Showing 123001 words to 126000 words out of 325075 words

Chapter 42 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29184

a rashin neman na kansuba, balle ai tunanin zama daga jiran na wani ko taskar masu mulki. Dukansu sunada sana'oinsu. To inhar mutane masu daraja irinsu sun yi gwagwarmayar neman halalinsu mu su wanene da bazamu tashi munema na kanmu ba".
Ajiyar zuciya Yoohan ya sauke. Murya a sanyaye yace, "Hakane Uncle. Tunanin hakan baizo min a rai ba shiyyasa".
"Karka damu ALLAH yana tare da mu. Insha ALLAHU mafita zatazo daga UBANGIJIN rahama da jin?ai".
"To shike nan Uncle nagode sosai. ALLAH ya ?ara lafiya da tsahon rai. Bara na barka ka huta dan yanzu na sami nutsuwa, ?azu kam hankalina a tashe yake sosai".
?ar dariya baba malam yay masa sukai sallama ran Yoohan fes. Da ?arfin zuciyarsa kuwa ya mi?e ya fara zame kayansa dan son watsa ruwa.

¡ï¡ï¡ï

Tunda suka ajiye wayar baba malam ya shiga dogon nazari, harga ALLAH yana jin son Yoohan cikin ransa. hakan har mamaki yake bashi wani lokacin. Duk da yasan UBANGIJI kan jefa soyayyar wani a zuciyar wani batare da wata ala?a ba a tsakaninsu
Har yanzu baisan abubuwa da yawa ba dangane da Yaron ba, amma sai ya keji zuciyarsa na tsananin ?yautata masa zato akan abubuwa da dama na rayuwar yau da gobe. Ha?uwarsu ta uku kenan kacal. Amma ya fahimci wasu ?yawawan halayya da ko a cikin musulman ma ba kowane ke da su ba. Ga ?yauttawa da yarda da yaron ke bashi ?ari bisa ?ari.
Numfashi ya ?an sauke wani gefen zuciyarsa na sake ?arfafa masa gwiwa akan alkarin da yake shirin aikatawa. Yayinda can kuma wata ke garga?arsa musamman akan ahalin da Yoohan ?in ya fito.........
"Malam lafiya kuwa ka zurfafa a tunani haka?". Umm data shigo tun ?azun tanata sallama bai jiba ta fa?a tana mai katsesa.
Ajiyar zuciya ya sauke da sauri tare da kallonta. Gefensa ya nuna mata da hannu alamar ta zauna. Batare da tayi musu ba ta zauna kuwa idanunta a kansa. Hannunsa ya sa?ala cikinnata yana ?an sake furzar da huci. "Jannat wani al'amarine yanzun nan UBANGIJI ya sa?aminshi a cikin tunanina akan yaron nan dana sanar miki jiya ya musulunta. Sai dai kuma wani sashi na zuciyar tawa yana garga?ina dason jefani a kokwanto game da al'amarin".
"Tom nidai a nawa tunanin sai naga kamar shai?anne Malam. mizai hana ka bama al'amarin wani ?an lokaci haka, sai ka du?ufa neman za?in ALLAH akan yuwuwarsa ko barinsa".
"Eh tabbas kinzo da shawarar hankali Jannat. Insha ALLAHU kuma zanyi amfani da ita. Amma kema inason ki tayani dan ALLAH".
"Insha ALLAHU zan tayaka Abban Nu'aymah, ALLAH ya tabbatar mana da alkairinsa".
"Amin ya rabbil-alamin". Ya fa?a cike da jin nutsuwa da gamsuwa akan shawararta".


______________¡ï¡ï¡ï

Kwanakin Nu'aymah uku a asibiti aka sallamota. Alhmdllh jikinta yayi ?yau sosai, sai dai ha?arin da Doctor ya tabbatarma iyayenta tana a ciki akan iya fuskantar loosing mamory shine ya jefasu a cikin matu?ar damuwa.
Yayinda ita kuma da batasan mike faruwa ba sai tata matsalar ta zama Naser. Dan a kwanaki biyun nan daya ?auka da zuwa gaba ?aya ya takurama kowanne irin motsinta. Duk da daga gaisuwa babu abinda ke sake ha?asu sai magana kamar kowa. Amma kallon da yake jifanta da shi da tarewa a asibiti da yayi ya tabbatar mata cewar zuwan nasa akwai manufa.
Tun bayan dawowarsu gida Umm ta taimaka mata tai wanka taci abinci da magungunanta ta kwanta danta huta. Shine ta samu damar yin tunani akan Naser ?in. Kamar daga sama ta dinga jiyo hayaniya na tashi a gidan, sosai mamaki ya kamata, duk da ta tabbatar hayaniyar bata fa?a bace tasan wannan ba ?abi'ar mutanen gidansu baceba hakan. 'To minene ya faru?' ta fa?a a fili cikin sake zurfafa mamakinta.
Kusan mintuna ashirin sai kuma taji hayaniyar ta lafa. bata ko motsa ba balle ai tunanin zata fita ta ganoma idanunta, haka ta cigaba da kwanciyarta tun tana tunani har barci mai nauyi ya ?auketa saboda a maganin nata akwai na barci daman.

