Showing 270001 words to 273000 words out of 304363 words

Chapter 91 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33275

koya masu yadda akeyinsa kuma.
Ko wani rana likita yace mu koma muna zuwa a ranan su dubani haka kuma sun tabbatar min abin cikin cikina lafiya kalau yake kwance kuma yana samun abincin da yake gina jiki.
Har watan haihuwana ya kama lokacin na gama fita a zahra na don nauyin cikin da yai min yawa sosai amma haka master ke ban kwarin gwiwa akan cikin yai min kyau sosai na daure na dinga ciki akoda yaushe don Allah har na haifa mai sha biyu.
Na kan kalleshi ince oh don na tsofe da sauri kaiko lokacin kaji dadin dauko yar yarinya kuna sheke ayan ku ina kallo yakan yi murmushi kawai bai ban amsa saidai yayi dariya ya fita.
Har ranan mukai haka gaban dije budan bakinta sai cewa tayi aiko daya zamo butulun duniya duk wanan harcin da kike masa yace zai dauko wata ya juya maki baya don ya kara aure.
Auren me zan kara kuma dije ku din nan ku biyu ku isheni a rayuwata don baku rageni da komai ba da har zanji wani sha,awan kara aure nan gaba kuma.
Kai dai kada kayi alkawarin hakan don maza baku da tabbas nan zakazo kana muna dadin bakin ku na maza kana fadin dije kibata hakkuri ta barni in kara.
Baki na turo ina fadin ni ina ruwana ni zanfiso ma ka kara yanzu basai lokacin dana fara ragwabewa ba lokacin da karfina ya kare in dinga ganin takaici a idona.
Duk yadda kika koma nan gaba haka nake son abina haka kuma zan zauna dake a cikin kauna don kin wadatar dani da komai a rayuwata.
Namiji ke nan na fada ina mikewa saboda fitsarin dake damuna a lokacin na barsu a wurin sai dai a zuciyana tunane nakeyi duk wanan cika bakin na yanzu ne dubama da tun bamu kai ko ina ba amma inna na burin taga ya kara aure.
Don hakane ban matsawa rayuwata cewa ba zai kara min kishiya ba don ko banza na taso a gidan mu naga uwata da kishiya don haka nima kuma matar musulmice kuma ba haushe ba zan debe raina ga kara kishiya ba nan gaba ko kusa.
Ga yan arewan mu dasun rike dan canji sunji aljihunsu da nauyi ba abinda ke zuwa masu farko sai karin iyali sai a manta da duk kokarin na gida idan ma ba a dace ba keta gida kinkai zuciya nisa ba.
Kece a karshe zaki koma abokiyar gaba ga mijin da amaryansa don zasu koma su hade maki kai sai diyan kine zasusan damuwanki da bukatanki saboda kin zama tamoji.
Watan haihuwana ya kama kullun mahaifinsa na kira ya tambayi lafiyata dana dije don itama tana ganin likita a nan din tun zuwan mu master ya kaita asibiti ana dubata.
Har Allah ya saukeni lafiya na samu baby girl fara sol da ita tun a asibitin mukayi posting din haihuwan wai ashe duk wanan abin mama da yaranta basu san cewa ina da ciki ba kuma ummah bata fadamasu ba.
Ta yayama zata fada masu mutanen dako sunana basuso a kira a gabansu tun bayan tafiyana tsanar mama ya karu a kaina.
Aishace ta fara gani tana duban status taga na saka Alhamdullahi Allah ya saukeni lafiya ga baby ku kuyi mata addua inganttace saboda Allah.
What ta fada da karfi hannu na rawa tayi zooming ta kara kallon photo da kyau ga nurse din turawa a kaina su biyu suna dariya daga gefena.
Zahra zahra ta fada sau biyu kafin ta danna kira layin mama tana dauka tace mama wai dama zahra ciki garetane har ta haihu bamu sani ba ?
Zahra wace zahra ke nan zahran mu mana mama zahra dai ta gidan mu yanzun naga tayi posting a waya ta haihu kuma a asiniti na ganta tare da nurse balle nace karyane.
Zahra ta haihu fa kikace dama cikine da zahran tunkan ta bar kasan nan ashe au kema mama baki sani ba ashe ?
Wallahi ban taba jin hakan ba ko a bakin Alh kuwa in kuma ya sani bai fada min ba sun munafunceni ke nan shida salma suna daukata muguwa ko me ?
