Showing 204001 words to 207000 words out of 325075 words

Chapter 69 - SARAN-BOYE COMPLETE

20 Jul 2024

29181

Idanu Yoohan ya lumshe a hankali saboda jin yanda taja sunansa akan harshenta, ya saka duka hannayensa ya rungumeta a jikinsa da ?yau dan jikinta wani irin karkarwa yakeyi. A haka ya ?ora bakinsa saman kunnenta ya shiga hura mata iska a ciki. Hannayensa kuwa na shafa bayanta. A hankali ta fara sassauta surutan da takeyi, rawar jikinta na raguwa. Sai kuma ta koma sauke ajiyar zuciya hawayenta dake fita masu ?umi na saukar masa a ?irji.
A haka ta sake sumewa, Hankalinsane ya tashi da wannan sumar, dan sumace da yake da tabbacin mai ha?arice a gareta. sai ji yay ta masa nauyi kawai. Ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na babu adadi, hankalinsa na ?ara afkawa cikin ?ololuwar damuwa. Ya bu?e idanunsa da suka rine da ja yana kallo ahanlinsa dake zagaye da su a cikin ?akin. Baice komai ba, dan bayason susan komai ?in, sai kwantar da ita da yayi a hankali yaja bargo ya rufa mata, tare da ?aukar remote ?in ac dake a durowar gefen gadon a ajiye ya ?ara gudunsa saboda sanyin da yasan tafi bu?ata a yanzun.
Sake maida hankalinsa yay gasu Momy yana musu alamar suje waje. Babu wanda yace komai duk suka fara fitowa shima ya biyo bayansu yaja ?ofar ya rufe mata dan dolene yaje ya nema mafita.
Dukansu babu wanda baibi jinin Gebrail daya fasa kai ba da kallo. Yoohan da yay ?arshen fitowa ya jinjina kansa kawai yana kallon jinin da tunani barkatai a ransa.
Momy Favour ce ta fara fa?in, "Wai miya sameta ne haka John?".
Kansa ya girgiza. Muryarsa na nuna alamun damuwa yace, "Aunt ban saniba nima. Ihunta kawai naji dai-dai muna shigowa gidan nan. Sai dai da alama wanine ya shigo ya tsoratata da duhu dan batason ganin duhu".
Kallon-kallo suka shigayi a tsakaninsu. Momy tace, "Amma babu kowa a gidan nan sai ita da su Blessing. Dan muma shigowarmu kenan daga church muke. Joy da Gebrail suna school. Miracle kuma bata dawo daga wajen aiki ba har yanzu da alama".
Batare da Yoohan yace wani abuba ya dubi Blessing da Uwaliya. Cikin sauri Blessing tace, "No Sir. na rantse da ALLAH muna bamusan miya sameta ba. Dan bamufi 5minutes da shigowaba mukaji ihunta. Ni inama backyard ina kwashe kayan dana shanya danai wanki ?azun. Uwaliya kuwa tacemin zataje tai salla sai dai ban saniba ko......."
"Wlhy nima salla na shigayi banje wajentaba saboda ganin zan makara". Uwaliya tai saurin tarar numfashin Blessing ?in.
Hannu Yoohan yasa a goshinsa yana ?an murzawa. Sai kuma ya furzar da huci mai zafi. Batare da ya sake magana ba ya nufi ?akinsa kawai.
Suma duk jan ?afafu sukai gwiwa a sage suka fita harsu mama debora da suka gaza cewa komai. Su Victoria kam dama sunsan idan Yoohan na magana da iyayensu baya bu?atar cewarsu, shiyyasa basu tofa ko 'A' ba a maganar. Daka gansu dai kasan tausayin Nu'aymah ya cika musu zukata.

