Showing 114001 words to 117000 words out of 304363 words

Chapter 39 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33329

fadawa su maryam cewa ba zanje bani saboda dare .
Don haka tunda naga su gwaggo sunci abinci sun kwanta a inda muka gyara masu nida maryam na dawo na kwanta abina a dakin tsohuwar nan.
Bayan mommy ta dawone ta samu sun kwanta take fada don me zasu kwanta a falon ni ina ina dana barsu a nan kwance gwaggo shaface tace aiko tayi kokarinta damu.
Don ko nan din ma itace ta gyara muna muka kwanta to ai sai ku tashi muje wurin dinner ta fada da sunso suki amma kuma suka shirya suka tafi.
Basu dawo ba sai karfe daya da wani abu na dare kowa ya samu wuri ya kwanta maryam ma bansan dawowanta gidan ba lokacin don na dade da tin barci ko ni.

Ayi hakkuri da wanan din busy nake kwana biyun nan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
3️⃣8️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Zaune suke shida malam musa a rumfar shan iska yayin da Shattu ke daga can gefe daya tana aikin tsuntar shimkafa a cikin tire ta mayar da hankalinta ga abinda takeyi din a lokacin.
Magana dattijon keyi saidai yaron bai motsa ba a lokacin ma,ana zuciyan shi nawani tunane a lokacin bai tare da dattijon a zahiri.
Ikon Allah yarona tunane kakeyi haka kai nisa har bakaji me nake fadi ba yana dan buga alkalamin dake hannun shi saman allo iccen da yake rubutu.
Hakan ya dawo dashi daga tunanen yana sauke ajiyan zuciya lokaci guda dattijon yake fadin kada ka halaka kanka da tunane dana insha Allah zaka sadu da mahaifinka da yardan ubangiji.
Zama ya gyara ya dan murmusa a fuskanshi yana sam baba ba wanan nake tunane ba a halin yanzu kakata dana bari a gida cikin damuwa don da sunan kwana daya.
Yanzun gashi ina batun shiga sati na biyu ban koma gida ba zuwa yanzu nasan tana can ta shiga damuwa don zata dauka cewa na mutu ko nayi hatsari ko kuma ansaceni ne abu dai makamancin hakan yasameni ne a tafiyana.
Nayi hakan ne kuma don nasan idan na fadi inda zanzo ba zasu taba barina nazo nan din ba ni kadai haka.
Haka zalika babu ranan da zasu kawoni gareshi har yasan ina raye ni bukatana a wurin mahaifina shine yasan ina raye a duniya ya dauke kamar ko wani da a gareshi koda bai bani komai nasa ba.
A rayuwana a hakan na fara fuskantar kalubulanta a wajen mutane don har wasu na tantama a kaina yanzu haka din wanan ne dalilun fitowana daga gida nazo nan neman mahaifin nawa.
Gaskiyane don ko baka fada ba nasan za a zo wanan wurin zuwa gaba don duk lokacin daka daukowa kanka zancen aure ko wani mukami wanan zance shi makiya zasu rike a makami gareka.
Dukko da sunsan cewa kai din ba shege bane amma haka bai hana a jefaka da wanan kalman mai zafi a zuciyar ka.
Sai dai barin gida da kayi ba tare da fadawa kowa inda zakaba a wana zamanin gaskiya kayi kuskure sosai a nan don hankalinsu zaiyi matukar tashi ga rashin sanin inda ka shiga yanzu.
Don haka kayi kokarin kira ka sanar masu cewa kana nan kuma ga abinda kazo yi a nan din kadai riga da kazo din duk mai wani korafi kan hakan yanzu ka shiga gaban shi kuma.
Ahmed din yace baba nagode insha Allahu zanyi yarda kace min din nayi zan kira in sheda masu ga inda na tafi su kwantar da hankalinsu a kaina.
Gaskiyane kayi kokarin yin hakan idan ka samu daman hakan kuma gaskiya suyi kokari wajen baka tarbiya irin haka mai amfani a gareka nan gaba zakayi alfahari da hakan in sha Allahu.
Nayi mamakin yadda mommy ta bata rai ga rashin zuwana wurin dinner har bata iya boye min bakin cikin hakan ba duk da har gwaggo shafa ta fada mata gaskiyane ban fitan dare don ina da matsalan hakan idan na fita din.
Batayi magana ba sai fuskan data canza min hakan bai dameni ba don ba haduwa mukeyi ba sai lokaci lokaci don haka canza fuskan bai wani damuna ba.