Mama ki dai binciki Abba ko ya sani wata kila shima bai sani ba fa kai amma salma takai makiran mace har zahra tayi ciki ta haihu bamu ji ba .
Lalai wanan matar a barta wurin zurfin ciki da bakin hali zanko nuna mata nima yar iskan kaina ne don inbata fada min da bakinta ba zan nuna mata kamar banji ba nima a tafi a hakan.
Sai ga wayan Rukky ta dauka tana fara,a tace wai mama ashe zahra ciki gareta ta haihu yanzu wata kawata ta bugo min amma zahra taji dadin ta wallahi.
Ke banson shashanci kawarki data bugo maki uwarkice ko kuwa idan naji kin kara zancen nan ranki zai baci kuma ki saurareni da kyau kiji kada inji kinwa salma barka idan kinzo gidan nan.
Amma mama ita ai tana kiran mu mu gaisa don haka kinga ba dadi ta haihu bamuyi mata barka ba ai ta fada cikin wani murya.
Idan ta kira ta fada maki yi mata murna a waya shike nan idan bata kira ba ki shareta kinji ai naji mama ta fada a sanyaye ta dangwarar da wayan tana jan tsuki.
Ba afi minti goma ba ummah tayi sallama dakin ta amsa a gyatsare ta shigo suka gaisa take fadin hjy kinyi sabuwar kushiya fa don Alh yau angone.
Yarki ta sauka lafiya dazun nan suka bugo muna ta haihu cikin iya tako ta dago kai tana fadin wace yar tawa tace zahra ta sauka yau da asuba din nan.
Zahra dama zahra nada cikine koda ta tafi haba hjy maimuna zakice bakiga ciki a jikinta ba lokacin ina zan gani tunda ba a taba fada min ba cewa tana da ciki.
To ta sauka dazun ummah ta fada Allah ya raya tace kafin ta fara kiran mai aikinta tazo ta dauke cup din data karya dashi a gabanta ganin hakan yasa ummah ta juya ta fita sai ji tayi mama din na fadin.
Saukin abin dai kowa ya haifa ai dan haka ba maima wani cin fuska kan da a gidan nan idan banyiwa mutum ba yace zai mun sai mu zuba dashi ai.
Kai jama,a ummah ta fada data shiga part din ta Tani ta kalleta tace tayi halin ko ummah tayi murmushi tace bari Tani gara da Allah yasa bakije din ba da kinsha bakar magana yau a wurinta.
Don cewa tayi bata san wanan yar tana da ciki bama wai wai mutum tsufa baisa ya tuna da mutuwarshine bafa a nan zamu tabbata ba fa ?
Abu dai anyishi tunda kurciya yanzu girma yazo ba za a gyara hali ba a zauna lafiya kullun abu sabo yake komawa kullun ya kamat ace zuwa yanzu an aje wanan kishin ana duba yara kuma.
Hjy ke mai tunane kika san wanan amma ita hjy ai har yanzu duniya sabo yake gareta sam wanan matar bata tunanen mutuwa ko kadan balle ta daina wani halin nata.
Tani me akewa kishin yanzu shima wanda ake fadan donshi ta kansa yakeyi yana neman lafiyasane da abin rufin asiri tunda komai ya kare yanzu kowa ya gudu.
Ai hjy akwai rufin asirin Allah don ba kowa bane zai gane hakan yanzu saina tare daku kadai zai gane gaskiyan su kuma masu gudun dama akwai ya kawosu ba mutunci ba.
Don shege akewa ya manta halarci yanzu mu mugudu muje ina ai sai duniya ta zagemu kan zunubin mu.
Abba ya bugowa mama waya yana zolayanta amma haka mama ta fuske ta nuna mashi shidai akaiwa haihuwa tunda yarshi ta haihu ba yarta ba.
Yaji maganan bambarakwai yasan akwai magana don haka yace to Allah ya sauwaka dama na kirane don mijin nata ya kirani kan zancen su, , ,
Alh ba uwarta na nan ba ka kirata mana ku shirya abinku don Allah ka fitar dani cikin wanan zancen bana son fitina ka barni kawai.
Ok shike nan Allah ya sauwaka zan kira ita salma din tace yafi ummah din ya kira suka aje yadda za ayi zasuyi taron sunan su a nan gida kamar yadda aka saba yiwa kowa.
