Showing 189001 words to 192000 words out of 304363 words

Chapter 64 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33325

abinda ake ciki game da mijinta.
Yadda take a rude hakan ta labartawa yar uwan nata komai hankali tashe itama yar uwan ta rude ta kwaso ashar ta dura masa tana fadin me yake nufi da gyarab daki a yanzu.
Shin aure yake nufin zai kara ko kuma dai shine zai koma ciki a yanzu ya barku nan haba dai yayata yaya za ayi shidake tsakiya ya koma gefe ko kin manta yadda tsarin gidab namu yakene wai ?
Tsarin dama na mutum biyune nasa a tsakiyan mu ba sai wani yaga dan uwa a cikin mu ba inyaso hakan da sauri yar ta dakatar da ita da fadin kedawa ?
A, a musali nake maki ai gara dai ki gyara don bani fatan ace za a kawo maki wata a cikin gidan nan yanzu da sunan kishiya kila kuma wanan kucakar ta nan zai dauka ya kai can yarta fada.
Ita kuma ta amsa da sauri tana fadin tazo ina aiko da komai ya lalace min a yanzu da gaske in har Naito tazo garin nan da sunan zama ko kin manta da cewa ya auretane da yardana wai ?
Maganan da ke nan ba yanzu ba don yanzu komai da mukayi a baya da alaman abubuwan sun badamu a yanzu gaskiya nima hakan dai nake gani amma ai idan yasan wata ai baisan wata ba.
Tundai zancen shigowan yaron nan da kika fada karkiji yanzu yadda nake jin zafin wanan zancen don irin masu shigowan nan tsakiya sai suzo su zama wani abu a gida naka na zaune.
Don Allah bar zancen nan aiko zan tafi hutuwace sam ba zan taba yarda da wanan shegen yaron ya shigo cikin mu yanzu dai gobe in Allah ya kaimu gobe zan tafi Nasarawa an fada muna wani boka a can wani kauye zamuyi tafiyan tare da hjy liyyatu zuwa can.
Duk wanan wayan a kunnen mai aikintane dake duke tana jera mata abincin don taba da umurnin a kawo mata abincin a dakinta lokacin tagama jerawa ta fita tana sheda mata angama komai.
Muna zaune aka gama tura koma zuwa ga e-mail din Bisi din duk wani takardan daya dace saida muka tura mai a lokacin bandai fadawa kowa komeye ba balle zancen ya yadu kafin hakan ya tabbata.
Wayanane ya dauki kara lokaci guda na lalubo daga cikin jakkata shine a Latin na dauka ina mashi sallama ya amsa na dora da ina wuni ya amsa da lafiya lau kun fito break ke nan ?
Nace eh amma yanzu gida zan tafi don ba zamu zauna karatun yamma ba yau yace test zamuyi OK idan kika koma don Allah kada ki kula duk wani abinda inna zatayi maki don Allah nasan har yanzu tana jin zafin zancen daya faru da safe tsakanin Ku.
Kai Waya fadama hakan sai naji yayi murmushi kafin yace au had kin manta na kiraki a ways lokacin kika bar wayan kunne da sunan zaki gaisa da Dije a lokacin don haka ban kashe wayan ba ai lokacin.
Naji koma naji duk abinda ya faru had amsa da kika bata dan haka banson wani zance kuma ya kara tasowa son run dazun nake son kiranki nasan kina class lokacin.
Ni ya wuce ai a wuri dama kawai don ta gane na bata amsa ai kuma shike nan ai yace na sani don Allah ki bar tankawa daga yau don tana sane take komai ai.
Kayi hakkuri idan hakan ya bata min yayi murmushi yace is OK mashin zaku hau yanzu ke nan ko nace eh don yau Nabila bata shigo ba nake gani motarta baya nan.
OK ki kulamin da kanki nace nagode harga Allah banji dadin da yaji wanan zance ba don ba komai nake son ya dinga jiba tsakanin mu muna gama waya dashi na mayar ke nan a jakka sai naji wani kiran ya shigo again
Na dauka shine kuma a lokacin ya sake kira said naji ummahce ashe dana dauko na dauka da sallama ta amsa ina kokarin gaida ita naji tana fadin.
Kina school din be had yanzu nace eh ummah amma yanzu make son in koma gida min tashi ke nan race to ki kira Aisha da mamaku kiyi masu gaisuwa .
