Showing 183001 words to 186000 words out of 304363 words
sani nida da guda na taba haihuwa a duniya ai ba zansa hakan ba yanzu tunda da yan uba na samu ubanshi.
Yanzun dai ki nuna masa kinyi kuskure a fili inyaso daga baya in mun gama tunane mayi wanan maganan mu nemi mafita jin hakan ya dan kwantar mata da hankalinta ta mike zuwa part din mijin nata.
Bayan fitan ashi daga gidan da kamar da minti ashirin ta shiga ta samu baya ciki asalima an rufe kofan daga baya duban inda abinci yake aje tayi.
Yadda aka jera mai ko cibi bai taba ba daga ciki hakana ya barshi ya tafi hakan yasata dan runtse idonta kadan tayi tana jin wani irin daci a zuciyanta kamar kafafuwanta ba zasu dauki jikinta ba lokacin.
Ba komai takewa takaici ba sai irin kudin data bayar aka kashe don ketarawa cameron wurin karbo maganin datayi amfani dashi a girkin yanzu duk ya tashi a banza ke nan gareta don ko sau daya tunda ta fara amfani da maganin tana kula ko ruwan gidan ya daina sha yanzu balle abincinsu na gidan.
Ya isa lafiya sai karfe hudu da rabi ya samu kiran gida yaji lafiyansu inda layin zahra din ya kira a lokacin don wayan inna yana da wuya ta dauka idan an kira layin.
Daidai lokacin nayi wanka na saka dogon riga a jikina sai hula dana kafa a kaina na hada cornflake ina sha ina zaune ina tatara takarduna da nake bukata wanan zangon.
Naji wayata yana ringing daga gefena nakai hannuna dauka bakon lamban kasan wajene naji tsoro da farko kamar ba zan dauka ba na danna ina fadin Assalamu Alaikum.
Naji an amsa min da amsa na musulunci a lokacin hankali ya dan kwanta naji maishi na fadin ko yana magana da zahra mayanace zamfara state ?
Na amsa da eh nice naso sheda mai maganan a lokacin amma na kasa gane inda na sanshi namijine kuma nasan wanan muryan a baya gaskiya.
Kina magana da brother din ki BISI Abdulbasti dana nan US ko kin tuna da mai sunan ya fada cikin zolaya sai yai shiru.
Aiko bai rufe baki ba na dan sake ihu tare da fadin lah kaine kana ina haka duk dadewan nan bamu kara jin kaba kuma ?
Yace ba kun koreni Naija ba kedasu Mum nace kizo mu gudu muyi aure kinki bina lokacin da sauri na tareshi da fadin haba dai brother in ace ciki daya muka fito dakai nayi haka yaya zakaji ?
Yace to meye tunda kinbi masoyinkine bazanji komai ba saidai in maku fatan alheri a duk inda kuke nace yare hoo a zuciyana wani yaren duk da musuluncinsu sai sin hada da al,ada mai kama da kafirci.
Amma kasan addinin mu da yaren mu bai yarda da hakan ba garemu don me ni zan ba iyayyena da yan uwana kunya a garin mu saboda namiji ?
Yace hakan dana sani yasa nabarki ai badon naso ba don lokacin inada hanyoyin da zan iya saceki cikinsu din amma sai kwanan nan mummy ke fada min wai kunyi aure keda sisters dinki.
Ke kin auri wani tallaka bawa Allah kika zaba akaina sam baji dadin yadda take fada min yanayin da kike ciki ba tana jin dadin hakan.
Wanan abin ya bata min rai sosai wallahi don nasan yadda kike da step mother din ki Alajah komai zata iya akanki don hakane yanzu na kiraki naji wani taimako zan iyayiw rayuwan ki a yanzu.
Ke zan taimaka ko mijinki zan taimakawa ya samu abin rikeki yanzu ke nake saurare naji amsan da zaki bani da fatan kuma shi mijin naki yayi karatun gaba da secondary ?
Shiru nayi ina sauraren shi don na rasa amsan da zan bashi saida yace kina tare dani kuwa nace ina jinka duk a cikin harshen turanci muke magana dashi lokacin.
Yace wa kika zaba a cikkn ku nace idan zaka taimaka min ka taimaki mijina don ya fini bukata yanzu yace good nima tunanen da nayi ke nan da farko amma kuma sai nazo nayi tunanen kanku hausawa don mazan ku basu da rikon amana ko kadan .
