Showing 48001 words to 51000 words out of 325075 words

Chapter 17 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29132

nasu ajiyesu saboda gudun abin kunya. Sai kuma UBANGIJI mai rahama yay musu gata ta hanyar wa?anda basusanma sanda kikaje kika aikata ?arnanrba.
An sha wa'azi mai ratsa jiki ga manyan malamai, tare da addu'oi ga wa?an nan yara. Sai ?yaututtuka daga manyan mutane ta hanyoyi da dama. Al'amarin dai sai muce Alhmdllh. Sosai su baba malam da ?annensa da Hajjo harma da iyalansu suke cikin dunbin farinci da zagayowar wannan rana a garesu, dan kuwa ba itace ta farko ba, dan wannan shine karo na bakwai da zasu aurar da yara a cikin wannan gida. Al'amarin kam ya burge mutane matu?a, inda wasu sukaji inama sune da wannan ?ya?y?yawar zuciyar haka irin tasu baba malam. Yayinda wasu kuma suka ?auki ?ammarar shigowa cikin tawagar a dama dasu da iya abinda ALLAH ya hore musu suma. Komai ya ?aytar, dan ya tafi cikin nutsuwa, sarki ya bama wa?anan yara ?yaututtuka, hakama Gwamna daya turo wakilinsa dan shi bai samu damar zuwaba ya dai bada tashi ?yautar ga wa?annan angwaye da amare.
Su Nu'aymah ansha kaikawo, dan kuwa sunyi ti?is kamar sune amarorin. Bayan an tashi daga walimar da ?yar suka rarrafa masaukinsu suna maida numfashin wahala. Su dai su Umm sunbi mazansu sun koma gida kamar yanda sukazo tare. Su Nu'aymah d Hajjo kuwa suna nan sai sunga ?wal uwar daka.

________________________

Bayan sallar isha'i baba malam ya tattara ?an uwansa su duka uku a falonsa. A tare sukaci abincin dare, tare da tattauna yanda walima ta tafi cikin aminci da farin ciki babu wata matsala. Sunyi godiya ga UBANGIJI da ya zamemusu garkuwa, sannan baba malam dake tsaye akan komai.
?an murmushi kawai yayi batare da yace dasu komai akan hakanba. Kafin cikin nutsuwa ya nuna musu leda ruwan ?asa da aka kawo ?azun kafin walima tare da kayan abinci. Kasancewar bai samu zama dasu ba ?azun sai bai sanar dasu komaiba ya bari sai sun dawo gida suyi maganar a tsanake sannan su duba abinda ke a ciki.
Abba Musbahu da ya kasance ?arami shi baba malam ya mikama ledan yana fa?in, "Musbahu bu?e muga minene a ciki, dan shi manager ?in kamfanin da aka kawo kayan ta hanyarsu yace dukkan bayanan da muke bukata zamu samu anan. Amma mu kwantar da hankalinmu wanda ya bada ?in baiyi da wata manufa ba, kuma shi yayine badan musan wanene shi ba, idanma muna tsoron wani abune to duk abinda mukaga be kwanta mana a raiba ko wata matsala ta biyo baya to mu nemesa shi, zai kaimu ga mai sa?on idan bu?atar hakan ta taso".
A tare sukace masha ALLAH, ALLAH ya sakanka masa da alkairi, ya biyasa da sakamakon abinda yafi wanda yayi. Shima ALLAH ya faranta masa fiye da yanda ya farantama mabukata.
"Amin". baba malam ya amsa musu, yayinda Abba Musbahu ya fiddo abinda ke na?e cikin leda mai ?yal?yali. Bu?e ledar yayi sai ga madaidaicin kwali ya bayyana. ya bu?e kwalin shima. Sun sami envelope guda biyu, ta farko check na ku?i da suka basu mamaki fiye da zato. Dan a irin wannan halin da ake ciki mai bada ?yautar irin wa?anan ku?i masu yawa haka ai dole a jinjina masa. Sai zungureriyar wasi?a, wadda bayanan cikinta ke magana akan su bada sunan yara talatin na gidan marayun da suka ?are sakandire, ya ?auki nauyin karatunsu na jami'a harsu ?are, maza 15, mata 15. sai sunan kuma wasu ashirin din, maza 10 mata 10 sukuma wa?anda suka kare karatun zai nema musu aiki. Daga ?arshe yace yana ro?onsu alfarmar sakashi cikin jerin mutane da zasu dinga hidima ga wannan gidan marayu gwargwadon ?arfinsa.
dukansu ajiyar zuciya suka shiga saukewa na mamaki da al'ajabin wannan mai sa?o. Kafin su shiga ja masa dogayen addu'oi, daga ?arshe suka tattauna sosai akan lamarin. Sun yake shawarar fa?ama UBANGIJI akan lamarin. Idan alkairine kuma mai wannan ?udiri bada niyyar cuta musu ya zoba ALLAH yay ri?o da hannayensu gaba ?aya. Idan kuma da wata manufa tattare da shi ALLAH yay musu maganinsa tunkan ya samu damar shiga jikinsu balle ya cutar da bayin ALLAH.
Daga haka suka tashi akan zasu mikama UBANGIJI kukansu tsahon kwanaki uku, inda zuciyarsu ta karkata akan al'amarin zasu ?aukesa a matsayin shine za?in da ALLAH yay musu, saisu yanke hukunci akan hakan. zasu cire ku?a?en daya rubuta ?in a maidasu asusun gidan marayun. bayan an gama ?urar ?aurin auren gobe idan ALLAH ya kaimu kuma saisu tantance yaran daya bu?ata game da cigaban karatunsu da kuma wa?anda za'a nemarwa aiki.

