Showing 180001 words to 183000 words out of 325075 words

Chapter 61 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29087

ransa fal tunanin lafiya kuwa? Sai kuma yay saurin kallon hannayensa biyu dake ri?e da gefe-gefen towel ?in. Ai baimasan sanda ya fashe da dariya ba. Ya saki towel ?in yana zama bakin gadon har sannan dariyar yake hannayensa ri?e da kansa. Pant ?in dake jikinsa fari ?al ya shafa yana fa?in, 'Silly girl, an gaya miki zan fito gabanki babu pant'.
Oho Aymah tuni takai ?akinta ita dai, ta fa?a toilet tana hakki idanunta a rufe kamar ance gashi gabanta. Taja kusan mintuna biyu sannan ta sami nutsuwa, ta ?an dafe kanta a ranta tanajin da sakamakon abinda zata gani kenan da bata biye masa tai wannan shararba. Dan dama tayine kawai saboda an koya musu biyayya gana gaba dasu, sannan nasihar iyayenta a gareta tana nan daram cikin ranta babu abinda ta manta a ciki. Daga haka itama ta zame kayanta ta hau yin wankan.

Ta kammala shirinta kenan cikin ba?ar doguwar rigar jallabiya data ji stones ya shigo. Saurin juya masa baya tayi tana ?ata fuska. Kansa ya girgiza ka?an ya cigaba da takowa cikin ?akin. A kan la??anta ta furta, 'Mayen suit ' dan tsaf ta gama ?are masa kallo ta cikin mirror ba tare da ya sani ba. Shima ?in dai kallonta yake daga sama har ?asa dan rigar ta mata ?yau sosai. Idonsa akan dokin wuyanta da kananun gashi ke kwance luf-luf yace, "Ni zan wuce porthercout, sai gobe idan ALLAH ya kaimu zan dawo".
Da sauri ta juyo tana kallonsa idanu a bu?e, tace, "Ni kuma ka barni a ina?".
Da mamaki yace, "A ina kike anan?".
"Gidanku".
ta bashi amsa kansa tsaye.
"Oh to anan zaki zauna kenan, tunda kinsan ni dai aiki zanje ko". Yanda yay maganar a dakile ne ya bata haushi. Cike da tsiwar tata data motsa tace, "He'em. Wlhy to nima ka kaini gidan Abbah dan bazan zauna ni ?aya ba. Sannan kuma nama Abbana maganar ?ar aiki daga can kano yace babu ruwansa saika amince. Please ka kirashi kace ka yarda".
Necktie ?insa dake rike a hannu da rigar saman suit ?in ya gyarama zama yana tsatstsare ta da idanunsa, "Duk wa?anan masu aikin dake gidan nan su menen amfaninsu da har sai an kawo mai aiki daga kano?". "Toni bana bu?atar aikinsu, ni dai kawai a akawomin YARENA ADDININA hankalina zaifi kwanciya. Amma ta ina zan yarda wa?an nan garadan na shigomin kai tsaye gasu da shegen kallo kamar ?a?an mayu".
?ala baice da itaba, dan shima ya tafi wani kuma tunani daban. A ganinsa zaiyi amfani da wannan damar wajen binciko abinda yay alwashi. Dan dole kam ya yarda sai sun sami kusanci da wani ?an gidansu Aymah anan sannan zai fahimci abinda yake zargin. Kuma ya tabbata idan aka kawo mai aikin duk wanda yayma Nu'aymah wancan ?ullin zai ha?a ala?a mai ?arfi da wanda za'a kawo musun saboda samun bayanai akanta. Shi kuma wannan shine mabu?in bincikensa...........
"Na shirya" data fa?a ne ya maidosa hankalinsa. Yay saurin dubanta da ?yau yana bin handbag ?in hannunta da kallo da ?aramar leda. 'Lallai kan yarinyar nan da motsi' ya ayyana a ransa yana ?auke idonsa a kanta. Duk da take masa kallon ba bahaushe ba duk yanda al'adunsu da dokokin musulinci sai da Hamza manager ya bashi haske a kansu daki-daki. Shi kuma ya ?auki ?ammarar bi da ita akansu kodan ta samu nutsuwar zama da shi.
"Karki ma ?atama kanki rai dan babu inda zakije. Idan abokan hira kike bukata gidan nan cike yake da mutane". "To ni........" ta kasa ?arasawa saboda matsota da yayi. "Ke me?". Ya fa?a yana tsuke fuskarsa da ?yau. Bata sake magana ba dan kwarjinin da yay mata da cika idanu. Ga kuma zuciyar ta gado ta yun?uro tazo gab da ma?oshi ta tsaya. Harya juya ya fita bata sake magana ba sai hawayene da suka cika mata idanu. Yana rufe mata ?ofar kuwa ta matsosu suka zubo.

