Showing 138001 words to 141000 words out of 304363 words

Chapter 47 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33305

dawo tana sallati take gayawa yarta abinda ya fada mata din duk suka dauki sallati mahaifiyar nasa cewa tayi waya hwadamai inda zai samai ?
Dan yau da zamani ki barshi kawai kai inna ni ban yarda ya samo mutumin nan ba dije tace nima abinda zuciyana ya bani yanzu ke nan.
Sayayya yayi sosai don bakin shi don kowa bai yarda da abinda ya fada ba an dai dauka wasu mutane na daban ya dauko suzo su tsaya mashi matsayin dangin ubanai don sunsa babusu ba kuma wanda yasan inda ubanai ya hito.
Abinci kan anyi unguwa ya dauka ai yan uwan mahaifinai na zasu taho nema mai auren da ya kakabawa kainai auren diyan mai kudi shina yayo hayan ubanan banza.
Mota biyu ras sukazo dashi kana ganin su kaga fulanin usuli dogaye farare dasu tas ga kama na jini da suke dashi da mahaifninasa basai an tambaya gaduk wanda yasan habu dan filo kamar yadda suke kiranshi a zamfara din.
Nan su malamTanimu aka fara kus kus lailai yan uwan ubanai na lalai suna sai wani kanin malam ladan yace meye shedan ku na yarda da hakan.
Sai kuma aka koma aka sare ai babu tabas dasu din ne daya ya dauko hoton mahaufin nasa ya nuna sai kowa jkkkn shi ya mutu aka yarda da zancen su.

ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
4️⃣7️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Basa jin hausa sosai sai filatanci don haka ba wai lalai bane wani ya zauna dasu yayi hira ga maganganun da yan uwan mahaifiyashi ke son yi dasu Amma rashin jin hausan da suka nuna basaji yasa sun barsu dama kuma gaisawa kawai akayi ya gabatar dasu gun yan uwa.
Daga nan ya kaisu masauki inda zasu sauka sun kwana washe gari karfe goma suna falon Abba zaune suna ganawa dashi inda Abban yasha mamaki ganin yaron ashe da gatanshi .
Ba bata lokaci suka gabatar mai da sadakin aure sukace kaya mata zasu kawo idan a ka gama hadawa sukai sallama suka barsu Abba da mamakin hakan a gaban su ya musa akai komai.
Dan uwan Abbane ya kalleshi yace dama na fadama in kana bin zancen mutane kai zaka kwana a cikinsa yaron nan kowa yasan ba shege bane da ubansa.
Ya kamata mutum yai amfani da iliminshi na zamanin nan kada a kaishi a baro shi yanzu gashi kaso kuresu ko ka tozarta uwar yan nan da ita yarinyar har yaron kaga Allah ya karesu.
Shiru Abban yayi shi kadai yasan abinda yake ji a zuciyarshi game da hakan don shi har yanzu laifina dani da ummah yake gani.
Basu fadawa kowa zancen zuwansu ba saida dare ina kwancene ummah ta shigo dakina tana fadin kizo Alh yana magana damu a falonshi.
Gabana nd yayi wani irin mugun faduwa ta juya ta fita ni kuma na mike na saka hijabi a jikina na fito ummah na gaba ina binta zuwa part din Abba din dake neman mu gabana sai faduwa yakeyi a lokacin.
Ashe kusan kowa na gidan namu kaf suna falon Abba sin nida ummah ce muka shigo a karshe don haka kusan kujerun duk an zazauna kowa na kallon mu yasa ya musa da ya jafar mikewa da sauri.
Suka kwashe tarkacen kujeran dake kusa da Abba sukaiwa ummah wurin zama dama sauran matan nasa duk sun hakince saman kujerun kusa dashi sai gashi yanzu ta fisuma zama kusa dashi din sosai.
Don ita a kujera daya suke da Abba din mama cika take daga inda take zaune tana hararan yaran nata dake faman rawan jiki kan ummah din ta samu wuri yadda kowa ya samu.
Nikan na zauna kusa da inda kafan ya musa yake na dukar da kaina kasa don jikina ya bani cewa wanan zaman akaina akayishi don yadda naga kowa na gidan ya hallara sai yan kanne uku da suke kananane ba a kira ba.
Mata mu godewa Allah idan kin samu haihuwa da wuri mussanman uwargida koba komai yayan nan zasu zame maki katangan dafawa a wani wajen.
