Showing 282001 words to 285000 words out of 304363 words
Ni dai duk ba wanan bane a gabana ba lokacin burina na kyala ido akan Abban mu dake asibiti kwance kuma inga mahaifiyata tare da yan uwana danayi shekaru bana tare dasu.
Mun shiga gidan komai zamzam a cikin gidan a falo muka zube don kafin mu iso har an tayar da injin din gidan ya dauki haske tako ina zama mukayi a nan don mu huta kafin su shigo da shehu ciki.
Muka gaisa yana wani kara ban girma kamar yagga wata babban mace irin yadda akewa mama a da can baya hakan ya fado min a zuciyana lokaci guda.
Nace a shehu ya muka sameku ya kuma kokari wallahi lafiya hjy na dan kalloshi Master yayi muna murmushi yana dukar da kai ban gane manufarsa ba a lokacin nayin hakan.
Mun samu abinci a wurin munci donshi da yara da dije sukaci sosai ga kuma mai aiki da wata yar matashiyar yarinya su biyu wai ummah ce ta dauko mun su daga can garin su da zamuzo din nan don su rika taimaka min da aiki.
Ai kuwa dai nasan akwai aiki don baya yarda da hakan nima kuma dai nafi da son nayi aikin abinda zanci da kaina don inada yawan tsanda ba girkin kowa nake iya ciba ni kaina shi kuma har yafini wanan halin tsanda din.
Sallolin dake kanmu muka rama kafin na dago ina kallonshi a inda nake nace amma yau zamu shiga wurinsu ko muga mai jikin yace naso hakan amma yanzu dare yayi ku zauna a gida sai gobe da safe na kaiku.
Zan tafi sani da shehu mu fara duba jikinasa mu gani don yanzun nan muka gama waya da Abba yake tambayana jikin nace ban karasa can ba tukun.
Ba a dade ba shehun ya dawo gidan dauke da katon katon na abubuwan sha dana sauran bukatun mu suka fita tare dashi zuwa asibitin kakace bacan din ma zasu ba a lokacin don ni haushi ya hanani yin magana.
Mama mama na kwala mata kira ta amsa tazo wanan matar da aka kawo min don bansan ya suke da mahaifiyata tunda ta haifi wanda ma ya girmeni don haka ban rage ba ai.
Mama a dauke kayan abincin nan aje aci idan kun koshi kuma a duba wani gida nan kusa don Allah a basu don abincin yayi yawa kada ya lalace a banza.
Tana godiya suka dauka nace ta turo wanan yarinyar ta tayamu saka kaya a daki na tashi sai lokacin na leka dakunan komai na gidan da gani kasa odan su akayo daga can masu kyau da tsada.
Kowani daki ba laifi an gyarashi tsab an saka komai a cikin dakunan kwanan saidai nawa da nasa sunfi tsaruwa dakin da yace shine nawa an yimai ado da kayan cikinsa yafi kowane tsada a gidan.
Komai na dakin nawa white and purple gwanin ban sha,awa hakan ya karawa dakin kyau da daukan ido a magariba aka kira yasa na shige daki tare da yarana dije kuma tana dakin daya kai kayanta ya nuna nan ne masaukinta.
Wai ashe duk abin nan inna bata san mun shigoma Nigeria ba sai ganinshi sukayi kwatsam kamar daga sama ya shigo gidan yana sallama.
Aishace kadaice a gida lokacin inna ta fita Asmau kuma bazawarinta yazo wai ta fita don aurenta da shekara daya ya mutu kuma da ciki lokacin Allah ya rufa mata asiri wurin haihuwa diyar batazo da rai ba shine yanzu take sabon zawarci don taki karatu ko secondary taki ta karasa wai ita aure take son yi tace.
Don haka kowa ya zuba mata ido ana kallonta don dama bata da kunya shi kadai take tsoro yanzu kuma bai kasan tare dasu sai abinda taso takeyi.
Da farko Aisha wai bata ganeshi ba saida yace Aisha ke kadaice a gidan wai ina sauran mutanen gidan ko inna har yanzun bata dawo bane wai ?
Yayan mu wai kaine dama ban gane kaba wallahi muryanka yasa na ganeka yanzu tana kallon bayanshi ko zata ganmu tare dashi mun shigo gidan muma.