A wurin mahaifinshi ya samu aka zana suna gidan inna da gidan mu akai taron sunan kamar yadda aka saba a al,adan bahaushe.
Inda yarinyar taci sunan khadija sunan dije ya roka a saka mashi mahaifin nasa ya saka mai nan ma gidan inna manyan raguna biyu tasa aka yanka gidan mu kuma rago daya da shanu gidansu kuma a can mambila Abban ya tura akayi komai Allah ya raya muna baby khadija Amin.
Ranan inna tayi yadda take so don komai daga ita sai diyanta suka katantane komai sukayi har da dije ta dauko suka sha rawa da zawarawan unguwar ana hakane sai ga yan gidan mu sun kawo masu gara .
Wanda a wurin mu ya zama kamar ibada idan bakayi ba abin fadene gareka inkayi din kuma yai kadan a fadi ko inyayi yawa a yaba.
Don haka ummah ta shirya gara na gani na fada aka kawo gidan inna din dako har sun fara yada magana da sukaga anyi azahar ba a kawo ba suka fara fadin su wa yan nan mutanen me suke nufi ba zasuyi gara ba ke nan sun samu hanyar cewa yarsu bata gari ko ?
Saiga robobi sunga ana shigowa dashi sai buhuhuna da jarkokin mai da sauran kayan miya na baki ya mutu ga kowa aka shiga kuma yaba kokarin mutanen gidan mu.
Inna ta kara rakashewa tayi yadda ranta yakeso a wanan harkan bamu me kwaba mata sai abinda taba mutane a can gidan mu kuma an kwasa da mama.
Don tun lokacin da taga shanu an kawo da ragp hankalinta ya tashi sosai ko kadan ummah bata sakata cikin sha,anin ba kamar yadda tace taje tayi ita kadai.
Nan kuma mama din ta shiga yankar kauna tana zagin su gwaggo shafa wai sune munafukai don sunga arziki yanzu idanunsu ya rufe a wurin ci.
Saidai duk abinda akayi ummah tana dibar mata nata har hjy tsohuwa kakarmu anci ansha don master ya taimakawa ummah da Abba da kudi yace su kara wurin harkan sunan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/6, 10:49 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
9️⃣2️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Zance komai Alhamdullahi a yanzu shekaran mu uku master ya zamo babban mutum don kwarewanshi ga aiki da kwazo yasa ya samu daukaka a wurin manyansu suka sandashi.
Hakan ya jawo mai farin jini garesu sosai inda brother Bisi shine ubangidanshi yanzu ko ya samu wasu amma dai suna tare yana bashi girmansa dai har goben kuma bai abu ba tare dashi ba.
Don haka alakansu take da karfi kamar yan uwa na jini ya daukeshi goes father din shi a can shi kuma ya rikemu as a kannensa na jini saidai har lokacin mahaifiyarshi bata da wanan labarin.
Don data sani da ta fadawa mama, mama kuma ta samu abin gori ga ummah ko ta dinga fadan abinda bashi ba ta yadawa a gari ga wanda baisan gaskiya.
Duk da kota sani din a yanzun babu wani abinda zata iyayi saidai sherin kawai bayan shi bata isa tayi wani abinda zaisa aikin mu ya soke ba shi kuma boda Bisi abinda baiso ke nan uwar taji ya zamo muna matsala ana muna gori yasa ya gargademu da kada mu fadawa kowa zancen.
A karshe shike fadawa mahaifiyarsu ashe zahra tana nan tare da mijinta don na gansu a wani shagali da akayi na karin girma cikinsu ko harda mijinta.
Yadda mahaifiyar nasa ta rude tun a wayan yasan ba a kwana bata fadawa mama wanan labarin ba sai ya godewa Allah da bai taba fada mata shiya samowa master aiki ba.
Aikuwa a ranan takira mama take labarta mata labarin dataji daga danta cewa ai yaga Zahra da mijinta ashe da gaske a nan yake aiki kuwa.
Sun dan taba maganganu a tsakaninsu kafin suyi sallama tun lokacin mama ta kara tsananta tsanarta akaina yayinda bangare ummah take yawan yi muna sadaka da sauran abubuwan da addini ya yarda dashi.
Ina can auren hannatu ya taso nayi bakin ciki da bani kasan a lokacin don haka nakira ummah mukai shawara da ita kan taje dakina duk abinda da take so ta dauka na bata shi saboda Allah don hannatu mutum ce a wurina gata kuma marainiyace gaba da bayanta.
