Showing 240001 words to 243000 words out of 304363 words

Chapter 81 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33363

abin bautansu.
Allah yayisu mutanene karfafa ga baki ga tsayi irin kiran samudawa mazansu da matansu yana da wuya ka samu wanda baida tsawo a cikinsu gaskiya.
Sun dogarane da noma da kiwo sai sana,oin da akasan malam bakar fata dashi irin su kira rini farauta da sauransu .
Zaman su makwabta da Nigeria yasa a yanzu idan kaje kasan zaka samu mutanen mu na nan Nigeria a can suna sana,an neman kudi don gaskiya akwai albarkan kasa a tare dasu sosai hakan yasa wasu ke ketarawa daga nan zuwa can su kama yan sana,oinsu na hannu.
Ko addinin na wa yan nan mutanen gashi nan dai ga kamarsane suna muna musulmaine su ko kirtancin don al,ada yaci gaban komai a garesu har yanzun basu yarda dabi,unsu ba a kasan.
Amma haka wasu mutanen mu suke shige suyi sana,a a tare dasu don a yanzu kowa ya fahinci dan uwan junane kasa daine ba daya ba dasu.
Akwai hatsari sosai shiga irin wa yan nan wajajen amma neman na kai yanzu yasa mutanen mu basu tsoron kutsawa irin kasashen nan matuka zasu samu abinda sukaje nema a wajensu din.
Darene sosai ko wanen su yana saye da rigan sanyi ga hula sun kafa don yanayin dajin da suke shiga din don zuwa cin kasuwan da akace shigan safe zasuyiwa kasuwan.
Gashi kuma an labarta masu cewa hatsinsu yana da sauki sosai kuma ana samu ba sai ya katse ba don haka suka shigo wanan kasar su gwada sa,ansu.
Wasu barci suke wasu kuma sabbin zuwa irin su Amadi sai bin surkukin dajin sukeyi da kallon tsoro tare da tunane kala kala a zukatansu.
A garin akwai Irin su shimkafa masara dawa shine dalilin yin wanan tafiyan na Amadi tare da abokan nansa da suka kwadaita mashi zuwa wanan garin neman hatsin irin wanda suke sayarwa.
Alhamdullahi sun isa lafiya sunje sun samu kamar yadda labarin yazo masu hadi da kari kuma sun gane cewa zaka iya daukan mai a nan Nigeria kaiwa mutanen shima akwai samu a cikinsa sosai saida hakan akwai wahala.
Wanda yai masu jagora zuwa garin suke bi a baya yayin da yake kara nausawa cikin kasuwan zuwa dasu wurin abokan cinikinsa .
Duk sammakonsu sun samu kasuwa ta faraci a lokacin don haka wuri ya fara cika sosai da mutane wanda yayo masu jagora yana ta ja masu kunne akan su kulla da kudinsu dai don akwai bariyi sosai a kasuwan.
Amadi bai yarda an barshi a baya ko gefe ya tsakiya cikin tawagansu har suka kai wajen ga kayan gona nan ko wani irin launi an baza a wajen gwanin burgewa.
Cinikin gaba daya aka fara yi suji kudin buhuhunan yayin da suka shagala da sauraron bayanin da mutumin keyi ake fassara masu haka kawai ba zato yaji anja bayan riganshi .
Cikin azama ya juyo a zatonshi barawone yake lalubenshi sai yaga wani tsoho a cikin shigar kamala na mutunci tsaye a bayan nasa yana mashi murmushi.
Nan take hankalin kowa ya dawo garesu sai kawai wanan tsohon ya zube kasa ya daga hannu kamar wanda yakewa wani basarake ko babban mutum gaisuwa ya fara jera mai kirari a cikin yaresu.
Ido kowa ya zuba masu yana kallonsu shi Amadin bai gusa ba haka shima dai bai dago daga yadda yaken ba sai faman jerawa mutumin kirari yakeyi.
Dama wanan din dan sarkin fulanine kuke tafe dashi wanan mutumin mai masu fassaran yare yake tambayan cikin mamaki.
Wanan din gaskiya ban tsamanin hakan don dai a sanina shidin kamar ba dan kowa bane fa da sauri wanan din yace a, a kada kace hakan saidai idan kaine baka sani ba gaskiya .
Amma abinda Alh ke fadi ya nuna alaman sarauta da kudi ga yaron shi kuma din kansa wani babbane nan gaba haka kawai basuyi aune ba sai suka fara ganin jinsin wasu kabila na kasuwan suna kawo mai gaisuwa lokaci guda.
