Showing 132001 words to 135000 words out of 304363 words

Chapter 45 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33307

hakan bamu nemi juna dashi mun gaisa ba.
Kamar yadda kowa ke rayuwa haka shima din a yanzu ya jajirce sosai a wurin neman na kasa kuma yana samu don Allah yai mai budi ga sana,an da yakeyi din.
A cikin hakane yayi shawaran tayar da daki ta wani barin gidan don da wanan burin ya taso a ranshi na ganin ya gyarawa dije dakin da take rayuwa a ciki wanda har itatuwa ansa daga baya an tangale mata su don kada ginan ya fadi.
Wanan yasa yasha alwashin idan ya samu budi zai tayar da gina yai masu dakuna su koma ci yanzun ma din da yaga yan canji na shigo mai sai ya yanke shawaran yin hakan sai gani kawai akayi ya tayar da gina a cikin gidan nasu.
Ba zargi don kowa yasan sana,anshi yana samu sosai a yanzu zai tafi gari gari ya dauko hatsi ya shigo dashi zamfara yabawa yan sari su sara su dora mashi riba gobema zai koma wata jahar ya dauko ya kawo ya sayar masu da haka sana,an nasa ya fara bunka sosai.
Ga nauyi ya karu mai a yanzu mijin mahaifiyar shi ya mutu a sanadiyar macijin nan daya sare shi zancen su dawo gida akeyi yanzu da iyalinta don ta haifi yan mata biyu da mutumin gashi ba wurin da zasu zauna a nan din idan sun dawo.
Maigidanshi ne ya bashi shawaran cewa ya tayar da dakuna biyu gami da nasa da zai zauna ciki da falo da bandaki ya hada da kitchen ya dinga karasawa a hankali.
Baiki shawaran maigidan nasa ba ya fara da hakan aka tayar da dakunan saidai lokacin da akazo fitar da foundation din ginan anyi dashi ya bari a sare iccen tunfafiyan nan yace sam bai yarda a saremai ita ba.
Don Allah yasan dalilin fitowanta gidansu gashi har makwabta yaga sun fara shigowa diban ta ta baje tayi kyau ta samu wuri gwanin ban sha,awa da ita.
Antayar da aikin zangazanga an fitar da ginan yadda yake son ya kasance don ya raba barin shi daban dana su Dije din a lokacin da ginan ya dan tasa sai aka dakata da nasa anci gaba da ginawa Dije da mahaifiyanshi inda zasu zauna su daga dayan barin kuma akaja nasa din kamar yadda maigidan nasa yace yayi din.
Abinka da kudi kasa tunda ba wani gina bane nasu dije din na azo agani nan da nan aka kai linta aka dakata bayan sati biyu kuma aka dora inda aka tsaya da ginan kafin wata biyu ya gama gina part din su Dije saiga gidan ya fito ras dashi ba zakace rubaben gidan su bane hakan yadda wurin ya haska.
Dakatawa yayi da ginan ya mayar da hankalinshi wurin sana,an shi don yanzu kan bai zama sam a garin ko yaushe yana wurin sana,an shi yana neman kudi yayin da ginan shi kuma yake danyinsa a hankali idan ya tara kudi.
Muna zaune nacewa hanne ta tashi muje ta rakani unguwa na karbo sako da ummah ke bina na kusan kwana uku ke nan kuma ina jin kiuyan hakan.
Mun karyo kwanan wani layi muka hade dashi saman yar mashin din hawanshi daya saya don zirga zirganshi na gida da sana,anshi kuma.
Yana goye da wata yar matashiyar budurwa da bazata wuce sha hudu ba da haihuwa Hannece ta fara ganinsa take fadin ikon Allah ga master namu can fa.
Jin hakan yasa na dan juya na ganshi goye da yarinyar saman mashin din shi duk ba komai a tsakanin mu saida na danji ba dadi a raina na danna masa horn yana ji horn din motana ya juyo ya ganmu da hanne din.
Ya biyo mu baya a guje ganin hakan yasa na samu wuri na Parker motar ya cin muna daidai saitina ya karaso da mashin din nasa na sauke glass mukai arba dashi.
Duk ya kara dan rama don ujulan da yanzu yakeyi din ya fara gaidamu tare da tambayan sai ina haka yanzu lokacin school hours ne fa kafin nayi magana hanne ke fadin .
Daga can muke yau malam bai shigo ba ya bamu hakkuru matarsace ba lafiya suna asibiti tun jiya yasa kaga mun fito yayi Allah ya sauwaka.
