Showing 207001 words to 210000 words out of 304363 words

Chapter 70 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33338

wani laifin nayi ba har kike nemana a yanzu duk da kauyancin shi ya isheta a lokacin amma haka ta daure tabiyewa wautanshi din take fadin a a ha wallahi nice dai ma nayi maku laifi ai kasan halinmu na mata da rashin tunane .
Na taba abokin kune yake fushi dani nace barin nemoku ku tayani bashi hakkuri don Allah don nasan yana jin shawaran ku idan kun bashi hakkuri din in yasa daga baya zamu magana daku musan abinyi a karshe zakuji sakona insha Allahu.
Jam jam meyasa ku masu kudi kuke tunanen cewa saboda kudi duk wani tallaka zai maku komai sai ku manta da zumunci da alaka irin ta addine akan zama tare.
Duk da ke matar tsohon abokinane kuma dan uwa a gareni, haka kuma aminina acan baya, duk da nasan irin abubuwan da kikeyi na ganin kin raba tsakanin shi da mu a tinanen ki shiya wuce ajin mu kamar yadda kika sha fada mana a baya din.
Tun bamu gane mai magananki ke nufi ba har mukazo muka gane gaskiyan zancen ki garemu muka kuma tsaya a matsayin da Allah ubangiji ya ajemu don musan dangaske ba finmu yayi ba a wurin Allah shi kadai yasan wanda yafi a wurinsa.
Kuyi hakkuri don Allah kuskurene amma ba wai haka nake nufi bani son Allah kuyi hakkuri da abinda ya faru ta kara fada a karshe.
Bakomai don daga mijin ki har ke bamu taba daukan ku da wani manufa ba a yazuciyar mu har yanzu a matsayin yan uwan juna muke kallon ku a idanun mu.
Nagode dama nasani shiyasa yanzun ma na kiraka don nasan ku kadai zaku iya shawo kan Allah ya janye maganan da yayi a kaina don Allah.
Ikon Allah harmu dinnan mun isa mu shiga tsakanin ku da Alh saidai mu dan gyara idan muga da bukatan hakan a tsakanin ku.
Zuwa lokacin yakai mata iya rai tana jin haushin sa yadda yake jan maganan tana tsawo kamar ace yana kusa ta makeshi dai da wanan iya yin na samun waje da yake mata din.
Nan dai ta daure ta koro mashi komai daya faru tsakanin su akarshe ta nemi da ya roka mata shi kada ta fice daga gidan kamar yadda ya bukata da tayi bayan bata mashi rai da tayi kan girkin dare data lalata.
Ya nuna mata laifinta tare da mata alkawarin kiran abokin nasa akan zai masa magana tayi mai godiya ta kashe wayan tana tunanen lalai abu ya baci gareta wai yau itace don lalacewa har take neman taimako a wajen wa yan nan mutane.
Shiyasa manya ke fadin wayasan gobe banda Allah ko a cikin yan kwanaki tana ganin kantane a matsayin macen da tafi kowa iya kama miji ta kammalashi da asiri sai abinda tace zuwa gareshi zaiyi.
Saukan safe sukayiwa kasan amma duk da hakan a nan suka samu wanda sukazo taronsu tun a jirgi yaso ya gane cewa bashi kadai bane a wanan tafiyan sai dai ya saka ido yai shiru yana kallon ikon Allah.
Ga wanda yazo taron su din a nan ya gane don sunayen su dake jere a wuri daya lokacin har su biyar maza hudu mace daya.
Bayan gama binciken su suka nufo wajen fita a nan suka samu mutum biyu suna jiransu sukai masu jagora zuwa wajen motocinsu na suka shiga aka kara gaisawa.
Sai kallon kallon sukewa junan su don ganin nisan tafiyan da sukayi a tare bada sanin cewa wuri daya zasu je ba sai a wanan gaban suka san cewa ai duk tafiya nasu dayane a lokacin.
Wani babban gina suka nufa bayan sunsha dan tafiya zuwa cikin garin suna baza ido wurin kallon abubuwan mamaki da suke gani.
Shiru Ahmed yayi yana fama tunane tare da ganin wautanshi na yarda yayi wanan tafiyan gashi bai fadawa kowa abinda zai tafi yi ba a lokacin haka kuma ya dauko hanya yabar garin har kasan zuwa amsa kiran wanda bai taba sanin shiba da sunan taimako.
