Showing 291001 words to 294000 words out of 304363 words

Chapter 98 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33375

dauka zancen mahaifiyarka zaka fara yimun duk da a yanzu din nayiwa Rashida nisa amma ita son kai sone ba kiba sai kuma gashi kazo min da akasin hakan akan yabi a yanzu.
Kada ka manta yabi da yan uwanta rayuwana suke so bani ba don wanda keson kwace maka dukiya ai rayuwanka yakeso ke nan ko wa yan nan diyan fitinan data haifa min na fara ganin irin halaiyan agaresu na fadama irin halin da yasir da salima suka shiga lokacin dana turasu karatu waje .
Nayi dana sanin wanan abin don a karshe kai din dama ban saka kwandala a karatun ka ba kaine ka zamo min abin nuwa tsarana dakai zanyi tun kaho a cikin abokaina.
Kawar da zancen yabi nayi maka bayanin komai a tsare nan mahaifin nasa ya dauko tarihinsu tiryan tiryan ya fara masa bayani har zaman karshe inda ya saki yabi din da irin sharadin daya kidaya ya kare da fadi.
Dukiyana ta hannun Bande ga baki daya na mallaka makashi a hannun ka don haka ina sin kafin ka koma zamu samu lokaci aje can din aga yawansu a lissafa haka nan kuma zaka fara sarrafasu walau nau,in madara kona nama don shanayen suyi yawa sosai gaskiya zasu iya bayar da madaran shanu dana rukumai.
Arzikina na gadone asalin mahaifiyata daga kasan Cameron suke arzikin su na gadon gadone don haka ko yaushe arzikin keda albarka amma akwai ka,ida duk wanda yasa shirme zasu kare su koma ga waninsa haka ka,idan abin yake amma su sunki su gane hakan.
Gyara zama yayi cikin ladabi ya kalli mahaifin nasa a rude yace amma Abba idan anyi hakan ba a shiga hakkon sauran magadanka ba kuwa don sai nake ganin kamar anyi son kai a cikin zancen.
Murmushi Alh yayi yace kai yaro ke nan ai yanzu dukiya dai tawace bata magada ba tukun don hanasu nayi yadda nake ganin ya dace ba tare dana shiga hakkin kowa a cikin ku ba.
Amma Abba hannu ya dagawa dan dake sonyin magana a lokacin yace ka barshi a hakana yadda na tsara don kai baka san komai ba yabi ta zalunceni sosai Allah ne ya ganar dani da wuri ko a hakan nasan ban maka komai ba cikin irin abinda sukai min da dukiyana.
Amma abin takaici da bakin ciki shine duk wanan uban dukiyan da yabi take murkusa wai ace basu ajeshi ba ko sun tanada sai a gun malamai da bokaye suke tafiya dashi don batan basira irin nasu na batatu da sukeyi.
Shiru Ahmed din yayi yana sauraren mahaifin nasu kafin ya sauke numfashi yace kayi hakkuri da hakan kamar yadda tasa nabawa kowansu gida a baya haka kaima na mallaka maka gidana na apo wanda na ginasune bada saninta ba.
Don haka idan kana kasan nan nan zaku dinga zama ba wani matsala na mallaka makasu halak malak daga cikin kyautatawana a gareka kuma ban son korafi a bayan hakan .
Abba na gode da wanan karamcin amma nima ina da yan uwa kuma a yanzu zasu fini bukatan dukiyan ka donsu a cikinsa suka taso kaimun shiru nace na riga dana gama maganata ya fada a hasale.
Nagode Abba ya fada mahaifin nasa ya amsa da shike nan zuwa safe sai a dakacesu idan sun kira muji halin da suke ciki Allah ya bashi lafiya.
Ya amsa da amin har ya daga mahaifin nasa sai kuma ya zauna yana fadin a yanzu nasan kafini mabukata a kusa dakai ina son ka samu lokaci ka ware ka kyautatawa yan uwan uwanka dana matarka dama wanda duk ya taimaka maka a baya daidai gwargwado kafin ka bar kasan ko bayan ka bari din hakan zai kara habbaka arzikin ka da samun ka a kullun.
Godiya yayi kafin ya kara sako zancen hjy yabi din yace amma Abba har yanzu ina roko a gafarce mu abar mummu yabi ta dawo dakinta ta zauna a cikin diyanta.
Dan dattijon ya kara murmushi yana fadin baka fahinceni bane har yanzu in har yabi zata dawo gidan ka tabbatar da uwarka zata dawo gareni ke nan final ya mike ya bar dan nasa a zaune wurin.