Lokacin naji ya dan juya yana cewa yarinyar daya goyo din ke baki iya gaisuwa bane halan a, a master ina fa zata gaidamu taga mun cika mata ido haka ?
Dan murmushi yayi don ya gane me hannen ke nufi yana fadin kai hanne baki da dama wanan sister dinace hindu kinsan sun dawo garin nan yanzu da zama har mama ai kwanaki na fadawa kawarki mutuwa mijin mama din ko ?
Sai lokacin na dago kai na dan kalli harinyar gaskiya suna da dan kama ta jini saidai shi yafita haske sosai ba kusa ba yake nayi a fuskana tare da fadin kai amma ai baka fada min suna garin nan ba .
Da munzo da hanne mun masu gaisuwa ai a nan ko yanzu ma bai baci ba zamu shigo ai idan muna free hannatu ta fada daga gefena.
Wanan me tsoron akuyar ce zata zo gidan mu Dije tun tana tambaya har yanzu ta gaji ta daina tambaya dana fada mata gaskiya.
Ita wanan wake maganantane da tsoro ko kadangare ta gani yanzune zakaga tana batun shudewa a wurin saboda tsoron tsiya na dan harari hannen nace magulmaciya.
Yace well barin kyale ku kada insa ku makara don naga kamar kuna nisa sai kuma wani lokacin ke nan idan mun hadu jakkata nake kokarin budewa naji ya tayar da mashin dinshi yana fadin zan kiraki zahra akai abinda nake son tambayan ki.
Saina jika nace ina mikawa yarinyar kudin dana dauko tare da fadin yar makaranta gashi tunda baki gaida muba nina sayi gaisuwan naki yanzu.
Alaman kunya ta nuna ta amsa tana min godiya naja motan na barsu a wurin kafin yayi magana muka karbo sakon tare da komawa school.
Sam na mace da zancen kiran nasa sai bayan kwana biyu har na kwanta naji wayana tana kuka na dauka na duba ina mamakin me kirana a zatona ma ko maryamce da a yanzu muka zama kawaye sosai muna waya kai dakai da ita.
Ahmed na gani yadda nayi serving din layinshi din na daga yake fadin na zata ai har kinyi barci ne zan kashe don kada in tayar dake daga barcin.
Nayi murmushi tare da fadin banyi ba ina dai shirin yi yanzu kenan ka kirani muka gaisa sai ya sanyi shiru kamar yadda nima nayi shirun ina saurarenshi.
Yake fadin Zahra dama akan zancen kudin kine dake hannuna ina son in mayar maki da abinki yanzu tunda na samu alheri sosai ta hanyar su.
Da wanan da muka tsunta din kema zance maki wani abu daga cikin kudin tunda an juya an kuma samu yanzu don gaskiya Alhamdullahi.
Uhumm kawai na iya fadi na dora da cewa aini ban baka din ka dawo min dasu ba taimaka maka nayi ka kara jari dama dasu don haka don Allah ka bar zancen nan please.
Zahra kudine masu yawa fa ko har kin manta yawansu ne wai nace ban kuma son in sake tunasu ko a yanzu in ma kana son wasu zan iya baka iya karfina don har gobe Abba yana bamu dakuma su yaya musa suna nan min ajiye din bana sayen komai ni.
Yanzun dai kina nufin naci gaba da juyasu ke nan baki da bukatansu yanzu eh ka juya din na fada a gajarce idan kin bukata lokacin da bandasu fa ya fada.
Don gina nakeyi yanzu ina tsoron kada kudin naki ya shige ciki dan murmushi nayi din jin meya fada kafin nace ayi gina mai kyau dai Allah ya bada ikon gamawa lafiya.
Zahra kin daureni da yawa bansan me zance dake ba yanzu nima haka don ban baka kudi da sunan aro ba sai don ka samu binda zaka tallafawa rayuwan ku .
Yanzun kuma wani nauyi ya kara hawa kanka tunda ga su mama sun dawo karkashin ka kuma yanzu don haka ni kyauta na baka kada mu kara zancensu dakai don Allah ina fadin hakan na kashe wayana.
Na barshi rike da waya da mamakina saiga text dinshi ya shigo min yana fadin zahra muna magana dake kin kashe waya godiyanane bakya son ji to nagode Allah ya bar zumunci a tsakanin mu ya karawa baba lafiya da mama.
