Showing 39001 words to 42000 words out of 304363 words

Chapter 14 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33291

suna wahala daga baya.
Kai gaskiya shiyasa aka bar arewa baya sosai saboda irin wanan matsalan na tara iyali da wuri kaiba shekaruba ba wani aiki ba amma an cika gida da iyali.
Munyi hira sosai akan matsalan daya shafi nahiyar mu da dalila dake kawosu har lokacin sallah yayi muka mike zuwa masalaci kafin mu dawo wani malami har yashiga ko saidai munyi sa,a bai koremu ba don yasan sallah aka tafiyi.
Da yamma lis muka fito sai ban tsaya komai ba na nufi wurin motana ina kokarin budewa na hangoshi yana fitowa da kumshin kayan shi ta bayan block din mu duk da kayan sun dan rijayeshi nake gani amma haka ya daukosu ya nufo hanyar da zai fitar dashi haraban wajen.
Sai naji zuciyana nason na taimaka mashi duk da bai kalli inda motana yake ajiye ba lpkacin haka yasa na tayar da motan na mike hanyar da zai sadani da inda naga ya bi..
Horn nayi mai haka baisa ya juyoba sai tafiya yake da sauri da kumshin kayan shi a kai lokacin da gani sauri yake sosai zuwa get inda zai samu abin hawa.
Ga wasu kayan rataye a hannayenshi glass na sauke a hankali ina fadin yayana muje in sauke ka mana don bansan sunan shi ba har lokacin.
Bai jiyo ba yasa na kara danna mai horn jin hakan yasa ya dan juyo mukai arba na danyi gaba na tsaya ya zagayo nake fadin .
Na bude booth already na fada yace for what zan saukekane inda zaka dan murmushi ya sake yana fadin nida zan yawata da kayana ina ni ina shiga mota nagode kwarai da taimakon ki ya juya yana kokarin cigaba da tafiya a wahalce.
Binshi nayi da kallo cikin tausayi na dan ja motan na cin mai hannuna yana cikin jakkata ina lalube naji kudin a inda na ajesu na jawo tare da fadin.
Ga wanan sakon don Allah ya juyo na mika mai da sauri ina fadin idan ka bude zaka ga takardane ya amsa yana mamaki na figi mota na na barshi wurin tsaye yana kallon envelope din dana mika mai din.
Bai budeba naga yaci gaba da tafiya yana turowa aljihun shi na halba saman titi bansan yadda ya karasa va don ni kaina bansan nawa bane ya musa ya ban ba gaba daya na mika mashi su wanan lokacin.
Tun daga get din gidan mu nagane anyi baki a gida saidai yanayin bakin maza ya nuna ba daga nan arewa suke ba ashe kawar mamace tazowa mama a bazata ita da yaranta daga lagos.
Saida na shiga gidane ummah ke fada min zuwan hjy Rafat din nasanta sosai farin sani duk wani iya shegen bariki itace ta koyawa mamashi zaman su a legas tare.
Don daya bai wanka ya bushe yana gidan daya mama ta iya shige shigen yarbawa kamar me haka al,adun su duk ta iya sosai don haka yaren lagos radau a bakunan mama da yaranta kaf.
Akwai wani dan hjy Rafat din daya samin ido sosai idan naje hutu yana cewa wai sona yakeyi wanan yasa dana fara girma na daina zuwa legos wurin su hutu kamar yadda na saba ina karama saina fake ga karatu a lokacin.
Kai tsaye na nufi dakina na soma cire kayan jikina sai nayi wani tunane hakan yasa na juya na fito falo na zauna naci abinci babu kowa daga cikin kannena a lokacin don hakane gidan yai shiru a lokacin.
Saidan motsin Tani dake aiki a kitchen lokacin kadai ke tashi a falon da sallaman zamani Rukkaiya ta shigo ta hangoni zaune saman dining table din mu ina cin abinci tace min ke mama na kiranki .
Nima juyowa nayi jin yadda tayi min magana na mayar mata da fadin wa,ni ina nuna kaina da hannuna tace ke mana ok idan na g
hada zanzo na bata amsa nima.
Kamar zata sake magana sai tayi shiru ta wani irin juyawa kamar a hasale lokacin ne tace ina zakizo kizo don ba mama bace ke son ganin mami Dele ne tazo dama akace akiraki ta hada da tsuki ta tafi.
