Showing 150001 words to 153000 words out of 304363 words

Chapter 51 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33309

ke gudana a tsakanin mu a wanan daren.
Saidai ban yarda nayi motsin da zaigane cewa na falkaba sai faman runtse idanuwana da nakeyi ina maijin yadda bakon yanayin ke ratsa min jikina har ina son kasa control din kaina a lokacin.
Sosai yayi duk wani wasan da zai motsa sha,awan da namiji da mace dani don a karshe na kasa hanashi ko boye nasan abinda ke faruwa a lokacin a hankali kunnuwa ke jiyo min kukan akuyan na a cikin wanan daren.
Wasa wasa ta fara wanan kukan nata cikin wani irin sauti hakan yasa naga ya mike zaune da sauri yana laluban fitilan hannun shi .
Sai can ya lalubota ya haska kan agogon bangon dakin da muke kwance din a cikinsa karfe hudu saura kwata lokacin sai kuma ya kashe ya san jima a zaune bai kwanta ba.
Ita kuma akuyan bata sake kukan ba don tayi shiru haka yasa ya koma ya kwanta a rigingine ko zataci gaba da irin kukua haka kukan da yasan bata faye yinshi ba sai idan wani abu ya faru da ita take haka.
Barci ya dan daukeshi kuma aka fara kiraye kirayem sallah yasa ya mike ya shiga bandaki wanka yayi ya fito ta samu na samu barci sosai ina kanyi a lokacin.
Ina jin bugo kofanshi na bude idanuna da kyar na iya mikewa na fada ban daki wanka nayi na dauro alwala na tayar da sallah ina idarwa nadan zauna nayi kirari ga ubangijin mu Allah tare da fado madhi irin bukatuna dake raina.
Na shafa na fito falon mu har lokacin kofan yana rufe yadda yake naji ana buga kofan ta baya sai mamakin hakan ya kamani a zatona wanine yake son shigowa part din
Yasa na nufi kofan da mamaki ina kai aka kara bugawa wanan karon da dan karfi yasa na fara kokarin bude kofan inga waye a wanan lokacin haka ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA[28/03 11:59 AM] Ummu Ammar: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
5️⃣2️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Allah sarki masu ganin laifina rashin sani yasa hakan amma duk wanda ya biya kudi yake karantawa a matsayin hakkin shi yasani saidana basu shawara tun farko.
Cewa zan dakatar da rubutu saboda yanayin karatuna a yanzu sukace naci gaba duk ranan dana samu dama na rubuta masu suna biye dani.
Su sunyi hakkuri amma sai masu karatun Allah ta isa suke korafi kan wai bana turowa kullun sai najawa mutane rai.
Yar uwa ki kwatanta da kanki mana idan kece kullun kike abinda nakeyi a yanzu zaki iya koda rabin yadda nakeyi din ?
A karshe ina maiba masoyana hakkuri don sunsan halinda nake ciki ban ci gaba da rubutu ba saida nayi shawara daku cewa zakukaga banbamcin a yanzu sosai.
Don Allah ku kara hakkuri dani don Allah yan uwa bama
Nayi mamakin ganin wace na gani tsaye kofan namu rike da buta a hannuta daya tana fadin shi yana inane wane irin bacina kukayi haka tun yanzu ya fara rashin zuwa sallan jam,i ?
Yana masalaci ai mama na fada bayan naji takai aya ga zancen ta na durkusa ina fadin ina kwana mama alokacin ne ya dawo daga sallah yana bin mu da kallon mamaki a fuskan shi.
Banji ta amsa min ba sai cewa datayi oho ai na zaci ko baku tashi bane har yanzu kuna kwance nidai na shige na barsu a nan ban koma dakin kwanan ba na dan fara gyaran falon duk da baida wani datti lokacin.
Naji ya shigo falon yana rufe part din da sakata zuwa ciki sam bansan ya kawo gareni ba sai ji nayi ya rungumeni daga baya har na dan zabura kadan alaman tsoro.
Aikin me kikeyi haka ki koma ki kwanta ki huta ki bari idan mun tashi zanyi komai ya fada a hankali kanshi na saman kafadana yake maganan.
No bari in nagama na kwanta don na saba da hakan tunda ina sammakon fita zuwa school kullun kada na zama lazy.