Lalai Abba ya dauko magana ke nan baisan yadda inna ta koma ba a yanzun din sai tafi hjy yabi wata kila baka matsala don haka ya mike kawai ya fice daga gidan shima zuwa masaukin su don bai sauka a gidan mahaifin nasa ba don tare yake dasu baba Ado a lokacin.
Ya samu musu girki da kula da gidansun kammala abinci sun kawo masu suna ci ya gaidasu ya haura zuwa dakin da yake ciki ya kwanta saman gado yana tunane.
Ina zai fara yace inna ta dawo gidan mahaifinsu yanzu abubuwa su taru su rikice masa ya rasa yadda zaiyi gashi karamin amana da suka bar mata na dan lokaci ta iya sayarwa balle nan da zataga dukiya a banza kamar ba a son su.
Kwanan su biyu abuja yakaisu suka sai tsaraba suka kamo hanyar gusau wurin iyalansu suka barshi can don bai gama abinda yakai shi ba a lokacin.
Su umma basu samu kira ba ranan da suka sauka sai washegari suka kira aka samu layin su nacan da suke amfani dashi a can din da suka tafi.
Mun gaisa take fada muna jikin na Abba da sauki sosai yanzu hakama an fara kula dashi don har ya dan dade zaune a yau din ta bani Abba din muka gaisa dashi yace jiki Alhamdullahi.
Lokacin hankalin kowa ya fara kwantawa banda mama dake fatan wani abu ya faru da Abba din don yan uwa su kuka damu sunan mu ya baci cikin dangi kaf.
Ya musa yazo gidan mu mun dade muna hira dashi a ranan sosai nan yake fada min irin abubuwan da suka faru dashi a lokacin.
Na tausaya masa sosai na kuma yi masa addua Allah ya kawo masa dauki cikin lamarinsa yace amin mukayi sallama dashi yace sai ya kara zagayowa nace ya jirani na shiga daki nafito da kudi a hannuna na mika mai yace .
Zahra bansan me zance maki ba kinga wanan dan zaman da kika ban lokacin ki mukayi yafi min komai dadi a yanzu don yafi min wanan kudin da kika bani don babu wanda ke zama dani muyi magana ta fahinta sai ummah saiko ke yanzu da muka zauna dake kika fahinceni.
Hawayene ya taru a idona nace yaya kowama yana fahitar ka kawai dai don baka dashi yanzu Abba kuma dake baka shima baidashi a yanzu yasa suke maka daukan mahaukaci.
Tare da taimakon ka kuma yaya don wanan shaye shayen shine ya kara sa mutane suna maka daukan mahaukaci ba girman ka bane da darajanka ace wai kana sha a yanzu.
Shekarun ku yakai ace kun fara aje mata a yanzu dakai da yaya jafar gurin su mama ke nan yanzu a kanku suga kun fara aje iyali a tare daku.
Dariya yayi yana fadin kai zahra waye zaisoni a haka ki dai tayani rokon Allah na samu abinyi na gina gidan kaina inda zan aje mata.
Muka kwashi lokaci tsaye muna magana ya sallameni ya tafi nima na koma ciki na zauna ina tunanen duniya gaskiya mutum ya godewa Allah idan Allah ya tsarkake masa zuciyan shi ga komai.
Yau yayan mamace ke wanan gararanban rayuwa haka rayuwa bashi da tabbas ga dan Adam don in kaine yau bakaine gobe ba na tuna yadda mama da yaranta suke kamar wani gwanati ga iko ga izza da takama da isa ga kowa sai tayima kallon banzan nan nata a wullakance zata kalli mutum.
Sai gashi a yanzu yadda naga su mama har yaranta mata da take mutuwan so duk sun koma abin tausayi don komai ya kare a yanzu din dama ashe da abin hannun Abba suke komai.
Amma a lokacin mama cewa takeyi ni ban dogara da abin Alh ba kun sani kodashi ko bashi sai inyi yadda nake so a rayuwata Allah ke nan yanzu tun a duniya yake jarabtan bawansa.
Wai yau mamace ke fadin sun rasa motan shiga a gidan mu ta manta lokacin data karbe min mota kuma ba ai komai ba haka maganan ya zauna motar ta karbu ke nan kuwa.
Don duk zaman auren da nayi gidan Abba banda mota shima baida shi dama kuma hakan akeson aga rayuwan mu ciki sai gashi da taimakon Allah abubuwa sun juya a yanzu.
