Showing 93001 words to 96000 words out of 304363 words

Chapter 32 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33355

To bari kaji garin nan kaf ba wanda naji ya taba zuwa garin da yace ya fito saidai naji sunan garin a gidan redio jefi jefi.
Amma dai ai cikin kasan nan yake ko koma ba kasan nan bane ya zama dole yanzu inje neman mahaifina duk da yayi banza dani nan cikin duniya amma nasan dole ina ranshi idan yana raye.
Wa hwada maka ga garin da yake da zama taka maimai ko nan daya taho ai a karkashin Alh Abu dan canji ya zauna shina ma yayi auwalin aurene har muka yarda muka bashi ita.
Daga baya da tahiya tayi nisa yake fada muna shima bai san garin su ba ya dai yaba da hankali nena ya tsaya mashi akai auren.
Gara ma tun wuri ka fitar da zancen shi a ranka don kila ma baya raye yanzu ni haka nafi sawa raina don gaskiya inda Auwalu na raye nasan daya taho nan ko don kai.
Dije ko bai raye zanje yan uwanshi su san dani a a nika zama nan ana tsangwamata kan laifin da ban aikata ba gara naje nasan asalina da anka fara fadin bani dashiya.
Aiki ko ja a gabanka zuwa wanan garin har uwar duniya don baka san iya kwanakin da zakayi a hanya kafin ka kai garin.
Zuwa lokacin yagama hasala da kakar tasa don da ace Dijen tasan yadda zuciyar shi ke tafarfasa a lokacin da bata yi wanan zancen dashi ba a lokacin.
Damace gareshi a yanzu don haka bai cewa Dije din komai sai shirin tafiya daya fara bayan ya tambayu kan yadda zai kai kanshi garin mahaifin shi na asali.
Tare da samun karin bayanin yadda zai iya gano mahaifin nasa idan ya isa wurin wasu abokan hurdan mahaifin nasa a nan gusau da yai zaman mutunci dasu a garin.
Sallah asuba nayi na zauna ina tulawa a wurin kafin gari ya kara haskawa na fara jin motsi a gidan na mutanen gidan dake kara kaina a tsakar gidan ina jin motsin duk abinda sukeyi saidai ban fito bane waje lokacin.
Bayan na shafa na mike na shiga bandaki wanka nayi don nayi saboda hakan don zuwa school dana saba fita da safe dana gama azzakar saina mike na shiga wanka.
Na fito na shirya cikin dinkin atampa da akai min buje da riga na fito yar shar dani na mike na fito zuwa falon gidan namu.
Babu kowa a falon saidai abinci da yan aiki suka jera a saman dining wata kafira da dan bujene a jikinta ta fito daga kitchen dauke da wani katon dood warmer a hannun ta tanufi dining din ta aje ta juyo sai lokacin ta ganni a zaune.
Ina kwana mah ta fada tana dan rage tsawonta kadan don ban girma a gareni na amsa ina kare mata kallo tare da kyaman yadda na ganta nasan ba musulma bace.
Don mu a lokacin zaman mu gidan ummah bata taba yarda ta dauki yar aiki kafira ta jefa cikin mu saidai musulma yar uwan mu da zata bamu tarbiya a tarevta dauketa tankar yarta na cikinta.
Idan zasu tafi kuma a rabu a cikin mutunci da dadin rai ana kewan juna kamar kada su tafi amma gashi yau arniyace a gidan take dan yawo da buje kuma cikin kazanta haka irin nasu ko don ina kyaman hakane a raina bansani ba ?
Hjy nakawo maki abincin ki a nan ne ta tambayene cikin girmamawa nace no ki barshi idan na tashi ci zan nemeki tace yes mah ta nufi kitchen inda suke aiki.
Daga kai nayi na kalli dakin ummah wanda a yanzu mallakin mommy ce wai sai naji zuwa Abujan nan ya zame min dana sani don abin bakin cikin da nake gani a gidan ga zuwana.