Tsohon na farko ya dago kai yanawa Amadi din wasu gwalancin cikin yarensu shidai ido kawai ya zuba masu yana binsu da kallo ya dauka hakan sallon wani yaudarane a gareshi suka fito mai dashi sai kokarin dafe madaurin kudin shi yakeyi lokacin.
Wai ku taimaka yaje gidansa kafin ya tafi akwai maganan da yake son yi dashi don Allah wani ya fada masu a cikin yaren hausa da sukeji don mutane kamar ko ina idan sunga abin mamaki harsun kewaye suna kallon ikon Allah .
Kai haba dai ina haka zai yuyu haka kawai bamu san mutum ba kuce ya bishi ya bishi zuwa ina iyakarmu cikin kasuwan nan saiko bakin motar mu in kaga mun daga nan wani babban mutum daga cikin su Amadi din ya fada.
Haba don Allah wanan Alh gambarine fa sananen mai kudi kuma basarake a cikin kasan nan ba wanan kasuwan ba duk wani kasuwa mai tashe a kasan nan asandashi sananen mutum ne shi sosai .
In bakai mamaki ba kusan kayan wajen nan nasa ne kafa wallahi don haka ba zai taba masa wani abuba gaskiya kawai dai akwai abinda ya sanine a game dashi.
Alh Bala ku bari kawai zan bishi inji ko me yake son fada min dole akwai wani abu don bai fadi karya ba ainihin tsotson mahaifina basarake ne a can kasansu don haka wani abin yake son sanar dani.
Kai Amadi wanan wani sabon zance kake son sanar damu kada kwadayin duniya ya kaika ka jawowa kanka wahala ba ruwan mu hatsi mukazo saya shi zamu saya mu koma.
Kafin ya karasa fadin maganan shi baiyi aune ba sai ganin Amadin ya daga wanan tsohon yayi ya kuma tsaya suna gwalanci dashi duk suka zuba masu idanu suna kallon su.
Zan bishi yace ba zamu dade ba yanzu zamu dawo kafin a gama lodin kayan mu idan an shirya suka amsa mashi tunda ikon Allah suke kallo a lokacin.
Wanan dattijon ya fito wani mutum yazo ya kaishi ga wanan mai masu jagora yake fadin zai tafi da wanan don ya dinga masa bayanin inda bai fahinceshi ba suka dan amsa da to kawai.
Nan suka fara kus kus dinshi shidai yabi bayan mutumin suka tafi tafiyan daya kawo karshen komai ya kuma walwalewa Amadin kai lokaci guda.
Da farko ya dauka kusane zasu tafi saida yaga anyi tafiya mai nisa ya fara dana sanin biyo wanan mutumin da bai sani ba bai kuma san mai ceton shi ba a lokacin bayan Allah.
Gidane irin nasu ginan na kasan komai da laka akayishi da duwatsu har shefen sumintin ginan nasu fari kal da alaman farar kasane akai amfani dashi ga ginan.
Saidai alama ya nuna cewa ginan gidan yanayin shi na babban mutum ne don yadda aka bambantashi da sauran ginan kauyen duk komai kallo yake kamar a mafalki lokacin.
Kauyen ya tuna mashi zuwanshi kasan mambila don yaren fulatancin daya samu sunayi a nan ba wancan yare ba da suka baro a cikin kasuwa ba.
Da hannu ya yafuto wani yazo a cikin dan sarsarfa irinta girmawawa yai masa yare sai ya juya yabi wani hanya yana sauri ya tafi.
Manyan tabarmin saka na kaba irin na gargajiya daya sani a da yaga an fito dasu ana shimfidawa a wani innuwan iccen daya samu wuri ya baje ya sake rassa sai innu da duhu har yana ba mutum tsoro.
Suka nufi wajen suka zauna yara nata kawo filo da tim tim sai binsu da kallo yake yana mamaki ya kalli wanan mutumin da sukazo tare yace ka fadawa bakon yayi hakkuri da yanayin mu na nan din.
Gashi kuma har wa yau ba yaren mu yake ji bashi da badon hakan ba dayasha bayani yau a bakina amma a gurguje ka fada mai muna mashi sannu da zuwa.
Ya saki jikinshi nan din gidane garshi idan ya sani ka kuma fads mai komai a gurguje zamuyishi yanzu don ba lokaci garemu zan bashi magani yasha a nan ko zai yarda yasha din ?
Nan wanan mutumin ya juyo yayiwa Amadi din bayanin duk abinda tsohon ya fada yayi dan murmushi yana gyara zama tare da kada kai.
