Showing 216001 words to 219000 words out of 304363 words
karatune yayi yawa sai nan da wata daya kila zai dawo amma Dije sai nake ganin kamar wani dan uwansa ne yazo daga can garinsu don naji ance daga mambila mai masa sallaman yake yanxu.
Mambila inane kuma hakana ta fada tana kallona cikin tsigar tambayan nace garin mahaifinsa mana Dije aikinsa sunan garin ke nan dama mambila ai.
Sai naga tayi wani irin juyawa da sauri ta nufi hanyan fita suka hade da wanan yaron daya shigo da farko yana fadin wai ance idan akwai wani babban yaro yazo don Allah.
Yaron ya fada da dan karfin murya daga inda yake tsaye din can naji Asma,u na fadin kai ka damemu da sallama ance bayana nan ka kuma dawo .
Shige mu tafi Dije ta fada tana bin yaron a baya shikuma ya nuya ya fara tafiya daga inda Aisha take tana fisgo hijabinta dake rataye tace Dije barin ga ko waye.
Ina tsaye ina tunanen kukan bakar akuyan nan na gidan data soma tunkan yaron ya shigo gidan sai ssutin hakan data kara a yanzu din.
Wanda hakan yasa nasha jinin jikina a lokacin don nariga dana yarda da camfin dana sawa kaina na gane alaman faruwan wani abu daga sautin kukan akuya duk lokacin da kaji kukanta wani abu ke shirin faruwa a gidan ke nan.
A hankali can kasab zuciyana na furta muji alheri ga wanan kukan da kikeyi na juya zuwa falona don in zauna in dama huran da nake kayan riko a hannuna din tunda Dije ta mika min shi.
Ina kaiwa zaune salatin Dije yasa na dago da sauri saidai bankai tsaye ba naji tana fadin ikon Allah bai karewa a duniya yau ga na manzon Allah a kofan gidan nan.
Inna dake daki ta fito da sauri kai babu dankwali tana fadin wani na manzon Allah kuma umma tace na manzo dai mahaifin Amadi da kika sani Rashida tsohon mijin ki shine yazo garemu da kansa inji Allah.
A lokacin har nakawo tsakar gidan kamar yadda kowa ya fito don jin me Dije ke fadi a lokacin inna ko kwasa tayi kamar zata kofan gidan kome ta tuna kuma sai taja ta tsaya wuri daya.
Dije ta bita da kallo tana fadin yau naga shashancin banza makin ki tura akai masu abin zama ko nan icenyan malam Tanimu sai ki fara shirme irin naki da ina zaki da zaki fita ?
Umma nace dake fita zanyi haka kawai dai zan dan leka nagani ko shi dinne da gaske ko kama kika gani kace hakan amma ni nasan ba zai taba zuwa nan garemu ba shi idan yasan kunya.
Zaki fara haukan naki Rashida shi Na Manzon Allah din zai bace min ne koda yake shekaru sun ja yanzu don nima dai ban ganeshi ba gaskiya saida ya fada min ko shi waye .
Ke Aisha maza ku debo tabarmin nan na dakina sabbi kuje kukai masu suna waje tsatsaye wajen motan su na barsu koda yake na aika a fadawa malam Tanimu zuwansu idan yana gida.
Sallama malam tanimu din ne a gagauce yana fadin Dije akawo masu wurin zama su zauna abar manyan mutane haka tsatsaye a waje suna jira jn kuma shigowa zasuyi nan ciki aisai su shigo din malam tanimu din ya fada a cikin hanzari.
A,a wallahi haram ina zasu shigo muna haka cikin gida bamu dako shiri a lokacinne Aisha ta fito da manyan tabarmi a hannunta guda biyu daga dakin Djje din kamar yadda ta umurce ta dayi.
Shi kuma malam Tanimu bai fita ba sai cewa yake Djje kinga ikon Allah yau na manzon Allah ne yazo garin nan wurin danshi Allah buwayi gagara musali.
Ni ai ganin abin nake kamar a mafalki yau ina Amadi gori dashagube yakare gareshi yau shima da yake kamar kowa a garin nan.
Juyawa nayi zuwa part dinna don tsayin baida amfani kitchen na fada na jawo manyan jug dina na ruwa set ne harda cups dinsu da tire ban taba amfani dasu ba tun zuwana gidan na shiga daurayewa .