Yana iya cewa zai rabu dake wata rana idan ya samu wata kinga ya kwaremu a nan ke nan don haka naga gara ke ki samu din don daman mutum daya nake dashi yanzu kuma na tambaya ance har yanzu karatu kikeyi ke.
No ka bashi banda matsala ga hakan idan ya samu kamar nice na samu ai don zai tallafa min yadda ya kama daidai gwargwado don ko yanzu yana kokarin shi dani ai.
Ok alama dai ya nuna kina matukar son mijin nan naki ba laifi zan turo maki da yadda zaku turo da takardunku saidai bana son wani ya taba sanin cewa nine na taimaka maku da wanan aikin understand nace nagode sai naji ya kashe wayanshi a lokacin bai kara fadin wani magana ba kuma.
Kallon wayan nayi na runtse idanuna gabana sai faduwa yakeyi sosai ina kuma tunanen wani irin aiki bisi din ya samu yanzu da har yake ikirarin taimakawa wani dashi.
Sai kuma na koma fadin ni yanzu ta yaya zan fitowa Master da wanan zancen me zan fada mashi alakata da Bisi idan zancen hakan ya taso a tsakanjn gashi kuma damace muka samu a hakan kada ya wuce mu duk da bansan ko wani irin aiki bane dai.
Amma zan gwada mai magana don haka na fara dan tsara yadda zan shirya mai zancen ko kadan banzan taba furta mashi zancen cewa Bisi din yaso aurena ba a cikin maganan.
Zan dai nuna mashi cewa dan abokin Abbane da muke mutunci dasu yaji labarin baya aiki yake son ya taimaka muna haka dai na zauna na tsara yadda zan fada mai koda yayi min tambaya mai zurfi kafin na dawo ga tunanen mommy Bisi data fada mai tana jin dadi.
Watau hakan ya nuna mama tana jin dadin halin danike ciki ke nan to ai ba wani zunubi na aikata ba da har Allah ya jarabeni da auren master din na tambayi kaina.
Ina cikin wanan tunanen ne kiran master din ya shigo a waya na dauka muka gaisa nayi mai ya hanya yace Alhamdullahi ya isa lafiya har sun fito daga lacturen ranan ai.
Ya tambayi lafiyan iyayyen shi nace kowa lafiya sai Dijece bayan tafiyan ka take fama da zazzabi yanzun ma nake shirin zuwa in gaida ita in tambaye abinda zataci in girka muna.
Da sauri naji ya tambaya badai sosai bane jikin ko nace da sauki gaskiya don har ta fito dazun da rana yanzun daine ban kara lekata ba yanzun nake shirin zuwa to idan kinje son Allah ki min flashing zanyi magana da ita.
Nace to naji ya kashe wayan lokaci guda ba tare da munkai ga yin maganan ba saidai kuma zancen ya tsaya min a raina sosai ina tunane har yanzu kan in fada ko kuma in kyalene.
Ya samu abokan nasa su uku dama wasu abokan arziki nasa duk sunzo tariyanshi a lokacin ba bata lokaci suka dauki hanyar mambila suna isa garin hjy yabi wace yarta ta bata shawara kan .
A yanzu kuka ko bacin rai ba nata bane ta sake jiki ta nuna mashi cewa tayi kuskure a baya ta nuna ba komai don haka ta daga waya ta kira layinshi.
Baiki dauka ba ya dauka take fadin kana ina ne haka ko abinci bakaci ba kafita ba bai tsaya jin komai ba shima ya bata amsa kalar makircinta da fadin ina mambila yanzu.
Baki sake take fadi a rude mambila Alh mambila ka tafi banda labari nan hankalinta ya kara tashi don gani take idan yaje mambila ba tare da itaba dayan kishiyar nata zata samu dama a gareta ke nan.
Asalima itace ke shirya masu tafiya duk lokcin da bukatan zuwa ya taso masu garin nasu sai gashi yau shida kanshi ya tafi ba tare daya sanar mata bama.
Nan hankalinta ya tashi maimakon lalashin data kirashi tayi mai kamar yadda yarta ta bata shawara sai gata tana kokarin fada mai bakar magana a lokacin.
Rabu da irin matan nan da suke mulki da gadara da isa idan abu ya kwace masu suna shitin zama powerles a wurin miji lokaci daya sukeyi kamar sun zare kan miji.