Don yarinyar nan jaririyar ta koma dazun aka kaita da sauri na furta innalillahi was inna alaihim raji,in yanzu yar nan ta rasu ummah ashe ?
Have eh wallahi kamar dama jira take ayi suna taiwan uwarta bara yadda aka fada son jiyama basu kwana a gida ba saida suka koma asibiti da ita a can ta cika.
Nayi mata adduan dacewa da Rahaman Allah ga musulmi nacewa ummah yanzu zan kira Aishan insha Allahu mukayi sallama ta kashe wayan nata.
Jikina yayi sanyi sosai ina dago kai hannatu na fadin yar Aisha ce ta koma ko nace wallahi a cikin wani irin yanayi murya a raunane .
Dama ai yana da wuya ta rayu irin hakan sai in yaro rabone zai zauna bayan ansha wahala karshe kuma ya taso a wahalce da ciwarwuta iri iri a jikinshi.
A hankali muke takowa data cikin school din muna maganan sai ga motar motana na gani ta gitta muna nabi motan da kallon mamaki.
Hannatuce ta rigani magana da fadin ikon Allah wancan kamar motarki zahra nace itace wallahi waye ke janta ciki nace naga kamar sanusi ne dan yayan mama dama dan dakintane shi sosai zakace shidin ma Dan gidan mune shi.
Kai wanan mama din gaskiya ba mutumiyar arziki bace yanzun mortar naki zata dauka ta ba dan uwanta bayan kowa yasan nakice dama taje su hau hannatu meye duniya baki dayanshi ma balls mota da zai lalace.
Wallahi ummah ta riga da tace koda andawo da motan ma bazan haushi ba ko hakan zai zama sanadin aurenta da Abba kuwa to kinga me zai dameni no yanzu da ita duk mai hawa ya hauta ba abinda ya dameni a yanzu.
Shiru tayi kafin can kuma tace dani amma wuri ta samu ina ji a gari ana fadin ko wanan amaryan Abba din yanzu hjy mama ta shiga gabanta amma fa yadda mutane ke fadine fa.
Murmushi nayi bance komai to waike zahra irin matan nan basu tuna cewa zasu mutu su koma ga Allahne wai mutum ya rungumi duniya yasa a gaba irin wanan halin me zataje ta fadawa Allah akan hakan ne wai ?
Kofa bata mutu ba zata iya tsufa ko ta nakasa kinga duk abinda tayi din nan ya tashi a banza yanzu ai gara mu biya ta gida muyi masu gaisuwa ko ta fada jin tana ta magana ban bata amsa ba lokacin.
Bari to na kira master in fada mashi na fada ina kokarin zaro wayana daga cikin jakata lokacin wanan Sanusin ya kara fitowa daga cikin makaranta ya kwaso wasu yan mata yan UG two a motan suna tafe suna shan kida sukazo suka wuce mu kamar farko.
Ina jin hannatu tace wallahi Allah ya isa dan iska dakai da uwar dakin naka sai kunyi kunya tun a nan duniya in Allah ya yarda wani irin dariya ta bani lokaci guda har ya dauki wayan ban sani ba ina karawa naji yana fadin a ina kike kike wanan dariyan kamar an maki bushara ?
Wallahi hannatuce take zagan min mama da sauri naji yace subbahanallahi wace maman naki ciki nace wallahi mama da mama ta gidan mu wai kawai don taga wanan sanusi din dan yayanta a cikin motana yana ja ya kwaso yan mata keja masu Allah ya isa.
Sai naji yayi murmushi yace kai hannatu bata rabuwa da shirme wallahi ta bari idan nayi kudi in saya maku motar daba me karbe muna saidai Allah.
Balle har wani gardi ya hauta wanan tamu dukane yanzu tunda na Abbane kowa yana da right din da zai hauta yanzu namu nan zuwa da yarda ubangiji.
Murmushi nayi tare da fadin Allah ya nufa saidai kada ai kudin sayen motan aje a dauko min wace zata hanani zaman lafiya dakai kuma.
What ya fada da karfi nayi murmushi tare da fadin nawa akayi muna gani dama tunanen ki ke nan zahra a kaina bari anji mu karasa mun samu dan mashin yanzu zamu shiga na bashi amsa na kashe wayan ina murmushi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA[05/05 10:37 AM] +234 803 180 3449: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
6️⃣6️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Rayuwa ke nan mutuwar yarinyar nan ya taba su mama zakace wani babban mutum ne ya mutu a lokacin ba yar jariri haka ba mundai isa nida hannatu munyi gaisuwa inda muka samu ana fama da uwar tayi hakkuri sai faman kuka take.