Kiran sallar magriba ne ya saka Umm shigowa ?akin Nu'aymah ta tadata. Da ?yar ta samu ta tashi dan barcin nata yayi nisa sosai. Taimaka mata tayi tai alwala kafin tai yun?urin fita zata barta.....
"Umm wai hayaniyar mi naji anayi ?azun?". Ta fa?a cikin katse hanzarin Umm dake ?o?arin fita.
Batare da Umm ta juyo ta kalleta ba tace, "Su Abdallah ne, sunma shigo dubaki kina barci".
Sosai gaban Nu'aymah ya fa?i, sai dai kafin ta sake cewa wani abu Umm ta fice abinta. Shiru tai tsaye hannunta ri?e da hijjab, dan zuciyarta cike take da tambayoyin miya kawo su Yah Ab ?in gida a yanzun bayan kuma shine da kansa yacema Hajjo sai bikin su aunty Hajarah daya rage saura kwanaki ashirin cif yau ayi. Ganin bata da mai bata amsarta sai ta saka hijjab ?inta ta kabbara salla kawai.
Koda ta idar bata fitaba tai zamanta a ?aki, sai da tai sallar isha'i da shafa'i da wutiri sanna ta fito falonsu danta ?ansha iska. Umm kawai ta tarar zaune. Ta zauna kusa da ita tare da ?ora kanta a gefen kafa?arta.
?an kallonta tayi, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta ?aura hannunta a wuyanta. Jin jikinta babu wani zafi ya saka Umm sauke ajiyar zuciya da janye hannunta.
"Umm nafa warke". Nu'aymah ta fa?a tana murmushi dajin ?aruwar ?aunar mahaifiyar tata a cikin rai. Itama Umm Murmushin tayi, ta shafa kumatun ?iyar tata da fa?in, "Ai haka muke fata Nu'aymah, ALLAH ya ?ara miki lafiya dai damu baki ?aya".
"Amin Umm". Ta amsa mata zuciyarta cike da damuwa. tasan iyayenta suna cike da damuwar halin data tsinci kanta, basu da damuwa sama da lafiyarta, basu kuma da burin da ya wuce su wayi gari suga ta warke.........
Sallamar Adawiya ta katse tunanin Nu'aymah. Ta ?an ?ago daga kafa?ar Umm tana amsawa. Sai dai ganin harda Yah Abdallah ya sata maida kan ta sake kwantarwa zuciyarta najin zafin kishi a kansa.
Rungumeta Adawiya tayi cike da munafincin data saba nunawa idan suna a gaban mutane. Itama sai Nu'aymah ta tarbeta fuskarta fes. Umm dai cike da jin da?i take dubansu. Yayinda Abdallah kam kallonsu kawai yakeyi.
Bayan sun gaisa da Umm, Nu'aymah ta gaida Abdallah batare data yarda sun ha?a ido ba duk da kuwa shi hakan yake bu?ata tun ?azun. A tunaninta zasu tafi ne, amma sai taga sunyi zamansu sunata hira da Umm. Kusan mintuna talatin basu da ko niyyar tafiyar, takaici ya cika Nu'aymah, dan haka kawai yau itama sai takejin zafin Adawiya akan Abdallah. Shiyyasa hirarma bata saka baki, tana lafe jikin Umm tamkar wata mage.
Basu bar sashen ba har sai da Baba malam ya shigo gidan, dama shi suke jira. Zama kuwa yay suka gaisa a ransa yana mai jin da?in ganin yanda Adawiya ta kwantar da hankalinta. Yanda tai ?iba ta ?ara ?yau kawai ya isa fahimtar da mai kallonta hankalinta a kwance yake sosai. Barci ne ya sake kwashe Nu'aymah har suka bar sashen bata saniba. Koda Umm datai tunanin anan Adawiya zata kwana amma taga sa?anin hakan sai da ta tashe Nu'aymahr ma ta rakata ?akinta saboda barcin da tayi.