Ganin tafiyan nasu wuri dayane yasa suka fara sake jiki da junan su inka debe Ahmed wanda yafi kowa takura a cikin su don gani yakeyi shi tasa ta kare ke nan daga nan.
Komai na wajen kusan da fari da blue akayishi blue mai hasken sararin samaniya sai wani tambari dake jikin ko wani gina na unguwar .
Da alaman ansan da zuwan su don suna zuwa wani bature ya taso yana gaishesu tare da fadin Najeriya suka amsa mashi da eh yace su biyoshi nan ya jasu zuwa dakunan da zasu sauka din dakina da a gida sai sarki ko wani hamshaki kawai zai kwana a cikinsa .
Sai gashi nan an ba kowansu nan ne masaukinsu na tsawon kwanakin da zasuyi a kasan har tafiyansu shikan wanka yayi ya dauro alwala tareda fargaban ta ina zai duba a wajen sallah a kasan.
Allah da ikonsa sai ga taswiran nuna yanayi ya hango makale a dakin ba bata lokaci ya tada niya yayi sallalolin dake kanshi da baiyi ba.
Yana gamawa duk da yunwar da yake ji a lokacin hakan bai hana wani barci mai mauyi ya daukweshi ba sai karfe hudu da wani abu na yamma ya falka daga barcin nasa.
A dan razane ya falka daga barcin yake bin dakin da kallo kafin tunanen shi ya tuno mai inda yake a lokacin hakan yasashi saukowa saman gadon da sauri yana dan dube dube lokaci guda.
Wurin window din dakin ya nufa ya dan daga labulen yana kallon wajen wurin zuciyarshi cike da mamakin komai na wurin don zakace ba hannu bane yayi aikinsu haka komai sai ya burgeka idan ka kalleshi.
Kofan yaji yana kara hakan ya dawo da hankalinshi zuwa inda yake jin kukan na fitowa koface alaman akwai wani a kofan dakin a lokacin karan bani yayi yai amfani da abinda ya gani a rubuce jikin kofan ya bude kofan lokacin.
Wani mutum ne tsaye a kofan dan gajere ya dan fara manyanta yana tsaye dauke da kayan abinci yace Mr Yusuf ya amsa masa da kai yace abincin rana na kawo ma tun safe muna zuwa muna samun kana barci.
Bayan tafiyan mutumin ya bude abincin ya irin abincinsune nacan don haka ya dan taba kadan don babu dadi a bakinshi irin yadda ya saba cin namu.
Bayan gama cin abincin ya dan fito ya zaga saidai bai yarda yayi nisa sosai ba don kada ya bace ya kasa gane dakin nasa.
Hutun kwana biyu sukayi kafin a sanar masu da taron da zasuyi washegarin ranan don haka kowa ya kwana dashiri sunawa Ahmed din kallon bakauye wanda baisan komai ba.
Sai gashi ya barsu da mamaki kan tambayoyin daya amsa masu a wurin interview din ya bar kowa da mamakin hakan don yadda ya amsa masu tambayoyin nasu basu zaci hakan ba daga yan kasan nan.
Lafiya dai wanan kiran haka cikin wanan daren don ban taba zaton hakan daga gareka ba Jabbo .
Murmushi yaji yayi tare da fadin kiran ya kamane na kiraka a yanzun din idan ka duba da cewa ban taba ma kira a cikin dare ba haka ai.
Murmushi ya sauke kafin yace nasan dai duk kuna kusa da wayan ke nan tunda naga ka kirani a yanzu din kwarai kuwa kusan kowa na wurin nan in an debe kaida baka kusa damu.
Sai ya kwashe da wani irin dariya wanda ya dade baiyi irinsa ba don fadin hakan ya tuna mashi da wasu abubuwan kurciya da suka faru dasu a baya suna yara.
Ba wanan ba yanzun dai mun kirakane mu baka hakkuri da shawara ba tare dayin binciken komai kayi hakkuri da mai dakinka don Allah.
Au har can kuma takai karana lalai yabi tana da alaman tabin hankali tunda har ta iya rufe ido wai tana neman taimakon ku a yanzu ?
Yaushe idan ita mai hankaline har zata iya tunkaranku kan zancenta dani matan da da karfibda yaji ta rabani da kowa na kusa dani da aka sanni dasu tun farko.
Ba abinda yake ci mun rai a yanzu kamar zancen ysron nan dana baro zamfara a baya koda an gashi yanzu da wani ido zan kalli yaron nan shida iyayyensa har in yana raye.