Harda wasu yan abi yarima asha kida suma suna kukan ita dai mama nasan damuwanta damuwar yartace Aisha.
Don Aisha yar gaban goshin mamace sosai a cikin yayanta koma zata iya yiwa Aisha din a rayuwa idan tana bukatan abu.
Ganin yamma yayi sosai mukai masu sallama muka dawo wurin ummah don mu sallameta bata part din tana part din daddy lokacin dole muka zauna zaman jiranta kada mu tafi bamu samu sallama da ita ba asalima bata ina cikin gidan ba a lokacin .
Uhmmm wai kiji min sister din nan naki daga Allah ya rabata da wahala ya karbi ran yarinyar a huta gardama wai shine take kuka haka ?
Hannatu rayuwace fa ta rasa dole tayi kuka ai balle da ance shiga ran uwa yakeyi sosai tun yana ciki kinga ke nan dole ta damu kona dan lokacine.
Balle ga wahalan daukan ciki gana haihuwa yaya mutum ba zaiyi kuka ba shiyasa nake ganin karfin halin irin matan nan masu daukan cikin shege a waje.
Suyi wahalan daukan nauyin ciki idan sun haihu kuma kiga mace wai taje ta yarda yaron a bola don rashin imani da tausayi ko shekaran jiya naji ance an sunci yaro a cikin wani kwalbati a gidan da mukaje kitso muke jin labarin haka.
Gidan gulma ke nan ai in kina neman labarin gari kije gidan kitso kona kumshi a nan zakiji labarin shege da shegiyan gari ke har kishiyan data gagara zakiji ko namijin da baya kula da matanshi ke ko wani labari na gidan kitson daya shahara a gari.
Kai hannatu ashe da gaskiyane da ake fadin tashin kaka daban suke ko wurin iya tsara maganansu irin na tsufine ke din nan akwai iya lafazi a bakin nan naki yanzu dai mudake zuwa gidan kitson mune yan gulman ?
Kafin tayi magana ummah ta shigo tana ganin mu mamaki ya kamata take fadin ku kuma yaushe kuka shigo daga school muka wuto zuwa nan don gobe muna da test ba zan samu shigowa da wuri ba.
Aikun kyauta gara da kukazo yau din nan dan uwa zai gane kana da muhinmanci a wurin shi don baka sanin ranan dan uwa ko dadinshi sai idan wani abin bakin ciki ya sameka dan uwa ke tsayawa ya tayaka kukan hakan.
Ta sake jiki kuwa Aishan don sunce tun safe da yar ta cika taki cin komai a cikinta har lokacin da na shiga dazun kara dubata abin ne akwai tausayi ummah ta fada.
Gaskiya kwance muka sameta tana kuka da muka shiga saidai tana jin muryan mu ta dago tana fadin zahra kinga babyn mu tayi tafiyanta ta barmu ko ?
Murmushi ummah tayi tace ai haka ta fada dana shiga dazun tace ummah zahra tana son yarinyar nan sosai jiya bakiga yadda take kafa kafa da itaba kada a dauketa ta wahala ashema duk hakan bazaiyi ba sai ta mutu.
Niko naga aita huta da rikincin su dake kwance kasa tunda ace mijin ma baizo ba har yanzu andaci karfinshine yayi suna yadda mutane ke fadi agari don akwai wata yar uwanshi a unguwan mu.
Kai hannatu aikece gidan kitso ko wani labari yana bakinki ku tashi dare yayi kuje gida barin kira Shehu yazo ya saukeku dama yanzu ya dawo kai motan wurin wanki da cewa wani dan yar uwar Abba daya leke shikuma wurin ummah tun yana karaminshi.
Mama tayi zagi tayi koranshi har hjy saida ta saka baki amma yaki barin ummah har gashi mun girma tun muna Abuja yana karami yake zuwa hutu wurin mu.
Ta daga waya ta kirashi dacewa idan ka dawo wanke motan gasu mahmah ka kaisu gida don Allah yace to gashi nan zuwa lokacin ummah ta kalleni tace ba zakije ku gaisa da Abban ku ba.
Wani har nayi da idanu alaman ban son zuwa tace kuje suna nan falo da hjy karima yanzun na barsu zaune tare ummah da dai ki bari sai nayi wani zuwan kuma idan yazo.