Ranan da aka daura auren kuma suka aza wani bidi,a wai wankin ango wanda ba kowane keyinsa ba sai dai yan son bidi,a irinsu.
Za a hadu maza da mata yaro da babba yan uwa da abokan arziki afito da ango da amaryan shi a dinga zuba kudi ace ana neman wanan ko waccan tazo ta sayi bakin angon da sauran su.
Inda yan gidan amarya suma zasuyi nasu bajinta su bada kudin ga ango daga mahaifan amarya din da sauransu dai.
Wanan kan naje wurin don karfe duhu akace za a fara amma basu fara ba sai karfe biyar aka aza bidian wuri ya dauki cida da mutane.
Don muyiwa mommy kara duk dana kula data raina da kuran gwaggonni din da matan ubanan namu dasuka zo mata karan sai ta sharesu basu ganin ta sai nice zan fito na nema masu abinci da ruwa ko wani lokaci .
Allah ya taimakeni na samu wanan matar da tun farko na sayeta take min komai yanzun ma din itace min tsaye da dawainiyar su gwaggo din don ita hjy karima batayi hikimar yin hakan ba a ranta.
Mun fito munyi barin kudi tare dasu maryam dasu gwaggo lokaci guda ba kunya saiga hjy karima dama ta manta da zancen su gwaggo din tazo tana washe baki a wurin mu tana fadin wai mun fitar da ita kunya sosai mun kara mata girma da kima a idon mutane ai.
Ko ta manta da maryam na wurin ne saidata wucene maryam ke fadin andaiyi hasara wallahi dafa su mummy na take wanan zancen wai.
Yan uwanta ke nan tayi adawa dasu inaga kishiyoyinta ina ganin daddy ku baisan auren ta biyar ba dashine na shida kuma bata zama da kishiya duk inda taje sai ta watsa matan gidan ta koma ita kadai karshe in mijin ya tsiyace ta gudu ta barshi bakunya ko tsoron Allah.
Irin wanan halin ne ke hadata fada da yan uwa don su basu son abinda takeyi din sai mama Rufaida da tasu yazo daya ko ina suna tare dasu a manne.
Koke dazun ai naji su maman mu na fadin wai zata fara nuna maki halinta don jiya taso kije wurin dinner nan don tasan akwai diyan manya taci kasuwa dake ta hakan .
Sai kuma tayi rashin sa,a bakije ba shine suke ta zaginki wai zatayi maganin ki ai sam mun manta gwaggo shafa tana tare damu take wanan zuban haka .
Saiji mukayi tana fadin dama ai daga ganin wanan matar da barikanci a idanunta ni wallahi kar nake kallon ta in ma iya shegene ai gidan tazo don tsab maimuna zatayi maganin ta.
Ke kuma nasan zuwan dole kikayi shiyasa banji komai ba koda maimuna ke fadin wai munafunci aka kulla da zuwanki wurinta hutu don ai mata bakin ciki ita da yaranta.
Ni kuma nasan idonta hjy salmace ba zaki taba zuwa ko ina ba idan ba tare da ita ba wanan zuwan ma nasan yayane ya saka kizo don tayi mai dadin baki.
Aifa da haka zata sayeku kaf daga karshe sai duk kun raina kanku da ita don bata da kyau idan halinta ya motsa kin ganta nan ni bakiga ko gaisuwa bamayi da ita ba .
Nidai shiru nayi ina saurarenta sai gwaggo shafane ma ta biye mata take bata amsa a karshe wuri na samu na zauna suma suka biyomu suka zauna din.
Muna nan zaune a wurin saiga wata tazo wai nazo don Allah yayanta keson magana dani yi nayi kamar badani take ba don hankalina yana gun wayana banko kallon bidirin da akeyi a wurin.
Maryam ce ta dan taboni nadago kai take fada min abinda budurwan tazo dashi dan murmushi nayi ina fadin ayyah don Allah ki fada mai tare da iyayyena nake zaune ai.
To ki ban number wayan ki saiya kiraki nace bana haka ni keko tashi mana kije kiji gwaggo sha ta fadi Allah ya taimakeni budurwan bata jimu ba nace ba inda zani numban dai aka bata ta tafi.
Ganin samari zasu rakura min kuma ga magariba yayi yasa nace su tashi mu tafi maryam tace ina zaku samu mota a nan.