Kowa ?akinsa ya nufa, sai dai Momy na shiga nata taci karo da Gebrail cikin toilet yana le?o kansa. Yanajin motsin za'a bu?e kofa yay saurin komawa zai rufe ?ofar. Da sauri momy tace, "Kai waye anan?".
Jin muryar momynsa ne ya sakashi fitowa jikinsa na rawa. Yay saurin fa?in, "Momy shiii!! Karkiyi magana Please".
Sosai gabanta ya fa?i ganin yanda jikinsa ke ?ari. Ga jini ya ji?e handkerchief ?in daya ?ora a goshinsa inda yaji ciwo garin gudu. Saurin ru?o masa hannu tayi suka koma cikin toilet ?in itama nata jikin yana rawa. Ta maida ?ofar ta rufe tana magana a matu?ar tashin hankali. "Gebrail! Badai kaine ka aikata ba?".
Hawaye na zuba masa a idanu jikinsa na karkarwa yace, "Momy idan Brother John yasan nine kasheni zaiyi. Na rantse tsautsayine momy kuma ban mata komai ba. Na rungumeta ne kawai na kashe wutar ?akin shine tamin ihu".
Kai momy ta dafe tana fa?in "Oh my lord". Sai kuma ta kama kafa?un Gebrail ta shiga girgizawa. "Gebrail baka da hankali. matar John? Bayan kasan halinsa a gidan nan".
"Momy na rantse tsautsayi ne, ina sonta da gaba ?aya zuciyata. Amma nasan Brother Yoohan zai halakani idan ya sani, kasheni zaiyi da hannunsa momy, ki taimakeni karki bari ya gane nine momy".
Kuka yake sosai jikinsa na karkarwa. Jansa tayi jikinsa ta rungume duk da itama harga ALLAH a mugun tsoracen take. Dan tasan shirun da Yoohan yayi tabbas bazai zama na banza ba. Sai da taji bugun zuciyar Gebrail ya?an dai-daita sannan ta ciresa a jikinta ta zaunar akan bathtub. Fita tai ta ?akko First aid box ta dawo toilet ?in bayan ta murzama ?ofar bedroom ?inta key. Zuwa tai tai masa dressing wajen. Ta mi?e tana fa?in, "Kayi wanka zanje na ?akko maka kaya a ?akinka, dolene kabar gidanann a daren nan Gebrail. Kaje ka kama hotel koka koma cikin hostel ?in makarantarku har sai wannan ciwon da kaji ya warke. Inba hakaba sai Yoohan ya gano kaine dan kowa yaga jinin daka zubar a sashen. Ka kuma san shi mutumne mai tsanani basira akan duk abinda ya ?wafa".
Kansa ya ?aga mata yana fa?in, "Thanks you momy, thanks you so much".
Bata sake cemasa komaiba ta fita tana tunanin yanda zata shiga ?akinsa ta ?akko kayan cikin dabara ba tare da kowa ya fahimta ba.