Tsohon basaraken nan ya kara tare numfashin mutumin a cikin yaren kasan yana fadin ka gaiya masa nace shi din jinin gidan Hardo Amadune kuma jika ga hardo Bukar na garin Chedi Garba ko ?
Don haka ya saki jiki babu cutarwa a tsakanin mu dashi zan taimaka mashi kan abinda baisan dashi bane a jikinshi dake biye dashi tun yana yaro karami .
Ko ya yarda da nasan shiko waye a yanzu sai mutumin ya kara masa bayani kamar yadda ya fada mai yace ya yarda yayin da wata zuciya ke fadin haka kawai zaka amince masa ba tare da sanin koshi waye ba gareka.
Bayani tsab yadda zai fahinta kuma wanan tsohon duk yaiwa mutumin ya gamsu da hakan din haka ya yarda a zuciyarshi koma meye zai karba yayi kamar yadda ya hango gaskiya a cikin idon mutumin lokaci guda.
Kaidin sun sani magajin chedine yasa suka daure duk wani hanya naka da zaisa ka hasaka a san da kai da badon naka mabiyan nagadon gida ba da komai ya gama faruwa dakai a yanzu.
Amma ka godewa Allah da taimakon wasu abubuwan sunki tafiya a yadda sukeson suje masu saidai abu daya shine wanda aka bizzine a wani tsohon rijiyan da yanzu har anshafeshi .
Shi wanan abin kuwa nake son na baka makarin shi a yanzu da zaran yabi jikin ka zaka iya tunkaran duk sauran matsalolin naka ba tare da wani abu ya sameka kaba.
Nasan kasan da hakan don an sanar dakai komai a baya kan hakan Allah ya taimaka fararen mabiya ke biye dakai masu karfi donsu ke hana jifan ya sameka yadda suke so.
Duk yana wanan bayanin ne yana kulla magani a cikin wani jakkar fatan dabban daji daya fito dashi daga cikin gidan nasa wanda babu komai a ciki sai tarin magani irin na gargajiya kala kala a cikin jakkar fatan.
Idan kayi amfani da wanan daga ranan su kansu zasusan komai ya kare garesu don abin zai koma garesu ga baki daya duk yadda sukaso samun ka ba zasu taba cinma ba da yardan ubangiji.
Saidai kaidin kada ka yarda kaiwa wani sheri koda ta zuciyane don wanan maganin da zan baka bana rama mugunta bane ga maishi saidai ka barwa Allah ikonshi kawai akan mutum.
Wanan mutumin ne ya kawo nono a cikon kwarya sabon tatsa ya karba yana mai godiya ya nan ya bude ya barbada wani garin magani ya rike kwaryan yana wasu maganganu kafin ya mikowa Amadin yana fadin duka zaka shanye yanzun nan ka bani kwaryan .
Amadin ya karba da bissimillah a zuciyar shi kafin yakai a bakinshi ya kurba ya fara zuka yana jin dumin nonon saidai sam maganin baida daci ko bauri haka ya sha ba tare da yaji komai alokacin ba.
Ya mikawa tsohon kwaryan ya karkadeshi ya kara miko mashi ya jawo kullin da yayi yanawa wanan mutumin bayani kadin ya mike ya karbi kwaryan yayi tako kamar biyar daga inda suke ya tarwatse wanan kwaryan ya bi kasa a ruguje don ba karamin bugashi a kasan yayi ba lokaci daya ya tarwarse a wajen.
Humm mai karatu kowaye ba asiri a duniya bata sameshi bane wallahi kedai kawai kara rike Allah don shine mai jin kan bayinsa dakuma tsare bawa daga duk wani sheri.
A daidai lokacin Amadin yaji kamar wani abu ya fita a kanshi yabi ta kunnuwan shi ya fita har yana jin tashin abin sama sai kuma ga guwaguwa ta hade a wurin ta nausa tayi yamma da inda suke zaune din.
Kuna da Tumfafiya a gida ko yaji mutumin ya tambayeshi wanda ke masa fassara din sai kuma tsohon yace akwaita kuma ya tsare dokokinta sosai bashi ba har matan shi tasan fa,idan wanan iccen yanzu itama.
Itama kusan laluran ku daya da ita saidai dan bambamcin kadan ne don ita nasu kawai suga rashin cigabansune kuma a zatonsu sun gani din don haka sun fita zancen saidai hassada da bakin ciki da zai biyo baya nan gaba kadan.
Karbi wanan ka kai mata zata sha wanan din a cikin dare yayin da kafa ya dauke wanan kuma sai ta turara kada tai magana da kowa sai da safe har kwana uku.
