Showing 12001 words to 15000 words out of 325075 words
su Baba malam basu sake maganar aureba har Momyn Abdallah ta haifi cikinta namiji, wanda aka maidama suna Omar, bayan kamar wata biyu da haihuwarta amaryar Musbahu ma ta haihu mace, ita kuma taci suna Jameela.
Hajjo nasan su Baba malam su ?ara aure, amma kuma tausayinsu yasa ta kasa takura musu, sai dai ta cigaba da binsu da addur fatan samun mata nagari da zasu maye musu gurbin matansu. Ansha kawo musu matan aure har gida, musamman kasancewarsu malamai kuma masu ku?i Alhmdllh. Sai dai basu ta?a amsaba, dan basu farfa?o daga magagin rashin family ?insu ba.
Bayan shekaru biyu da rasa iyalansu ?watsam ALLAH ya ha?a Baba malam da Firdausi (Umm) a wajen wani walimar yaye ?aliban makarantar BUK. Tunda ya ?yalla ido akanta bai ?aukeba, duk inda ta shiga ta fita idanunsa a kanta, gashi babu damar mata magana saboda sune manyan ba?i a wajen, hasalima shine yay lecture wa ?aliban mai ratsa jiki. Inda itama anan Umm ta mutu ason wanda tasan ko kallo batama ishesaba, amma kasancewarta mace miskila ta gaske, kuma mara son yawan magana sai ko a fuska bata nunaba.
Kamar yanda Firdausi (Umm) ta mutu akan son Malam Sooraj Hashim haka babbar ?awarta, aminiyarta Fauza (Addah) itama ta mutu akansa lokaci guda, sai dai itama ?in dai bakinta bai furtaba, sai dai kasancewarta mace mai faranfaran da barkwanci dason jama'a sai taita yabashi har Firdausi ta gaji tai mata ?orafin ta isheta. Dariya tayi a wancan lokacin, dan itace ka?ai ta iya zama da Umm kasancewarta mace mai bahagon hali, ga rashin son wasa, dan sam Umm bata da fara'a, bakuma tason yawan wasa kamar ?awarta Fauza (Addah).
Ahaka taro ya tashi lafiya Fauza da Firdausi na begen abinda basa tunanin zasu samu a zukatansu, sai dai kuma abinda basu saniba shine Malam Sooraj tunkam yabar makarantar yasa ake bibiyar masa Umm, har aka tashi kowa ya kama gabansa ana binsu a baya har gida anguwarsu. Mai bin nasu yana ganin inda suka shiga ya koma da baya yaje ya sanarma Malam Sooraj Hashim. Baba malam yaji da?i matu?a, bai kumayi ?asa a gwiwa ba ya sake sakawa aka bincika masa mahaifin Firdausi (Umm).
Firdausi (Umm) da Fauza (Addah) ?awayene konace aminai. Anguwarsu ?aya, hasalima katangarsu ?aya, sannan iyayensu Aminaine tun zamanin ?uruciya. Hakanne ya saka iyayensu matama zama ?awaye na ?ut da ?ut da babu maijin kansu. A tai?ace ma dai sun zama ?an uwa. Umm itace ta sakama Fauza suna Addah, saboda sunan babbar yayarsu kenan itama, suna kiranta Addah, shine itama sai take cema ?awarta Fauza Addah, ahankali suma sauran ?an gidan suka koma kiranta Addah.
Mahaifin Fauza (Addah) yafi na Firdausi (Umm) arzi?i, dan yana ?aya daga cikin ?an kasuwar leda da akeji dasu a cikin kano a wancan lokacin, sannan kuma ?an boko ne sosai. Mahaifin Fauza (Addah) shike ?auke da nauyin karatun Umm tun daga firamare har zuwa jami'a. Dan yayun Umm duk iya aji shida na firamare babansu ya ciresu yay musu aure. Itako tana bala'in son karatu, musamman da taga Fauza (Addah) zata cigaba dayi, tata ro?on baban ya barta amma ya?i, yace itama aure zai mata kamar yayunta. Hankalinta ya tashi, dan haka ta nufi mahaifin Addah ta sanar masa. Shine ya lallasheta, ya kumace ta kwantar ta hankalinta indai karatune zatayi insha ALLAH, shinema zai ?auki nauyin komai na karatun nata har sai iya inda ta gaji ita da Addah.