Duk da yaji tausayinta a ransa haka ya fice daga sashen nasu, a falo ya iske duk a halin gidan suna breakfast a babban dining ?insu. Cike da girmamawa yaran duk suka shiga gaishesa. Ya amsa sau ?aya shima yana gaida su Momynsa dake binsa da wani irin kallo da ya kasa bama fassara. Da yake tasan kullum itace ke saka masa necktie indai yana gida saita taso. Amsa tayi ta saka masa, tare da taimaka masa ya ?ora rigar saman itama. Yanda batai magana ba shima sai baiyi ba. Sai da ta gama saka masa sannan yace, "Mu an daina bamu breakfast ne a gidan Momy?".
Da sauri tace, "No my boy, dama na sanarma Blessing ne takai muku tunda har yanzu kaga dota tana tare da ba?unta".
Idanunsa ya?an lumahe ya bu?e a kanta. Hakan ba karamin sumar da ita yake ba, dan tana masifa-masifar son wannan salon da ya zame ma ?an nata ?abi'arsa. Yace, "Wasa nake nima Momy, ga amanar matana nan na bar miki, ni zanje porthercout ne, amma zan dawo gobe".
Da ?yar ta danne zafin da takeji a zuciyarta. Ta kai hannu bisa tattausan sajensa ta shafa tana lumshe idanu, "Babu damuwa My Son, kaje lafiya ka dawo cikin nasara". Hannunsa yasa ya janye nata daga fuskar tasa. Ya sumbaci bayan hannun yana jinjina mata kai da fa?in, "Thanks you sweetheart".
Daga haka ya juya ga kakaninsa. Fuska ya tsuke da ?yau yana kallonsu. "Granny's na dawo gareku, dan nasan kunfi kowa tarin matsala a gidan nan yanzun. Baku barma kanku ba balle wani. Ga matata nan zan bari, idan na dawo naga ko ?warzanen damuwa a fuskarta nasan maganinku".
Cike da hayaniya Momy Debora ta hayayya?o masa cikin yarensu, dan dama da yare yay maganar shima. Itama Mama mi?ewa tai tana zazzaga masa nata. Bai kulasu ba ya duba kannensa suma yay muau nasa garga?in da idanu, sannan ya duba ?anen papa su Momy Destiny. A girmame yace, "Auntys kuma na baku amanar matata, karku bari wa?anan tom and jerry ?in su mata ko kallon banza". Cike da kulawa suka kar?a masa. Dan sukam har cikin ransu suna ?aunar ?an ?an uwan nasu, musamman daya kasance Yoohan tsaye yake akan bukatunsu na yau da kullum harma da ?a?ansu.
Har mota ?annensa da Momy sukai masa rakkiya, Gebrail ma motar ya shiga zai bisa har airport dan yanason ya tambayi ku?i a wajensa. Solomon dai nata faman cin maganin da shi Yoohan ?inma bai san yanayi ba. Sai da motocin suka fice sannan suka koma cikin gidan.

