Showing 78001 words to 81000 words out of 304363 words
don Allah ki yafe muna munyi kuskure hakan ba zai sake faruwa ba itama ta fice.
Sai mama dake mikewa tana fadin na kula matan nan da sunana tashigo gidan nan wallahi sai nasa tayi nadama fadowa rayuwata a cikin gidan nan.
Keko kikan fara maganan ki yanzu me kikaji ance dake kan abinda ta fada hjy tsohuwa ta fada sai Abba ya amsa da zandai fada din hjy yanzu ina dadin irin wanan abinda maimuna tayi ai gaskiya karima ta fada yanzu.
Kece da girki a dakin ki kuma hjy take zaune amma kin kasa girka mata abinda zataci don shashanci kuma in anyi magana hjy ki tare kada a fadi.
To ai yanzu ga yar gaskiyan nan ta fadakar dakai gaskiyan ko da hakan wanan saurin sanyin hali irim naka har kazo ka sake ta juyama gida daga kai har iyalin ka kuna kallo.
Hjy wanan zancen gaskiyane ta fada wanan itace mai laifi kuma baki son a fadi saiki tare mata to kiyi hankali da karima da kike gani haka sosai don nasan da tana daga maki kafane akan komai .
Ficewa tayi bata tsaya jin karshem maganan shiba don bai goyi bayanta ta dau fushi dashi tana kulla hjy karima a zuciyar ta don in batayi hankali zata iya kafa gwaunatinta a wurin Abba don irin haka.
Shara ya tashi dashi yana gyaran gida da kone konen da bai samu tsayawa yayi masu gyaran sallaba a gidan yazo kusa don haka ysu ya tashi da gyare gyaren cikin gidan nasu.
Yazo gurin wanan tumfafiyan daya fito masu a gefen katangan gidasu din ta cikin gidan nasu mikewa yayi tsaye daga duken da yake ya zubawa tsiron ido yana mamakin saurin girman da dan icen yayi lokaci guda.
Wurin randan ruwansu ya nufa ya fara debo ruwa yana zubawa icen zakace an shuka icen ne ana son yayi girma a lokacin .
Dijece ta fito daga dakinta da niyar tambayanshi ya jikin nasa saidai tana fitowan idonta yai tozali dashi a wurin tumfafiya ya kura mai idanu kaman yana nazarin tsiron ne.
Amadi kardai kuma cireshi kake sonyi tanan din bayan ka barshi ya girma ya gama hayayyefa a gidan nan koda ka cireshi a nan din indai tumfafiyace komai daren dadewa wata rana sai ya dawo gidan nan kuma .
Ba cireshi zanyi ba ruwa nake zuba mashi don an dade da dauke ruwan sama baya samun ruwa murmushi ta sake tare da fadin kaiya yaro dai yarone .
Kai in banda abinka Amadi kataba jin wanda yaiwa tumfafiya banruwa don ya tofu da kyawo shida keda ruwan Allah a jikinshi ina ruwanshi da wani ruwa can.
Ganin bai kulata ba yaci gaba da harkokin gaban shi yasa Dije din barin wurin ta nufi wurin murhunta don ta hura wuta ta dora masu abin kari a gidan.
Ta gwama dan icen daya saura masu a gidan cikin wuta na karshen take sakawa a murhun mafarkin icen da mutumin dayazo yana mata sallama a na gobe za a fara azumi ya fado mata a rai.
Zubur ta dago daga duken da take ta juyo tana kallon jikin nata dake aiki kafin ta kai kallonta gun uwargarke dake tsaye tana kiwon ta sosai gashin jikinta ya dawo yayi kyau yanzu.
Ta zama cikkakiyar akuyan data koshi da kiwo tayi bulbul da ita a yanzu kodai sai kuma ta kasa fadan abindake kasan zuciyar nata .
Aikin dake gabanta ta fara bayan ta hura wuta ta dauko tukunya ta dora saman murhun ruwa ta debo ta zuba cikin tukunyan daki ta nufa ta dauko Sauran tuwon jiya daya rage masu gidan ta dawo ta zauna tana barewa.
Har lokacin mafalkin na mata yawo a zuciyarta tana kokarin tuno da abinda bakon fuskan cikin mafalinta ya fada a ranan saidai ta kasa gin hakan .
Bata jin zata iya tunawa da abin saidai nan gaba kila muryan Amadine ke fadin yanzu idan mutum yace zai tafi garin mahaifina nawa zai kashe kudin mota Dije ?