Taji da?i sosai, dan tasan indai yayama babanta magana bazai musaba saboda ?aunar da sukema juna. Ilai kuwa, baban Addah nama baban Umm magana ya amince, atare aka kaisu makarantar sakandire, bayan sun kammala kuma suka nufi jami'a duk da Mahaifin Umm baiso hakaba, amma kunyar amininsa ta hanashi yin magana ya zuba ido.
To da yake komai aka sakama rana zaizo ?arahe sai gashi cikin hukuncin ALLAH sun kammala, a randa suka kammala ?in kuma Umm tai gamo da mijin aure.
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
Wannan littafi SARAN ?OYE na ku?ine, yana ?aya daga zafafa biyar, idan kana bu?ata kaima wa?anan numbers ?in magana ka biya ku?insa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka ya?a dan ALLAH idan ka gani??????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
____________________________
Bayan kwana biyu da ha?uwar Umm da Malam Sooraj Hashim Jibiya yazo har gida da kansa wajen babanta ya nema izinin yin magana da ita, tare da tambayar ko an mata mijine?.
Baban Umm yaji da?i sosai, dan babu wani mahaluki dazai?i jinin gidan Malam Hashim Jibiya, nagartaccen gidan dake cike da nagartattun mutane, manyan malamai da ake alfahari dasu a ciki da wajen ?asarma gaba ?aya.
A take babu wani jan zance ya amsa masa da ya nema so wajenta, inhar tana sonsa shikuma yayi al?awarin aura masa ita. Malam Sooraj (Baba Malam) yayi farin ciki da wannan karamci, haka ya koma gida cike da ?okin wannan al'amari, da tarin godiyar UBANGIJI kuma. A ranar baiyi magana da Umm ba, sai bayan kamar kwanaki biyu ya sake dawowa gareta. Inda akai masa masauki a gidan su Addah, a falon babansu.
Duk da Addah tayi murnar ganinsa a gidansu sai bata za?eba har saida taji dalilin zuwan nasa. Jikinta yayi sanyi hartasha kuka jin ba wajenta yazo ba. Dan tun ran walimar yayesu zuciyarta sam bata huta daga begensaba, tanason fa?ama ?ar uwarta Firdausi (Umm) amma takasa furtawa, duk sanda ta tunkareta da zancen sai taji gabanta na fa?uwa.
A yau da taji ?ar uwarta yake so saita godema ALLAH da bata furta mata zancenba, ta kumayi al?awarin mantawa da Malam Sooraj Hashim jibiya a ranta har abada, dan tafi ?auna da farin cikin ?ar uwarta ta samesa fiye da ita. Haka ta cire komai a ranta taita ?o?arin mantawa da shi, ta kuma cigaba dama ?ar uwarta addu'a da murnar samunsa matsayin mijin aure.
Tun daga wannan ranar Addah bata sake zama tayi koda tunanin Malam Sooraj ba har aka ?aura musu aure da Umm. A ranar da aka kai Umn gidan Malam Sooraj Hashim Jibiya, aranar Addah tai gamo da Malam Mustapha ?aninsa da yazo ?aukar amarya. A take shima soyayyar Addah ta shigesa, baiyi ?asa a gwiwa ba kuma ya sanarma ?an uwansa. Kamar yanda yabi nasa neman auren bisa matakin shari'a haka ya bima ?aninsa har iyayen Addah suka amince suma.
Kwatanta muku kalar farin cikin da Addah da Umm suka shiga a wannan lokacin ?atama lokacine, sunyi kuka sunyi murna har basu san adadiba, ba ?aramin godiya sukaima UBANGIJI ba daya sake dun?ulesu a gida ?aya matsayin matan yaya da ?ani. Itama Addah ba'aja wani dogon lokaci ba aka ?aura aurenta da Mustapha aka kawota.