Au har yanzu baki daina wanan sakatcin naki ba ashe ubankine fa kome kikeji a ranki game dashi gara ki aje donshi ko a jikinshi duk da dai jiya ya tambayeni wai ko kema kina da cikine yaga kinyi kiba ?
Ciki kuma nikan banda komai wallahi idan nayi ciki yanzu ai asirina saiya tono ina gab da zana jerabawana kuma ciki yazo min dan zugurana hannatu tayi wai na daina maganan a gaban ummah haka rashin kunyanefa.
Dole dau muka nufi wurin Abba yadda ummah din ta fada hakane da hjy karima suna zaune suna hira mukayi sallama muka shiga falon nasa da ummah din ta gyara tas sai kamshin turaren shikka yake tashi a cikinsa.
Suka amsa muna muka shiga hjy karimace tace a, a kune ashe kuji mutuwar yar ke nan nace eh ina school dazun ummah ta kirani tana fada min daga can shine nazo nan.
Mijin naki ya dawone Abba ya tambaya a,a yana can waya mukayi dashi dai OK wanan itace kawar nan taki lokacin buki ko hjy karima ta tambaya nace eh tare da fadin Abba ya mukaji da hakkuri kuma ?
To hakkuri sai Allah shiya bayar kuma ya karba sai ai fatan lafiya yanzu ga uwar nace hakane tare da fadin to zamu koma idan kun tafi Allah ya kaiku lafiya.
Ai muna nan sati daya zamuyi hjy karima ta fada daga inda take zaune nace Allah sarki tau mun mike naji yace tunda mijin ki baya gari barin baki wani abu kona shiga school kya samu.
Lah Abba da ke Abban naku zai maki alheri kiki karba eh to ba mamaki kinsan mijinta last donen ne ai matar mai kudin sakaine Abba ya bada amsa yana miko muna sabbin kudi yan dari biyar.
Na duka na karba ina gidiya ya miko wani tare da fadin ke kuma gashi ki rike hannatu tazo da sauri ta karba tana godiya a lokacin ne hjy karima tace da motarki kikazo ko ?
Naga dare ya somayi ga unguwar naku da dan nisa kai na girgiza kafin inyi magana hannatu tace ai tunda aka karbi motan da bukinta ba a mayar mata dashi ba.
What kina nufin motar haya kike hawa kome da ita mukazo hannatun ta kara fadi Alh yaya akai haka za a barta tana shiga motan haya a gari ita kadai da sauri nace.
Mommy hakan yafi min yanzu ma kinga na farko a yanzu ban iya laluran motar kuma gidan kingani babu inda zan aje motana ai a gidan.
Dazunma kafin muzo nan muga wani yana yawo da motan ya kwaso yan mata acikinsa ai kunnena ya tsinkayi hannatu na fada a bayana.
Kaji ko motar ma ba a aje matashi ba wani ke shigarta yanzu wanan son kai gaskiya da yawa yake in anyi magana kace wai wani abu da sauri na bar falon hannatu ma ta biyoni baya.
Gaskiya hannatu bata taba bata min raina irin na wanan ranan ba don har nayi nadaman zuwa da ita gidan mu din a lokacin .
Don haka har na kasa boyeewa saida fuskana ya nuna hakan muna komawa gun ummah na samu shehu ya iso yana jirab mu a falonta mukai sallama muka nuna mata kudin da Abban ya bamu tace angode ta mikowa ko wanin mu leda na karba ina godiya muka fito har muka shiga mota na kama hira da shehu.
Ita muka fara saukewa don ina gaba da ita sai ya tafi dani har kofan gida ya kaini na sauka nayi mai godiya ya tafi ni kuma na shiga cikin gidan.
Kwananshi biyu a south Africa na uku ya dawo da safe saidai ya samu ba kowa a gidan hakan yaba yar aikin daman labarta mai abinda taji daga bakin hjy yabi ranan.
Ba koma nagode Asabe ki kara kula yacewa tsohuwar yau din nan matana na biyu zata iso garin nan da fatan zaki bata hadin kai a zauna lafiya banda tsegumi don Allah a tsakanin su yarda da aminci yasa na baki amana.
Tsohuwar ta gyara tana fadin insha Allahu Alh nakuma gode nima ka fitar dani daga zargin ubangijina Allah don wanan abin yana damuna shekara da shekaru wallahi bandai da bakin maganane kawai.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login