Ummah bataki shawarana ba don haka ta kira hannatun tace ta karbi makulin dake hannunta taje ta bude dakin ta dauki duk abinda take bukata injini.
Kuka ta dinga yiwa ummah tana fada mata irin yadda yan uwa suka bata baya yanzu da auren nata ya taso sai hakkuri ummah kawai ta bata tareda yan shawarwari.
Lokacin da hannatu taje don ta bude daki cewa inna tayi bazata bude dakin ba don ba,a shawarceta ba ai da za ace azo daukan kaya itama ai akwai kayan danta a ciki kada a hada mai dasu.
Ta kyaleta ta fito ranan bata samu daukan komai ba sai daga baya taje ta fadawa ummah shine ummah ta kirani tana fada min nayi mamakin hakan har nake fadawa Dije.
Itama Dijen mamaki tayi take fadin ikon Allah amma Rashida tana da karfin hali kodaya yadawo itace ke fada mashi ranshi ya baci sosai da jin hakan.
Shine ya kira inna din a cikin fushi yace inna wai meyasa kike hakane ai kinsam banda komai a dakin nan komai na zahra ne idan ba tufafina ba don me zaki hanasu daukan abinsu tunda suke da abinsu.
To yanzu ka kiranine kayi min fada ko me yace fada kuma inna ni kawai na kirakine ki bari su dauki kayansu tunkan rayuka su kai ga baci don Allah tunda bani na saya mata suba.
Duk muna zaune a lokacin muna sauraren yadda suke kwasa da ita a karshe dai ta fafada mashi bakar magana ta kashe wayan nata rai bace ya kalli dije yace wanan yasa nace zahra ta bayar da key din gidansu don gudun matsala ashe ba a tsira ba.
Shine daga baya nacewa ummah hannatu ta diba har gadon ta kwashe a kwashe komai wanda bata so ummah ta mayar wurinta hakan ko akayi.
Sun samu bata gida don haka hannatu ta tatara komai ta fita dashi daga gidan su Asmau na kallo duk gulma ya isheta a lokacin.
Hannatu kan Allah ya kashe ya bata don master da kansa yace ta hada da gadon da komai ta dauka don ko mun dawo ba a gidan zamu sauka ba saboda yana gina a can .
Wanda sai lokacin muka san da zancen ginan da yakeyi din a nan gusau wanda wani aminsa da shehun ummah suke kula mai dasu don ya mayar da ummah kamar mahaifiyar cikin saboda hankalinshi yafi kwanci da ita yasa duk wani shawara da ita yakeyi yanzu.
Lokacin da aka kawo kayan nawa gida an samu mama na waje nan suka saka ido suna kallo tare da sake sake a zuciyarta saidata fadawa diyan ta sukace mu muka sani dai ai koma meyasa aka dawo dasu gida din.
Muna can kuma har wayau bayan anyi wanan an lafa labari ya samemu cewa an kama ya musa wai ashe wai suna smogal ne shine sunan shi ya fito.
Sai da kyar aka samu aka sakoshi har da mahaifin master saida ya sa baki kuma ya kashe kudi sosai saboda Abba yanzu baida zarahi.
Kuma duk Abba yayiwa mama da ummah bayani bayan daya dawo gida da yaya musa din tarasu yake fada masu duk yadda abubuwa ya faru ga Aisha da Rukkaya a wurin.
Bayan sun koma dakin sune Aisha ta fara magana wai hum, ummm for god sake saida mijin zahra ya saka hannu fa ki duba don Allah mama.
Daga inda Rukky take zaune tayi tagumi tace ba ina fada maku sunyi karfi sosai ba yanzu nifa a wurin wanan kawar nata kawana kejin labarin su wallahi ance yayi kudi sosai a can yanzu.
Kai ni kina ban mamaki wani kudi aida mun gani ko a nan wurin uwarta tunda su ba abin boyo bane da za a boyewa mutane.
Sunyi tayin halin nasu kafin su dawo zancen dan uwansu dayaja masu abin magana badon Allah ya gyara ba da ba, a san yadda za akaya ba a karshe.
Ban rasa komai ba a rayuwata don haka ba abinda na nema na rasa a duniya don master gaskiya mutum ne mai fitar da hakin iyalinsa dana iyayye.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login