A daidai lokacin umma tana fitowa daga kingun shiga dakunan kwanan mu na part din ta bita da kallo saida ta karaso take tambayan meya kawo wanan nan ?
Wai inzo inji hjyn Lagos ta fada ai dama zaki kigaida ita tunda batai maki komai ba koda tayi kuma ai bata fitar a fili ba angani.
Saiki tashi kije kada kuma taje ta fada masu wani abin daba don karamin aikin Rukkaiyane hadin fada kindai san halinsu ba sai na fada maki ba.
Dole na mike nabi bayan ta na shiga da sallamana falo suke zaune gaba dayan su jin sallaman nawa yasa suka juyo suna kallona banda mama da yan uwana da suka hade rai a wurin.
Hjy Rafat da diyan ta uku suka fara sake min murmushi tare da fadin see u you na your face be dis kowan su fuskan shi dauke da fara,a a gareni.
Da dan sarsarfa na karasa gun mami din saidai na dungumeta kadan na saketa nakai kasa tare da fadin your welcome mah ta shafo kaina tana fadin ji yadda kika koma wata babba dake haka Zarah?
Na danyi murmushi kadan tare da tambayanta ya hanya na dago kai ina gaida yaya nata da duk suka zubo min idanuwan su a kaina lokaci guda.
Bayan na gaidasu mama data mike tun shigowana ta dawo ta zauna kusa da mami din na dago a cikin fargaba ina gaida ita ta amsa min da fadin lafiya kalau kun dawo ke nan ?
Eh na fada na dukar da kaina kasa muryan mami Dele dince ke fadin u no see you man Dele, he de worry me asking you yanzu kuma ya ganki ya noke kamar bashi ba.
Nayi murmushi sai kanin nasa yace shima yaji mamakin girman tane haka ta koma wata babban mace da ita shekaran ki nawa yanzu a jami, a ?
Bai samu kanshi wanan yinin ba balle ya tuna da zancen envelope din ba don haka har yamma bai san meke cikin envelope din nan don bai koma ta kanshi bama alokacin.
Don yana raragewa kasuwa ya koma don ya saro wasu kayan da zai fita dasu da safe yakoyi sa,a ya samu an bude a gaban shi.
Don haka dilace mai kyau na kayan maza ya samu giredi kamar anzabo mashi sune daga can ya taki sa,a matuka don yana zuwa ana bude dila saidai kudin shi basu kai ya saye dilan duka ba lokacin.
Don haka ya zaba tare da rokan mai kayan ya aje mai zuwa safe ko yamma zai dawo ya saye sauran ga baki daya .
Mutumin yai shiru na dan lokaci kafin ya duba sabo da kwazon yaron yace amma idan bakai bane banayin haka gaskiya tunda inada masaya.
Ida har bakazo ba zuwa biyar zan sayar dasu duka gaskiya yana magana yana hada sauran kayan a wuri daya don ya adana mashi kada wani yazo ya dauka bai sani ba.
Ya bashi kudin tare da godiya kan karancin da yayi mai saboda sabo da juna da sukayi ya dauko kayan shi zuwa inda zai samu abin hawa da zai kaishi unguwarsu.
Da kayan shi niki niki ya shigo bai tsaya ba sai kofan dakin Dije data riga ta tayar da sallah magariba a lokaci shima buta ya dauka ya fara alwala kada ya rasa jam,i.
Bai dawo gidan ba sai yamma lis ya dawo duk a gajiye yake sosai a lokacin hakan bai hana shi zuwa wurin uwar garke dake kwance ba ita da yayan ta..
Duban abin abincin su yayi babu komai a cikin kwanon haka yasa ya fita gidan ba tare da sanin Dije ba yaje gidan da ake sayar da abincin dabbobi unguwar don ya sayo masu.
Dije wace taji shigowan shi gidan saidai bata karajin motsin shi ba a zatonta yana dakin shi yana hada kaya ta fito tana magana taji shiru.
Yau ga ja,iri kafita ne koka kewaya ban dakine wai ita kadai take maganan a tsakar gida sai gashi ya bullo a cikin duhu har saida ta dan kadu dan ganin shi a lokacin.
Tambaya yayi lafiya kike nan a tsaye cikin duhu wai kai na fito nema naji motsin ka kuma nazo naji shiru ashema kana waje.
