Showing 108001 words to 111000 words out of 304363 words

Chapter 37 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33303

mu din .
Wurin ya cika da taron maza da mata ga motoci nan ko ina ka duba anyi decoration irin na gargajiya anko kan ba a maganan shi yafi kala goma da idona ya gani a wurin.
Yadda akai taron ya nuna angon dan gatane sosai don yannen nasa naji dashi muna tsaye a bakin motan da mukazo cikin shi don tawagan ango muka biyo mu.
Wayana ne yake vibration daga cikin jakata nake laluboshi mommy ce na dauka take fadin kun iso ko nace eh mommy take fadin ki fadawa maryam cewa zaku shigo da angone akwai yan matan da zakuzo a tare din kifayi masa liki sosai a san dakin shigo na danyi murmushi ina kashe wayan.
Abinda na kula dashi shine na farko mommy nada son asani sai nabiyu kamar suna da adawa a tsakanin su da yan uwanta sai kuma nayi tunanen ko don Abba ya ban kudin bukine a gaban ta oho ?
Mun kai minti ashirin kafin ace mu shiga fili amarya naciki aka bamu hanya mc na shelan fadin ga angonne zasu shigo suyi liki.
Kidan ya canza saiga wani da sauri cikin abokan angon na fadin ke dake dake ya nunamu mu hudu yace wai mune a gaba don Allah ace ni cikin mamaki maryam ta tabani na juyo ina kallonta.
Alama tayi min da ido nace OK ya juya ya tafi haka din kuwa muka shiga wurin muna gaba sauran tawagan na bayan mu.
Sam ban yarda nayi wani rawan zakewaba don dama ba gwanan rawa bace ni din har zuwa tsakiyan taron angon yazo ya tsaya kusa da amaryan shi.
Nan wuri ya rude da rawa na fara ja baya kadan na samu wuri na tsaya ina kallon abindake wakana a wurin don babu ma yadda zaka shiga kace zakayi liki ai.
Har yakai mc din ya roki mutane da a fita a ba amarya da ango fili don Allah saida kyar mutane suka dan rage wata gwaggonsu ta karbi abin magana tace bata son ganin kowa a cikin fili sai amarya da angonta kawai a fili.
Dole mutane suka rage yawa bayani me gamsarwa tayi wanda yasa mutane suka natsu akaci gaba da gudanar da event din.
A wanan lokacin da akace yan uwan ango su fito su nuna farin cikinsu ga ango maryam data dawo kusa dani ta tsaya take fadin muje mu dan likawa uncle mu fito.
Tare muka shigo duk yadda bakuwa ko bako yake a wuri za ayi saurin gane hakan don daga ni har maryam din bakine dan dama ita wasu sunsan mahaifiyar ta.
Amma nikan sai mamare sukeyi a kaina da tambayan yar waye ni din cikinsu ba amsa don basu tambaya kusa da wanda ya sani.
Yan dari biyar biyar nake masu liki wanan yasa mc tambayan suna aka fada mai Zahra nan yake ta ambatan zahra Abuja.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
3️⃣6️⃣
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Muna fitowa ina rike a hannun maryam dake jana muka fito daga cikin filin zuwa waje lokacin naji wani shakat a zuciyana jikin mota na dan jingina ina dan fifita da hannuna.
Wani wanda wanan ta ukun tamu da muka hadu muke tare ta kira tace don Allah ko zai wucene ya saukemu gida ta fadi sunan gidan su mommy din.
Yace muzo ya kaimu mommy na kira na sheda matagamu zamu tafi gida don ban yarda inyi wani abinda bata sani ba ya zama min matsala a karshe.
Mai motan yana ganin yan mata ya tsaya a wani shop yayi muna sayayyan kayan sanyi da su nama muka karasa unguwan lokacin dare soma yi.
Bayi na shiga na samu wanan matar ta gyara dakin ta wanke bayin ta cika robobin dake ciki da ruwa tayi aiki gwanin ban sha,awa nayi sauri nayi alwala na fito har lokacin su maryam din ma basu shigo ba.
Ina idar da isha,i na soma jin muryan mutane a gidan dake nuna an soma dawowa daga wurin taron ke nan a lokacin na cire kayan jikina na sauya zuwa dan rigan barci saiga maryam da yarinyar sun shigo sun sameni.
Suna fadin ke ashe bayan mu anyi fitinane da yan gidan amarya sosai ayyah abu baiyi dadi ba na fada tace wallahi nan suke ban labari yayin da maryam ta miko min ledan tana fadin kici fa naga kamar har kina shirin kwanciya.