Ko kin tafi ina nan ai zan dinga gyarawa kafin ki dawo aikin me nakeyi yanzu da safeni ki barshi kawai kada ki matsawa kanki da wani aiki a yanzu.
Zan iya ai don ina son in saba idan baka nan wa zai dinga min aiki gara kawai in saba da hakan tunda ba kullun ne kake gidan ba ai.
Sai kawai naji ya kara matseni da hannayen shi ya fara dan murmushi kafin yace kamar a cikin rada yanzun ko da nake nan nace ki huta ni zanyi komai har girkin da zamuci duk ni zan girka muna shi.
Jin hakan dayai min yasa na dan lumshe idanuna saidai maganan shi ta karshece yasa nayi kokarin juyowa in kalleshi sai bai bani daman hakan ba don kuwa ji nayi ya daukeni cak kamar wata yarinya karama zuwa cikin dakin kwanan mu.
Tsakiyan gado ya ajeni tare da hawa gadon shima ina kokarin mirginawa ya samu daman cafkana a lokacin yana fadin No zahra kada kiyi kokarin hanani jin dumin jikin ki bayan Allah ya halatta min hakan gareki a yanzu.
Baki na dan turo sai hannuwan shi naji saman bakin nawa ya cafkesu yana fadin kin san dai haramun kike kokarin aikatawa ga hakan da kike kokarin yi a yanzu.
Kaji nace zan aikata abinda Allah zai yi fushi da, , , ban kai karshen maganata ba naji saukan nufashin shi a fuskana ban kumayi aune ba lokacin naji bakin mu ya hadu wuri daya da nasa abinda yasa na runtse idanuwana ke nan lokaci guda.
Abinda hannuwan shikeyine a lokacin yasa ni jin wani yar ga dukkan sasan jikina lokaci guda na kara lumshe idanuwana a cikin jin bakon yanayin da ban taba jin irin shiba arayuwa na ba.
Mun kai wani lokaci a hakan dashi yana abinda yaga dama da sassan jikina duk inda yaga dama yana tabawa.
Yayin da idanuwana suke fitar da wasu irin hawaye masu dumi ina jin kamar na kurma ihu azo a ceceni don jin hakan nake kamar a dole yake min hakan.
Kada kadakiga laifina mai karatu don na fadi hakan a yanzu idan zakiyi min adalci duba ga ba wani cutship mukayi dashi ba iyaka sabone amma bana soyayya ba sabone kawai da muke jin junan kamar yan uwana jini a zamana dashi.
Dolene a yanzu zanka abin a wani bambarakwai duba ga yadda auren namu yake dashi ba wani shirin hakane a zuciyana ba dole ko inga hakan a girshi gareni.
Muryan shi naji cikin sanyi yana fadin idan na bata maki rai Zahra kiyi hakkuri dole hakan ya kasance a garemu tunda muna daki daya dake.
Nina mijine mai lafiya a jikina ba zan iya zura ido ina kallon kyakyawan suranki yana min gizo da yawo a idanuna ba ba tare dana tabaki ba alhalin kina matar sunna a gareni yanzu.
Yana fadin hakan naji mikewan shi can naji ya shige bandaki motsinshi naji yana wanka bayan ya fitone najishi yana dan gyare gyaren jikinshi.
Har lokacin ina kwace rub da ciki ban motsa a yadda ya barni ba na zata fita zaiyi a lokaci sai kawai naji ya hau gadon ya kwanta daga bayana yana fadin.
Ki samu barci ki huta ki natsu najishi yana gyara kwanciyan shi tashi nayi tsab naje na shige ban dakin kafin in watsa ruwa a jikin saidana tsaya na gyara ko ina na bayin na samu natsuwa don na saba ban dakina ni kadaine a gida don haka yanzu abin ya zama min bakon yanayi a yanzu sai nake ganin an takura min a haka a rayuwana.
Nayi wanka kamar yadda sharia ya koyar ayi duk da nasan bamu shiga juna nidashi ba amma zuciyana bai bani ba saida nayi wankan tsarkin na samu natsuwa a zuciyana.
Nafito na zauna na gyara jikina ban biye masa ba bayan na gama sai na mike na fita zuwa kitchen dina sai karan bude kofana da yaji kawai lokacin ya fara barci don shi ya samu dan natsuwa a zuciyar shi a hakan daya faru tsakanin mu din.
Kitchen din nabi da kallo naga komai akwaishi a lokacin cikin kitchen din shawara nayi na dauki roba na dauko na debo arishi na fara ferewa.