Hawaye sosai Aymah ta dingayi dan kewar gidace sosai ta dawo mata sabuwa fil. Daga ?arshe ma sai ta koma gado ta kwanta abinta. Tun tana tunanin mafita akan wannan auren har barci yay awon gaba da ita batare data shirya hakanba.
Barcin kusan awa guda da rabi tayi kafin ta tashi, koba komai taji sakayau bakamar ?azunba. Ganin lokacin walha ya wuce sai kawai ta shiga toilet tai uzirinta ta fito. A ranta take ayyanawa bazatai zaman takura kai ba, gara ta fitama ta zagaya gidan kar masu gidan su ?auka ko tsoronsu takeji su sami nayi a kanta. A falo taci karo da breakfast da Blessing ta kawo mata tun ?azun. Ta matsa gaban tray ?in tana bu?e kwanikan. gasashen plantain ne, sai miyar ?wai da ruwan tea da farfesun kifi. Ba yunwar take jiba. dan haka ta ?auki gasashshen plantain ?in guda biyu tasa miya a gefe ta zauna taci, koda ta gama saita ?auka trayn gaba ?aya ta fito da shi.
Tunda ta fara sakkowa daga steps ?in benan duk suka zuba mata idanu. Babu wanda bai yaba ?yawunta ba a cikin ransa. Tare da ganin dacewarta da Yoohan ?in nasu. Miracle ce ta fara jan tsaki tana kauda kanta gefe. Karaf kuwa a idon Aymah dake sakkowa. Wani ?oyayyen murmushi ta saki a ranta tana ayyana 'kece zaki fara ?aukar lesson kenan ?ar lukuta'. A fili kam saita dubi Blessing data hangota tazo wajen da saurin domin amsar tiren hannunta. Yanda Blessing ?in ta gaidata da girmamawa haka itama ta amsa mata da girmamawa tana mi?a mata tiren..
Cikin falon ta ?arasa fuskarta ?auke da ?an murmushi, ta zauna a kujerar data rage. Su mama debora ta fara gaidawa, suka amsa mata fuska a ?aure. Bata damuba ta gaida Momy, ita dai babu yabo babu fallasa ta amsa. Daga haka ta gaida su Momy Favour da suka amsa mata sukam da fara'a, har suna tambayarta ya ba?unta?. ko kallon inda su Joy suke batai ba, sai da su Victoria na gaisheta ne ta amsa musu da kulawa tana tambayarsu ya school?.
Wani wawan tsoki Miracle ta sake ja tana mi?ewa tana wani fifita fuska da hannu alamar wula?anci dai.
Tana zuwa saitin Aymah tasa ?afa ta ta?eta batare da kowa ya lura da yanda akai ba, sai ganin Miracle sukai a ?asa wanwar bakinta ya daki gefen centre table aiko ya fashe.............?

Tofa, mutuniyarku zata fara taro mana world cup a gidan Pastor goshpower??????.


yanzu haka an kusa kai ?arhe, gamai bu?ata zai iya garzayawa ya biya zafafa kar agama shanye romo babu shi??????.

Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 49

_____________

_Ina ma'abota karance karance littafin hausa? Wanda ke nishadantar wa ya fadakar? Kana ya tsunduma ku a kogin lobayyar kauna..?_

_*REAL FEEDO* hazikar marubuciyar nan ta zo muku da wani gangariyar littafi mai suna: *BA AMO...!* *BA AMO* wani nazartaccen littafi ne daya zo da wani irin salo na daban..._