Ni har nayi sallah zan kwantane yanzu kallon juna sukayi tace gashi munce zamu fita kuwa ke kuma kice zaki kwanta.
Ai bani fitan dareni kome ki akeyi don yana zama min lalura hakan sai daya tayi saurin fadin ashe ba zaki dinner ba ke nan gobe ?
Kaina gyada idan da darene sosai ba zani ba gaskiya kici mu bari muyi sallah nace komai ba zan iya ci ba yanzu saidai gobe kuma ?
Humm,Ummm wanan akida kamar wata baturiya haka kina da ra,ayi kala kala a rayuwan ki maryam ta fada toke baki ganin su yayan hutune dama irin su kuma sai aure gidan gwanoni ko yan majalisa.
Aiko baki fahinceni ba kowa da kalan ra,ayinshine bana dai cine yanzu karfe takwas nake cin abinci koda zanci din kuma takwas ya wuce yanzu.
Aishiyasa nace sai yayan shugaban kasa nace niko kinga tallaka nake son in aura don a nan nake hango kwanciyan hankali yake sam bani da ra,ayin auren mai kudi ko mulki a rayuwana.
Ke raba kanki da wahala yanzu na rabaki da auren tallaka wallahi garama mutum ya auri mai kudin komai ta famjama fanjau da ka auri tallaka sai kudi yazo kinga hutu a lokacin zai dauko maki yar gaban mota ace ke baki iya ba baki waye ba .
Ai maza wallahi barsu nan inda kika gansu kawai matan yanzune daidai dasu mace ta juyasu yadda ranta yakeso kana kallo in kayi magana ace kishine .
Zaman gidan mune ya fado min a raina don gaskiya ta fada tunda ga yar uwansu nan a yanzu ta mayar da Abban mu kamar karamin yaro sai yadda ta juyashi a yanzu.
Mama dake magana ana ganin kishinta da hauka wai bata son shi da karuwa sai ita da yayanta kawai a gidan take son ganin shi dasu.
Suna ta zancen su dai ina jinsu rabi rabi kuma yana ga tunanen zamani dake raina har barci ya daukeni a hakan na barsu nan suna hira ko sallah basuje sunyi ba a lokacin.
Mommy ta leko ta samu nayi barci ko ta fita ban falka ba sai washegari da asuba na tashi don motsin tsohuwar da naji a lokacin ta shigo zuwa bandaki.
Sun shiga gidan sun samu Shattu ta gama girki har ta kwashe tayi masu shimfida ta aje masu a cikin rumfar shan iskansu na gidan.
Sukai sallama suka shigo takewa mijinta sannu da zuwa shima Ahmed din ya gaida ita tayi mai ya gajiyan hanya ?
Ya amsa da alhamdullahi ta ga batar masu da abincin ta koma gefe daya ta zauna tana cin nata bayan sun zauna baban yayi mai bissimillah ga abinci muci.
Ya gyara zama yana fadin baba kaci ka barmin idan kagama zanci ba zan iya hada hannu da kaiba kada nayi rashin da,a ga hakan .
Daga can inda shatu din take zaune tana jiyosu tace dama nayi tunanen hakan yasa nayi dubaran zuma masa nasa shi kadai gashi can nakai mashi daki na rufe tun dazun ai.
Lalai kana cikkn mutanen da yaro duk dabi,un ka na tarbiyan kwarai ne ka samu duk wanda ya baka tarbiya haka bai bayar a wurin banza ba .
Dakai wani yaron zamanine zaka zauna mucine ba tare da daukan hakan komai ba samun irin ku yanzun a cikkn al,umma yana da wuya sosai gaskiya.
Shattu ne ta mike ta nufi dakin ta dauko abincin ta kawo mashi yayi godiya ya zauna ya fara wanko hannunshi yazo ya zauna ya bude kwanon abincin .
Kamshin man shanune ya biyo hancin shi da sauri ya lumshe idanun shi don Allah yayi shi da son man shanu a rayuwan shi sosai shi samune kawai baiyi yasa ya hakkura dashi.
Bayan sun gama cin abincin dan hirane suka taba inda tsohin ke bashi labarin irin yadda suke kiwo su a nan don yanayi yasa komai ya dan banbanta da nasu yanzu.