Da farko ganin kan Addah da Umm a ha?e yake ya saka Momyn Abdallah jin haushinsu, ta ware kanta bata shiga cikinsu duk da ?anta Abdallah kullum yana wajen Umm. Dan tunda tazo gidan yazama ?an ?akin amarya, ahankalima ya dinga zare kayansa yana komawa dasu sashen Umm. Tun Momynsa na fa?a harta ha?ura ta zuba masa ido kawai. Daga baya kuma ma saita kwantar da hankalinta suka ?ulle kansu su hu?u ganin Addah da Umm basu da damuwa. Ita dama matar Abba Musbahu babu ruwanta, dukansu tana girmamasu da mutintasu kasancewarsu matan yayun mijinta. Duk da kuwa bazasu girmetaba sai dai suyi sa'anni ma. Ita kanta Momyn Abdallah ba girmarsu zataiba, kawai dai an mata auren wurine sa?anin su da duk sunyi karatu.
Addah ta samu ciki da zuwanta gidan, amma Umm shiru kakeji. Sunyi murna sosai da cikin Addah, har ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo ?anta Namiji santalele. Wanda yaci suna Hashim, amma suna kiransa da malam ?arami. Babu jimawa matar Musbahu ta haifo nata cikin itama Namiji, yaci suna Ahmad. Itama tsakaninsu babu nisa da Momyn Abdallah datai haihuwa ta biyar, itama ta haifo mace aka sake maida mata Aysha.
Sosai su Baba malam sukai farin ciki family ?insu ya dawo kamar da. Inda sukema Umm Addu'ar itama ALLAH ta kawo mai albarka. Haka haihuwar matan gidan ta cigaba da tafiya a jajjere. Sai da sukai haihuwa hurhu?u kafin ALLAH ya bama Umm ciki itama. Kowa ya tayata farin ciki sosai, musamman ma Addah da ayanzu takeda yara hu?u, ?aya namiji Uku mata. Sai Momyn Abdallah nada hu?u, maza biyu mata biyu. Matar Abba Musbahu nada hu?u itama duk maza.
Umm ta haihu Namiji sannan su Addah duk suna fama da laulayi ?ananun ciki, sai dai kuma kwanan jaririn Uku ya koma. Sosai Umm tasha kuka, amma daga ?arshe saita share hawayenta dan tasan ALLAHn daya bata ya kar?a ya fita sonsa. sannan ma yaran gidan babu wanda kemata shamaki da nasa, fa?i tashinsu sukeyi a sashenta kamar nata, musamman ma Abdallah da ?a?an Addah da inba fa?a maka akaiba bazaka ta?a sanin ba nata baneba.
Cikin amincin ALLAH bata rufa wata uku da haihuwa ba saiga wani cikin, inda shima Baba malam yay murna matu?a fiye ma dana farko. Su Addah sun rigata haihuwa. Matar Abbah Musbahu ce ta fara haihuwar ?arta mace da taci suna Yusrah, sai Addah ta haihu itama mace, aka saka mata Adawiya, sai Momyn Abdallah ta haihu itama dai mace, aka saka Safiyya sunan mahaifiyarta, sai dai ana mata alkunya da Amal. Bayan haihuwarsu da watanni itama Umm ta sake haifo ?arta mace mai kama da ita. Wadda taci suna Zainab, da yake sunan hajjo ne sai ake mata alkunya da Nu'aymah.
Bayan haihuwar Nu'aymah da kusan shekara biyar Umm ta sake haihuwar yaro ?aya namiji Muhammad, daga nan kuma shiru kakeji bata sake ko ?atan wata ba. A lokacin Addah ta sake haihuwa uku, mata biyu da namiji ?aya. Sai yazam tana da yara bakwai. Mata shidda maza biyu. Itama Momyn Abdallah ta ?ara biyu ?ammata tagwaye, tanada mata hu?u maza uku itama. matar Abbah Musbahu ko ?aya ta ?ara shima namiji, tanada maza biyar mace ?aya kenan. Daga haka haihuwar ta tsaya musu su duka babu wanda ya ?arayi.