_Labarin *BA AMO* ya faru akan wata yarinya da d'an sarkin garin su, yarinyar gidan su gidan yawa ne...Baban su yana auri saki ya tara 'ya'ya da mata da yawa. Tirqashi! To ita yarinya sunan ta KHAIRAT... Tun farko dangin mahaifin su sun tsani mahaifiyar tasu,Bayan ya auro ta, Ta haifi yara mata zallah suna kiran ta da uwar mata kuma kwata-kwata basa kaunar ita da 'ya'yan nata. To ita yarinya ta gama karatun ta.... wato KHAIRAT.. shekarun ta 22 matan gidan nasu suna mata gorin tayi kwantai tak'i aure. Kwatsam wata rana yarinyar ta samu labarin d'an sarkin garin su ya bude sabon company ya fara daukan sabbin ma'aikata, ?????¡á???cikin ikon Allah ta zuwa ta samu aiki. Ta fara zuwa aikin ta, a karshe su kansu da suka fahimci kwazan ta da nutsuwar ta samu karin matsayi. To a lokacin ne kuma Yarima da PA dinsa suka sami matsala aka kore ta a ma'aikata sai aka daura ita Khairat d'in a matsayin P.A dinsa. Tafiyar tasu batama yi nisa ba! Aka yi makiya suka yi masu sharrin wai karuwar sa ce, har labarin yaje gun mai martaba. Itama Khairat d'in labarin yaje ga mahaifin ta har ya nemi korar ta daga gidan sa, da kyar aka lallashe shi ya hakura.._

_Tab rungutsumi din fa kenan??Ya zata kaya ne ga YAREEMAH GA KHAIRAT..a roof d'aya? Ya rabbi?? labarin kauna yayi.. Amma fa Za'a sha rikici.. Karku manta khairat daga gidan yawa tafito??Ga basuda wani hali.. Shin sarki zai yadda da Khairat amatsayin personal assistant din yareemah ko kuwa.? Duk wannan ruguntsumi n REAL FEEDO ce kadai zata iya warware mana.._

_BA AMO::::: (Ba Labari...)_

_DOMIN MALLAKAR NAKI/'NAKA sai ku baza idanu domin free ne yana nan yana yawo a kowane group_????


___________

No. 49

............Kusan duk falon sai da kowa ya mi?e saboda uban ihun da Miracle ta ?wallo. Hannunta ?aya ri?e da baki ?aya ri?e da ?afarta data bugi kujera. Duk kanta suka nufa cike da tashin hankali.
Banda Aymah data wani ?aura ?afa ?aya bisa ?aya tamkar ba itace ta aikata tsiyar ba. Cikin mintuna ?alilan bakin Miracle ya suntume, gashi an ?agata ta kasa taka ?afar sai faman ihu take tana kiran Jesus. Tayi yare tayi turanci hawaye sha?e-sha?e da fuska.
Abu kamar wasa sai ga jikin Miracle ya rine da zazz?i dan harga ALLAH taji fa?uwar musamman data kasance a bazata tazo mata. Gata masha ALLAH tanada jiki. Ko a kwalar rigar Nu'aymah, dan saida ta gama shan ?amshinta sannan ta ?an matsa gab da Mira da aka kwantar a doguwar kujera dake kusa da inda Aymah take zaune ana jiran Doctor yazo ya dubata. Da wani salon iskanci tace, "Ayyah Aunty Orrobo sorry yeah, wannan baki haka kamar shantu? Gobe kam ya sake yin tsaki batare da ya tantance inda zaiyi ba". Babu wanda yaji mita fa?a a maganarta ta ?arshe bayan sannu da taima Mira. Dan kuwa da hausa tayi, yanda kuma ta kwa?e fuska sai ka ?auka duk tausayin Mira ?inne takeyi.
A gefe kuma suna ganin Aymah ba wani turancin kirki takeji ba shiyyasa ta ?arasa sannu wa Miracle ?in da hausa. Haka suka cigaba da zama har isowar Doctor, ya duba Miracle ?in sai ga sakamakon targa?e a ?afar data buge. Dole yace su shirya a kaita asibiti dan a duba ?afar da ?yau, a kuma yimata ?inki a gefen bakinta da ya shafce.