Don nasan da ace ummah Allah yaba haihuwan wuri ta haifi yara da yanzu kidon dole Abba ya daga mata kafa a wani wajen.
Don yadda naga mama tana shakan iska sosai yanzu tana nuna tafi kowa komai a gidan sai abinda tace dole kowa zaibi.
Wanan kuwa ya samo asaline da yayan ta maza manya da yanzu take ganin su wuce sanin kowa a wurin Abba din.
Can Abba din ya dago yace OK kowa yazo ko eh dama su ake jira ai gasu kuma sunzo OK dama na tara ku nan ne badon komai ba sai zancen auren yaran nan daya taso musanman naki ke zahra ya kira sunana karo na farko har yasa na daga kao na dan kalleshi.
Yaci gaba da fadin kada ki kuka da kowa duk abinda kikaje gidan yaron nan kika gani ki kuka da kanki don kece kika zabo abinki kuma na baki shi.
Ummah ta dago kai ta kalleshi ashe Abban ya ganta yace yes da in zauna ta jawo min wani zance gara kawai na mika mashi ita suje can su karata a gidanshi tunda ita tafi karfina yanzu.
Kuka na sake lokaci guda yace ai baki kuka ba sai kinji dokokin da zan kidanya a kanki yanzu don ba zan sayar da akuyana ba ta dawo tana ci min dangan gidana daga baya kuma.
Don haka abinda nake nufi a nan shine ban yarda wani ko wata yace zai taimaka maki ba daga cikin dukiyana har idan naji hakan zan sabawa mashi fiye da tsamaninsa ko waye.
Abba ya musa ya fada sai ya dagawa ya musa din hannu mama tace kai wani irin tsagerana wai ubanka na magana komu matanshi ba wanda yai magana sai kai.
Amma mama kinji abinda Abba yake fadi sai naga wanan dokan kamar yayi tsauri da yawa ga yarinyar nan kowaye ma aisai ya nemi taimako a wurin wani balle ita da zata auri wanda baida karfi.
Kai kaimin shiru ko yanzu ranka ya baci a nan na fada na kara kada wanda ya daukar min wani abinda ya fito daga tsatsona da sunan taimakawa zahra dashi.
Ai tunda ka fada an gama dama ai don ka akeyi inji mama don me za a taka dokan ka kuma, sai hjy karima tace amma dai daka sasauta dokan nan a kanta don Allah .
Iya zancena ke na sai zancen kaya don kada uwarki tace nayi bambanci su wa yan nan na riga dana masu sayayyansu a Dubai tun lokacin da suka tsayar da mazajensu don haka a yanzu banda lokacin komawa Dubai nace zan sayo maki kaya acan anan Nigerua nasa hjy karima ta duba maki kuma kayan zasu shigo wani sati sai ya fada maki inda za a aje kayan.
Idan yaga dama yai maki lefe in kuma baiyi bama wanan matsalan kuce don ni na riga na gama maganata a kanki ko kowa nan kuma yaji abinda na fada dai.
Ya jafar ne da hankalinshi ke kan waya zuciyasa na tafasa don rashin gaskiyan da yaga ana shukawa a wurin wayan nasa yayi kara ya dauka tare da mikewa don barin falon a daidai lokacin da ummah tace shike nan ko ?
Tana tambayan Abba din yace eh shike nan ko akwai wani magana ne tace a,a babu komai wallahi mun gode Allah kara arziki yasawa auren su albarka ga baki daya sai ta mike don barin falon.
Ya musa ma ya mike shima mama ko sai mere baki da takeyi tana kumshe dariyan ta hjy karima kuma cewa tayi Allah kyauta abindai baiyi dadi ba wallahi.
Dadin ke nan tunda haka suke so ai an masu Abba ya fada a hasale ko waye yace ba zaiji maganata ba haka zan masa kafin ya tozartani garin nan.

Sheshekan kuka kawai nakeyi na mike nima na nufi dakina ban samu ummah a falo ba na shige ciki a yau ne karo na farko da zance nayi bakin cikin fitowa daga cikin zurian Abba.
Ba dan komai ba sai dan irin tozarcin da yai min nida uwana a gaban kowa na gidan yana ji wanda nasan hakan ba karamin nakasu zaija min a wurin dangina ba.