Kaita dago tana mashi kallon mamaki don jin abinda ya fada din a lokacin cikin mamaki ta sake tambaysn shi Manbila fa kace Amadi ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
2️⃣5️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Ki daure ki biya ba tare da shiga hakkin wasu ba yar uwa zaki karu na karu har wasuma su karu damu.
Eh Dije ina son jin kudin mota zuwa can ne don naji idan nisa ko yawan kudin mota ya hana mahaifina zuwa ya dubani har wanan lokacin na kuma san shin yana raye ya watsar dani haka na zama mara gata a cikin garin mutane ko wani dalili zai ban nayin hakan dani.
Amadi meye damuwan ka ga hakan yanzu don ibrahim ya tafi ya barmu da kai hakan ya hanaka rayuwane a duniya ba komai yasa yai muna hakan ba sai kawai don muki yarda da bukatanshi na rafiya da mahaifiyanka can kasar tasu.
Yanzu Dije da kuka hanashi tafiya da inna a wancan lokacin yau ina innan take ?
Amadi auren ta da dan gida yafi muna kwanciyan hankali don ko banza dai munajin labarinta ai jefi jefi kuma nan da can din inda take zamu iya yinshi a cikjn wuni daya mu isa gareta.
Humm Dije ke nan yana fadin hakan ya girgiza kai kawai ya juya ya nufi dan dakin da yake kwana a cikinsa ya turo kofan bayan ya shiga da karfi ta tsaya tana kallon kofan dakin dake makwabtaka da kofan gidansu.
Magana ta farayi ita kadai a bakin murhun da take aiki abinda kowa ya gujewa yarinyar nan ke nan tunfarko da auren bako.
Amma dan uwan ubanta ya tsaya ya kafe cewa tunda shi din musulmine da uwan mu kuma tana so yana so gara kawai a hadasu ai matar mutum kabarisane.
Yau me gari ya waya a hakan da yake mayaudarine yaso cuta bai tashi cewa zai koma gida ba gaban iyayyen shi saida yaga sun samu rabo a tsakanin su ya bijirowa mutane da zancen barin gari.
Ina zan yarda ya tafi min da ya wani uwar duniya can me nisa da kowa ka tambaya yace ma bai taba zuwa ba yana dai jin sunan garin a bakin mutanene kawaishi.
Wama ya sani ko shi din wani halin banza ke gareshi dama ya baro gida yazo nan ko kuma ya dauketa yaje ya sayar irin haka anyi sunfi goma muna ji a jakkar mogori ana fada.
Har dije ta rarage aikin nata bata bar wanan jininin da takeyi ba ita kadai a tsakar gidan nata kamar tababa sai yankan fada takeyi.
Yan dabbobinta na gefe tsaye sunyi shiru suna kallonta kamar mutane suna saurarenta dan ko motsi basayi a lokacin sai gidan da yayi tsit lokaci guda.
Kwana hudu ke nan da sallah amma gidan namu babu dadin zama ga iyayyen mu don haka fitama a lokacin baida dadi ga kowa dama can ni din ba ma,abociyar yin hakan bane.
Dan dama lokacin da muka dawo sabo sabo garin muna dasawa da mama a lokacin idan na dawo daga school naci abinci zandan je part din ta mu danyi hira da ita.
Sai na fahinci yin hakan wani hanyane da mama din kanyi amfani dashi wurin zolayana taji wani abu game da ummah na saina daina yawan shigan har haka yazo ya faru yanzu.
Don yanzu saidai idan mun hadu zan gaida ita kota amsa min ko kuma ta kyaleni saidai hakan baisa na fasa gaida ita din ba .
Wanka nayi na shirya don tun ranan sallah da nayi kwalliyan sallah din ban kara saka sabbin tufafina da ummah ta tura kudi har Abuja aka dinko min su ba ina kwance ina fama da dogayen riguna irin na shan iskan zaman gida.
Abba ma dukda suna garin ban sakashi a idona ba tin ranan da yai min fada din nan tace kuma in turo mashi Ahmed idan nafita.
Sai yau da korafin ummah dake yawan min fada kan rashin zuwa nagaida mutane yasa na shirya tunda safe na fito dakinta na fara zuwa nagaida ita da kwana.