Tun bayan wucewar su Miracle da Gebrail da Joy suka tafi rakawa asibiti Aymah ta koma sama dan lokacin sallar zuhur yayi. Dariya ta dinga she?awa tunda ta shigo kamar wata zararriya. Sai da tayi mai isarta sannan ta ?auro alwala tana fa?in, 'Duk wanda ya shirya match dani ai ya sani nima da shirina nake. Babu ta yanda za'ayi na zauna mushirikai su hau kaina suci tuwo. Wasa kam yanzu aka fara a wanga gida dan na kula basusan wacece Zainabu jikar Hajjo ?iyar baba malam ba'.
Sallarta ta gabatar a nutse, tana idarwa ta ?auki Al-qur'ani ta hau karatu cikin zazza?ar muryarta. Blessing ce ta shigo kawo mata lunch, sai dai a falo ta ajiye bata shigoba. Ta matso jikin ?ofar danta sanar mata ga abinci nan kunnenta ya jiye mata zazza?ar muryar Nu'aymah na raira karatun littafi mai tsarki. Tsayawa cak tayi daga yun?urin knocking ?in tana sake matsar da kunnenta dan taji sosai. Kamar wasa sai gashi ta share mintuna kusan goma tana saurarenta. Sai da taji tsoron kar wanu ya shigo ya ganta ne sannan tai saurin barin sashen.
Oho, Aymah batasan tanayiba. Karatunta ta sha na kusan awa ?aya sannan tai addu'a ta mi?e. Sosai takejin kewar ahalinta, musamman ma Muhammad abokin dambenta. Gudun kar damuwa taima ranta yawa yasa ta fito falon danta ?anyi ko kallo ne. Sai da ta fara duba abincin da Blessing ta ajiye, duk da taga shinkafa da miya hakan bai sata jin zataci ba. Itafa gaskiya bazata jura cin abincinsu ba. Ya dawo zata fa?a masa ita zatana girkintane kawai. Da wannan tunanin ta maida kulolin ta rufe. Saurarrakin biscuits ?in data ci ?azun ta ?ebo. ta dawo cikin kujera ta kunna tv a ranta tana mamakin yanda koda yaushe suke cikin wutar nepa. A maimakon kallon ma sai tai ta Searching tashoshi tana duba masu amfanin da ri?e Numbers ?insu a kanta. Hakan ya jata lokaci mai tsayi har aka kira la'asar. Salla taje tayi, ta sake wanka. Tsaf ta fito tana baza ?amshi ta sauka ?asa.
Yanzunma duk a falin ta iskesu an dawo da Mira data sha ?auri a ?afa da hannunta data kulje, kunburin bakin kam ya ?ara fa?i dan ya kusa shanye rabin kumatunta. Batare da Nu'aymah ta duba ko inda take ba tacema su Destiny suzo su rakata taga gidan. Harara mama debora ta zuba musu da musu garga?i da idanu. Amma duk sai suka ma?e kafa?a suka mi?e. Tsaf Aymah na lura da komai, dan haka tai murmushi kawai (Mama debo karfa kizama next level??lol).
Suna fita Joy tace, "Yarinyar nan na kula da rawan kai ta shigo gidan nan, wlhy ni sai nagama kamar itace ta sama Mira ?afa ta fa?i fa?".
Gebrail da ya bi Aymah da kallo kamar idanun zasu zubo ?asa yay saurin waigowa yana duban Joy ?in. "Hy madam banda ?arya fa, dan kawai tana rayuwanta kai tsaye sai ace tana rawan kai?. Kufa ?azun kuke gulman hausawa bagidadawa ne. Sai kuma gashi ita ta ?aryataku yanzun tunda ta nuna kanta a bu?e yake. Da kun sone ta ?unshe kanta a ?aki komi? Mtsoww amebo girl".
Zumbur Joy ta mi?e kansa, Momy ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login