¡ï¡ï¡ï¡ï

Tabbas yau Gebrail ya sako Aymah cikin mummunan matsala. Musamman daya kasance a irin wannan lokacin ana lalla?a lafiyar tata ne, domin aikin da Yoohan keta kaikawo wajen ganin da shine za'ai mata shi saboda ha?arinsa. Sai dai Alhmdllh, isowar Yoohan ?in akan lokaci ya zama rahama a gareta. Duk da shima kuwa dawowar tasa bata lafiya bace ba. Ciwonsa ne na rashin barci ya dawo, yau kwanakinsa uku kenan baya iya barci, koya ?aukesa saboda addu'a da yake yi baya gaza mintuna ashirin yake farkawa. Ganin al'amarin nasa na ?ara fa?ine ya sakashi tattarowa ya taho gida. Sai gashi kuma ya iske wani tashin hankalin da shima ya nema birkita tashi ?walwar kan.
Duk yanda yake tunanin bama Nu'aymah taimako da kansa anan kafin wa'adin da za'ai mata aikin ya fahimci babu mafita. Dole ya yabar ?asar nan da ita a gobe idan ALLAH ya kaimu, dan inhar ta wuce awa saba'in da wani abu komai zai iya faruwa da ita. Shi a yanzu hakama ya rasa wane taimako zai bata. Duk wata basirarsa ta likitanci ta kufce, man kansa ya tsiyaye tas. Waya ya ?auka ya shiga nema wata abokiyar aikinsa Dr Shukurah dake anan General hospital na Abuja. Dan itama likitace mai ?wazo da sanin makamar aiki. Gata babbar mace kuma dan momy ma Yoohan ke kiranta ita kuma tana cemasa Son. Tun ganinta da shi na farko lokacin an turasa bautar ?asa a asibitinsu kamanninsa da yaron ?anwarta yaja hankalinta. Ta kuma kasa ha?uri sai da tai maganar kamannin nasu. Sai dai shi Yoohan har yanzu bai ?auki abin da muhimmanci ba, saboda bai ta?a ganin wancan datake fa?in suna kamar ba. Amma tayi al?awarin wataran sai ta ha?asu dan wancan duk da ba'a Najeriya yake ba.
Duk da Dr Shikurah ta tashi da ga aiki yanda taji muryar Yoohan ?in sai yay matu?ar tada mata da hankali. Dan haka ta nema alfarmar mijinta akan zataje. Da yake mutumne shi mai sau?in kai sai ma yace bara ya kaita da kansa tunda darene duk da bawai can sosai ba.
Kasancewar tasan gidan su Yoohan ?in dama basusha wani wahalar neman address ba. Cikin mintuna ?alilan sai gasu sun iso. Solomon ne yay mata iso cikin gidan. Har lokacin su momy na tsaye a ?ofar sashen cirko-cirko kowa da abinda ya damesa. Dan da farko basu ?auki al'amarin da zafi ba. sai da sukaga yanda Yoohan ?in ke a birkice ne yanata shige da fice suka sanfa aiki ne babba kenan.
Sama-sama ya iyayma Dr Shikurah bayani akan matsalar Nu'aymah. Itama sosai hankalin nata ya tashi ta shiga fa?a akan dan miyasa za'ai gangancin sakata a duhun? Bayan kuma yana cikin abunda zai iya burkita ?wa?walwar ta a lokaci ?aya babu jinkiri. A yanzu hakanma basu da tabbacin ba'a samu matsalar da suke tsoronba. Shi dai Yoohan ma ya gaza cewa komai. Sai dai idanunsa sun sake ka?awa jazur. Yana tsananin tausayin yarinyar nan fiye da tunani. Shiyyasa yake ta lalla?a yanayin nata har kwanakin da zasu wuce ai mata aikin su cika. Amma dan tsabar zalunci an samu wani yazo yana neman ?wa?e masa aiki. Dolene wanda ya aikata wannan ya fuskanci mummunan hukunci daga garesa a gidan nan koda kuwa wanene. Amma a yanzu bashi da lokacinsu sai matarsa ta dawo hankalinta insha ALLAHU.
Dukkan wani taimako daya dace Dr Shikurah ta bama Aymah, dan yau ko allurar nan da yake mata biyu akai mata, dama uku ce ta rage. Ta kuma tunatar dashi akan dolene kafin nan da awanni saba'in aimata aikin da ya sanar mata sun gama booking.
Kansa kawai ya iya jinjina mata, tare da godiya akan ?o?arinta. Daga haka yayo mata rakkiya ta wuce.
Sai a lokacinne yacema su Momy ya kamata suje su kwanta abinsu tunda da sau?i. Dama a ?age Momy take da kowa ya shige ?in. Dan har yanzu Gebrail na ?akinta neman hanyar da zai gudu take bukata.