Shima Ahmed din yana labarta mashi yadda wurin su yake da irin yanayin da jaharsu yanzun yake ciki sun dan kai wani lokaci suna hira a tsakanin su shattune ta fara mikewa ta shiga ciki yayin da Ahmed din shima ya ga ya dace ya shiga masaukin shi ya barsu su dan gana hakana da iyalan shi.
Yayiwa tsohon saida safe ya shige dakin ya turo sai lokacin ya tuno da wayanshi daya mutu tun a cikin mota ya dauko ko dan wuta bata kawowa don ta dauke da kantane.
Zahra yaso ya kira lokacin yaji lafiyanta saidai hakan bai yuyuwa gareshi yanzu don daukewan da wayan tasa tayi din.
Don haka ya lafe a saman gadon karan yana maida numfashi yayi da zuciyar shi ke cike da tunanen abubuwa kala kala yana nazari.
Da farko mamakin ganin akuyan nan mai kama da uwargarkenshi yakeyi don yasan babu yadda za ayi uwargarke ta kawo nan idan ba aikin aljannu ba haka ?
Sai kuma tunanen yadda zai iya samun mahaifinshi dayai kasadan fitowa gida ba tare daya fadawa kowa kudirin shi ba ya kamo hanya ya fito da badan Allah daya hadashi da bayin Allah nan ba da yaya zaiyi a wanan garin ta ina ma zai soma hakan yace yana neman mahaifinshi a haka.
Sai kuma ya tuna da Dije wace yasan yanzu ta gama tayar da hankalinta gareshi na rashin dawowan shi gida din na tsawon kwanaki da baiyi ba kuma bai fada mata inda ya nufa ba da zai bar gida din.
Donshi baida babban waya irin ta matasan zamani balle yaga abinda duniya ke ciki da idonshi ya gane masa yadda aka juye labarin tafiyan shi ya karade gari cewa an masa kurciyane ya bata.
A karshe kuma ya koma tunanen zahra a gaskiya yanzun ya gama yarda da cewa skn zahra yakeyi sona gaskiya da baikoyiwa kansashi.
Amma kuma akwai abubuwa masu nauyi a tsakanin su din na farko babban shine tabbatarwa mutane shi din ba shege bane da ubanshi.
Tunda ya fara ganin kyama a idon mutane dake nuna mai cewa shidin baida asali yasan wanan zancen ba akan zahra ba kan ko wace mace yaje nema za a fada mashi hakan don ba a aure babu waliyyai ga mutum najini.
Idan hakan ya taso mashi tunda ba zai zauna baiyi aure ba suwa zai nuna a matsayin iyayyen shi yanzu dolene hakan daya yanke din wa kanshi don yasan idan ya tsaya ba Dije shawara ba zata taba yarda da bukatanshi ba kai tsaye kuma ita ba zuwa zatayi ba nema mashi mahaifin nasa ba.
Gashi ya kwaso kafa yazo garin mutane ba tare da sanin komai kan mahaifin nasa ba don baida wani sheda da zai gabatar da zaisa ayi saurin gano waye mahaifin nasa a yanzu.
Dan dagowa yayi daga kwancen da yake saman gadon karan da yasha bargo mai laushi ya canza kama har baka gane cewa ba gadon zamani bane a dakin da sauri.
Don tuno da lokacin da za a sakashi makarantar boko ake muhawaran sunan da za a saka mashi son anyi niyar saka mashi sunan kakan shi ladan a lokacin.
Amma sai headmaster makarantan ya bada shawara a saka mashi sunan mahaifinshi don ko wani da yana son alfahari da sunan ubanshine ai a duniya.
Sai yaji kakan nasa yacewa headmaster buba sunan mahaifin nasa sai headmaster ya gyara da fadin buba ai Abubakar ne akewa lakanin hakan wani lokaci don haka yake da Ahmed Abubakar a sunan shi.
Lalai wanan zai iya taimaka masu yanzu wurin gano waye mahaifin shi indai har da sunan nan biyu yake amfani a nan din to hakan zai iya taimaka masu a ganoshi watakila.
Da wanan zancen ya kwana a zuciyan shi cewa lalai zai fadawa tsohon wanan maganan ko zai iya taimakon su agane da sauri.
Da wanan barci ya daukeshi sai gashi yana mafalki da uwargarke tana binshi tana wani kuka gwanin ban tausayi jin kukan nata yasa ya tsaya akuyan tazo tana dona kahonta a jikinshi kamar tana susa.
Ganin haka yasa ya dauki hannun shi ya dora a bayanta yana shafa a hankali ji yayi ta rage kukan da takeyi din ya jawo hakki ya mika mata a baki sai taki ci tsugunnawa yayi yana fuskantan akuyan ya soma fadin.