Washe gari Nu'aymah ta tashi ne duk a takure. Ba komai ya jawo hakanba sai zuwan su Yah Ab da zaman Naser a gidan. Ma?alewa tayi a sashensu ta?i fita har rana. Sai da Umm ma ta takura mata ?aukar abincin Hajjo ta kai mata sannan ta fita badan taso ba.
Tunda taga takalma birjik a ?ofar Hajjo taji kamar ta juya. Amma gudun kar Umm tai mata fa?a sai ta daure tayi sallama. Sai da aka bata izinin shiga sannan ta shiga da wata sallamar a bakinta. Duk samarin gidanne a she. Sai Rufaida da Hajjo. Nu'aymah ba wani shiri sukeyi da Rufaidah ba itama, dan ta girmesu, gata kuma da shegen son girman tsiya, shiyyasa take ganin sai dai su bita. Ita kuma Nu'aymah tsiwa.
A tare kawai tace dasu "Ina yinin ku". batabi takan dawa-dawa ya amsa ba ta nufi Hajjo daketa binta da kallon jin da?in ganin jikinta ya sake warwarewa.
"Hajjo barka da gida. Ga abinci inji Umm na".
"To takwara sannu kinji, yaya jikin naki?".
"Naji sau?i Hajjo".
"Alhmdllh ai haka akeso dama. Tun ?azun nake tsumayen ganinki amma shiru. Tashi ki duba a firiji na ajiye miki fura".
Sosai da?i ya kanata. Cike da ?oki ta nufi fridge ?in hajjo ta ?akko kofin furar tana sakema hajjo godiya. Har zata fice Naser ya kirata. Badan tasoba ta amsa tare da juyowa tana kallonsa. Ya sakar mata sassanyan murmushi tare da mi?ewa ya nufo inda take tsaye. Bayare da yay magana ba yay gaba da mata alamar ta biyoshi.
Bataso hakanba, amma sai ta bisa kawai gudun kar yaga kamar ta masa wula?anci. ?aya daga rumfar bunun da aka jera guda uku a harabar gidan ya nufa. Nu'aymah ma dai na biye da shi. Kujera ya ja mata baya yace ta zauna. Nanma bata musaba tayi yanda yake bu?ata. Sai da ta zauna sannan shima yaja wata ya zauna.
Yana zama Abdallah na isowa wajen kamar daga sama. Daga ita har Naser kallonsa sukai. Yayi kicin-kicin da fuska tamkar zai fasa ihu. Batare da yace dasu uffanba yaja kujerar ?anyan gefen Nu'aymahn ya zauna suka sakata a tsakkiya.
'Ikon ALLAH '. Nu'aymah ta fa?a a cikin ranta tana kallonsu da mamaki.