*_ABUJA_*

Bayan tafiyar Yoohan da kamar awa biyu sai ga papa da tawagarsa shi kuma ya dawo gida. Dama sunje taron manyan fastocine daya gudana a jihar Lagos, yau kwanansu biyar kenan a can. Ya samu tarba daga iyalansa da ma'aikatan gidansa, inda madam Chioma ke ma?ale da shi har sashensa tai masa rakkiya.
Bayan ya ?imtsa ya fito sukai zaman yin lunch su duka a dining, sosai suka cika falon da surutu kamar ba abinci suke ciba, kowa na bama papa labarin abinda ya faru da baya gida. A cikin surutun nasu ne Abraham ke fa?ama papansu an fasama Brother Yoohan motarsa a kano.
Cak Papa ya tsaya daga cin abincin yana kallon Abraham ?in, kafin ya maida kallonsa ga Madam Chioma da a lokaci guda ?acin rai ya mamaye fuskarta. "Mi naji Abraham na fa?a Darling?". Kanta ta jinjina masa tana ?an karta cokalin hannunta akan filet ?in abincinta, "Hakane Honey, jiya da yaje Kano abin ya faru, dama jira nake ka dawo asan matakin daya dace a ?auka, shiyyasa bance masa komaiba dan karya ce bayaso ayi komai dan kasan halinsa dai".
?an dukan table ?in papa yayi da ture kofin da aka zuba masa lemo ya fa?i. A tare yaran duk suka zabura dan tsorota. Ya mi?e a fusace yana fa?in, "Miyasa tun a jiyan baki sanar minba, Gebrail ka tattaramin guards ?in Yoohan gaba ?ayansu yanzun nan".
Cike da jin da?i Gebrail ya amsa ma papa yana mi?ewa. Dan shima burinsa a ?auki matakin dama.