Hakane yazu yake shirin faruwa da ita don gaba daya sai take ganin kamar duniya ta kita a lokacin ita kadai ta manta irin mulkin da isan da take shimfidawa a baya gareshi.
Yanzu Allah ya fara kwato shi ya fara samun walwala daga daurin boyen datayi mai wanda dama baya tabba ga bawa idan ba rai ya kare ba gareshi.
Daga bangareshi kuwa amsa ya bata da fadin banda niyar saikin sanda zanzo yau don na fara gano me kike nufi dani yanzu ya kashe wayan ya barta a cikin mamakinshi lokacin.
Ranan kan zarewa tayi gaba daya sai fama kiraye kirayen waya takeyi hankali tashe duk wanda ta kira sai hannkuri suke bata kan tabishi sannu in ma asiri akai mai ba inda zaikai.
Wasu kuma don daukan alhaki sai su danganta abinda fadin mariyace kishiyarta tayi wani aiki a kansu yanzu da yaci don itama aiba zata zauna ta zuba maki ido ba dama.
Jin irin hakan ya kara tayar mata da hankali sosai lokaci guda duk ta fita hankalinta har zazzabi mai karfi ya rufeta nan yarta babban ta fara fada da ita tana fadin .
Akan daddy mummy kike son halaka kanki ki manta dashi mana yadda shima ya nuna kodake koba ke a yanzu zaiyi rayuwa .
Jin hakan yasa ta dago kai tana fadin kina da hankali kuwa daddy zakice mu kyale duk wani abinda muke takama dashi da karfin wa muke duk abinda mukeyi a garin nan yanzu.
Don suwa nake wanan haukan haka ba duk a kanku bane nake wanan wahalan kina ganin idan ya dauko wanan shege dan nashi ba zai mayar da hankalinshi bane a kansa ya kyale mu.
Ko kuma yayi kokarin yaga ya mayar dashi wani abu yanzu kamar ku duk komai ma zai iya faruwane akai wanan ne damuwana don ko banza kinsa yana yawan complain cewa yasir baya jin maganan shi.
Shiru yar nata tayi tana saurarenta tare da nazarin abinda uwar nata ke fadi kafin ta bude baki tace duk da haka mummy ki nuna masa rashin damuwan ki da hakan zaifi sauki.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[01/05 1:05 PM] Ummu Ammar: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
6️⃣3️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Na samu taji dama tana zaune ta idar da sallah nagaida ita tare da tambayanta karfin jikin nata tare da kokatin nemanshi a layin wayan shi.
Yana dauka na mika mata ta karba suka fara gaisawa dashi yake tambayanta karfin jiki naji tace dashi naji sauki ai dama bata fadama ba jikin nawa ai kullunne ni.
Banji me yace mata ba sai tace zan mata magana idan jikin ya matsa min tayi mai godiya tare da adduan neman tsari agareshi ta miko min wayan na karba.
Na mayar a kunnena yake fada min na fada mata idan jikin yakiya tayi maki magana kuje asibiti don Allah da ita ko ki kaita chemist abata magani nasan baki rasa kudi har in dawo ai ?
Zamu anjima idan na gama girki su bata maganin daya dace yace shine daidai don haka zatayi ta fadin taji sauki amma jikin na nan.
Sai kuma ya koma tambayan badai matsala komai ko bayan tafiyana nace ba komai wallahi saidai wani brother dina dake zaune USA yayi waya dazun yake fadin na hadoma shi civic din ka akwai wani aiki da zasu dauka na tsunci bakina yana fadin haka.
Yaya Musa ko ya Jafar ya tambaya da sauri nace a,a brother Bisi na lagos dake can zaune makwabtan mune inda muka zauna a lagos muka zama kamar yan uwa dasu lokacin har yanzu kuma ana zumunci dasu sosai.
Shine ya kira dazun yana fadin na turo takardun ka ko nawa saidai ni ban gama karatu ba a yanzu sai a fara turo naka idan suna complet sai naji yayi shiru na dan lokaci.
Itako Dije dake gefen mu sai faman fadin take madallah madallah Allah abin godiya Allah maji rokon bawansa Allah mungodema.
Kina dakin Dije har yanzu ke nan na amsa maida eh ok idan kin koma part din mu zamuyi magana sai ya kashe wayan nabi wayan da kallo don dama na zaci hakam tunda ban taba bashi labarin Bisi a cikin yan uwan mu ba.