Wani iri naji har hakan yasa nadan runtse idanuwana tausayi ya ban naga duk irin cin mutuncin da Abban mu yayi mashi hakan bai hanashi yiwa Abba din addua mai kyau haka ba.
Har muna batun fara exam banyi zancen zuwa gidansu Ahmed ba ganin hakan yasa hannatu ta tuna min zancen zuwa gidan banyi magana sai washe gari na dauketa mukaje wani shago muka danyi sayayya a shagon .
Da kwatance muka iso gidan saidai yaran muka samu manyan basa gida tun waje suka taremu suna fada muna muka mika masu kayan da muka sayo din hannatu tace idan sunzo a fada masu cewa abokan karatun Ahmed ne suka zo masu gaisuwa.
Muka ja mota muka tafi ina godewa Allah da bankai ga shiga gidan ba muka samu wucewa don na tsani ganin wanan bakar akuyan dake gidan.
Gashi su sunki rabuwa da akuyar kamar ta tsafi a gidan ina wanan tunanen har bansan lokacin danaja tsuki a fili ba har hanne ta juyo tana tambayana ko lafiya ?
Just forget about it wanan bakar akuyan tasu nake tsoro nake godewa Allah da ban shiga ba na ganta yau daba zan iya barci ba sai nayi mafalkinta a karshe.
Lokacin da Ahmed ya dawo ya shiga gaidasu ne Dije tana washe baki tana fadin yau da alaman yar arzikin nan ta shigo wai tazo yiwa uwarka gaisuwa bama nan.
Har suka kawo muna wanan abin arzikin haka wai ace muna abokan karatun kane suka zo da motar su yaran nan na fadin abun gwanin ban sha,awa.
Dan Dije ina kasan yaran masu kudi haka har suna zuwa da wanan irin alherin mai yawa haka uwar ta jefo mashi tambaya daga inda take zaune kofan dakinta tana cin abinci.
Yace mama gashi sun fada abokan karatunane su din yar gidan wani mai kudine a garin nan jinin mu ya hadu dasu muke cin alherin su haka.
Dan Dije kabi sannu banson daukan magana ka tsaya matsayim ka da Allah ya ajeka kada ka dauko muna fitinan da yafi karfin mu don hurda dasu tonon asirine a gareka karshe.
Wane irin magana kikayi haka mara dadin ji don suna mutunci shina ka zama tonon asirinai ?
Ba hakana bane inna ke san yadda duniya yanzu ta koma kowa baison ka rabai ka karu yar mai kudi sai dan mai kudi irin ta hakama dan tallaka ya tsaya matsayinai.
Yafiki sanin haka shida a namiji yana jin irin abubuwan daka hwaru a gari yace maki soyayya yakai da ita ina zai fara haka gwalmadiya,i ya debowa kainai ruwan dahwa kaine .
Wane uba ka tsaya mai duk garin nan a bashi yar gidan mai kudi dan dama dama da ubanai ya tuna dashi har ansanshi a dauki mata a bashi.
Nina dade ina jiyowan wan ga ranan gare mu don nasan a lokacin nan za a tayar muna da tsohon hwamin daka zuciyoyin mu anyi haka dauri balle yanzu da kan kowa ya waye.
Wani iri yaji a zuciyar shi daga shi har mahaifiyan tasa sai da kibiyan tsoro ya caki zuciyar su lokaci guda uwar tasa ta dauka da fadin .
Yanzu ai kin gane abinda naka nufi ke nan ni rigimana banison ya dauko wa kanshi da abinda yasan bashi yuyuwa garai.
Wanda ko ubane bai taba gani ba sunan kana dan halal ne kawai kaka zuwa gidan masu hannu da shuni kakai kan ka ?
Wa hwada maki bansan ubana ba saukin abindai ina da uba da yan uwan uba don haka kko hwada min ina bashi amsa yanzu.
Ya mike tare da saka takalmanshi ya fice a gidan Dije na kiranshi yazo yaci abinci baiko tsaya kulata ba ya wuce don rashi daya baci fa baki daya a lokacin.
Wuri ya samu ya zauna a gaban gidan su baisan lokacin da hawayen bakin ciki ya soma fito mashi ba sai ranan ya tuna da malam musa.
Waya ya ciro a cikin aljihun shi da niyar ta kira tsohon don sun kwana biyu basuyi waya da dattijon ba da yanzu ya zame mai kamar mahaifin shi yake jinshi a ranshi.