Karan budan kofa naji yasa na dago kai mommyce tafito daga dakinta tana kokarin nufar dakin Abba dake rufe sai kuma ta juyo ta dawo zuwa dining da nufin duba abinda aka girka na breakfast.
Kullan farko ta bude ta rufe ta fara kwalawa kiran sunan wata da Tabitha daga can kitchen mai sunan ta amsa sai gata da sauri hjy ta fara fadin banace idan kun gama ku fada min kafin ku kawo kitchen wai meyasa ku bakwa jin magana ne ko koyaushe sai na dinga nanata maku hakan ne ?
Dauki kikai min daki idan na gama zan kiraki fito dashi sorry ma Janet naba ta kawo ashe nan ta aje ai ban manta da dokanki ba.
Common dauki ki tafi kin tsaya kina surutu tana fadi ta juya ta shige daki matashiyar matan tabi bayan ta duk wanan abin bata kula da cewa ina falon zaune ba ta shige dakin.
Gabana ne ya fadi me za a jeyi da Abincin kuma a dakin mommy tsam na mike daga inda nake zaune din na nufi dakina dana fito gado na haye na kwanta ina faman tunane.
Barcine ya soma daukana a hakan naji an turo kofa na bude idona mommyce tashigo a cikin shirin ta na fita aiki ganina na shirya tsam kamar mai shirin fita ta saki murmushi a fuskanta tana fadin.
A, a my daughter wanan kwalliyan haka rangas ko wani wurin zaki tafi dagowa nayi da dan murmushi a fuskana na zauna ina kokarin sauka daga gadon tare da fadin ina kwana mommy ?
Lafiya kalau ya gajiyan hanya koda yake da alama kin sauke gajiyan ma ai tunda naga harkin shirya haka fita zakiyine ta sake tambayana.
A, a mommy ba inda zani kawai dai haka na saba dashi damani na fada na koma saman gado na zauna tace to ai hakan yai min dadi sosai don dama ga abinci can an gama sai ki fito muci kafin Alh ya fita dama baku wani gaisa sosai ba jiya ya shige part dinshi.
Mommy bana karyawa da safe haka sai dai in an jima zan fito nace wajajen karfe goma kice min yar tawa baturiyace kema kina irin tsarinsu ke nan dai ?
A a mommy haka dai na saba daman ni to ki fito ku gaisa da Abbanki yana falo zaune zan fada masu kadasu kwashe kayan abincin sai idan kin karya din yanzu taso muje kafin ya fita.
Zaune Abba yake yana waya tana fitowa yake fadin kinsan fa sauri nakeyi kin kuma je kin zauna abinki can sai gani na fito bayanta hakan yasa yai shiru a lokacin.
Har kasa nakai ina fadin Abba ina kwana lafiya ya amsa min dashi yace ya gida ya kika barsu a can , ?
Kowa lafiya suna gaida ku amma ban samu zuwa gidan hjy na sallameta ba don nasan zai tambayeni hakan.
Ba laifi ya fada yaci gaba da cin abincin shi da mommy din ta zuba mai wanan din kuma datasa akai mata daki dazun.
Ta juyo tana fadin daughter idan kinzo karyawa wanan ferfesune a cikin cooler zakiji dadim shi sosai ga Abban kinan ma zai sha kefa Abba ya fada naji tace ai kasan ban faye cin kifi haka da safe ba.
Kofa aka bude wasu mata biyune suka fito a cikin shirinsu duk muka dago muna kallo su .


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
3️⃣0️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Matane sunsha kwaliyan su sosai zasu fita saidai ganin masu gidan yasa suka nufo dining din suna gaidasu da kwana a take naga Abba bayan ya amsa ya dukarda kanshi taci gaba da cin abincin shi.
Sai addua nakeyi a raina a wurin don na sheda dayan wace jiya na fara ganine dana iso kafin mommy ta dawo ganin cewa ba zanyi masu magana ba don ko daga kai na kalli inda suke banyi ba alokacin.
