Showing 276001 words to 279000 words out of 325075 words
a haka kafin ta janye bakinta a cikin nashi suna maida numfashi. Batare data bari wani cikinsu ya sake magana ba ta kama hanunsa suka wuce bedroom. Sai da ta rakasa har bayi, duk da tana fama da kanta ta taimaka masa yay wanka. Da suka fito ?inma da taimakonta ya shirya sannan sukai salla.
Bata samu matsala da shi ba sai a wajen cin abinci, dan cayay mata shi ya ?oshi. Hankalin Nu'aymah ya sake tashi matu?a saboda ta kasa gane kansa gaba ?aya. da ?yar dai ta samu yaci ka?an ya sata ta ?akko masa magani ya duba wanda ya dace ya sha. Bedroom ya koma ya kwanta daga haka sai barci.
Gadon tazo ta sauna tai tagumi kawai ta zuba masa idanu tana kallonsa cike da tausayi da damuwa akan da tasa damuwar data fahimci yana son ?oye mata ne kawai.
*_KANO NIGERIA_*
A lokacin da madam Chioma ke can neman sa'a akan Yoohan anan kano su Little bee ne suka samu damar ?wamushe Rabi mai aikin su Aymah da ta zo yima Umm aika a kasuwa.
Tunda ta fito gida suke biye da ita batare data sani ba. Sai da tazo bakin titi domin tsallakawa taga mota a gabanta kawai. Kafin ta wani yun?uri aka fisgota ciki tare da da?e mata baki yanda ta kasa ihu. Daga ?arshe ma suka danna mata allurar data bugar da ita. Harko suka iso garin abuja bata sake sanin ina hankalinta yake ba, sai wayar gari tayi taga kanta a wani ?akin da bata saniba. Da matu?ar tashin hankali ta tashi tana ?an waige-waige, sai kuma ta fashe da kuka ganin da gaske dai fa ba?on waje aka kawota......
Tsawar da aka daka matane ta sakata sake gigicewa harda sakin guntun fitsari. Mur?e?en ?atone da iya gani kasan ya dam?i namiji ma sai ya shinshino ?amshin lahira bare ita mace da girma ya kama. Abincin hannunsa ya dangwarar a tebirin ?akin dake tare da kujera ?aya. Sai yololuwar guntuwar katifar da Rabi ta kwana agefe. Da tsananin kaushin murya yace, "An gaya miki nan gidan kuka ne. Karna dawo na samu wannan abincin da hawayen fuskanki". Ya ?are maganar da juyawa ya fita abinsa.
Tashin hankali iya tashin hankali Rabi ta shiga. Hakan yasa ta share hawayen nata ta zauna ta fara cin abincin data san bazata ?oshiba. Ga uban yaji a ciki na tashin hankali. Amma tasan inhar batacinba yunwa halakata zatayi. Mutumin nan kuma kashetama zai iyayi ?ila. Sai da ta kammala da kusan minti talatin, zuwa lokacin yajin ya gama wajiga rayuwarta sannan aka kawo mata ruwa rabin gora. Jikinta har rawa yake wajen ?auka ta sha, dan ita ka?ai tasan a tashin hakalin da take ciki game da cin yajin nan...
Haka aka ringa wajiga rayuwar Rabi har tsahon kwana goma. Tayi kuka harta rasa hawayen zubarwa. Sai da suka tabbaar tayi laushi iya laushi sannan suka nema su sanarma su Yoohan. Sai dai an samu akasi Yoohan ya wuce U.S sai Omar kawai ne ya amsa zaizo, dan jikin madam Chioma yayi sau?i sosai anma sallameta tun kusan kwanaki uku kenan, satinta ?aya a asibitin. Ranta dai na nan dan?are da damuwar rashin sanin inda Yoohan ya nufa da kuma rashin samun cikar burinta. Duk da tun a asibiti sun yake magana da Rebecca zasu koma gidan Bangaruta, sannan Marcy ma tace zata rakata wajen wani bokan a Lagos.
____________¡ï
Bayan isowar Umar kai tsaye office ?in Dawood sukaje. Sai da sukai zaman jiran Bilkisu Adam Makaho, mata ga Oga Jay sannan, dan itace oga kwata-kwata akan case ?in. Tana isowa kuwa suka amsa kira ta hanyar telephone.
Sun sameta a office ?inta. Bayan sun gaisheta ta basu iznin zama. Sam babu wasa tattare da ita, dan yanzu bayan miskilancinta girma ya ?aru ga daraja. Babbar Officer ce da aikinta ke girgiza sansanin duk wani mai kunnen ?ashi.