Ya kira bai shiga ba ya sauke ajiyan zuciya yana sake kiran dattijon sai tayi sa,a kiran ya shiga ya dauka suka fara gaisawa yake tambayanshi shattu .
Sun dan jima suna magana kafin su kashe wayan suyi sallama da junan nan su ya bike ya buga mashin dinshi ya bar unguwar bai dawo ba sai cikin dare sosai ya shigo gidan ya samu wuri ya kwanta.
Lalai kan naji labarin cewa su Aisha sun tsayar da mazajen aure kuma na tayasu murna sosai ga hakan sam ban kawo rai da cewa wai don sunyi hakan nima na fitar da miji kona fara kula samari ba don ba rasasu nayi akwai su saidai babu fuska gareni ne don irin tsawatawan da Abba yai min a baya.
Yasa yanzu na kara mayar da hankalina sosai wajen karatuna ban yarda koda wasa ma in tsaya da wani wai ina zance.
Allah sarki ashe duk da hakan ba tsira nayi ba a wajen mama don sun hada min bom nida ummah dayasa zukata baci a gidan namu don ko Abba yai wani zuwa gaisuwa .
Don anyi rasuwa suka zo hardasu yaya musa da ya jafar lokacin nan mazajen su Aisha suka zo gaida Abba din kuma suyi masu gaisuwa.
Bayan sun wuce ne da dare suna falonshi da yayyunmu maza ana maganan a kai har aka jefo zancena cewa ni wana tsayar ya musa ne ya tare da fadin.
Haba dai Abba Zahra fa karatu takeyi yanzu bawai lalai bane ace sai tare za ai masu aure dasu kafin ya karasa mama ta haushi da fada tana fadin to uban mu.
Zama zarayi gidan ku jikata kusha ko me yarinya da wanda take so zaka wani kawo tsurku ka tare kana fadin wai tana wani karatune yanzu.
Suma din ai karatun sukeyi bawai sun gama bane ko wanene take so yanzu din Abban ya tambayi mama din tace a wanan yaron daine na kwanaki mana don basu rabu ba tunda shi take so.
Yaron da baida asali din dana rabata dashi ashe ta nace saishi mama tace a toh suna dai tare don basu rabu ba gaskiya tunda bata ba wani fuskan zuwa ba.
Abba baida asali kamar yaya ya musa ya fada cikin dan bacin rai yace ta fada min fa ubanshi dan shiyoyin gabas din nan nd kuma har yana zuwa garinsu .
Mama tayi saurin fadin kaji ba Alh ai na fadama ka barta kawai tayi don kada ta jawo muna abin kunya don Allah shi aure ai mukaddarine in Allah yayi shine mijin ta ba makawa sai anyi auren nan Alh.
Da rabo yazo ya kashe ai gara ka yarda ka aura matashi a zauna lafiya haba haba mama wanan maganan bai dace ba haka ga zahra don kowa yasan irin natsuwan zahra din.
Wanan yarinyar na gane abin kunya take son ta jawo muna kawai Abban ya fada cikin bacin rai mama tace ai shi nake fadama wa yan nan sakarkaru suna wani tarewa kada in fada.
Karshe in wani mugun abu ya faru duk laifin mu za azo agani ace mun saka ido akai barna a gidan nan yadda take magana zakace wani mugun abu nakeyi a rayuwana.
Abba yai shiru na dan lokaci kafin yace shiyasa kwanaki da sukaje kano karima ta samo mata wani a can yarinyar nan taki zancen nan .
Kadai fada kaima yanzu ai indai har abu ya kwabe wanan kuma kai kajawa kanka Alh Abba din bai iya cewa komai ba a lokacin sai shirun da yayi.
Bayan kwana biyu abin yana cinsa sosai a ranshi ya kira maigadin gidan mu yana tambayan shi wayaga yana zuwa wurina ?
Mamakine ya kama maigadin yace Allah ai mama boyar Allah ce don ban taba ganin wani yazo gidan nan ba wurinta da sunan hira ba.
Idan ta dawo ta shige gida ta shige ke nan sai kuma idan zata fita da safe gata bata kara lokaci ga yadda ta saba dawowa kullun.
Tashi kaje kawai Abba ya fada ya mike yana mashi godiya ya fice daga falon Abba ya dade zaune yana tunane kafin ya yanke shawaran abjnda yake gani daidai a gareshi yabarwa cikin shi sauran zancen.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
4️⃣6️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login