Kafin na dago na fita zuwa part din mama da nayi sa,a tana falo zaune da yaranta yanayin su kawai zaka kalla kasan wani abu mai muhinmanci suke tataunawa a tsakaninsu.
Dagani fitowan dole tayi lokacin zuwa falon nata ta zauna tana saye da hijjab mai ruwan makuba har kasa suma yaran da hijjaban su sun dunkule sama kujera.
Nayi sallama a kofa suka kalloni na karaso har inda mama din take zaune na dan rage tsawo na gaida ita ta amsa a cikin irin izzanta na manyan mata.
Tare da fadin yau an tuna da gaisuwan ke nan ko dan kuya ya kamani nace kiyi hakkuri mama kwana biyu ina daki bana jin dadine sosai.
Na juya wirin yan uwana da suka kyaleni nace ina kwanan ku lafiya kawai suka amsa min dashi suna kawar dakai ga kallona lokaci guda.
Na juya zan fita muryan mamane ya dakatar dani tana fadin Zahra kuna dai ganin irin cin fuskan da mahaifin ku ke muna a gidan nan yanzu don yayi sabon aure ko ?
Mamah Aisha ta fada daga inda take zaune tana jan tsuki ta kawar da kanta gefe daya ta nuna bata so uwar ta fito min da zancen ba a lokacin .
Dan dawowa nayi ina fadin mama kuyi hakkuri ku barshi kome yayi shida Allah don Abba ba yaro bane yasan abinda ya kamata da wanda bai kamata ba.
Ita kuma idan tazo maku da wata manufane donta musguna maku kanta hakan zai koma watarana don Allah bai yafe hakkin wani kan wani.
Shiru tayi nasan don diyanta da suka nuna basu so tafito min da zancen ba wanda ni kuma nasan damuwa ne ya saka mama yin wanan zancen dani a ranan .
Na dan tsaya nayi jim don narasa abinda zan fada bayan hakan don ban saba irin maganganun nan tsakanina da ummah na ba yasa naji abin bambarakwai sai wanan amsan Allah yaban ikon in bata a lokacin.
Allah ya sauwaka na fada naja kafata zan fita koda ban waigo na dubaba nasan cewa tsukin Aishace mama waida wanan banzan zakiyi wanan maganan kome ?
Ni dai na fice na basu wuri dakin mommy na nufa yana rufe na kwankwasa sai wanan matarce a ciki muka gaisa take fada min cewa tana part din Abban mu na nufi can din don mu gaisa dasu da kwana.
Suna zaune suna karyawa a dining nayi sallama suka amsa min na shigo suka kalloni nakai gurfane Abba na fara gayarwa sai ita saidai Abban tunda ya amsa min bai kara kallon inda nake ba sai ita ke fadin.
Dama kina gidan nan na daina ganin ki ko part din ku na shiga nadan murmusa kadan tare da fadin ina nan mommy yanzu na fito part dinki akace kina nan.
Daughter ke nan ko fushi kikeyi da kowa a gidan a, a nace da sauri lokaci guda don tsoron Abba dake wurin kuma banso ta furta hakan ba gareni.
Yaushe zakuyi hutune nace nan da one month in sha Allah OK zan turo a daukeki zuwa Abuja daga can zamu tafi buki gidan mu autan mu zaiyi aure.
Kallon Abba nayi da sauri don sanin ba zai yarda da hakan ba shima sai ta juya tana fadin Alh kaji na rokawa daughter tare da ita zamuyi wanan tafiyan idan lokaci yayi.
Ba ruwana da zancen ta yanzu tunda bata jin magana ta a yanzu har zahra ce zata fara soyayya da wanan yaron da baida asali baida sana,an yi takamaimai ko wani jigo mai karfi don kawai ta bata min sunan iyalina a gari gaba daya kallon Abban mukayi lokaci guda.
Idona ne ya kawo hawaye lokaci guda don jin abinda Abba ya fada game dani din sai naji tace daga inda take zaune ina wanan zancen anyishi ya wuce ko, Alh bai kamata kana kara tayar da zancen ba a yanzu kuma.
Ya juyo da kyau yana fuskantana tare da min kallon ido da ido yafara fadin kuma ki sani duk na kara jin cewa kin kara kula wanan yaron nan saina saba maki a gidan nan .
Kasa nayi da kaina kafin na iya budan baki da kyar ina fadin kayi hakkuri Abba niba soyayya nakeyi dashi ba dama muna mutuncine dashi kawai a makaranta don taimakona da yayi ranan da kowa ya gudu a wurina da ciwona ya tashi sai ya kawo min taimako tun wanan ranan muke gaisuwan mutuci dashi.