Bayan nagamane na dauko kankaran nan biyu da Dije ta kawo min in dama fura na jefa cikin ko wani na koma daki na dauko kwalayen drinks irin wanda master kan sawo min din nan na aje don baki guda uku duk mm a jera a cikin ture din.
Sanan na fito na kwalawa Aisha kira tazo ta dauka har lokacin suna tsakar gida tsatsaye Aisha na basu labarin abinda idonta ya gano mata a wajen.
Ta dauka ta fito dashi zuwa waje inna tabi da kallo don ba wanda yasan saitin kayan jug din kaf gidan nan na fito na samu Dije tana godiya ga Allah na wanan ranan tare da fadin.
Dama malam yana fadin wata rana zai dawo zai dawo nan ko son dansa mu daiyi hakkuri lokaci na zuwa yauko ga zancen nasa ya fito don ko gashi da kafanshi yazo don dansa.
Butocina Aisha ta shiga ta dayko ta cicika da ruwa ta fita dasu nikan nabi jikin bango na lafe ina kallon re action din kowa a gidan mu samman inna data kasa zaune ta kasa tsaye kan zuwan nasu.
Ganin tsayuwan ba zai mun ba yasa koma part dina ina tunane ta hanyan hayewa kujera na na kwanta ba abinda nake tunane sai hiran da master yai min kan mahaifin nasa duk da nashi hakkuri akan baisan uzurinsa nayin hakan gareshi ba.
Amma nasan hakan baisa ya sauke kudirinshi a kanshi don bana jin kalami mai taushi akan tsohon a bakin shi ko yaushe zance irin haka abinda yake fadi dayane shine baison suma hadu dashi ga baki daya.
Idan nace ya daina fadan haka don Allah mahaifi mahaifine sai tace bari zahra baki san komai ba ke don Allah kawai dai mu tafi a hakan dashi shike nan.
Yau kuma sai gashi Allah ya kado munashi garin saidai master din bayanan a wanan lokacin gabana ya fadin don tunowa da nayi da cewa idan mun boyewa su Dije inda yaje yanzu ai ba zan boyewa mahaifin inda yake ba.
Haka na zauna inata tsara mezan fada masu da zaiyi kama da maganan farko Aishace ta fado dakin tana fadin Dije tace kibada wuri a saka masu fura da aka sayo masu gidan mai dawo.
Nan na mike muka shiga kitchen tare muma nemo waje muka juye furan aka dora saman wani ture din golden ta fita masu dashi inna ko ban kara ganin giccen taba duk lokaci tana daki she waya takeyi .
Can naga ana shigowa da tsaraba irin kayan hanyar abuja sak don mahaifinmu ya saba sayowa muna gani da subutan baki nace gasu kamar sun fito Abuja mana ?
Wani Abuja suda suka fito can nisa akace kusa da fita Najeriya zaki wani ce Abuja kuma Asmau ta tareni da fadin hakan a lokacin ne mukaji sallaman mutane zasu shigo a zaton muma sune zasu shigo sai mukaga.
Yan uwan mahaifin su innane sune suka shigo lokacin duk da dattije nai amma idon su akaina hakan yasa na tsargu duk da shigana lokacin ba laifi ina cikin suturana mai rufe jiki.
Gaishesu mukayi suka nufi wurin Dije nikan a lokacin na shige part dina na rufo kofana don ban ma son naji kome zasu tatauna a lokacin sai gasu Aisha sun biyoni ciki suma.
Nan muka zauna dasu Asmau na fadin ji munafukai basu zo gidan nan ba saida gulma ya samu sunji ance manyan mutane sunzo sunzo su samu canjin kashewa shegun matan su.
Kai Asmau halin nan naki baida kyau wallahi iyayyen naki kewa wanan kazafin na fada a cikin daure fuska gareta .
Tace barsu anface sune suka kashe auren inna da mutumin nan da badon suba da yanzu muma shine mahaifin mu ai suka kwafsa muna.
Kallon takaici muka watsa mata lokaci guda don jin abinda ta fada din game da tsofin na takaici nice nace baki san wani baya haihuwan dan wanu ba dama haka Allah ya tsara abinsa.[6/19, 8:05 AM] Mmn Bibo: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
7️⃣5️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Dan shirune ya biyo baya a wayan kafin cikin muryan mamaki shi Ahmrd din ya kawar da shirun ta hanyar fadin mahaifina mahaifina fa kace ?