Rayuwar gidan tacigaba da gudana cike da birgewa da ban sha'awa, inda ALLAH keta ?ara ?aga darajar mazajensu ta ?angaren ya?a da'awa da ilmantar da bayin ALLAH da taimakonsu ta hanyoyi da dama. Suma kuma ba'a barsu a bayaba wajen yima addini hidima. ?a?ansu sun tashi kansu a ha?e cike da tarbiyya kula. Komai tare ake musu.
Akwai sha?uwa sosai tsakanin Abdallah da Nu'aymah, dan tunda aka haifeta ya kasa ya tsare. Komai yaci sai ya ragema Nu'aymah duk da alokacin yayi girma sosai, dan harma ya kammala firamare yana shirin shiga sakandire. Babu mai dukan Nu'aymah ya kwana lafiya a gidan. Umm ce kawai yake ma ?an kawaici, itama zaita fushi da itane koda bazaiyi maganaba. Komai ma Abdallah na Nu'aymah ne, firarsa Nu'aymah, fushinsa sai an ta?a Nu'aymah, kukansa sai Nu'aymah na kuka.
Itama kamar tasan abinda yake yi, tanama kowa ?iwa a gidan amma banda Yah Ab, duk abinda ta samu saita rage ta ajiye masa. Tun kowa na ?aukar lamarin nasu wasa har aka fahimci yafi ?arfin wasan aka koma binsu da addu'a.
Nu'aymah nada shekaru tara a duniya su Baba malam suka bu?e kamfanin mangya?a a garin Lagos, hakan yasa dole Malam Rudwan Hashim Jibiya (Abban Abdallah) ya koma can da iyalansa dan ya dinga kula da shi. Lokacin komawar tasu kam anga tashin hankali wajen Abdallah saboda rabuwa da Nu'aymah. Da ?yar aka yakicesa daga jikinta, danfa shi yace inhar zaije sai dai da ita, kokuma a barsa anan wajensu. Ganin yanda yay matu?ar ?aga hankalinsa yasa Hajjo sakawa a barsa nan gida badan Momynsa tasoba. Idan anyi hutu ya ringa zuwa musu, idan kuma sunzo shikenan.
Haka yana gani iyayensa suka lula Lagos aka barsa a kano saboda Nu'aymah. Bayan tafiyarsu Abban Abdallah da shekar biyu shima Abba Musbahu daya ?ara auren mata ta biyu ya bisa tare da Ammin Ahmad, yabar amaryarsa anan gidan yana zuwa weekend, dan aiki yayma Abban Abdallah yawa acan shi ka?ai, ga harkar Addini gata kasuwanci, ga nashi kuma yanayi shima.
Gida sai ya koma daga hajjo sai Umm da Addah da Ummah amaryar Abba Musbahu. Iyalan Baba Malam dana Abba Mustapha kenan. Sai idan sun sami hutune matan kanzo da yaran nan suyi, sukuma su Abbah sai suke zuwa weekend idan matan nasu sunzo nan.
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya, sha?uwa na sake ?ulluwa tsakanin Nu'aymah da Abdallah, hakama tsakanin Adawiya da Nu'aymah, dan sun taso sa'anni su biyu tunda su Yusrah suna Lagos.
Komansu tare ake musu, babu maijin kansu, Hassana da Hussaina ma ake kiransu saboda sha?uwa. A hankali Adawiya ta kwaso kayanta ta dawo ?akin Nu'aymah dake sashensu, suka zama a ?aki guda, makaranarsu ?aya, ajinsu ?aya. Kai komaima nasu ?ayane. Gefe ga soyayyar Nu'aymah da Abdallah, inda itama Adawiya son Abdallah keta mata sa?a a zuciya batare da kowa ya saniba har ita kanta. Bata tashi farga dason da take masaba sai da yay mata babbar illa a jini da zuciya, har takai bazata iya ha?ura ta barma Nu'aymah ba.