Abinda ya wuce abar tunashi sai hakkuri da istigifari don neman yardan ubangiji ga bawa amma duk ake tuna irin wanan abin ba zai taba wucewa a zuciyar mutum ba ai.
Amma kasan ko komai ya wuce zancen yaron nan ba zai taba barin zuciyana ba don bansan da wani ido zanwa Allah bayani ba a kanshi.
Jabbo kasan ba karamin cutana yabi da yan uwanta sukayi ba yanzu gashi duk wanda na tura sai ya dawo yace min wai ba a gane komai ba game da yaron da iyayyensa ba.
Don haka yadda ta rabani da kowa nima a yanzun banson ganinta gidanan ta fice min daga gida ko zan samu sallama a rayuwata.
Zaka samu insha Allah kaidai ka kwantar da hankalinka yanzu idan ja yake hukunci a cikin fushi ai baka kaiga cinwa manufarka akanta ba ke nan idan Allah yayi yaron ka ya baiyana kaga bataji komai ba game da dawowan nasa.
Ga hjy murja data dawo yanzu shima ba wani zama sukayi tare da da zaisa ta fara nadaman abinda takewa mutane a baya ba don haka kayi hakkuri ta zauna dakinta don Allah.
Zata zauna amma wanan karon ina son ta fara dandana irin abinda naji a kanta itama don haka kona sati dayane sai ta bar gidan nan taji itama in hakan yana da dadi.
Zata bar gidan na kwana biyu kawai tunda kace hakan amma na sati daya gaakiya yayi yawa to shike nan ta bar min gidan nawa shine kawai saukin zuciyana a yanzu game da ita.
Dole hakan akayi saidai bata dawo gida ba nan ta zauna a Abujan a cikin wani gida nata data saye boye yana jin hakan yace ai idan ba gida garinsu ta koma ba akaje can akai magana ba zata taba dawo masa gida ba.
Gashi wanan tafiyan ya bashi daman tone wasu abubuwa data binne a gidan dama aikin da kowa baisan lokacin da tayi shi sai hakan ya kara sashi cikin sallama yake jin tankar ace hjy yabi din ta tafi ke nan daga rayuwan shi har Abada.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
7️⃣2️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,


Kwance yake ya lafe zakace barci yake a lokacin saidai a zahiri ba barci yakeyi ba tunane fam a zuciyar shi da suke hanashi sukuni a wanan lokacin tun bayan da hankalinshi ya dawo gareshi.
Irin wanan yanayin yake damun shi har yakanyi kokarin fita hayacinshi wani lokacin a cikin hakane yana kwancen wayan shi ya dauki kara lokacin guda.
Hakan yasa ya motsa har zaka gane ba barci yakeyi ba a lokacin damuwane kawai yai masa yawa na tunanen dansa da yake ganin ya mutu a lokacin kamar baya raye.
Wanan ya jawo mashi damuwa har yanayinsa ya nuna kamar yana cikin rashin lafiyane yanayinsa ya nuna ya mika hannu ya dauki wayan yana duban mekiran nasa alokacin.
Daya daga cikin yan uwansa kuma abokin nasane daga gida yake kiranshi a lokaci ya dauka suna gaisawa tare da tambayan iyalin juna a tsakanin su.
A karshe yake tambayanshi ko lafiya yaji muryanshi haka yake fada masa damuwan shi shiru yayi yana sauraron bayanin da yake masa a lokacin.
Bayan sun gama wayan da shi jabbi dinne yaga rashin kyautawansu na rashin sanar dashi gaskiya akan dan nasa da yanzu ya kwallafa rai a tunanensa fiye da komai lokaci guda.
Hakan ya kara tabbatar masu cewa asirine tun farko akanshi kan dan nasa yanzu kuma da taimakon ubangiji kamar komai ya karye a kansa din a yanzu.
Shiryawa yayi ya fice daga gidanshi sai gidan jabbo ida ya sameshi da maganan tare da shawara akan lokaci yayi da zasu sanar mai da gaskiyan al,amarin kada Allah ya kamasu da laifin hakan a kansu.
Shima Jabbo din yace dashi nasa tunanen ke nan don ya fahinci cewa aminin nasu yana cikin wani hali a lokacin a nan dai suka yanke shawara kanshi cewa zasu sameshi a abuja akan zance biyu na ya mayar da hjy matarshi dakin ta da kuma zancen baiyanan dan nasa garesu.