Batare data kallesu ba tace, "Dawood azomin da matar nan".
"Okay maa". Dawood ya fa?a da sauri yana mi?ewa. Kusan mintuna goma sai gashi ya dawo tare da Rabi dake wujiga-wujiga, dukta fita hayyacinta a kwanaki goma kacal. Kuma babu zagi babu duka. Zai gurfanar da ita a ?asa Bily ta hanashi. Wata kujera dake can gefe ta bashi umarnin ya bama Rabi ta zauna. Shi dai Omar nata kallonsu ne da mamakin ganin yanda Rabi ta koma. Gashi kuma ko ?warzanen duka shi dai bai gani a jikinta ba. Itako bama ta gane Umar ba saboda a jigacen da take.
Little bee ce ta shigo bayan tayi knocking an bata izini. Tai salute ?in mahaifiyar tata kuma ogarta a wajen aiki kafin ta ajiye takardun hannunta a tebir ?in. Takardun Bily taja gabanta ta duba kafin ta ajiyesu gefe ta kalli Rabi.
"Nasan dai zuwa yanzu kinsan a inda yake ba wajen wasan nanaye bane. Dan haka ya rage ruwanki nutsuwa ki bamu duk amsar tambayar da zamu miki, ko kimana ?arya".
Muryar Rabi na rawa tace, "In ALLAH ya yarda bazanyi ba ranki ya da?e".
"Wannan ya rage naki".
Bily ta fa?a cikin halin ko in kula tana sake ?aukar takardun da Little bee ta shigo da su. A gaban Rabi ta diresu dai -dai lokacin da fuskar Yoohan dake zaune a office alamar yana a asibiti ta bayyana a cikin lap-top ?in da Omar ya ajiye inda Yoohan zaiga kowa dake office ?in.
"Wannan takardun bayanai na duk abinda ke cikin wayarki. Randa kika sayi layi, randa kika fara ?orashi a waya. Sau nawa kina canja shi a wasu wayoyi. Mutanen da kika ta?a kira ko suka kiraki duk akwai bayanansu anan. Dan haka ki nutsu sosai".
"In ALLAH ya yarda ranki ya da?e".
Kallon sashen da Dawood da Little bee suke Bily tayi, kafin ta kalli lap-top ?in. Kai Yoohan ya risinar cike da girmamawa ya gaisheta. Itama ta amsa masa da kulawa kafin ta nuna masa Rabi.
"Ina fatan kana ganinta da ?yau?".
"Yes maaa!".
Duk da Rabi ta kalli fuskar lap-top ?in itama bata kawo komaiba, tadai ga kamar hoton mijin Nu'aymah, kafin tunaninta ya fa?a?a Little bee ta katseta da fa?in, "Minene sunanki?".
Murya na rawa tace, "Rabi?".
"Shekararki nawa kina aiki a gidan Sheikh Soorajidden Hashim Jibiya?".
"Goma sha takwas. Dan an kainine lokacin matarsa nada tsohon cikin dake wahal da ita dan na taimaketa".
"Kin ta?a aure?".
"Eh na ta?ayi harda yarana biyu".
"Keda ke aure miya kaiki gidan aiki har tsahon wannan shekarun?".
"Ranki ya da?e ai auren ya mutu ne a wancan lokacin. To domin neman na kaina saina samu aikatau ?in dan nayi saboda iyayena duk sun rasu ni marainiyace".
"?wa?ayin zama gidan masu ku?i yasa baki sake tunanin sake ?ara aure ba kenan?".
Shiru tayi kanta a ?asa ta kasa bada amsa. Shima Dawood da yay maganar sai ya shareta da ga haka ya sake jeho mata wata tambayar.
"Waye ya kaiki gidan?".
A take ta ru?e jikin na rawa, sai in ina take ta kasa bada amsa. Hakan yasa Dawood daka matsa gigitacciyar tsawa. Fashewa Rabi tayi da kuka. "Dan ALLAH ku gafarce ni zan fa?a".
Babu wanda ya tanka mata. Sai bindiga da little bee ta ciro a gefen ?ugunta ta dire a gaban Rabi. Hakan yasa ta kuma diriricewa. Cikin hadiye kukanta tace,
"Ranku ya da?e ni bansan ainahin wadda tasa aka kaini gidan ba. amma naje ta hannun wata matace amma yanzu ALLAH yay mata rasuwa".
"Oho, idan na fahimci amsar nan taki kenan dama an kaiki gidan ne da wata manufa? Ba wadda kike a wajenta bace tasa aka kawoki gidan!!".