Naje nan gidan malu ce na karbowa dabbobin nan abinci don naga basu da abinci saidai dusan gwaunatice na samu na gargajiyan ya kare tace.
Dadina dakai Amadi akwai kula duk da wanan gajiyan daka kwaso bai hana ka tuna da bayin Allah nan ba a ranka Dije dole mu kula dasu tunda mun turkesu a wuri daya idan bamu basu abinci ba sai Allah ya tambayemu hakkin su akan mu.
Yana bata amsa ya duka yana zubawa dabbobin abinci kafin yakai hannu ga uwar garke yana fadin uwar garke tashi kiyi kiwo kada ki kwana da yunwa kinji kuci sai na sayo maku haki gobe insha Allahu.
Zakace da mutane yake wanan maganan yadda dabbobin suka mike suka fara kiwo lokaci guda abin shan ruwan su ya dauka ya daure guntun jarkan da aka yanke ana zuba masu ruwan sha a ciki yaje har randan ruwan su ya debo ruwa lokacin ya farga da basu sa ruwa a gidan ashe.
Yana gamawa da dabbobin ruwa ya fara diban masu yana cika kayan zuba ruwan Dije duk ya samu ya cika don ya samu ba mutane sosai wurin ruwan.
Sai goma da wani abu ya samu kanshi ya sauya kayan jikinshi ya nufo dakin Dije wace ke shirin kwanciya hannu dauke da takardan da yarinyar nan da sunan gidan su ya sani na MAYANA.
Zama yayi yana bude takardan don ganin meke ciki kudine suka zobo daga cikin takardan zuwa jikin shi sabi dasu kar saida ya dan kadu da ganin hakan.
Kai din da yace yasa Dije juyowa inda yake tana kalloshi idonta ya sauka saman kudin da yake tattarawa a jikinshi.
Amadi ina kafito da wanan kudin sabbi haka kar dasu tana tambaya take tsureshi da ido a cikin tsaro da son jin ina ya fito da wa yan nan kudin masu yawa.
Bai dago kaiba don tsayawa da yayi kidaya kudin dubu darine cif din su a mike dinsu suna daukan ido tambaya ta jefo mai da ina kafito da wanan kudin Amadi ?
Wallahi Dije ina wanan yarinyar da matar nan tazo gidan nan karbawa magani wurin malam tanimu ranan to itace dazun ta bani shi tace don Allah na karba kada in bude sai nazo gida.
Nina dauka ma wani takardan wani abune a ciki ai ashe kudine ta saka haka a cikin takardan nan ta bani har tana fadim nayi hakkuri dashi don Allah.
Amadi kudi lafiya mace ce zata baka kudi haka kuma yarinya karama kadafa ta jawo muna matsala muna zaune kalau a yanzu ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[06/01 9:38 AM] Ummu Ammar: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , ,
1️⃣4️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Na sayar da wanan labarin don Allah kada wani ko wata yayi audiovisual din labarin nan don Allah yin hakan taka dokane.
Duk da akwai matsala a tsakani mama da ummah sai nayi mamakin ganin ai ummahce mai dawainiya da bakin mama din kuma da duk wani abinda zasici zasu sha daga wirin umma yake fitowa .
Naso nayi wanan tambaya saida ba fuskan yin hakan gareni naja bakina nayi shiru ina kallon su a fakaice don nikan washe gari tun safe na fita zuwa school ban dawo ba sai shidda na yamma na iso gida.
A wajen gidan mu na samu su Dele sun fito shan iska har na karaso cikin gidan na aje mota idonsu yana kaina gashi naki jin hakan a rayuwana mutum ya kura min ido ba daukewa.
Naso sharesu amma ganin hakan ba zai yuyu gareni ba yasa dana fito na nufi inda suke zaune din don na gaidasu.
Tun kan na karaso kabir kanin Dele ke fadin wow what a beautiful car is this sister kunyi kyau dake da motar taki baki daya so wanan ce motar da mami jafar ke fadin an saya maki dama ba a saiwa su Aisha ba gaskiya motar nada kyau sosai wallahi.
Nagode na fada kafin na dago kai wurin Dele ina gaidashi ya amsa min cikin dan nisawa yana gyara zaman shi tare da fadin kin dawo ashe nace eh ya sabon yanayi.