Ina su Dije da anty yaya yace ba zaki gaidani ba nida kika fara gani suna can na barsu to ya fada yana bin gidan da kallo ko ina don gaba daya gidan ya sauya mashi kamar ba mutane a cikinsa.
Dakin Dije da yanzu Aisha din ke zama a cikinsa ta shiga da sauri ta fito da kujerun roba farare guda biyu hade tana fadin inna sai dare kila ko kuma anjima kadan ni kadai ta a gidan yanzu.
Ta aje kujerun yace tunda bata nan ba zan zauna ba amma kice mata nazo gobe zamu dawo yaya har zaka tafi ko ruwa baka sha ba fa yace sauri nakeyi zanje asibitine na subo mahaifin zahra .
Subbahanallahi yana asibitine kuma yaya yace eh ance yana asibitin kwance ba lafiya walle ban sani ba aida naje na subashi kwanaki dai naje nagaida ummah da sallah.
Kin kyauta ai ina ita Asmau din ya fada yana kallonta hummm ta fita bansan inda taje ba na daiga tayi wanka ta fita dazun saidai ka dawo yaya mun zauna ai.
Har kofan gida ta rakoshi ya shiga mota tare da shehu yaja ita kuma ta koma cikin gidan cike da mamakin ganin bazatan da tayiwa yayan nasu haka kwatsan gashi kuma ba a gidan ya sauka ba ko ina ya sauka oho don dai tasan shi ba mai yawan abokai bane balle tace gidan wani abokinsa ya sauka.
Alwala tayi don magariba daya gabato a lokacin ta shiga daki ke nan don tayi sallah taji muryan inna tare da Asmau data daukowa inna kaya tana fadin wai wanan kamshin fa haka Aisha ?
Sai da ta idar ta fito tana masu sannu da dawowa Asamau ke sake fadin Aisha ina kika samo wanan turare mai mugun kamshi dadi hakane walle daji turaren manyane wanan kam.
Tace turare ni ban saka turare ba ai wallahi gidan ga tun shigowan mutum daga kofa kamshi zai tareka balle inka karaso cikin gidan.
Tace kodai kamshin turaren yaya ne kikaji har yanzu bai fita ba tace yaya wani yaya kuma yaya da bai gari shekara nawa yayan mu da bai nan.
Kafin tayi magana inna tace koda yake nan ma wani turare yaka sakawa shi banda shirmen ki yayan mu fa nace inna yazo yau yana garin nan bai dade da fita gidan nan ba don yazo bai sameki ba yace zai tafi saida safe ya dawo.
Cikin dafe kirji inna din tace shin dan Dije kinkace yazo garin nan wai da gaskiya ko wasa kikai sai Aisha din race inna na taba irin wasan gana ?
Ya taho shin to ina kikace mashi na tafi sai yarinyar tace kauye mana wurin tallan kayan ki na mata shi kuma yace tunda baki nan bari yai tahiya nai sai gobe zai dawowa.
Dan dije ya taho shina bai sanarwa kowa da zuwan shi ba yanzu ina ya sauka nima walle inna ban tambayeshi ba inna baki ga yadda ya koma ba don ko ganeshi banyi ba murya nai dai nagane shina.
Ashe yau muyi barcin mu hankali kwance tunda kudi sun taho Asmau ke fadi cikin jin dadi tace ai ya tambayeni keya nice mai kin hita.
Bada mata tai ya taho ba ke nan ko balle umma shike nan su umma su suyi zaman turai bata dawowa wasu kuma su tai ?
Gaskiya da gani shi kadaina ya taho yace ma wai asibiti yayi daga nan zaitai ya dubu mahaifin mata tai dake kwance asibitin.
Ikon Allah yanzu da ya tsaya har in dawo gwama yatai dubiyan uban mata tai ko yaushe rabonai damu muganeshi sallon dan abinda ya taho dashi ya tai can ya zazage masu suwa.
Aikema kinsan karamin aikinai na yanzu kam inna ai sai abinda munka samu garai, don walle sai ya basuwa dama yayi balle yanzu da aka gani nai mai kudina shiya.
Uwar tayi shiru tana nazarin zancen Asmau din kafin tace ni indama zatai ya kwana kodai zaitai asibitin ne ya dubuso ya dawo nan ke ku tashi ku shere mai ko inda zai kwantana kafin ya dawo.
A a inna ina zaya kwanta koke mata babu komai a dakin nasune yanzu barshi inma ya dawo din ai zai gani da idonai basu bar mashi komai a dakin ba sai yasan dabara da zaiyi.