Tau gamu dai mun zo naji muryan Asmau dake shigowa gidan tana fadi hakan ya katse min tunanena na gidan mu a lokacin na koma kallon Asmau dasuka shigo da kawayen ta gidan.
Mamaki naji yadda akayi suka san gidan na taresu da haba haba ina masu sannu da zuwa nasa aka kawo masu abinci da abinsha da sauran abin motsa baki.
Aisha ta fito tana masu sannu da zuwa suka amsa nan Asmau ta fara sake magana a fakaice dana fahinci dani sukeyi na mike ina fadin jummai idan bakin sun fita ki gyara wurin ni zan kwantane na kallesu a wullakance nace sai anjiman ku ko .
Na hada kan yarana dake wasa muka shige ciki abina na dasu na rufo kofa na barsu a falon zaune sai ta muzanta a wurin kawayen nata a lokacin irin yadda nayi masu din don haka basu dade bama sukace zasu tafi.
Tana zuwa gida take ba inna labari tace inna yau naga duniya naje gidan yaya da tambaya da komai saida nagano gidan wallahi can fa New GRA gidan yake cikin manyan mutane inna.
Hummm kinga Zahra yadda take mulki lallai Zahra ta gama maki da da wallahi saidai hakkuri bayama gari ashe Aisha ke fada muna dije ko har muka fito gidan bata fito mun gaisa da ita ba.
Yau inna naga abu ke wallahi inna wani abin ma na gidan ban taba ganin sa nidai Zahra wai harda cewa a wanke kayan da mukaci abincin dashi idan mun gama yaran nason zuwa wurin mu ta hana.
Halan daga gidan ubanta tazo dasu ko taki ko taso dai dole ace daku kanen ubansune kuma ciki daya kuka kwanta da ubansu.
Abinda nake hangowa ke nan tun farko naso tun lokacin ya kara aure don gudun irin hakan dama nasan tunda ba raggo baneshi yana samu hakace zata kasance dashi sai yadda suka juyashi.
Yanzu gashi sun mallakeshi komai suke tsara mai yadda zaiyi bai daukemu a bakin komai ba ga umma ta mallake masa zuciya kamar itace ta haifoshi duniya.
Dije kan ji take kamar itace uwarsu don a yanzu nunawa take kamar itace uwarshi dole inna sai kinyiwa abin tufka gaba dayansu ke seta masu hankalinsu harshi kansa din ki nuna masu kece uwarshi dai.
Gobe sammako zan masu a gidan wai nan suga yan birni sun barmu a rubaben gida sun koma sabo na gani na fada nida wahalan ciki na haifi da suda jin dadinshi a yanzu.
Lalai dai kan inna sai kin nuna masu cewa kema da sauranki zasu shiga hankalinsu dake don wallahi inkince zaki zuba ido ana abubuwa haka za a shaki a banza bagas.
Don da gangan Dije keyi hakan don bata son ki ni na taba ganin ace wai kaka ta shige gaban uwa ta kicicine komai ta hana gaba ta hana baya duk ta tare kofa babu wuri duk wanda yazo ba zai shiga ba.
Ai kilama asiri ta hadashi dashi da bai ganin kowa da mutunci sai ita don komai Dije zata iya akanshi inba haka yaya zai rika barin ki ya kama dije sai matarshi.
Uwar tace ba asiri bane kafazucin juna sukeyi ita dashi don tun lokacin dana haifeshi a hannunta yake har yau din nan kiga kuwa yafi saninta dani.
Nima yanzun nake jin haushin hakan yadda na barshi kamar ba dana bane nasan harda abubuwan da babanku yai ta masa a lokacin ya hada yake jin haushina yanzu a kansa.
Ni kuma Allah ya gani lokacin dana san babanku zai tafi ya barmu ne dana kamashi sosai wallahi amma a lokacin sai nake tsoron kada in matsawa son dana baban naku ya sakoni kan hakan a fara kirga min dakin aure yasa na biyewa hauka irin nasa nakin agola a gidansa.
Atoh ki daiyi wani abu ake kika haifesa ba dije ba don me yanzu dije zata dinga jin dadinsa ita kadai ke a wareki a gefe dole kan sai kinyi wani abu zasu tuna da hakan.
Sallama aka kwada suka amsa wani daga kofa yace masu ginane sukazo duban wuri muna son a bamu izini mu shigo mu duba gidan don Allah ?
Kallon juna sukayi kafin ita Asmau tace anya malam nane kuwa akace kazo ka duba yace kwarai banan bane gidansu Master tsoho wanda ke auren zahra yar gidan Ali custom yanzu ?