Nace kada ku damu zamu samu a daidata sai mu shiga hakan mukayi muka samu masu adaidaita muka shiga sai zuwa gidan don da ankai unguwar zan gane kwanan gidansu.
Dan bayaro ne yayi sallama kofan gidan malam musa yace ace anawa saurayin gidan nan bako sallama yaron na shiga ya samesu a zaune tare malam musa ya fadi sakon dan bayaron .
Da fillanci saidai ba wai irin filancin nan da kowa ya iya irinsa bane wanan zakace wani yare na daban yakeyi ba filanci ba.
Shi malam musa din yacewa yaron yaje yace yana zuwa bayan fitan yarone malam musan ke fadin kayi hankali da yaran garin nan kasan mu fulani akwai mu da zuciya sosai.
Kasan yadda zaka taka da kowa ka samu ka rabu lafiya dasu har ka bar garin nan kada ka yarda ka jefa kanka cikin wani kungiya tasu nan din.
Nagode baba ya fada yana mikewa ya saka takalman shi ya fice daga gidan tsaye ya samu dan bayaro ya bada baya ya tokare hannun shi a jikin iccen mangoron dake kofan gidan ya kuwa wani waje idanu yana kallo gami da tunane.
Kamar yadda addini ya koyar ga musulmai suyiwa dan uwa sallama don falalan ladan dake cikin hakan shima dai sallaman yayiwa saurayin jin hakan ya juyo yana karbawa.
Suka mikawa juna hannu suka gaisa kadin dan bayaro ya fara bayani da fadin wallahi Allah ka ganeni nazo maka a bazata so nake ka rakani cikin mambilla naje na sayo yadi ai min irin dinkin nan naka kafin ka koma dan kayan yana matukar karban jikin ka sosai.
Kowa a karkaran nan yana maganan hakan kaidin ka iya kwalliya na birgewa sosai wallahi sai muje tare ka tayani zabben yadi mu bada dinki daga nan ma sai mu dan yawata kaga garin sosai.
Dan shirun mamaki Ahmed din yayi kafin wata shawara tazo mai yace to dan bayaro barin koma ciki in sanar da babana cewa zamu fita tare dakai idan ya yarda da hakan ai sai in rakaka ba wani matsala bane hakan.
To amma fitan ma sai baffan ka ya sani sai kace wani mace can yace haka na saba dashi tun a gida bana zuwa wuri ba tare dana fadawa iyayyena don haka sukai min tarbiya.
Koda wurin mace zaka dan bayaron ya tambayeshi cikin zollaya yana dan murmushi yace ai ban isa fara zuwa wurin mace bani yanzu saidai nan gaba kila.
Daga haka ya juya ya koma cikin gidan shi kuma dan bayaron ya bishi da kallon mamaki a fuskanshi don shi yanzu zancen kara mata na biyu yakeyi sanan wanan din kato dashi yace mai wai bai isa zuwa gun mace bama shi.
Sosai malam musa din yayi mamaki amma sai ya kara yabawa da tarbiyan yaron da yayi dabaran fada mai kafin ya bishi dan mutum yanzu ba abin yarda bane gara kasan komai a kan wanda duk kake tare dashi a zamanin nan don boyon baya da amfani ga dan uwa yanzu.
Allah ya tsare a dawo lafiya dattijon yai mashi hakama Shattu dake madafa tana shirin dora masu abincin rana tayi mai Allah ya tsare a dawo lafiya.
Ya fito ya samu dan bayaron suka fice daga unguwar sai binsu ake da kallo don ganin danbayon tare da bakon fuska da yanayin shigarshi ya nuna ba daga nahiyar su yake bashi.
Akwai dan tazara da inda gidajen su yake da cikin gari don haka suna tafiya dan bayon yana masa bayanin komai ba abinda tafi tsaya mai a rai kamar ganin wasu kabila da yayi a cikinsu.
Gasu dai fulanine su amma kuma ba musulmai ba nan dan bayaron yake mai bayanin cewa a cikin su akwai musulmai da kafirai da masu zuwa coci.
Sun isa kasuwan garin ba zaka kira garin da birni ba haka kuma ba zakace dashi kauye ba garine mai abubuwan mamaki ga ni,iman ubangiji a wurin don ko tsaunukan dake zagaye da garin lub suke da korayen ganyayaki.
Shanuko shi zai iya fadin a nan asalin shanun duniya suka fito ga farare ga jajaye ga masu fari da baki ko wani kuma zaka gani garkene tafe sai inda idon ka ya tsayama da kallo.