Dole ranar a ?akin ya kwana. Dama gashi ba barci yake iya yi ba. Sai dai sa?anin baya da yake kwana cikin ?unci da ba?in ciki yanzu ba haka baneba. Zuciyar tasa kam a ?untacen take, ga ciwon kai mai tsanani. sai dai kuma ya raya kaso biyu bisa uku na daren ne da nafilfili yana mi?ama UBANGIJI kukansa. Sauran kaso ?ayan kam duk akan duba na'urorin da aka sakama Aymah ne lokaci-lokacin domin duba yanayin tafiyarsu, sai kuma neman hanyar da zai matso da maganar aikin da za'ai mata kafin wa?anan awannin su cika. Alhmdllh babu wata damuwa har suka wayi gari. Bayan yayi sallar asuba toilet ?inta ya shiga yay wanka. Sannan yaje ?akinsa yay shiri ya sake dawowa. Wayarsa ya ?auka kamar zai kira baba malam sai kuma ya fasa bisa wani tunani da yayi.
Dubata yayi, ya tabbatar kozata iya farkawa sai nan da wasu awa kamar hu?u. Insha ALLAH kuma zuwa sannan zai kammala usirinsa ya dawo. Hannunta ya kama a hankali ya sumbata, kafin ya shafi kumatunta yana mai mata addu'ar samun lafiya mai ?orewa. Daga haka ya fito. A falo ya iske Uwaliya na gyarawa. Ta gaidashi da girmamawa tana tambayarsa mai jiki. A takaice ya amsa mata. Tare fa?a mata ta ajiye aikin taje ta zauna a ?akin Nu'aymah. Ta amsa masa da to, ta ajiye kayan sharar ta nufi ?akin shi kuma ya fita.
Masu gidan duk suna ?aki, ma'aikatanne kawai ke aikin gyara gidan. Papa baya nan yayi tafiya shima.
Har Yoohan ya nufi downstairs yana amsa gaisuwar da ma'aikatan gidan ke masa sai kuma ya dawo. ?akin Momy ya nufa kai tsaye. Ya tsaya a bakin ?ofa yay knocking. Sai da ta bashi izinin shiga sannan ya shigo. Rikicewa tai, dan a bazata ta gansa. Duk zatonta su Victoria ne sukazo mata sallama zasu wuce school. Ta tura wayar da take amsawa ?ar?ashin filo cike da rashin gaskiya. Shi dai da yake hankalinsa ba a jikinsa yake ba yanda ya kamata baima fahimci halin da take ciki ba. Ya gaidata da girmamawa kamar yanda ya saba. Sai dai yanda ta amsa masa murya na rawa da kuma kamar a daburce ne ya bashi mamaki.
"Mom are you ok? Hope you are well?".
"Y..yes yes Son. It is Okay. Mika gani?".
"No, dama banga Gebrail bane tunda na dawo. Where is he?".
Ba ?aramin bugawa ?irjin momy yayi ba, harda taune harshenta saboda a bazata tambayar tazo mata. Ta shiga girgiza kanta tana fa?in, "Uh...Uhm ai yayi tafiya ne?". Tai maganar da sosa ?eya tana wani washe ha?wara.
"Tafiya? Where did he go?". Yay maganar yana tsuke fuska da ?yau.
Sosai Madam Chioma ta ?ara rikicewa. dan gani take kamar Yoohan ?in ya shinshino wani abune. da ?yar ta iya control ?in kanta tace, "Ban sani ba Yoohan. Dama inason ka dawo na zauna da kai akan lamarin Gebrail. Rashin jinsa ya fara yawa. Tunda suka shiga University ?in nan ?ara kangarewa yakeyi". Yanda ta ?are maganar ne tamkar zatayi kuka ya saka Yoohan sassauta muryarsa yana sauke nannauyan numfashin ?acin rai. Ya cije lip ?insa yana mi?ewa daga zaman da yayi. "Babu damuwa ki barni da shi. amma Mom kema harda laifinki. Kece ke zama da yaran nan fiye da kowa. Amma miyasa idan kinga irin haka ta fara faruwa bazaki sanar min ba. Yanzu daban tambayaba maybe harna sake barin ?asar bazaki sanar minba. Zanci ubansane. Tunta bayaji zaiko cigaba da karatu a Nageria".
Daga haka ya fice batare da ya sake bata damar cewa wani abuba. Itama da?in hakan taji, dan inhar suka cigaba da zama a haka zata tonama kanta a siri, zata kuma iya aikata abinda ke ranta game da yaron nata. Dan a yanayin da yake na sanyi-sanyi yau sai ya wani tada mata tsuminta. Ji take kamar tai.....
Ta matse idanu da ?arfi tana fa?awa saman gadon batare data iya ?arasa ru?a??en tunanin nata ba. Oho shi Yoohan ma baisan tanayiba. Dan har sun fice daga gidan shi da guards ?insa.