Kuka kan dagani har ummah munyi shi mun gaji sai hakkuri ni dai ba zance naga ummah na wani shiri ba akan auren nan na fada na kara fadin hakan.
Ashe abinda ban sani ba shine zama da manya mata umma ta gano shirin da ake son mata don ta gama fahintar kowa zuwa lokacin.
Ta kuma gama shirin da zasuyi ko a gidan tare da yan uwanta da aminan ta kallon kowa takeyi kawai ta zuba masu idanu an kai kayan an jera washegari kuma kawar ummah tazo da nata kayan aka kwashe wanan aka jera min wasu tare da kara gyara gidan suka saka ayi abubuwan daya dace ayi.
Abu mafi girma da ummah tayi min daya dauki hankalim mutane shine saya min manya manyan freezer guda biyu wanda daga shigowa gidan part dina sune zasu tare ka sai wani tsaye na amfanina.
Mai ilimin zai fahinta iya fahintar shi da hikimar ummh na tanadar min abubuwa irin haka a matsayina na matar tallaka da zan aura.
Mama sai famkama da isa da izza sukeyi zata aurar da diya cikin gata da sa,a gari kuma ya dauki zancen bukin kowa da irin abinda yake fada a kan auren.
Ya musa duk abin rabo na buki da yai muna a ko ina zai daza hotunanmu mu uku tare da mazajen mu zakaji ana fadan wallahi mun dace munyi kyau sosai a photon.
Bansan inda hanne ta samu labari ba sai ganinta nayi kawai ta fado gida namu da ummah ta fara magana kafinta nufo dakinda nake.
Ummah abinda nake ji gaskiyane wai zahra zatayi aure bata fada maki bane ko me ummah ta tambaya sukai na dan arewa ka tambayeshi ya tamnayeka shima.
Nan dai ta mike ta shigo dakin ta sameni ina kwance naji sallamam ta don bansan ta shigo gidan ba na dago ina amsawa do na sheda muryanta.
Amma zahra baki da kirki yanzu ashe zancen auren ki akeyi har lokaci ya gabato haka amma baki fada min ba ke nan ke baki daukeni a yadda na daukiki ba ke zuciyar ki ?
Na dan harareta ina fadin yanzun ba gashi kin ji ba har kin zo nima yadda kikaji hakan naji zancen a bazata na kwashe yadda akayi na labarta mata ina kuka.
Itama kukan takeyi kafjn tayi shiru tana fadin zahra na fahinci sheri akeson kulla maku ke da ummah.
So ake aga iya kan ku a nuna maku kuba komai bane a gidan sun manta hassada ko sheri wani lokaci yana zama alheri ga bawa.
Insha Allahu auren ki da master alherine a rayuwan ki yanzu abinda nake so dake shine ki saki jiki don Allah mu fara shirin komai banji dadin rashin fada min abinda ke faru haka da bakiyi ba.
Yanzu mai kuka tsara keda master din game da bukin bamu tsara komai ba amma ban sani ba koshi ya tsara din a bangarenshi.
Gaskiya ban tsamani yan uwanki zasu hada bukin su dake don haka mu zamuyi wallima a namu bangaren walima wanda ya amsa sunan wallima duk mai zagin mu saidai ya zagemu zamuyi na farko a gidan yan uwanki sai na biyun idan an kaiki zamuyi a gidan ki ko ya kika gani ?
Duk abinda kikayi yayi daidai na bata amsa tace zan kira su manir musan abinyi yanzu kafin nan barin je falo in shawarci ummah naji.
Ta mike zuwa falon wurun ummah na koma na kwanta ina lumshe idanuna lokaci guda tare da tuno Abubuwa da dama a rayuwana.
Amadi bansan me zance da kai ba yanzu yaron nan saida katai wurin yan uwan ubaka kagano su ?
Duk da haka na da kyau don zuaan yai muna amfani don sjn taho su fishe mu kunya a idon jama,a masu maka kallon mara gata da baka da kowa yanzu saisu shiga taitaiyin su.
To Dije mi zance maki ai yanzu ke sani ko nan ya fara bata labarin yadda yayi tafiyan nasa bai fada mata komai ba son ya boye mata abubuwa da dama a cikin hiran nasa.
Ta nisa tana dafin ashe habu mutumin asalina haka da gatanai ya baro gida zuwa nan rabon haihuwanka na ya jawoshi.