Dijeko sai fadi takeyi madallah wanan dan uwa naki Allah ya saka mai da alheri abinda yake nema na alheri Allah ya bashi na amsa da amin tare da fadin tuwo zan maki kici ko Dije ?
Tace to tuwon naso tunda rana amma wa yanan makiyautan sunki girka min sai hanjin bature da suka sulala wai shine abincin gayanan na kasaci tundazun ma.
Na kalli roban da suka zubo mata taliyan a ciki har ya fara bushewa gashi hankade da dan jajage kadan a sama nace zakisha shayi mai zafi yanzu in fara hada maki ?
Tace idan na samu zansha tun kunun safene a cikina sai naji ta bani tausayi sosai naga harda sakacina a cikin barinta da yunwa tunda ina gidan nima ai da sauri na mike na hado mata shayi mai zafi da kauri da guntun bread din da mukai amfani dashi da safe.
Na kawo mata nadan zauna na fifita mata saiga Asmau ta leko tana gani take fadin a a a yar tsohuwa dama ciwon kwadai kikeyi ashe shayi kika samu haka da kauri Dije.
Shayi na samu wurin yar arzikin data san ciwona ba irin ku masu nema su kwace min ba sukayi ta musayan baki ina masu dariya.
Ta tafi na bata tasha saiga zufa ya karyo mata a raina nace kila harda yunwa ke damun tsohuwarma lokacin nan na mike na fito ina mata sannu ina saka takalmana a kofa naji muryan inna na fadin.
Mu ina zamu samu muna yar dangote a gida duk wani nema nasa yanzu ai can yake karewa wurinta yaushe zai tsaya bamu wani kayan shayi can yanzun ma kafin ya tafi da yaya ya hada muna abincin da zamuci ?
Raina ya baci ranan na bayar da amsa nace ba diyar dangote nake ba amma yar babana nake shayi kuma ba a gidan nan na koyi shanshi ba da abina ya ganeni bama na wahala irin wanan ba.
Don ko yaushe kaje gida mu zaka samu kayan shayi zube saman dining table don babu mai kula dashi ban karban kudin daki ko na hanashi ya sai maku abu amma inna kin dauka nice ke hanashi baki abinda kikeso gareshi.
An fada ko bakiso na fada auren kine yake kokarin juya min baya a yanzu bani gane kan dana amma ke gidan ku ai yana kai masu don a yabeshi.
Kadin nayi magana naji muryan Dije na fadin ke kan Rashida kinji kunya tun yar nan bata baki amsa har yau an wayi gari ta gaji da halinki takai ga baki amsa daidai dake.
Dama ke zaton ki shi dan naki yana iya daukan duk lalurantane kome ki rabu da So sone kawai ke aikinsa nan amma ko kallon yar nan kikayi kinsa ba kalan danki bane ita.
Sai kuma ta juyo gareni tana fadin yi tafiyan ki ki kyalesu da ita mara tausayin wace taje ta fada masu din dan kin tausaya min kin hado min ruwan zafi nasha naji karfin jikina Allah ne maganin su.
Marasa godiyan Allah kawai in kina da kunya ke har kyayi wanan maganan don ta taimaki uwarki ina zaki san ta taimakeni kina daki da diyan ki tun safe kuma shewa zan mutu ku kwashi ganima.
Nikan ganin abin zai rikice masu naja kafana na koma part dina cike da bacin rai na barsu ina jin hayaniyarsu daga part dina ina mamakin hali na inna da zata tsaya tana sa,insa da mahaifiyarta haka.
Yanzu nagane da danta be kula al,amarinta ashe yasan halin abinshi har ina ganin laifin farkon shigowana gidan sai yanzu na fahinci inna irin mutanen nan ne da basu danne zuciyarsu subar abu a cikin su komai kankantanshi.
Hakan yasa na manta da wayana dake kuryan daki ashe yayi ta kirana ban sani ba saidana gama aiki na dauko waya naga six misscall din shi a wayan.
Ban kirashi ba don raina yana bace sai gashi ya kira banyi saurin daukan wayan ba saida ya kusa katsewa na daga murya ciki ciki nake amsa mashi.
Naji yana tambayana kina inane waya nata rinngin baki daga ba ina kitchen na bashi amsa a dakile yace banace inkin dawo part din mu zamuyi magana ba na sake fadin aigani yanzu.
Jin hakan yasashi fadin wai meke damunkine