Kwarai kuwa ko kana maki hankane dana nine dai Alh, , , , look malam kake ko Alh idan ma ka kiranine don ka zolayeni ko wani abu ka batawa kanka lokaci a yanzu bani Ahmed ba.
Don haka ka bari saboda ni na dade da rufe wanan zancen a zuciya don dai ni Ahmed nasan banda uba a duniyan nan ko ina dashi kuma ya dade da barin diniya a wurina.
Don kowa yana da shedan hakan kuma a hakan jama,a suke daukana suna min kallon mutum mara asali a cikinsu don haka kada ka zolayi kanka ka zolayeni a yanzu da wanan sunan na kaine mahaifina.
Don haka kada ka kara kirana ko kuma layina idan ba haka ba zan maka abinda baka taba zatoba a rayuwanka don hukumace zata rabani da kai..
Yana fadin hakan ya kashe wayan nasa a hasale tare da mikewa daga inda yake zaine din yana shan iska a cikin bacin rai da be taba jin irinsa ba.
Tafiya yake zuwa dakin shi na masaukinsu yayin da wani irin mamaki ya lulube ziciyanshi lokaci guda duk da yasan ko waye mai kiransa din a lokacin.
Amma abin mamakinsa shine a ina ya samu layin nasa har ya kirashi a ranan shine mamakin dake ci masa zuciya don yasan banda zahransa ba wanda yake da layinsa a Nigeria to a ina yaga zahra din ya karbi layinsa din ?
Shima Alh bai taba zaton hakan a gareshi ba don ya dauka dan zaiyi farin ciki dajin shine a ranan sai yaji sabanin hakan gareshi take mamaki ya lulubeshi.
A karshe ya gane cewa dan nasa jarumine na sosai don haka akwai sauran aiki a gabasa ke nan da zai fuskanta nan gaba gun dan nasa duk da bai dauki hakan a wani matsala babba ba .
Yadai kashe wayansa yana mamakin jarumta irin na yaron a lokacin koda yake kila bai gama fahintar shi bane oho idan yasan koshi waye dole zai dawo hanya yabi ai .
Nima dai tun bayan tafiyan nasu na koma wata irin mara lakka dani ina faman tunanen abubuwan da suka faru haka da wanda zai faru din don nasan master ba mutum bane mai saukin kai lokaci guda ba.
Bani kadai ba don ko inna da Dije na hango damu a fuskokinsu tun zuwan bakin namu saidai bansan damuwansu ba su na daifi tsanmanin zuwan nasune ya mayar dasu din haka.
Don hakanema na shige dakina na kwanta zakice barci nakeyi a lokscin amma idona biyu gidan ne kawai ba dadi a ranan garemu .
Shigowan Aisha take fada min dije tana magana dani wurinta hakan yasa na tashi naje lokacin karfe takwas na dare anyi sallh isha,i ke nan na ranan .
A tare muka jera da ita bayan na rufo part dina don ban faye fita da dare ba zuwa cikin gida master kuma ya gargadeni idan zan shi cikin gida na dinga rufe kofa hakan yasa na jawo kofata na rufe muka shiga.
A tsakar gida na samu inna zaune ita kadai tayi tagumi tana zaune daga ita sai dan farin vest a jikinta mai siririn hannu ta kurawa waje daya idanu jin sallamana yasa ta dago tana sauke ajiyan zuciya ta amsa min a sanyaye.
Gaida ita nayi da wuni a sanyaye ta karba zakice wani abin yana damunta lokacin ban tsaya ba tunda ba dogon hira nakeyi da itaba dama na shige wurin dije mm a sameta a zaune daga kofa.
Dan buhun abincinsu dake gefe daya a dakin dan dama a dakin nata ake ajewa sai za a dafa aje a diba ya fada don kullun cikin cinsa ake nan nakai zaune ina gaida ita da wuni.
Ta amsa min cikin jan zuciya saida naga ta leka kamar bata son aji me zata fada a lokacin ina dai kallonta tace dani karbi kudin nan ki kirga min su kinji .
Don ban yarda da yan banzan yaran nan ba suna iya biyo dare suzo su sace min su kuma uwarsu ta hana ayi magana idan taji na mika hannu na karbi kudin na fara kirgawa har nakai karshe.
Na dago kai nace dubu darine Dije da sauri ta kalloni tana fadin dari yar nan har kin kirga da kyau ko kin gani nifa dana gansu a haka na dauka ko ashirin ne ?