Allah ya taimakeni nan da nan na gama na dora mai a wuta kamar yadda ummah ta koya min idan za a soya don haka kawai wata rana idan muna hutu ummah zata shigo da safe tace in fito muyi girkin abinci.
Wunin ranan gaba daya tare zamuyishi muna girki koda Tani tazo saidai tace ta huta ko tayi dan gyare gyaren gida a wanan wunin.
Hakan yasa na koyi wasu abubuwa da dama a rayuwana ummah kance gara na koya don ba,a san gidan da zan fada ba sai wanan lokacin nakan tuna da abubuwan da suke faruwa in muna ta jajirce tana koya min abubuwan daya kamata ya mace ta koya tunna gida don irin wanan kaddaran akewa gudu dama.
A tsanake nagama duk abinda nake sonyi na zuzuba a cikin warmers na aje na iyayyenshi a gefe daya don ina jin kunyan shiga part din nasuni.
Daki na koma na gyaro ko ina sai gadon da yake kwancene kawai ban gyara ba lokacin duk da gajiya ban yarda na kwanta ba a lokacim saima wutan abincin dana dora a lokacin don ba saurin aikine dani ba.
Yasa nayi hakan son kada na dinga jimawa suga nawata har suzo muna ganin laifin juna dasu don dole in dinga girki dasu kodon hakkin makwabtaka dana haihuwa.
Yayi mamaki daya tashi yaga irin aikin danayi duk yana kwance yana barci yake ta gaidani da aiki yana fadin sannu da aiki har sau biyu.
Na dan juyo daga inda nake zaune ina kara kwaliyan a fuskana ina gadin abincin su mama na nan a kitchen barin dauko maka ka mika masu don Allah.
Yace haba dai aida bakiyi dasu ba don suna da komai suma a part din sun an aje masu wannan namune nan nidake aka aje muna ai.
Haba dai ka taba ganin hakan zai yuyu na dafa abinci a gidan nan ban zuba masu ba ai sai a zageni idan nayi hakan tun yanzu.
Wa zai zageki kan hakan dole ki daina don duk abinda na sayo insha Allahu zan saya dasu don me za a dinga yin girki biyu kuma ?
Ki dafa iya cikin mu daga yau ninace kiyi hakan aiba wani ba yana fadin hakan ya fice zuwa wurin su bayan ya dauki abincin ya fita dashi zuwa part din.
A waje ya samesu suna hada shayi ya gaidasu suka amsa mai ya aje kayan abincin a gaban Dije dake zaune yana fadin Dije ga abincin amarya tace a kawo maku.
Don da Dijen yafi sabawa kuma ko banza tana gaba da uwar tashi ai kuma ga kara kannen shi da sauri suka taso suna bude Dije na kwabe masu hannu tana fadin nida aka kawowa ban bude na gani ba zaku bude.
A, a innan mu Allah sa dai ba kwajabon yaran zamanin nan bane wai abinci aka kawo maki kici ki zure zuwa anjima uwarshi ta fada.
Kema ke sani misun ka iya yanzu balle wanga da ta fito gidan masu kudi mizata iya banda kwaliya da saka turare mai kamshi.
Yana jin su ya kara daure fuska ya mike yana fadin zan duba dabbobin nan don yau da dare uwar garke wani kuka naji tanayi kamar taga wani abu.
Wace su zasu tsaya jiran ka har wanan lokacin kana can kwance kana kwana tun wuri kada ka dauko wanan hutun na safe ya tabama bidan ka.
Bai juyo ba yasa kai ya wuce wurin dabbobin a baya a lokacin ne Dije take fadin wai Rashida mi da baki kama girman kina ?
Shiru sukayi gaba dayan su wurin kafin can mahaifiyar nasa tace a, a wallah in ya koma maki baran bujen mace aike zaki ganin takaici nai ke daya.
Ke inna mu gara aimai fada ya gane hakan da ya dauko mata bashi da amfani tun wuri kada azo da baya abubuwa su biyo baya kuma.
Bamu ganin komai sai alheri tunda ita tace tana sonai da amarai mi zaya biyo baya kuma amren da sunkayi na soyayya tsakanin su ?
Tana fadin haka ta dauki kwano ta shige daki ta barsu da kayan a wirin don haka yar babban ta jawo basket din ta bude tana kallon abinda ke cikin warmes din tana yamutsan baki tare da fadin.