Uwargarke me kike so sai yaga akuyan ta juya baya kamar tana nuna mai wani abu ganin hakan yasashi dago kai ya kalli wurin da akuyan ke kallo.
Baiga komai ba sai ganyayakin tumfafiya da suke birit a wurin gwanin ban sha,awa dasu suwa wurin lup lup dasu juyawa akuyan tayi ta nufi wurin da tumfafiyan suke.
Shima mikewa yayi ya bita suna ta ratsa iccen tumfafiyan dake wajen sai ya hango wani mutum a zaune saman wata kujera ta alfarma ya bada baya yana zaune shi kadai a wurin.
Tana kaiwa gaban mutumin daya shadda yana hakince saman kujera sai kamshin turare ke tashi jikinshi saita ta zube a wurin shima ya karaso yanawa mutumin sallama dago kan da mutumin zaiyi sai yaga wani dattijo farine.
Mai son kamani dashi saidai wanan ba yaro bane shi kuma babban mutum ne a yadda ya ganshi zaune din da kuma kalar shiganshi da kujeran da yake zaune a kai.
Ji yayi kamar an dukeshi ya tashi daga barcin sai gashi kawai ya bude idanun shi ya ganshi kwance cikin dakin nan na gidan tsohon da suka bashi ya zauna a ciki.
Duk da yanayin sanyin dake garin hakan bai hanashi zufa ba dako har rufa yayi don sanyin daya kama mai jiki kafin barcin ya daukeshi bin dakin yayi da kallo na dan lokaci kafin mafarkin da yayi din ya dawo mashi sabo a ranshi.
Daki daki yake tuno da abinda ya gani a cikin mafarkin nasa hakan yasa ya mike zaune yana kokarin sako kafafuwan shi kasan gadon karan .
Kukan dabbobin tsohon yake ji daga waje wanda hakan yasa hankalin shi ya dauku a lokacin ya maida hankalin shi ga sauraren su.
Kuka sosai sukeyi wanda ke nuna cewa wani abu yana faruwa da dabbobin a lokacin kusan tare suka bude kofa da tsohon daya fito a gigice shima yana fadin miko min fitilan mai haske shattu.
Shima Ahmed din komawa yayi ya lalubo tashi fitilan suka cice daga gidan da sauri shida tsohon lokaci guda suka nufi wurin dabbobin da sauri suna haska fitila.
Tun daga nisa suka hango babban bajimin saniyar tsohon a kwance yana shure shure hankali tashi suka nufi wajen tsohon duk a rude yake yana kiran innalillahi shi kawai yake ambatowa a lokacin.
Baba kuna da tumfafiya a unguwar nan Ahmed ya jefo mai wanan tabayan shima a rude lokaci guda tsohon yace akwaishi can barin kadan yace ta ina ya nuna mai ya juya da sauri zai nufi wajen.
Dakata muje tare da sauran dare ayanzu babu komai baba insha Allahu ya sheka guje tsohon bai yarda ba ya biyoshi a baya gudun kar wani abu ya sameshi.
Suna zuwa da addua a bakin Ahmed din yakai hannu ya karo wani reshe na tumfafiyan ya juyo da sauri suka hade da tsohon tare suka juya Ahmed din yana sauri tun a hanya ya kara wasu ganye yake murzawa a hannun shi.
Tsohon yana biye dashi ya rike saura ganyen da suka fadi a hannun shi yana zuwa gaban bajimin san dake kwace ya nemi hancin saniyan ya murza mai wanan tumfafiyan a hancin shi.
Ya kara kallo wani ganyen ya murza yabi fuskan saniyan dashi duka har zuwa kahon zuciyar shi tsohon dai yana tsaye yana kallon ikon Allah don shi bai taba sanin wanan ismin ba a rayuwan shi.
Zuwa lokacin kuma har wasu makwabta dake jiyosu sun fito daga gidajen su sunzo inda abin yake faruwa suna mamakin hakan.
Bin gadon bayan saniyan yayi yana dan murza mata sauran ganyen a hankali yayin da saniyan kuma ta rage karfin shure shuren da rakeyi da farko din da alama abin dake damunta din yana gushewa a hankali gareta lokacin sun koma gefe daya suna kallon ikon Allah.
Wai mamaki lokaci guda saiga saniyan ta fara atishawa irin ta dabbobi din nan da karfi zakace murane takeyi sosai a lokacin take fitar da wanan majinan a hancinta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login