A,a darine na fada ina miko mata tace a, a ki ban goma kawai koshi don inbawa abokan arzikina irinsu mai fura da mukai zaman arziki dasu suma su sheda baiyanan mahaifin mijiki garemu.
Murmushi nayi kafin nace ba zaki sayo abin dadi kitaci ba Dije don haka ya baki da yawa fa itama dariya zancena ya bata don naga ta washe baki kafin tace.
Wani dadi zanci ai ajesu zanyi har mijinki ya dawo jn mika masa su ko yaji dan saukjn yi muna cefane kinga ai a kara ko tunda Allah ya kawo muna su har gida.
Hakane amma dai koshi ya dawo nasan abinda zai fada ke nan ai tace bari yar nan ina tausayin yaron sosai wallahi muci musha muyi tufafi duk a jikinsane kuma baya fushi da hakan.
Ga ita wanan taki mayar da yaran nan ga dangin ubansu ta kwaso ta kawo mashi sunan yana bakar wahala dasu yan banzan yara tundai ace Asamaun nan ba ma,u arziki bace sam.
Wata kila yarintane ke damunta zata zo ta bari ai ta barme yarinya haka da rawan kai don mashi Amadi ya zamo namijim gaske aida ba karaman tantiriya bace.
Duk irin taurin kan uwarsu ta kwasoshi dan haka itama lokacin nan ta kafe sai habu fari take so mutumin da baida komai bai kuma da kowa a garin nan.
Ni kin sani ance dare daya Allah kanyi bature ba abinda ya tsaya min a rai sai arzikin bawan Allah nan mahaifin ku don wallahi da can baya ko sadaki saida akai mai tarbace aka hada mashi su.
Amma yau shine yazo gidan nan a matsayin attajiri da mutane ke binsa a baya haka duk da ance kudin yanzu basu da wuyan nema amma da alama a yanzu shi din wani hamshakin mai kudine.
Dama dije haka Allah kanyi ikonsa ga bawa sannu a hankali za a gane dalilin kudin nasa nan gaba ai amma mutum ya tashi haka ba kudi aganshi dasu da rana tsaka gaskiya abin tambayane ga mai hankali tace aishi nagani.
Amma kinga mara hankalin nan tun dazun ganin mijin nata a yau yasa duk tabi ta sukurkuce ga baki daya Allah na tuba a yanzu yadda yaken nan ko a kafa aka daura mai Rashida me zaiyi da ita kuma ?
A, a haba Dije inna ba mace bace kuma matarsa aishi zai gyarata tunda akwai kudin aiki mukan ai muna son su koma gaskiya in hakan zai samu su koma din.
Wace don ni ina jin ko ganetama baiyi ba don shi a haukace yake da son ganin dansa bai tsaya tambayan wata Rashida ba can don haka wahalan rayuwa kawai take son dorawa kanta.
Don itama tasan a yanzu yafi karfinta sau dubu ko makaho ya laluba yasan haka kawai yanzu ni bansan da wani tsiga mijinki zai tarbi mahaifin nasa ba idan ya dawo.
Ni Umma bance ina tunanen hakan gareshi ba damuwata damuwatace nina nasan abinda nake tunane muryan innace daga inda take take bamu amsa.
Koda muka rabu dashi aiba fada mukayi dashi ba ko wani abu kawai dai kaddarace aita rabamu a lokacin ba wani abu ba.
Kinji ko dama aina fada maki kina wani tarewa wai kuma kuna son hakan ya faru take fada min daga can inna din ta sake fadin umma bashi yayi kansa hakan ba yanzu Allahne yayisa.
Ko ya tambayeni ko kada ya tambaya duk dayane a gareni don na masa abinda kowa bai masa a baya can to me zai dameni a yanzu kuma ?
Mikewa nayi da niyar fita daga dakin ganin inna ta dauki maganan da zafi a zuciyar ta lokacin don yadda take halako ya nuna cewa ranta ya gama baci sosai a lokacin.
Nakoma part dina na samu wayata da misscall dinshi nayi shirin kwanciya ya kara kira na dauka yake fadin ina kika shiga waya keta ringing tun dazun baki dauka ba ?
Nace ina wuri Dije muna hira nabar wayan a daki waya karbi layina a hannun ki ya tambaya ba tare daya tsaya mu gaisa ba ko yaji ya lafiyan mu take ya jefo min wanan tambayan.
Sam na manta da zancen mahaifin shi ya