Cikin mintuna ?alilan guards ?in Yoohan suka taru a falon, kallo guda zakai musu ka fahimci hankalinsu a matu?ar tashe yake. Musamman da suka shigo falon suka iske Papa nata kai kawo rai ?ace, kai kace gadin wani abu ya keyi. Sunkai tsayuwar mintuna goma kansu a ?asa kafin ya kallesu da jajayen idanunsa.
"Inaga baku da wani amfani game da tsare lafiyar Yoohan, zamu sallameku mu canzaku da wa?anda zasu iya, dan na inhar kune zaku cigaba da kulamin da yaro wataran sai an masa yankan rago kuna kallo baku iya yin komaiba akai".
Cikin ?ololuwar tashin hankali suke bashi ha?uri da ro?onsa. Suka ?ora da fa?in, ba laifinsu bane suma, boss ?in nasune ya hanasu kowanne irin yun?uri akan yarinyar. Kuma suna isowa sukaima Madam bayanin komai da ya faru....
Tsawa papa ya daka musu wadda ta sakasu yin shiru lokaci guda. "Idan ya hanaku ?aukar mataki miyasa bazaku kirani tun a lokacin ku sanar mini ba?! Tunkan ku fara aiki ban sanar muku duk randa kukayi kuskure wani abu ya faru da yarona abakin aikinku ba?".
Ka fa?a mana sir. Suka bashi amsa kowanne rai a dagule a tsorace kuma.
Hannu yasa ya bugi kujerar gabansa, "Oh shine kuma baku tuna wannan dokarba?!!".
Madam Chioma dake bayansa ta kama hannunsa ta ri?e cikin nata tana ?an murzawa alamar lallashi, dan bata bu?atar a sallami guards ?in, itama suna mata nata aikin ne daban. "Darling relax, kasan halin Yoohan ?in namu ai, kai musu afuwa su kiyaye gaba kawai. Sai kuma musan abinda ya dace a ayi, idan aikawa za'ayi a kamo mana yarinyar shikenan, dan bana goyon bayan a barta".
Iska ya furzar daga bakinsa, ya zare hannunsa daga nata ya zagaya cikin falon sosai ya zauna a kujera. Kwalba dake a saman ?aramin tray ya ?auka ya tsiyaya abinda ke a cikinta a kofin glass ?an ?arami da shima yake a kan tray ?in. Gaba ?aya ya juye a baki yana ya mutsa fuska, kafin ya ajiye kofin ya kallesu ?aya bayan ?aya.
"A ina abin ya faru?".
"A ?ofar gate ?in wani orphanage ne sir, kuma muna ?yautata zaton yarinyar itama ?ar gidan ce, dan ciki boss yasa muka shiga akai treatment ?in yaron".
"Daga nan zuwa safiyar gobe ku tabbatar wannan yarinyar tana nan cikin abuja, inba hakaba a bakin aikinku".
A tare suka saki murmushin jin da?i, dan koba komai suma dama ?ulle suke da yarinyar, da kuma takaicin hanasu ?aukar mataki da Yoohan yayi jiya. Yanzukan sun sami damar cin ubanta dai-dai gwargwado. Cike da girmamawa da al?awarin yin abinda papan ya sakasu suka amsa. kafin ya basu izinin barin falon.

Ko cikakken mintuna ashirin basu ?araba a gidan suka ?akko hanyar kano duk da kuwa a lokacin ?arfe ?aya na rana ya gota.

Tofa, ana wata ga wata kenan???? .

_____________________
*_NU'AYMAH_*

A ?angaren su Nu'aymah suma a washe garin wannan ranar bayan sakkowa sallar juma'a a massallacin aka ?aura auren yara talatin da shida dake a gidan marayu na ?AN JIBIYA FAMILY. Inda bayan kammala ?aurin auren aka rakasu da addu'oin fatan alkairi kuma.