Tunda Abdallah ya kai minzalin aure bayan kammala karatunsa na degree aketa fama da shi yayi aure amma ya?i, acewarsa Nu'aymah yake so. An lalla?ashi akan ya auri wata idan Nu'aymah ta isa saiya ?ara da ita, amma sam yace bazata sa?uba, zai jirata ko shekara nawane. Abin ya bama kowa mamaki, dan lokacinma fa Nu'aymah da Adawiya suna firamare aji shidda ne. Haka kowa ya ha?ura aka zuba masa ido, sai ma ya koma karatu da kasuwancinsa na kansa daya ?ir?ira, ya du?ufa wajen fa?a?a karatunsa na addini kuma tamkar iyayensa.
A wannan shekarar Abban Abdallah ya sake komawa Abuja da zama inda canma suka bu?e reshen Company ?insu na mangya?a, sai aka bar Abba Musbahu a Lagos. Tunda suka dawo Abuja Momyn Abdallah ta fara jan yaronta jikinta sosai, a hankali ta janye ra'ayinsa ya koma Abuja da zama wajensu, inda harkokin kasuwancinsa suka fara fa?a?a daga Nigeria zuwa ?asar Saudia. Lokacin kuma Adawiya da Nu'aymah sun shiga sakandire.
Suna aji uku a secondary Abdallah ya koma kara fa?a?a iliminsa na addini a ?asar Saudia inda yake kasuwancinsa yanzu, sai yazam baya zuwa sai dai aiko da kaya Nigeria Omar da Ahmad na kulawa dasu suma suna aika masa na Nigeria can.
Nu'aymah yarinyace ?ya?y?yawa fara masha ALLAH, dan tana kama da mahaifiyarta sosai, yarinyace mai shegen wayo ga rashin tsoro ga tsiwa. Tsula tsiyarsu suke ita da Adawiya fiye da zato, kullum cikin jan fa?a suke a makaranta daga boko har islamiyya. Duk da rashin jinsu yarane masu kaifin basira da haza?a musamman ma Nu'aymah, tana da matu?ar ?o?ari, dan tun tana aji biyu na secondary tayi saukar Qur'ani, bayan tayi da shekara ?aya itama Adawiya tayi. Bayan duk sunyi sauka suka juya hadda, tare da karatun sauran littatafai kuma.
Haza?ar Nu'aymah a makaranta yasa suna aji biyar wani malami ya bada shawarar a barta kawai ta zana ssce a wannan shekarar, koba komai zata kammala jami'a da ?arancin shekaru. Baba malam ya amshi wannan shawarar, musamman daya duba maganar auren Nu'aymah da Abdallah da kowa ke jira, ya yanke shawarar tana zana ssce za'ayi auren sai taje ta cigaba da karatunta a ?akin mijinta kawai. amma saiya sa suyi ssce ?in tare da Adawiya. Wannan shine ya sakasu gama makaranta a wannan shekarar. Adawiya dasu Amal nada shekaru sha bakwai cif, Nu'aymah kuwa bata cikaba har yanzu, tana sha shida da wasu watanni dan su Adawiya sun girmeta...............?
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo??
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).????
Mamu gee??
MIN ?ALB!!????
Hafsat rano??
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!????
Safiyya huguma?? SIRA?IN RAYUWA????
Bilyn Abdull??
SARAN ?OYE????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????
?aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu?u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????
09033181070
????????????????????
TEAM----ZAFAFA BIYAR????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu??????.
[3/8, 1:16 PM] +234 901 860 0202: *_Typing??_*
*_SARAN ?OYE!!_*
*_Bilyn Abdull ce????_*
Free page??
_Daga yau free pages sun ?are masoya. Ku garzayo domin samun wa?anan littatafai guda biyar akan farashi mai sau?i. Dan girman ALLAH kibi ta hanyar data dace ki mallaki naki??, karki