__________________

Tunda Yoohan yabar gidan yaketa faman shigi da fici. Duk da azabar ciwon kai dake damunsa haka ya jure yanata kai kawo ko takan breakfast bai bi ba. Baima tunawa da yunwar duk da kuwa jiya ko bu?a bakin kirki baiyi zaman yiba tunda ya kai azumi.
Sai wajen sha biyu saura ya kammala duk abinda ya dace. Ta office ?in Abban Abdallah ya biya. Suka tarbi juna cike da girmamawa da surukuta. Anan ne Abba ya fahimci kamar baida lafiya. Sai dai bai tambayesa kai tsayeba sai a cikin hikima. Yoohan ?in bai ?oye masa ba ya sanar masa.
Kai kawai Abba ya dinga jinjinawa. cike da damuwa yace, "Yahya anya kuwa a lamarinka babu sihiri?". Yoohan bai fahimci abinda Abba ke nufi ba. Dan haka ya ?ago rinanun idanunsa yana kallonsa. Kai Abban ya sake jinjinawa. Cike da tabbatarwa yace, "Tabbas akwai sihiri a wannan al'amarin. Amma karka damu zanyi magana da Yaya. Insha ALLAH komai zai wuce. bara yanzu nai maka kamu sai na rubuta addu'oin nan idan kaje gida mamana ta zauna tayisu dan duk ta sani. Ka fara shansu su zama kamar ruwa a gareka".
Godiya Yoohan yay masa. amma sai ya sanar masa ma ai zasu wuce da Nu'aymah ne a yau da daddare dan jikinta ya motsa. Sai dai bayason baba malam ya sani da wuri har sai sun isa can dan karya tada hankalinsa.
Cikin tsananin damuwa Abbah ke jera mata addu'oin samun lafiya. Ya ?ora da fa?in, "Duk da nasan Yaya bazai shiga ?imuwar da kake hasashen ba na goyi bayan a ?oye masa ?in har sai kunje. Amma insha ALLAH muma zamu biyo bayanku ko zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu ne. ALLAH ya ?ara muku lafiya damu baki ?aya".
Da amin Yoohan ya amsa masa.
Baibar Office ?inba sai da Abba yay masa addu'oi sosai, har a cikin ruwa ya bashi ya sha sannan yay masa sallama ya wuce yana maijin ?aunar wa?anan bayin ALLAH har cikin ?asan zuciyarsa.

¡ï¡ï

Daga wajen Abbah gida ya koma. Inda ya iske farkawar Nu'aymah kenan kamar an auna da dawowar tasa. Uwaliya kawai ya iske a ?akin kamar yanda ya garga?eta karta bar kowa ya zauna dan ba'a bukatar yin hayaniya komin kan?antarta. Hakan yasa ?an gidan duk wanda yazo ya dubata sai ya fice baya zama.
Saurin ?arasawa yay cikin ?akin. Hakanne ya saka Uwaliya dake ri?e da hannunta tana jera mata sannu saurin matsawa baya ta bashi waje. Zama yay a bakin gadon kusa da ita. Ya cire duk na'urorin dake manne da kanta da kunne. Yanayi yana addu'ar neman nasara ga UBANGIJI.
Batayi maganaba, sai dai hawaye dake silalo mata a kan fuska a hankali. Sake matsawa yay sosai kusa da fuskarta, ya dafa hannayensa a gefe da gefenta yana mai tsurama hawayen nata ido. Da ?yar ya ha?iye abinda ya tokare masa ma?oshi, ya ?an furzar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login