Asmau ce ta mike ta fita don taga ko suwaye ta samu mutum hudu a tsaye waje kallo ta bisu dashi tana fadin master ne ya turomu muzo mu duba gidan nan za ai masa aikine a ciki.
Wani murguda baki tayi tana fadin mu ai bai fada muna cewa zakuzo ba don haka bamu san da zancen ba mu sai ku koma ku fada mashi bamu da labarin wani aiki a gidan nan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/16, 2:27 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
9️⃣9️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Allah muna rokon ka cikin kyawawan sunanka tsarkakkaku masu daraja da daukaka ka saukaka ka sanyaya kaji kai ka sahile kashiga lamarin baby Zahra ka kawo mata dauki da daukin ka ya Allah kaba wanan yarinyar lafiya a cikin sauki komai yazowa iyayyenta a saukake ya Allah ka hore masu abinda zasu dubeta dashi har karewan wanan jerabawan nasu.
Ya Allah kabawa baby Zahra lafiya inganttace da ita da duk kan sauran musulmin Allah na duniya marasa lafiya Allah ka basu lafiya masu lafiya Allah ka kara masu Allah kabawa baby Zahra lafiya ka yayye mata wanan laluran nata a saukake ya Allah.
Wanda suka taimaka Allah ka basu ladan taimako wanda keda niya baida halin hakan ubangiji Allah ka hore masa ka basa ladan niyyasa.
Ya ubangiji kasa a shiga da ita a sa,a a fito da ita lafiya masu lalura irin nata dama wanda ba irin nata ba ubangiji ka basu lafiya Allahuma Amin Allah.
Ya Allah kasa ayi aikin nan nata dana sauran musulmai a cikin nasara Allah ka dubawa iyayyen yarinyar nan laluransu ka haskakawa rayuwan su Amin ya Allah na Annabi ya tayamu da Amin ya Allahu 👏

Karfe hudu da rabi yana cikin gidan nasa na gusau wanda dawowan shi ke nan lokacin daga tafiyan da yayi Abuja zuwa rakiyan su Abban mu daga can kuma ya tsaya yin wasu aiyuka a office dinsu na nan Nigeria.
Waya yakeyi yana fita motar kunnensa na makale da yar wayasan a cikin fada yake fadin gaskiya salisu ban dauka har zan dawo garin nan baku fara wanan aikin ba.
Wanda suke wayan dashine ya tsaya masa bayani can yace amma kasan muyi dakai ai zaka duba abin daga karshe kayi min bayanin yadda ya kamata a tsara wajen yanzu.
A daidai lokacin ne kuma idonshi ya sauka a dan tsiron daya fito a can manne da jikin gatangan gidan nasa wanda yasha interlock ko ina da akabi akai ado da launin ja a tsakiya.
A hankali yake takawa zuwa wurin wanan tsiron yana sauraren salisu din yana kuma bin wanan tsiron da kallo har ya durkusa yakai tsugune yana kai hannunsa daya a saman tsiron yana duban shi cikin mamaki kafin ya sake wani shu,umin murmushi a fuskanshi yana fadin ba matsala kuje din yanzu ku diba ina gida nan gusau din sai kuzo kuyi min bayani idan kun fito.
Don banson aikin ya dauki lokaci mai tsawo don Allah don koda yaushe zan iya komawa da iyalina US a yanzu to sai kazo ya fada yana mikewa tare da kara kai hannunshi a jikin dan tsiron yana mamaki a lokacin.
Juyawa yayi ya kalli Bala maigadi da sharesharen filin gidan sai ya gansu dukkansu su ukun tsaye bayan shi suna jiran ya gama wayan suyi mai sannu da zuwa yace.
Malam bala ashe kana kusa don Allah wanan tsiron kada a kuskura a cireshi a wurin nan a barshi nan don kyautane daga Allah duk inda nake irin hakan yake fitowa a wajen saboda haka kada ka cire min shi don Allah.
Duk ma wani kalansa da zai fito a barshi a ciki gidan nan don Allah da sauri isah mai gugu ya karbe da fadin maigida ai kamar tumfafiyace uwar kwankwanmai cireta ma ai gangancine a wuri.
To don Allah a barshi kada a cire ya kara fada yana kokarin shiga cikin gidan kai tsaye lokacin ne suka samu daman mika gaisuwansu gareshi ya tsaya ya amsa ya shige ciki.
Ya barsu a wurin malam balane ya fara magana yana fadin kai wanan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login