Wanga abu aiko ni daya ina iya cinyeshi innan mu kega abinda akan zubu muna wai mu duk addashi haka tana karkata abin abincin don takaici.
Cikin kashe murya kada Dije taji su uwar tace a,a wallah waka magana yanzun innan mu tayo cikinai tace za a damu yara.
Walle magana akai ke tai kice ta karo muna wanga ko ku baya isa balle mu duka yar naima da bakin rowan tsiya kamar nagode wanga abincina za a kawowa mutane shiya.
Ina daga cikin dakin zaune ina zancen zuci naji muryan sama sama ana sallama a gadarance na bude labule ba gaisuwa ko wani magana yarinyar ke fadi a wullakance .
Wai inno tace ki zubo muna mai yawa wanga daki bayar baya isan mu ko muna balle dasuwa na kasa fahintar mai take fada saida ta kara maimaita mun maganan ta na gane.
Cikin dan fara,a nace ayyah wallahi shi kadai na zuba babu wani sai naga tayi min wani kallo kafin ta juya tana magana kasa kasa cikin fisge fisge ta tafi.
Na juya ina shiga daki tare da dinbin mamaki bansan lokacin da hawaye ya zubo min ba a fuskana natakaici da bakin ciki don bawa kowa rainin wayau banso kuma ni ayimin hakan ko kadan.
Ga wa yan nan mutanen da alama suna da irin halin wullakanta mutane din nan irin na nakasa dayiwa mutum kallon rainin wayau da wullakanci.
Mii kawoki sashena ya tsare kanwar da tambaya tayi tsuru tsuru da idanu nan ta fara inda inda tana fadin innota tace in taho a karo muna abincin don baya isan mu .
Idan bai isa ba kuba zaku iya dafawa ba koba akwaishi a wurin kuba an kai maku naku nan dai ya tsare yarinyar da fada sosai yaci mata mutunci ta tafi .
Tana shiga part din su ta dangware kulan dake hannunta ta fara cicika uwar ke tambayan ta da mi ankai maki kuma kinka dawo kina wagga cika haka ?
Ni dai naji motsin shigowan shi dakin amma banga ya shigo ciki ba naji fitan shi kuma can ya samesu a part din baiga Dije ba a wajen ya shige dakin Dije din ya sameta zaune.
Yake fadin Dije mi da baku dafa abincin ku ba nan ba komai na aje maku ba ga kuma wanda aka kawo gidan su princess.
Wani abu akayi ko wanda ta sako muna kaka magana kaine yake fada mata an tura Asmau ta karbo wani yanzu wai wanan baya isan su.
Sallati Dije din ta saka tana kokarin mike tsaye ta tashine kanwar mahaifiyarshi ta shigo tana fadin kai dan Dije karanmu kakawo inda innan mu don mun aikawa matarka ta kara muna abinci wanga data sako muna bai isan mu ?
Inna Shatu dole in yi magana yarinya ga bata saba da rayuwa haka ba yanzu yanzu da kawota zaku daga mata hankali don gudun hakana hau yasa na kawo komai nan na aje maku.
A,a yanzu ai shike nan ni gobema tahiyata zanyi gida dama son tasan wadda akayine ta gyara yasa ankayi mata magana nikan gobema gidana nayi gumi zan komawata.
In ke tashi kitai anka nice kitai anka wane irin dabia na haka wai kuka son tsirowa mutane dashi yace dije saida nace kadama tayi da kuwa.
Tace a, a ko banza akwai hakkin makwantaka bata iya girki gaku gida bata saka maku shiya ba data bi maganata ta kyale da duk wanga ba ayita ba tsakanin mu.
Waishi hauda yakayi don abinci walle da yaranga basu cishi ba da an maisuwa masu da abincin su kaka zuwa nan ka kawo wa mutane diban albarka wai kai mai mata.
I aniya in baka koma mijin tace ba gidan nan jin fadan mahaifiyar nasa yasa ya mike ya tsaye ya fice daga dakin dije din kaitsaye ya shige su ya fice suka bishi da kallo.
Ayadda nake ya sameni yana sallama ban iya amsa mai ba yake fadin lafiya ko wani abin tazo tayi maki a nan din ?
Kai na iya girgiza masa don ba zan iya magana ba shiko yayi min tambaya kala kala

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login