Basu sha wuya ba samun yadin dan bambamcin kudin yadin kadan ne suka yanka mai yadin ne yayi masu kwatancen tellan da zasu kaiwa dinki yaimasu irin wanda sukeso din yayi kyau .
Don haka dan bayaron yabi dasu inda zasu kai ga tellan da akai masu kwatance din wuri ne mai kyau da aka gyara ga telolinan a shaguna zazaune suna aikinsu.
Ya fadi sunan wanda suke nema din aka nuna masu shi suka karasa shagon nasa tun kan su isa danbayo ya fara fadin aradu wajen nan sai sunci kudin dinki sosai kai malam da ganin yadda aka gyara shagon nan kasan sai wanda ya isane ke kawo dinki wurin nan.
Sallama sukayi shagon suna tambayan Isa tella aka nuna masu shi ya juyo yana fadin wake nema na idon shi ya sauka a kan masu neman nasa sai ya sake murmushi yana fadin.
Ah a a malam Yasir saukan yaushe haka kasan banda labari nazo amsan tsarabata kaga ko shekarab jiya mun hadu da mummuni amma bai fada min ka dawo ba.
Sam shi Ahmed din bai san dashi ake zancen ba sai da ya dan waiga yaga dai shi matashin tellan ke kallo a lokacin .
Hannu ya mika masu suka gaisa a nan ya dan kallesu tsab ya gane cewa ba wanda yake zato bane ashe a cikin yaresu na mambilla yake fadin wallahi nayi zaton Yasir ne dan gidan Alh dan gaske.
A,a wanan kan bakone shi daga wajajen sokoto yake dan bayaro ya bashi amsa yace ikon Allah malam wallahi kana da kama da yaran gidan dan gaske sosai don har kamar ya baci.
Tellan ya fada da hausa danshi da gani ya dan taba barin gari yasan ta kan duniya sosai a, a bashi bana Ahmed din ya fada ya fara yiwa tellan bayanin abinda ya kawosu din yace ya gane a wurin cinikin dinkin ne dan bayaron ya tsure don jin kudin da tellan ya tsaga mashi ya bayar.
Kaiko dai ina laifin kace muna dari biyar shikanshi Ahmed dinn murmushi yayi don jin abinda abokin tafiyanshi din ya fada a lokacin.
Jin yadda dan bayaron keson badasu yasa yace kai mune dubu da dari biyu yasa hannu ya ciro kudi yabawa tellan yace yaushe zamuzo mu karba.
Ikon Allah halin ma iri dayane wallahi tellan ya fada koshi yasir baya son dogon jayayya sosai haka yake min idan yazo ya samu muna ciniki da wani a nan.
Murmushi kawai yayi ya kara fadin yaushe zamu zo karba tellan ya dan tsaya yana tunane kafin yace kuzo ranan jumma,a da karfe hudu in sha Allahu zaku samu na hada don ma kaidin ne don da sai bayan sati biyu kuzo ku karba din.
Sukayi sallama dashi yana jin suna maganan shi a shagon ta kamarsu da wancan da suka kira da yasir yasa kai ya tafi yana jin wani abu a zuciyar shi game da hakan.
Sayayya dan bayaron ya danyi shi kuma bread da kayan tea ya sayo masu sai kayan miya daya rikowa shattu masu yawan gaske.
Har sun kamo hanya sai dan bayoron yake fadin barin bi dakai ta cikin gari don kaga garin mu da kyau kasan garin mu ba kauye bane Allah ya albarkaci garin nan da arziki mai yawa sosai ga kiwo ga noma da mutanen mu keyi duk da bamu da wajen noma sosai amma haka mutanen wanan yankin namu ke kokari.
Madaran shannu daga ko ina har kasan waje ana zuwa a dauka nan suna tafiya dashi kasashe da dama shiyasa mu nan da kiwo muka dagora sosai a nan.
Kaga ikon Allah ashe rabo ke kiran mu ga dangaske gari ko bamu samu komai ba masha kallo a gidan nasa ai kaga inda daulan duniya ta yanke saka a nan.
Shi din mai kudine sosai suke kuma da sauratan garin nan a yadda naji ana fada a gari cewa kaf karkaran nan daga chedi wuro garba chedi gembo duk babu wanda yai arzikin shi a kasan nan.
Baffa na ban tarihin shi cewa a baya an turashi cikin duniya saida aka tashi tsaya rana tsaka sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login