Sun aje magana kwana biyu mai zuwa zasu sameshi can abujan ba tare da sanar masa ba daga can sai asan abinyi zuwa wurin iyayyen yaron tare dasu.
Yau asabarce bana fita ko ina a ranan nakan zauna inyi dan gyare gyraren gida nayi wankin yan tufafin dana saka a cikin satin in goge duk wanan aikin aurena a gidan Ahmed na koyesu a yanzu.
Don da can baya wanan aikin saidai duk masu aiki suyi min iyakata na dauka in saka idan an wanke an kawo min su dakin wanda tanice take karbo min ta jera min su a wardrobe dina.
Sai gashi yanzu nice da kaina nake wanan aikin wanda yakin mata ya saka min hakan nayi wanki na dafa abinci naci kuma irin hakan sai duk abubuwa su taru suyi min yawa a lokaci daya wanda duk sanadin aure na riski kaina a cikin hakan yanzu.
Saidai duk da hakan ban faye damuwa da wanan yanayin da nake cikinsa ba a yanzun din don na fawalawa Allah komai game da rayuwan nawa a yanzu din.
Saidai banda kuzari wanda ban fahinci hakan rauni bane a gareni saida inna ta fara korafin hakan a gareni idan ina girki zatace ba zasu girka ba tunda na dora da rana tafi yin min hakan idan ina gida ban fita ba.
Saidai kafin na gama korafine hakan ne yakan biyo baya zata fara yada magana ta yadda zanji tana fadin mace kamar ba jini a gareta aiki sai kace tsohuwa na aiki ?
Kamar wace ba lakka a jikinta ai tsiyan abin ke nan a nunawa yaro gatan da baida rana a gareshi yanzu gashi me gari ya waya a hakan ace diya mace ba zata iya aikin da karamar yarinya zatayi shi ba cikin sauri.
Tun ban damuwa da hakan har yakai na fara damu ina nuna bacin rai har wani lokacin nakan kare aikin ina kuka na bakin cikin irin yadda inna ke nuna min kiyayya a fili.
Dondai shida ya ajeni bai taba nuna min hakan ba illa ma ya taimaka min da wani aikin irinsu wanki da sharan gida amma ita inna ga yaranta bata ganin laifinsu saidai laifina zata gani a lokacin .
Na samu nagama da kyar nakai masu tunkan na dawo part dina naji inna nafadin ai mukan mun shigesu da cin yaji kan agidan nan sai kaga mace har mace fes a waje amma ka bincika bata iya aikin daya dace ba wai a haka ake auren ?
Itako Asmau cewa tayi ai inna yajin yayi daidai gishiri daine ba a sakaba a cikin girkin tana fada tana kai cibi abinki da zafin shi yadda na kawo masu shi lokacin.
Wani bakin ciki da takaicine ya rufe min idona lokaci guda na juya na wuce ina hawaye sai yau nake tabbbatar da zancen ummah a gareni idan tanayi min fada lokacin da nake gida takan ce dani.
Gara ki koya tun a gida dan zaki je gidan wasu kiyi kigama kuma ba a gode maki ba karshe ma kiji wullakanci ga hakan don wasu dangin miji bala,ine.
Nakan ji haushin wanan kalamin na ummah lokacin sai inga ina ruwana da dangin mijina tunda basu zasu aureni ba a haka har na koyi dan abinda na iya a gida.
Ko kallon abincin banyi ba duk da yunwan da nake ji haka na fada saman kujera ina hawaye ni kadai a daki ba mai bani hakkuri kan wullakancin inna da diyanta da nake gani a lokacin.
Firgigit na dago daka yadda nake kwance don jin kukan akuyan nan da yanzu nayi noticing din kukanta idan tayi wani sign ne a garemu da cewa wani abu mai muhinmanci zai faru a gidan ke nan.
Bansan koni kadaine nayi noticing din hakan ba amma tun bayan faruwan mafalkina da ita da har na kwanta ciwo din nan na fara gane hakan akanta damuma dake gidan.
A hankali na dinga jin dan magana daga cikin gida yana tashi sai tarin da nake ji na muryan inna din a lokacin banyi niyar fita ba dole din jin hayaniyan yayi yawa na fito zuwa sashen nasu.
Innace wai ta kwarai da abincin tana ta faman tari har tana kwalla daya dan lafa taje yin magana sai tari ya biyo baya nima na shiga cikin masu mata sannu a lokacin.
Ta wahala sosai a ranan dole tana ganin abincin ta barshi nan data samu ya lafa mata takai kwance sai barci nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login