Da yamma su Nu'aymah suka ?anyi shagalinsu iya mata a sashen matan, suma mazan anguna sukayi nasu a sashensu tare da sauran angunan da ba'a gidan marayun suke ba suma. Bayan sallar la'asar kusan ?arfe biyar da tai dai-dai da isowar tawagar guards ?in Yoohan gidan marayun aka kwashi amare gaba ?ayansu aka mi?asu ?akunan mazansu, bisa rakkiyar iyayensu su baba malam. bayan doguwar nasiha da sukasha daga garesu tamkar yanda mahaifa kema ?a?ansu idan zasu mi?asu gidan miji.
Duk wani jan ido da barazanar Guards ?in Yoohan securitys sun hanasu shiga cikin Orphanage ?in, acewarsu sai dai su fa?i miya kawosu anan gate, idan sunga da damar barinsu su shiga shikenan, idan sunga babu damar hakan kuma sai dai su juya. Ran guards ?in ya ?aci matu?a, sunji kamar su harbesu kowama ya huta. amma sai suka danne sukai musu bayani akan abinda ya kawosu, tare da tabbatar musu suna tare da ?an sanda.
Duk da securitys ?in gidan marayun sun gane wa ake nufi da kuma miya faru jiya sai suka nuna bama su ganesuba, dan a ganinsu bai kamata su bada damar da za'aci zarafin ?a ?aya tilo ga wanda bai ta?a gajiyawa wajen musu hidimaba. Sun ka?asu dambu taliya sunce basu gane Nu'aymah ba, su bama susan anyi wani abuba.
Ran guards ?in yayi ?ololuwar ?aci, sai dai ?aukar mataki ya gagaresu, dan suma securitys ?in gidan marayun bawai kanwar lasa bane. Sun san ta?asu babban bala'ine ga ogan nasu papa balle su ?in karan ka?a miya. Dan haka suka bar orphanage ?in ransu a ?ace, akan zasuje su sake shiri gobe su dawo.
Hotel suka kama, kafin su kira papa su sanar masa da komai daya faru.

¡ï¡ï¡ï¡ï

Su Nu'aymah da basusan wainar da ake toyawaba ana kammala mi?a amare baba malam yasa Yah Ahmad ya tattara masa su aka wuce dasu gida badan sunso hakanba. Dan so sukai sukam sai sunyi sati ?ai-?ai a gidan kafin su koma gida. Sai dai baba malam ya ?ata musu shirinsu.
Aiko koda suka koma gidan sai suka dinga fushi da kumbure-kumbure. Kayan biki da baba habi ta ha?a musu ma sun?i kulawa. Babu wanda yabi takansu a gidan, saisu Kubrah ne ma ke musu dariyar tsokana suna sake ?ulal dasu dan duk suna sashen Hajjo ne da suka dawo tare.

____________________


Gaba ?aya ran guards ?in Yoohan a ?ace yake, tunda suka iso hotel ?in da suka kama basu zaunaba, sai faman ?ulle-?ullen yanda zasu sami Nu'aymah da matakin da zasu ?auka a kanta sukeyi. Kai kace wata babbar ?ar ta'adda suke bibiya.
Sun ?ulla yafi sau hamsin suna warwarewa. Suna tsaka da sake ?ullawa sa?o ya iso garesu daga hannun ?aya daga ma'aikatan hotel ?in. Number wayace daga wani, ya basu damar su kirashi idan suna bu?atar sanin inda wadda suke nema take..
Da yake burinsu kenan jiki na ?ari suka kira kuwa. Ba'a ?agaba har sai da ta kusan tsinkewa. ?inyin magana akayi. sai da ?aya daga cikin guards ?in ya fara magana.
"Duk da bamusan ko wanene ba, mun maka al?awarin inhar ka sanar mana inda yarinyar take zamu biyaka da ku?i masu nauyi, oganmu ma zai maka ?yauta ta musamman".
Batare da an basu amsaba aka yanke wayar. Kallon juna suka shigayi tambayoyi fal ransu. Kafin ?ayansu ya iya furta wani abu sai ga sa?o ya shigo. Da sauri suka bu?e ganin Number da suka kira ?ince. Ba komai bane a sa?on face cikakken address ?in gidansu Nu'aymah, da sunanta harma da hotonta.
Da?ine yay mugun kamasu, dan kuwa sun sake tabbatar da ita?ince, dan haka jiki na rawa suka sake kiran wanda ya tura musu ?in. Yanzun ma dai baiyi maganaba, sai sune suka bu?aci ya turo musu accaunt details nashi ko nata zasu tura masa ladan aikinsa. ?itt aka yanke wayar batare da ance komaiba. Mintuna ka?an kuwa saiga accaunt Number an turo. A take suma sukaima papa massege bayan sun kirashi sun sanar masa komai.