Balle yace min sai da safe zai dawowa ina yaka iya kwana cikin gidan ga yanzu baki ganai bane fa inna ya zama dan binni wayaye ko tufafin jikinai abin kallo na.
Shikan daga asibiti can ma sunce basu ganeshi ba don ya samu su baba Adone kawai da ummah tare da Abba din don ummah ta tafi yin sallah don haka basu shedashi ba.
Jikin na Abban mu da dan dama saidai ya rame sosai duk jikin nan nasa ya zube ga farin geme dana kai daya dan tara yanzu alaman wahala da tsufa dakuma ciwo a tare dashi.
Ya dan dade akan Abba din wanda yai karfin halin tashi a lokacin suna gaisawa yana tambayanshi mu yace muna gida yanzun nan muka iso shine yace shi bari ya fara zuwa ya dubashi kafin mu natsa mu yace su dai huta zuwa safe in Allah ya kaimu ai sai su shigo.
Lokacin ne ummah ta shigo ta samesu take mashi sannu da zuwa ya tsuguna har kasa ya gaida ita kamar yadda ya gaida sauran ya tambayeta ya mai jiki da kanne na.
Sun dan jima a nan har yake tambayan ta kome Abba din keci yanzu tace to sun dai ce sugar ya shiga ciji yanzu ba komai yake ci ba sai abinda akayi da wake ko accha yake dan ci.
Ummah aida an fada muna daga can sai mu sayo abincin irin masu laluran azo dashi amma yanzu bari shehu mu fita mu zaga manyan shaguna ko za a samu wani abu na daban sai a sayo ya dan canza launin abincin in babu zanyi waya da Abbana zuwa gobe sai a kawo muna.
Na duba likitan inji kome ke nan ance ya fita zuwa gida sai dai zuwa safe mu ganshi sai asan abinyi don ina son mu wuce gaba dashi a kaishi kasan waje.
Allahu akbar baba Ado ya fada daga bayansu don yana jin maganan da sukeyi din yace ance in baka mutu ba ba a gama halittanka ba yau yaron nan shine zai dauki dawai niyar Alh haka ?
Gaskiya hakkuri bai bar komai ba don wanga abu wani babban isharace Allah ke nuna muna haka dan mutum dan baiwane ba abin raina bane idan ka ganshi ganin farko don baka san baiwan da Allah yayi mai ba gaba.
Baba haruna yace ai kaji tsoron Allah in ya tashi nuna ikonsa a inda yaso kai dai kawai ka rike Allah da mazonsa ka dauki kowa da zuciya daya.
Daga can gefen su Abba din suke wanan maganan shidai master yayi masu sallama akan zaije ya dawo suka fita bai dade ba kuwa suka dawo da abubuwa da Abban zai danci ya canza bakinsa akan waken da ake ta dankara masa a yanzu.
Sun dan jima har yake tambayan mama da bai gani a wurin ba aka ce masa tana gida tunda rana ta koma mi zata tsaya yi yanzu tunda ba wani abinda zatawa handama baba haruna ya fada a dan hasale.
Ko daya dawo gida karfe sha daya da rabi na dare lokacin duk su dije da yaran sunyi barci nice a zaune muna hira da hannatu fa charting ya shigo.
Sannu da zuwa nayi mai ina mai tambayan jikin Abba din ya amsa yana fadin ashe baki barci ba nace wanan mai surutun ce hannatu muke charting da ita.
Ya kwabe kayan jikinsa ya shiga bandaki ba tare daya ban amsa ba ruwa ya watsa a jikinsa ya fito yana goge jiki duk ina zaune yace gaskiya Abba yaji jiki sosai amma yanzu da sauki sosai .
Don da kansa ya mike zaune amma ummah ta fada min cewa da sai an kwantar an tayar dashi amma a dan kwanakin nan gaskiya sunga sauki.
Wani iri naji a raina nayi shiru ina tunanw kafin na nisa a hankali nace Allah dai ya bashi lafiya yasa hakan kaffarane gaskiya Abba ya bautu da ciwon nan a jikinsa don tun kan mu tafi fa
yake dan fama a tsatsaye.
Har yanzu yakai ga kayar dashi ina dai tsoron kada ya zama sai kuma nayi shiru don banson ma in furta wani abu amma duk da hakan saida ya gane menaso fada.