Yoohan yay magana a matu?ar zafafe. Maimaita mata Dawood yayi da hausa. Dan duk da Yoohan ya ha?a da kalmomin hausa a maganar Rabi bata fahimta da ?yau ba. Amma shi Alhmdllh yana fahimtarta sosai tunda jin nasa yafi fa?i da baki.
A take Rabi ta ?ara rikicewa, dan har ga ALLAH tazatafa hoton Yoohan ?inne kawai a wajen. Suma dai su Bily yanda yay maganar duk sai da ya sakasu kallonsa. Tebir ?in Little bee ta daka da hannu, da tsawa tace, "Ki basa amsar tambayarsa malama kin ?ata mana lokaci".
Jikin rabi na cigaba da rawa tace, "Ranka ya da?e ba haka nake nufi ba. Ni dai kawai an kawonine na kula da mai ciki, daga haka babu wani dalili dana sani na rantse muku da girman wanda ya halicceni".
A karan farko taji saukar mari mai gigitarwa a fuskarta. Kafin ta dawo hayyacinta Dawood ya ?ara mata wani. Sannan kuma Bily dake zaune duk tana kallonsu ta hanata kuka. Dole Rabi ta ha?iye hawayenta sai ajiyar zuciya.
Dawood yace, "Inhar zakiyi mana ?arya to zakiyita amsar irin wa?anan marukan babu ?a??autawa. Wa kikema aiki a gidan?".
"Wlhy yalla?ai iya gaskiyata nake fa?a muku. Bani yima kowa aiki sai Hajiya Firdausi matar Sheikh Sooraj ?in".
Sai a yanzu Umar yay magana. "Eh ansan dama ita kikema aiki a zahiri. a ba?ini kuma akwai ogarki mai sakaki shiryamata sharri ita da tilon ?arta. Bayan ?yautatawar data dinga miki a rayuwarki na tsahon shekaru goma sha takwas".
Dawood ne ya sake fassara mata. Dan haka cikin rawar harshe da kuka mai cin rai tace, "Na rantse da ALLAH. wlhy tallahi ban ta?a cutar da Hajiya Firdausi da zuriyar ta ba. Ko Nu'aymah da muke yawan fa?a wani lokacin ina takalartane kawai wlhy saboda nasan bata barin saita kwana. Amma bada wata manufaba. Ko a mafarki bana fatan na cutar da wa?an nan bayin ALLAH ai balle a zahiri".
Cike da ?aurewar kai suka shiga kallon juna. Amma duk da haka bayan Dawood ya gama sanarma Omar abinda ta fa?a sai Umar ?in ya bada vr ?in nan na kwanaki da sukaji tare da Nu'aymah. Aka kuma tabbatar mata a wayar wanda aka samu.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni Rabi. Wlhy wlhy kinji na rantse ni ban ta?a waya da mai aikin Nu'aymah ba. Hasalima sam ban santaba tunda randa akazo za'a wuce da ita abuja a sashen hajjo Umm taje ta sameta itama. Yanzu haka ko zaku kasheni bazan iya nuna fuskartaba balle harna samu Number ta nayi waya da ita akan Nu'aymah. To niko idan ta fa?amin halin da Aymah ke ciki gidan aurenta ribar mi zanci bayin ALLAH?".
Tsawa little bee ta daka mata. "K bama son rainin hankali. Idan kince bake bace wa?an nan lambobin dake akan wayarki harda ta Uwaliya ?in na uwar waye? Wa kuma ya sakasu da har zaiyi zaman magana da su a wayarki batare da kin saniba?".
"Wlhy iya gaskiyata nake fa?a muku. Ni yanzu haka ko waya zanyi ma sai naba Muhammad ya dubamin lamba. Dan shine kemin sebi idan ko zansa lambar wani ?an uwana. Idan kuma zanyi kira shima ke dubamin abinda ya samun dan banyi boko ba. Da Nu'aymah ko Adawiya kemin, to sai suyita jamin rai, shine na koma bama Muhammad ganin ya iya. Amma ni lambar ma ?an gidan bata kowa gareniba wlhy".
Hannu Dawood ya ?aga zai ?wa?a mata mari Bily ta dakatar da shi. Dan ita duk shirun datai musu nazarin komi takeyi. sannan kuma Jay ma duk yana saurarensu daga office ?insa ta hanyar na'ura. Shinema yay saurin cema Bily ?in kar Dawood ya mareta yanzun ta hanyar abibda ke a kunnenta da su basu fahimta ba.