Har a lokacin cike yake da ?acin ran abinda ya faru, dan yaje yaga yanda akaima motar bugu na fitar hankali, shiyyasa ransa ya sake ?aci, ya kuma tabbatarma kansa ko ?iyar uban wacece yarinyar sai ta yabama aya za?inta.
Babu ko tantama ana turo masa accaunt details ?in ya antayama maishi ku?i masu tsoka, dan a ganinsa bukatarsa ta biya. Mizaisa yaji ciwon biyan wanda ya taimakesu.

________________________________
*_NU'AYMAH_*

Yau sama-sama Nu'aymah ta wayi gari, dan ta tashi da ciwon ?afa alamar zuwan period ?inta. Ita dama takan fara da ciwon ?afane, randa yazo kuma zataita amai har saita jigata. Kafin daga bisani ta koma normal sai shegen ?wa?ayi kamar taci mutum ?anye.
Tunda Umm ta shiga tadasu sallar asuba ta lura batajin da?i, dan maimakon kwance saita isketa zaune ?asa a bakin gado kan kafet ta kife kanta a kan gadon. Yusrah da Amal nata barcinsu a kan gadon su. Ita ta fara tadawa kafin su Amal, har zata juya ta fita sai kuma ta dakata ta kalli Nu'aymahn data maida kanta ta kife tsakanin ?afafunta.......
"Ke kuma lafiya?". Da ?yar Nu'aymah ta ?aga kai ta kalli Umm, sai dai gudun kar ace ta shirya aje asibiti a mata allura sai ta daure tace, "Umm lafiya lau, kawai gajiyace tasa ?afafuna ciwo".
?an ?ura mata idanu Umm tayi na wasu mintuna, kafin ta janye tai ficewarta batare data sake cewa komaiba. Yusrah ce ta ?araso wajen Nu'aymah ?in ta dur?usa. "Baby ?arya kikaima Umm wlhy, daga gani baki da lafiya".
Yamutsa fuska Nu'aymah tayi ka?an tana maida ?wallar data cika mata ido. "?afafuna ke ciwo wlhy Yusrah, nasan kuma period ?inane zaizo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ko anjima".
Amal dake fitowa daga bayi tace, "To miyasa kika?i fa?ar gaskiya?". Yusrah data harbo jirgin Nu'aymah tai saurin cewa, "Allura". A tare suka kwashe da dariya ita da Amal. Nu'aymah kuma tai tsaki idonta cike da ?walla ta mi?e. Da ?ingishi ta shiga bayi batare data kula dariyar dasu Yusrah ke mataba har yanzun.

Bayan sun idar da salla Yusrah da Amal suka fice taya iyayensu aiki, Nu'aymah kam saita koma saman gado ta kwanta. Babu jimawa barci yay gaba da ita.

Umm da duk ta gama fahimtarta bata nemeta ba, dan tasan zata gama zagayenta ne tazo ta nemeta. Bayan sun kammala breakfast ita da ?an aiki ta shirya na baba malam da sauran ?an uwansa a falonsa da kanta kamar yanda ta saba inhar duk suna gari, dan tare sukecin abincin safe da dare. Na rana ne dai bai zama dole su dukansu suna a gidaba shiyyasa. Garama idan ta kama juma'a ace dan duk basa zuwa ko ina a wannan ranar sai massallaci.
Sai da taga komai ya mata yanda takeso sannan ta saka turaren wuta ta le?a bedroom ?insa. Yana wanka, sai kawai ta bu?e Wadrobe ?insa ta za?o masa kayan da zai saka, saboda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login