Sai lokacin ya danyi murmushin gefe a fuskanshi yace ba matsala ina enjoyed din garin ai don weather din ku na da kyau sosai.
Gaskiya yarinya daddy ku ya fito dake gari dole mamin jafar tace ojuju ku kaiwa daddy ku har ya sawo maki wanan mota haka mai tsada no warder ta kira mamin mu hankaki tashe tana kuka wai mamanki dake zaku karbe mata miji a hannun ta .
Kabir dan uwan nasa ya fada a dake ya hade hannayen shi wuri daya bai motsa a yadda na sameshi ba sai idon daya zuba min kawai yana kallona kamar yaga photo.
Kabir din ya juyo yana fadin is what they said, now aiba karya na fada ba brother ayi mata magana su gyara idan sun san sufada don kada suje su kaisu wurim babalawo ya halakasu a banza.
Shit kasan sin din da kake aikatawa kuwa kabir kasan wanan yana iya jawo fitina kai meyasa kake shiga shirmen matane wai don Allah?
Na fada maka idan kaji suna shirmen su ka daina kula balle ka dauka wani abu zai iya faruwa kawai dai shirmene na mata kawai suke fadin hakan.
Nisawa nayi na gaida su suke tambayana daga ina nake nace school kabir bau dadara ba ya sake fadin lalai mami jafar saida dai tasa kikayi karatu a garin nan ke nan duk da daddy ku baiso hakaba.
I don no why wasu mata suke irin haka kan yayan mijin su meye laifin dan mijiki gareki ne wai da sukeyin wickedness akan yayan mazajen sune wai ?
Murmushi na kakaro a fuskana tare da fadin har yanzu dai kana nan yadda kake ashe daba mutum dariya shima murmushin yayi tare da fadin.
Kina ban tausayine a cikin su da kawai kizo mu koma lagos muyi zaman mu can ki kyalw kowa a nan zaifi amma idan that mumu Rukkaiya and Aisha suna ganin ki nan ba zasu bari a zauna lafiya ba And you know what ?
Na girgiza kai yace don kifisu da komaine fa yasa sukejin haushin ki har mami Jafar din Zahar ya fada daga inda yake zaune na dago ido na kalleshi yace go inside.
Cikin daure fuska nasan halinshi shiru shirune sosai shi baya da yawan magana sosai gashi bai iya bacin rai ba don dukkan su nasan halinsu tun ina karama dama kabir abokin wasanane idan mun hadu dashi.
Saidai yanzu dana girma na rage irin sakewan da nakeyi dasu a baya can don yanzu hankali yazo min na gane cewa su din ba muharamina bane yanzu.
Don hakane ban iya sakin jikina dasu a yanzu jin hakan danayi daga bakin Dele yasa na juya kawai na shige ciki abina na barsu wurin.
Ina shiga ina jiyo hayaniyar su mama a part din su da alama dai akwai bakin da sukazo masu don gaida mami din da zuwa ke nan lokacin.
Part din mu nashiga ummah tana zaune ita kadai a falon nayi sallama ta amsa na karasa ina gaida ita da tayi min ya karatun nace alhamdullahi.
Har na juya zan shige naji tana fadin kinga su kabir kuwa da dan uwanshi a nan yau suka wuni zaune tun zuwan su gaidani basu
sameki ba suka zauna na basu dade da fita ba ai.
Suna waje zaune na juyo ina bata amsa na shige ciki don zuciyana tayi nisa ga tsoron abinda naji a bakin kabir din kan zancen motana idan nayi tunane dakyau mami Dele tazone kan kiran gagawan da mama tayi mata ke nan a yanzu.
Dama nasani ko a baya idan sun samu wani matsala da Abban mu idan naje hutu wanda a yanzu na tuno da hakan bai wuce kan zancena zasu samu baraka dashi sai mami Dele din tazo zasu shige daki su dade a ciki karshe ma su gice gidan tare sai dare sosai mama take dawowa.
Don akwai wani zuwa da nayi hutu lagos din datun wanan lokacin zuwa hutun ya fara fita raina abinda ya faru shine da lokacin komawana yayi ranan muna cin abinci Abba ke fadin .
Maamah tunda zaki koma
sai yayan ki musa ya kaiki shopping ki zabi duk abinda ranki keso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login