Naji yace inda ciwo ko ba ciwo lokacin mutum yayi dole a tafi fatan mu dai mu cika da kyau da imanin ubangijin mu a zuciyar mu na amsa da Amin ya saka riga ya dawo bakin gadon ya zauna ya dan kalleni har lokacin ina cikin tunane yace.
Shiyasa nace barin fara zuwa na dubashi shima Abban da kansa fa yace na barku har gobe kwazo ku dubashi akwai gajiya a jkkin ku kuma kinga ba ke kadai bace yanzu.
Don haka ki cire duk wani damuwa insha Allahu da alaman sauki sosai a tare dashi don duk alaman sauki ya dan fara baiyana a jjkin nasa.
Nama je gidan su inna daga can jin hakan yasa na dago kai na kalleshi kafin in tambaya yaya suke yace saida babu kowa a gidan sai Aisha kawai na sama itama ta dawo ke nan daga school lokacin.
Inna kuma wai ta tafi kauye wurin talla bata gidan ma har yamman nan nace talla kuma yace talla mana shiyasa don in kamata ai ban fadawa kowansu zuwab mu ba gashi ko nagani da idona.
For god sake zahra me inna ke nema a duniyan nan wanda ban mata ba ace wai sai inna ta fita yawon talla don Allah ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA[7/11, 11:00 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
9️⃣6️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Karfe takwas na safe duk mun gama shirin mu a lokacin don ina kitchen dina na sabon gidan mu tun karfe biyar da yan min tuna bayan na idar da sallah mu shiga hada abincin da zamu kai asibitin na safe.
Mun kare akan lokaci mukayi wanka har yaran da yan aiki muka shirya gaba daya gidan zuwa asibiti duba jikin Abba din dake kwance a nan.
Still dai su baba dasu ummah ne akansa har lokacin suna dubanshi mukai sallama muka shigo dakin ya dauki murna da ganin mu kamar ba mara lafiya ke kwance ba harshi Abba din sai daya dan dago yana kallon mu a cikin fara,a.
Sama sama na gaisa da mutanen na nufi wurin gadon ina aje nasa abincin dana ruguma a wani dan carving dake gefenshi tare da fadin sannu Abba ya jikin nakai kasa idanuna cike da hawayen ganin Abban mu daya koma hakan lokaci guda don ciwo.
Zakace shi dim wani tsohone tukuf a lokacin lalai mutum ba a bakin komai yake ba idan bawa ya gane yabi duniya a sannu shine alheri ga bawa mai ganewa.
Yayin da su kuma suke min kallon mamakin ganin yadda na canza na zama wata mai class abin sha,awa a cikin dangi a lokacin.
Master ya shigo dakin dauke da yaranshi su biyu da basu yarda da kowa idan bashi ba saiko dije dake tafe a bayan shi suna gaida mutanen daki kaina a duke saman cinyan ummah ina kuka ya kalleni yace a harshen turanci wanan ai tayarwa mutane hankali kikeyi hakan be strong kamar yadda addinin mu ya koyar damu don Allah.
Kamar yadda Abban Ahmed yaso yaran suzo sukaki hakana kowa na dakin yaso daukan su sukaki zuwa gunsu dole ubansu da bai gajiya ya rike su hakana.
Ya koma daidai kan Abba suna magana lokacin na dago ina sauranransu bayani yakewa Abban cewa idan likitan ya fito zu a nemi refer zuwa wani wajen either Abuja ko zuwa indiya dasu don a dibashi asan takamaimain abinda yake damun shi.
Lokacin su mama suka shigo tana fadin gamu sai yanzu motan ne bamu samu ba duk motocin ba lafiya ta Alh kuma shashanga ya tafi sokoto da ita tun jiya bai dawo ba sai yanzu.
Ganin bakin fuska yasa suka tsaya suna kallon mu har na juyo duk kallon su waye suke muna sai dana mike don in karbi jakkar ledan kayan Abba dake hannunta Aisha tace wai Zahrace dama saukan yaushe kuma ?
Jiya muka zo na fada a cikin muryan dakushewan kuka a gareni suka bini da shu,umin kallo tun daga samana zuwa kasa sai can Rukkaiya tace wai dama zahra ce saukan yaushe amma bamu da labarin zuwan ki kasan ma nace shekaran jiya muka sauka.
Muna Abuja gidan daddy jiya muka karaso nan din