne kawai dan gudun shiga tsakanin alkairin iyayensu da zumincinsu. Taji da?in ganin wayar babu wani lock. Daga Number baba malam harta Umm da hajjo a cikin kanta suke tsaf. Dan haka babu wani shan wahala ta saka Number Umm ta kira. Sai dai harta yanke ba'a ?aga ba. Ta sake kira nanma ba'a ?aga ?inba. Ta baba malam ta saka. Tunkan ta karasa ma *Uncle S* ya bayyana. alamar da haka yay sebin lambar kenan. Cikin sa'a kuwa bugu biyu aka ?aga. Jikinta har rawa yake najin da?i. Hawayen da take ma?alewa suka sake silalowa jin muryar Abbanta ya ranga?a sallama da muryarnan tasa mai tarin kamala.
"Abba na!" ta fa?a kukanta na ?wacewa da sauti.
Murmushi baba malam yayi daga can, cike da tsokana yace, "Anya mamana bata girmi kuka ba yanzun?".
Ai kamar ya sake zugata ma, saita ?ara sautin kuka nata. Baba malam daketa ?o?arin danne kewar ?ar ?iyar tasa yace, "Tom ya isa haka kuka. Inba hakaba kuma zan yanke wayata....."
"A'a Abbah, dan ALLAH karka kashe. Ina kwana?".
Murmushin ya sakeyi sannan ya amsa mata. Bayan sun gama gaisawa ta tambayi kowa da kowa na gidan nasu. Ya tabbatar mata da duk lafiya suke harsu Ananah da tuni sun isa gida.
"Amma Abbah shine basu sake zuwa nan ba?".
"Ai kinga da safe sosai suka taho mamana, kinga idan sunce sai sunzo nan zasu makara. Mijinki ne ma da kansa yaje ya kaisu airport".
Hawayene suka sake ziraro mata. A ranta tace, 'Mugu shine yaki tashina muje tare'. a fili kuwa sai ta saka hannu ta share hawayen nata. Murya na rawa tace, "Dama na kiraka ne muyi magana Abbah".
Zamansa ya sake gyarawa da ?yau yace, "ina jinki mamana".
"Abbah dan ALLAH ka fahimceni, wlhy ba ?azafi nake masa ba. Mutumin nan fa kafirine, ya ?oye muku ne kawai har kuka bashi aure na......."
"A'a Mamana shi ba kafiri baneba a yanzu. Ki nutsu ki saurareni za miki bayani yanzun nan kinji".
Kanta ta ?aga masa tamkar tana a gabansa. cikin nutsuwa baba malam ya sanar mata komai game da musulintar Yoohan, ya kuma nuna mata muhimmancin zama da shi da dalilin aura mata shi dansu raba gardama tsakanin Abdallah da Naseer gudun kar zuminci ya samu gi?i. Itama kuma zata huta idan tayi nesa da su. Harga ALLAH taji da?in jin cewa Yoohan ?in yanzu musulmi ne, sai dai bawai hakan na nufin zata so shi bane ba, zataima iyayenta biyayya har lokacin da UBANGIJI zai iyakance mata zama tare da shi. Dan bataji zata iya rayuwar dindindin ta aure da shi ba balle wa?an nan dangin nasa masu kama da ojuju.
Baba malam ya mata doguwar nasiha mai ratsa jiki da ?argo. taji kuma tayi ?ammarar yin amfani da ita, amma bata ?auki al?awarin ha?urin zama da Yoohan ba tabbas. A ?arshen wayar ta ro?a baba malam a kawo mata koda ?ar aiki ce daga nan kano. hakan zaisa ta samu abokin hira kafin ta saba da jama'ar gidan.
Baba malam bai?i kar?ar alfarmar tata ba. Dan koba komai yasan hakan zai bata nutsuwa ta ?an kwantar da hankalinta yanda yake bukata da fata. Sai dai yace sai mijinta ya amince sannan.

Koda suka ajiye wayarma tashi tai tana shar?ar hawaye. Batare data cire hijjabin data zumbula ba balle ta nema kayan sakawa ta fa?a saman gado ta cigaba da kukanta da batasan na minene ba. Jitai zazza?in na sake lullu?e ta. Taja lallausan bargon dake saman gadon ta kudundune zuciyarta fal ?unci.

Yoohan dake can ?akin Momy da itama babu lafiyar bayan ya lalla?ata tasha tea ya saka mata ?arin ruwa. Sai da yaga barci ya ?auketa ne ya zare hannunsa dake cikin nata a hankali ya lullu?a mata bargo ya fito. A corridor yaci karo da Miracle. Kallo ?aya yay nata ya ?auke kansa saboda shegun kayan barcin dake a jikinta bata da maraba da tsirara. Da alama ma yanzu ta tashi barci. Cike da kishi tace masa "good morning". Batare daya amsata ba ya wuce abinsa ya barta da ?amshinsa.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login