"Alhaji lafiya kuwa?". Naser ya fa?a a lalace yana kallon Abdallah. Murtani Yah Ab ya maida masa cike da dizgi. "Itace ta kawo haka".
"Humm!" Naser ya fa?a yana ?auke kansa daga garesa ya maida ga Nu'aymah da mamaki ke cigaba da nu?ur?usarta a zuciya.
"Kayi ha?uri ka bamu waje magana nakeson yi da ita Abdallah".
"Wannan isar ce kuma baka yiba. Duk abinda zaka fa?a mata inhar kasan ba mara ?yau bane ka fa?a a gabana mana".
"Mtsoww! Ai kasan baka isa sakani yin abinda banyi niyya ba. Nu'aymah tashi muje can..."
Batayi niyyar binsaba a yanzu. Tayi niyyar kawai tabar musu wajen. Sai dai tana yun?urawa zata mi?e Abdallah ya daka mata tsawa. "Koma ki zauna kona mareki!!". Ya fa?a yana ?aga hannun tamkar zai maketa.
?ata fuska sosai tayi tamkar zata fasa kuka. Dan ita kam sun sakata a tsaka mai wuya.
A fusace Naser yace, "Abdallah karka bari nakai bango da kai, wai shin ina ruwanka dani ne? Naga dai Nu'aymahr nan ba matarka bace balle kace zakama mutane iko. Idan ada kayi ikon saboda akwai al?awarin aure a tsakaninku yanzu saika tuna babu wannan. Ita ?in allura ce cikin ruwa mai rabo ka ?auka........"
"Nine mai rabon kuma insha ALLAHU!!, dan haka ka kama kanka karka bari a jimu da kai Naseer".
"Hhhhhh! Abin dariya. Sannu Abdallah ubana mai bani umarni. ai ka sani kayi sake tun a farkon dama, a yanzu kuma ta su?uce maka har avada. A da canma dan ba'a bata dama bane akaso mata auren dole da kai, amma sai UBANGIJI yay dubeta ya hana hakan....."
"Naser!!!"
Abdallah ya kirashi cikin ?araji da fusata tare da dun?ule hannu tamkar zai kai masa naushi. ?ar zabura baya Naser yayi kamar irin yaji tsoro ?in nan. Sai kuma ya kwashe da dariya ya kuma ?aure fuska duk a lokaci ?aya. "Oh to ko dukan nawa zakayi ne?!".
Bai gama rufe baki ba kuwa Abdallah ya kai masa naushi. Da sauri Naser ya du?e naushin yabi iska. Ya sake kai masa wani Baba malam da ke bayansu shi dasu Abbah ya daka musu tsawa.
"Kai!! wane irin shashanci ne haka kukema mutane a cikin gida da hankalinku?. Ko kunya bakujiba kuka zauna fa?a a gaban ?aramar ?anwarku, wannan ai rashin hankaline da sakarci".
Duk ?asa sukai da kawunansu kowa na huci. Abban su Adawiya yace, "Ku wuce muje ciki. Kema Nu'aymah shige".
Sum-sum ta wuce tana danne dariyar dake cinta a rai tun fara rigimar yayun nata. Tana shiga falonsu kuwa ta fashe da dariya. Da sauri Umm da Rabi dake a kitchen suna aiki duk suka le?o.
"K lafiyarki kuwa kike wannan dariyar ta rashin hankali?".
Hannu Nu'aymah tasa da sauri ta danne bakinta, da ?yar ta ha?iye dariyar tata sannan ta kalle su. "Wlhy Umm su Yah Ab ne suka bani dariya".
Batare da Umm ta tsaya jin ba'asi ba tai tsaki ta koma kitchen. Rabi kam sai ta nufota tana tambayarta wai miya faru?. Da sauri Nu'aymah ta ha?e fuska tare da zuba mata harara tabar wajen. Itama Rabin da harara ta raka Nu'aymahn, a ranta kuwa fa?i take, 'Zaki gane shayi ruwa ne yarinya, shegiya mai kama da ?a?an aljanu'.
Oho Nu'aymah batasan tanai ba. Dan tuni ta shige ?akinta. Sai dai itama a ranta tana matu?ar mamakin munafunci irin na Rabi. amma sam Umm ta kasa fahimtar akwai wani abu a zuciyar Rabi, dan ita ta jima da fahimtar hakan, harma a ranta tana zargi Rabin da ?aukar sirrin Umm tana fitarwa. Dan akwai ranar data ta?a ganinta bayan ?akinsu tare da wanda bata fahimci namiji ne ko mace ba suna magana. Sai dai kafin ta zagaya taga wanene ta iske sunbar wajen Rabin ma harta shigo ciki. Tun daga lokacin ta saka mata kahon zu?a. Taso fahimtar da Umm amma saita hauta da fa?a akan batason wannan halin banzar, dan Rabi a haife ta haifi Nu'aymah harma wanda ya fita. Kuma tun Nu'aymah na ?arama suke tare ita bata ta?a ganin wani abu mara ?yau daga gareta ba.
Tsaki tayi kawai da kauda zancen Rabi a ranta ta koma tuno su Abdallah. Haka kawai takejin al'amarin nasu na sakata nisha?i. Ba sai an fa?a ba kowa yasan tana tsananin son Abdallah, ?addara ce kawai ta shiga tsakanin al'amarinsu. Amma a yau sai kawai yanda Naser yay sai shima ya birgeta. Har takeji zata iya aurensa duk da zuciyarta bawai tana sonsa bane ba. Amma tunda ta ha?ura da Yah Ab zata iya maye gurbinsa da Naser ?in. Sai dai fa tasan lallai akwai ?ura a cikin faruwar hakan kuma.

¡ï¡ï¡ï

A ?angaren su Abdallah kuwa fa?a sosai su Baba malam sukai musu akan abinda suka aikata. Dan a gabansu mafi yawan rigimar ta faru shiyyasa basu bi takan jin yanda akai ba. Sai da baba malam ya tabbatar jikinsu yayi sanyi sannan ya ?ora musu da nasiha kuma, ya kuma sakasu bama juna ha?uri sannan suka sallamesu.
Suna fitowa kowanne ya wurgama ?an uwansa harara da jan tsaki.............?

Kuyi manage Please, inada ba?i??????.



_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________


Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????

Mamu gee??
MIN ?ALB!!????

Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????

Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????

Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????

?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????

09033181070

????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu??????*_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.


No. 34

............Abu kamar wasa sai ga ?aramar magana na neman zama babba. Dan kuwa dai rikici sosai ke wakana a tsakanin Abdallah da Naser akan Nu'aymah. Amma sai suka canja taku yanda iyayensu bazasu fahimta ba. A duk sanda Naseer yasa aka kira masa Nu'aymah sai Abdallah yazo ya tsare. Hakama duk lokacin da Abdallah ya bu?aci ganawa da Nu'aymah sai Naser yazo ya hana hakan ta hanyar zama tsakaninsu kamar yanda Abdallahn keyi.
Hajjo da mafi yawan rigimar a sashenta akeyi tana kallonsu amma tai kunnen uwar shegu da su kamar bata ganiba. Wani lokacinma da biyu take sakawa a nemo mata Nu'aymah ta zauna a sashenta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login