A zatona kamar jikin Abba din ne yayi sanyi a lokacin amma sai naji yace koma meye na fada maki bana son in kara ganin kuna hurda dashi again don yaron bakma kwanta min a raina ba.
Jeki daughter zamuyi maganan dake daga baya zan shigo part din ku in sameki hjy karima din ta fada da sauri na mike zuwa waje kafin nakai part din mu kukan da nake rikewa yaki tsaya min dole da kuka na shigo part din namu.
Kallona umma da kannena da sukai cirko cirko suna min kallon mamaki dakina na nufa ban tsaya gun ummah ba don nasan hakan kara min wani laifin zaiyi kuma.
Gado na fada na fara kuka ina hadiyan zuciya kafin can na mike zuwa bandaki na wanko fuskana na dawo na kara hayewa saman gadon na zauna ina faman tunanen abubuwa da dama a zuciyana.
Kofa aka turo azatona ummace ta shigo dakin don ban dago kai na duba wanda ke shigowa dakin ba lokacin muryan Tani naji a kaina tana fadin .
Haba uwar dakina meyayi zafi haka zaki kulle kanki a daki kina kuka haka kome yayi zafi hakkurine maganin shi kibi umurnin iyayye a zauna lafiya yadda suke son .
Don jayayya dasu baida amfani wani lokacin don abinda babba ya hango yaro baya hango hakan don haka shawaran da zan baki shine kibi umurninsu a yanzu kiyi yadda suka amince maki dayi sai komai ya wuce a tsakanin ku.
Yanzu share hawayen ki barin kawo maki abin karyawa ki karya saiki sake jiki ki nuna komai ya wuce a wurin ki koma kamar kowa a gidan nan.
Don kinsan dama hakan akeso aga kin samu matsala da mahaufin ki shine farin cikin wasu gidan nan ki nuna masu cewa ke din mai tarbiyace da bin umurnin iyayyenki.
Maza ki mike ki saki jikin ki kada ki yarda mahaifinki ya wuce da fushin ki a zuciyarki nan zan kawo maki ko falo zan kai maki abincin naki ?
Da kyat na iya budan bakina da yai nauyi lokacin nace a barshi zan fito falo in karya a nan na fada mata ta juya zata fita nace nagode tace kai ba komai uwardakina ai muna tare ina bayan ki har kullun don mu hjy tayi muna komai wallahi dolene mugani ko mu maganta a zancen.
Ta fita na sauke ajiyan zuciya ina tunane don a gaskiya ba zance ga dalilin kukana ba saidai abinda nasani shine yin hakan da Abba yai min a yanzu zai iya jawo min matsala a karatuna nishi nake ganin dalilin damuwana a lokacin.
Mikewa nayi daga zaune din na nufi falo kai tsaye wurin daning na nufa tun kan nakai zaune kannena suka rufa min da taimakon hiran da suke min har na samu na dan sake .
A wurin Abban mu ya sameni zaune muna hira da yan uwana suna ganin shi suka nufeshi suna fadin yaushe za,a kawo muna keken mu.
Daga inda nake zaune nake fadin welcome Abba ya amsa min yake fadawa yaran cewa yau idan na koma zan sayo maku na aiko maku dashi.
Hakan yasa na fahinci cewa a rana zasu koma ke nan ashe bedroom din ummah ya nufa yaran suka dare don ba mai shiga idan Abba din ya shiga nan din.
Muna zaune tare dasu suna murna ya dan jima sai gashi ya fito daga dakin a tsakiyan falo ya tsaya yace maamah zo nan na taso da sauri daga inda nake din zaune nazo na sameshi tare da dan rage tsayina gareshi .
Hannuna ya riko ya dagoni ya fara fadin ki kula da kanki mamana bana son yawan shiririta ki natsu kiyi karatu yadda ya dace kamar kowa ni da kaina zan zaba maki abinda ya dace dake in sha Allahu.
Na amsa da to Abba na gode in sha Allahu zan kiyayye ka yafe min abinda kake zaton inayi a bayan ka wallahi Abba hakan ba gaskiya bane.
Is OK ya fada yasa hannu a aljihunshi ya ciro kudi masu yawa ya miko min yana fadin ki kula na fada maki ga wanan ki mayar da