Shi wanan din wanan tsohuwar akuyan ta gidan ku mai bidilwan nan igiyan daureta zaka zuba akara dakawa duk wani mugu idan kunyi amfani dashi zaiji tsoron tunkaranka a lokacin
Haka kuma matarka itama ta dage kuna da kokarin addua sosai kuna kula da addinin ku shiyasa basu taba nasara akanku kai mata wanan din.
Idan tayi zata sha mamaki bani ba kadai har yan uwata da mahaifiyan mu yabawa wani magani akawo muna shi kuma Amadin aka dafashi sosai karfe biyun rana suka dawo kasuwan kamar yadda tsohon ya fada hakan suka sama ana lodin kayan da suka saya sai kuma abin mamaki kayan Amadi din ya fi yawa a cikin kayan sai abin ya daure masa kai sosai.
Duk da tun cikin motan kanshi ya fara daurewa na farko dai abokan tafiyan nasa da suka fara nuna mai hassada da zargi a fili saidai wanan sirin shine don haka bai kulasu ba.
Sai kuma jikinshi da yake ji kamar ba nasa ba lokacin guda kasala ya rufeshi nan ya fara zagin kansa da yarda da wanan tsohon basaraken da bai taba sani ba duk daya kawo masa Allah kusa.
A dadafe ya iso gida saidai ya samu a hakanan da yake ya wakilta wanda zai loda masa kayansa a store dinsu shi kuma ya hau mashin zuwa gida.
Ina tsaka da gyaran daki don ranan ya kasance asabar sai ganin shi nayi ya fado mkn dakin daga yanayin yadda yake magana na gane ba lafiya gareshi lokacin.
Gaisawa mukayi kawai naga ya shige uwardaka na dauka bandaki ya shiga a lokacin don haka ban matsa sai na shiga dakin ba sai kawai naci gaba da aikina.
Kayan dana wanke naje in kai dakin sai ganin mutum ya lulube da bargo yana rawan sanyi nan na rafka salati na nufi wajen shi da sauri ina tambayan shi bai iya nan amsa ba.
Ganin haka yasa na fita da sauri zuwa kiran mutanen gida da nake jiyo dariyan su a lokacin ina fada masu abinda ke varies hankali tashe.
Gaba dayansu suka taso zuwa dakin don su ganewa idon su abindake faruwa dashi yana kwance yarda na barshi Dijece ke kwala mai kira da Amadi lafiya ka dawo haka ?
Da kyat ya iya budan baki yana fadin banda lafiyane dije sai yayi shiru kowa ido ya zuba mai kafin inna ta kawar da kallon ta ga dan nata tana bin uwar dakin nawa da kallo kamar tana neman wani abu a cikin dakin lokacin.
Kasha maganine na fada hannu ya dago yai min alaman a,a can nace ko asibiti zamune haba dai kudai baku raina zancen asibiti daga ciwo kadan kuce aje asibiti.
Watakila fa gajiyan tafiyane ya kamashi tunda ba yau ai ya fara tafiya irin haka ba inna din ke duk wanan maganan lokacin.
Kafin kuma tace dani daya dawo din nan kodai kin bashi wani abu yacine hakan ya sameshi yanzu lokaci guds naji wani irin bazatan tambayan da tayi min din.
Nace idan na bashi mike nan hakan ke nufi inna ke nan inason kasheshi ke nan kome ai da zan kasheshi da ban aureshi na zauna dashi ba har wanan lokacin.
Hannu ya daga alaman ya isa hakana don Allah ganin hakan da yayi yasa nayi shiru ina mai zuba masa idanu ina kallon yadda yake fama a saman gadon lokacin.
Dijece tace su fita su barshi iya abinda ta iya fada kawai ke nan a lokacin ta bar jikan nata cikin wani yanayi gidan malam tanimu ta nufa bayan taga fitan kowa daga part din namu tajawo kofan ta rufe.


ZAINAB IDRIS MAKAWA[6/20, 8:52 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
8️⃣3️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Kwanan sa biyu a hakan yana fama kafin ya fara dan samun sauki duk da hakan yaki yarda yaje asibiti idan anyi magana zaice a barshi ciwonsa bana asibiti bane shiyasan abindake damun shi.
Hardai muka fara ganin sauki a gareshi a cikin hakane da yamma na dawo daga school rana dana fara fita muna zaune yake cewa dani yana son idan yaji sauki ya fita kasauwa washegari don sunyi waya wai ana samu wanda zai saye kayansa daya sayo gaba daya don ana neman abincin a yanzu sosai.
Zan bashi amsa wayan shi ya dauki kara ya dauks yana dubawa sai naga ga kallo inda nake da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login