Dakatawa kuwa Dawood yayi yana huci. Bily dake kallon Rabi cike da nazari tace, "To amma ranar da Nu'aymah tai bleeding ko zamu iya sanin miya faru? Dan bincikenmu ya nuna mana kece kika bata abu na ?arshe tasha a gidan. Daga haka ta fara ciwon ciki sai jini kuma ya ?alle".
Shiru Rabi tayi tana tunani dan tama manta. Sai zuwa can kuma tace, "Lallai kuwa ranki ya da?e kamar anyi hakan. Ta sakani na dafa mata ruwan shayi ba?i".
"Kenan a ciki kika saka mata maganin zubda jini da aka ?auka cikine ta zubar??"..............?
*_Tofa masu karatu man kai na fa zai fara malalewa a dalilin amsoshin Rabi, nama rasa mizan tunano kuma. amma bari mu bita muji wace amsa zata bada a gaba??????._*
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[7/3, 1:13 PM] +234 901 860 0202: *_LITTAFIN nan na ku?i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki ha?ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki ya?a mana????_*.
No. 71
..............Saurin zaro ido waje Rabi tayi tana mai girgiza kanta. "Wlhy ba haka bane ranki ya da?e. Mizaisa na aikata hakan ga Nu'Aymah. Bayan sikari da Lipton sai ruwan dana dafashi da shi ne kawai a ciki".
Wani irin tafasa zuciyar Yoohan takeyi daga can, ji yake kamar ya ziro hannu ya sha?o wuyan Rabi ta cikin system ?in, sai dai babu dama.
Little bee zatai magana Bily ta dakatar da ita ta hanyar ?aga mata hannu. "Inaga ku maidata inda aka ?akkota tukkunna".
Babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu. Sai tasa ?eyar Rabi da aka saka wani jami'i yay tana kuka aka maidata inda aka ?akkota.
Bayan fitarsu ajiyar zuciya bily ta sauke tana rubuce-rubuce. Kusan mintuna biyu kafin ta ?ago ta kalli Yoohan da zuciya ta kume daga can. "I'm sorry Dear wannan case ?in duk yanda kuke tunaninsa ya wuce haka. Akwai wani abu dana fahimta dangane da wnanan matar wanda sam na kula ku duk baku gansaba. Kodai ya kasance amfani akeyi da ita a gidan batare da ita kanta ta sani ba. Kokuma tana kan sani ta fi yarda ta shanye duk wata azabar data fuskanta anan danta rufama wancan asiri. Kokuma an mata garga?i mai girma da tsoratarwa akan sanarwa tun ba yanzuba.
Dole wannan wayar tata na bu?atar sabon bincike. Sannan wa?annan voice recording ?in suma zamu sake bincike sosai a kansu, idanma har ba'ita ?in bace zamu gano ainahin mai muryar insha ALLAHU".
Dukansu sun fahimceta. Hakan yasa Yoohan tabbatar musu da shima zai shigo Nigeria zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, kuma harda Nu'aymah. Dan ya fahimci lallai wasan na gaske ne.
_____________¡ï¡ï
Tunda ya shigo gidan yau taketa faman binsa da kallon mamaki. Dan tun randa ya dawo daga 9ja ta kasa gane kansa gaba ?aya. Kullum yana cikin ?unci da tunani, baya son yawan magana, sai su yini su tashi har dare magana sau biyar bata shiga tsakaninsa da shi ba. Tayi tambayar harta gaji tayi fushi ta ?yalesa. Daga ?arshe ma sai ya koma fita asibiti. Idan ya tafi tunda safe sai tayi barci zai dawo. Ta fahimci yana hakane duk dan karta cigaba da masa tambaya akan abinda ke damunsa. Dan idan ya fita yata yawan kiranta kenan wai yaji yaya take ita da Unborn ?insa.
Hakan data ?ara fahimtane ya sata sake tattare maganar damuwar tasa ta watsar gefe. to shinefa a?an kwanaki ukun nan ya fara sakin jikinsa yana kuma dawowa gidan kafin tayi barci. Yau kuma abin mamaki sai gashi kusan ?arfe uku ya shigo mata.
Yanda batai maganaba shima baiyiba. Sai dai kallonta yake cike da tausayawa a gareta. Tana zaune ne a kujera ta mi?e ?afafunta bisa centre table ?in falon. Sai filo ?arami a cinyarta ta ?ora lap-top a kai tana sauraren lecture da akeyi daga can school ?insu.
A ?an kwanki goma sha hu?u ?in nan duk ta rame saboda damuwarsa da itama ke damunta. Hakan yasa cikin nata ?an watanni bakwai sake fitowa sosai gamai kallo. Musamman yanzuma da take sanye da skirt