Don rabo in ya rantse sai mai shi gaskiya shi nice wai ahin meya asalin waga diya da mutumin nan ya baka na ?
Shin yarinyar nada wani nakasu na ko tana da tabone yasa uban ya dauka ya baka don kowa dai yasan bakakai matsayin auren diyanai ba.
Haba dije yanzun fa kika gama fadin rabo in ya rantse sai maishi wallae zahra yar arziki ta kema kin sheda haka ni kawai na dauki wanga abu dai mukaddarina daga Allah.
Duk cikin gidansu ta fisu kyau da halin kwarai kawai sai rabona yasa mahaifin hushin zuciya don kawai tana mu,amulan karatu da niya.
Yan gulma suka dauki zancen suka kai mashi wai soyayya ya tai takai da dan tallaka da farko ya nemi da in rabu mai da diyatai nakumayi hakan.
Amma kuma anka koma anka hwada cewa ya tai har yanzu tana tare dani wai zan lalata ma wanan yasa yai hushin zuciya yace ya bani.
Ikon Allah a,a uba ka hushi haka da diyanai irin haka ya dau yarshi yabawa dan tallaka kamar ka Amadi nina dan tallaka amma dai kesan yanzu ina iya rike mata ko ?
Ko huduna amma banda diyan mai karfi irin wanan ina ya wanga gida taka iya zama gidan ga kasan fa su a cikin dadi suka taso a rayuwan su.
Dije amma aure ai zata zo yi nan ko don haka tasan ba zama irin na gidan su na komai a baje shi ba yadda rai kaso.
Namijin duniya alama dai ya nuna baka jin komai ga dauko yarga zuwa gidan ga ta zauna amma ni ina jiya maka abinda zai tai ya dawo nan gaba.
Don waga aure kamar tonon asirina a garemu in baka iya riketa ba kasan sakinta zakayi abu ya dawo ana dana sani a kanta.
A,uzu billahi Dije wane irin fatana kikayi muna haka jam banji bakinki ba walla ke da yakamata kiyi muna addua ke hwadin wagga maganan yanzu ina ga mutanen waje can su mi zasu hwada min.
Ai suna nan suna fadi batutuwa akan auren ga wasu cewa sukai auren jarina kayi wasu kuma hwadi sukai kwadena ya kai ka da sauran su.
Murmushi yayi ya mike lokaci guda ya saka takalman shi dijen na fadin ina kuma zaka muna magana kallon Dije din yayi yana fadin.
Maganan ki bata min rai yakai gara in tai zuwa inda yafi min zama sauraren wagga zance mi ruwana da mutane wa kullMin lokacin da nike cikin damuwa.
Allah ar samuna wagga yarinya a sanadin komai gareni don itata ta hwara taimakamin a rayuwana ta hito dani fili anka hwara sani na yanzu.
Ni banda abinda zan sakawa yarinya ga dashi sai fatan Allah ya bani ikon in riketa ammana inyi fatan Allah ya ban abinda zan cisheta in tufatar da ita.
Muma shina fatan mu gareku dama abinda uwarka taka damuwa kaine na yasa na hwada maka don a san abinda ake ciki kafin akai ga daurin auren.
Babu komai sai alheri in sha Allahu zahra alheri na a rayuwan mu baki daya dije ni dai ki hwadawa mama ta tayini sonta yadda nika sonta.
Yarinyar data zabeni cikin dubu tace ni taka so mi a ban iya mata a rayuwata kamamin bakin ka da bare bare tun baka san mi take ciki ba ka hwara sake zance haka.
Juyawa yayi yana kallon mahaifiyar shi dake tsaye kofan dakin tun fara maganan nasu da Dije din sai ya soke kai kasa don baiyi tunanen cewa tana wajen ba lokacin.
Ya juya a hankali ya barsu suna maganan yana magana zuciyan shi na bashi cewa idan baiyi hankali ba zai samu matsala daga mahaifiyar shi.
Don haka dole ya san yadda zai shawowa wanan lamarin tunkan yar mutane tazo azo a samu matsala a tsakanin su.
Gidan baida wani girmane da ace shi wani mai wadatane da zai ginawa zahra gidanta daban ya killance ta ya bata rayuwa mai inganci ya nuna mata kauna da soyayyan daya dade yana mata a cikon zuciuashi.
Zahra mace da ko wani cikkaken namiji zaiyi fatan ya samu a rayuwanshi don ta kumshi abubuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login