Zahra meet my sisters lawisa and Aina suma suna zama damune a nan gidan though suna service ne a yanzu su suna gaba dake ke nan ga komai.
Ina kwanan ku na fada na kawar da kaina ban daiji amsan su ba nadai ji suna sallaman yar uwan tasu da fadin mun fita sai mun dawo ke nan tace yauma ba zaku karya ba ke nan?
Mun makara zamu karya a can daya ta fada nidai ba zance naji sun gaisa da Abba ba ko sun sallameshi har suka fice daga gidan.
Mikewa nayi ina sake kujera daga inda nake zaune OK zaki koma kifito anjima fa kici abinci ta kara nanata min nace to mommy na juya ina fadin Abba adawo lafiya ya amsa min kamar ba Abban mu dana sani ba a baya.
Don gaba daya sai naga dabi,un shi ya canza min ga baki daya wanda hakan ya daure min kaina na kasa fahintar komai sai na nasa ko har yanzu yana fushi danine kan zance na da Amadi ?
Ko kuma wani sabon sauyine kuma yazowa Abba din a yanzu ya daina yawan damuwa damu yadda ya saba nuna kulawanshi garemu a baya.
Na fara kula da hakane tun zuwansu sallah inda baida lokacin kowa koda yaushe suna tare da hjy karima a falon shi ko sun fita zuwa unguwa ko a part dinta sunfi yin hakan a ranan girkin mama yafi sintiri part din hjy karima din.
Sai gashi naga haka a nan kuma danazo dan kana daya kawai danayi a gidan na fara fahintar hakan ga Abba din nakai wani lokaci kafin na danyi barci sai shadaya daidai na falka don lokacin karyawana da yayi har ya wuce a lokacin.
Namike daga saman gadon na nufi bandaki na kewaya na fito falon gidan na nufo da har lokacin kayan abincin na nan yadda suka fita suka barshi a wurin.
Nasan mommy tabada umurni kansu aje min shi kada su taba haka kawai sai naji habkali bai kwanta danaci ba kitchen na nufa wurin masu aikin dake dan shakatawan su a lokacin.
Ga wakan coci yana tashi a wayansu dayan ma tana kwance ta daga kafa ido rufe tana bin wakan da suke saurare din sai dayan dake tsayene tana fere doya taga shigowana.
Sannu da fitowa tace min nace sannu kema nace ko zan iya samun ruwan zafi please na tambayeta da sauri dayan wace naji hjy ta kira da Tabitha ta mike zaune tana fadin.
Anty kin tashi mene kikeso ayi maki a lokacin na dan kakaro murmushin dole a fuskana nace ina son ruwan zafine sai naga tana kokarin mikewa zaune da niyar tashi ta dora min ruwan.
Nace no barshi barin dora kawai don nasan komai saboda wasu kayan kitchen din ma wanda mukai amfani dasune a baya har yanzu basuyi komai ba don ni dai banga wani abu sabo sosai ba a gidan da hjyn tazo dashi ba.
Duk kayan da ummah ta barine da zamu koma zamfara Abba yace ta barsu nan koda zuwa ya kamata ya saka masu komai a can ma shine ummah ta barsu nan din don mun tafine da sunan zamu dinga zuwa hutu wurin Abba din lokaci lokaci.
Zamu komane ne kawai gida mu saba da yan uwa da al,adun gida irin namu na can tundai wanan hearter dana daga ban mantawa fita mukayi da ummah da kawarta ta sayoshi a sahadda store lokacin sun bude tsore din sabo sabon budewa mukaje.
Ban mantawa don ina da wayona a lokacin batayi amfani dashi ba sai daya dade aje sai haihuwan jamila ta fito dashi gashi ba a dadeba muka bar Abuja din zuwa zamfara.
Wani bakin cikine ya kama min zuciyana nake fadin don me Abba yakewa ummah hakane wai duka maza dama haka suke su dinga banzatar da matayesu akan wata kodai Abban namune kawai halinshi haka wai.
Iya sanina a nan Abuja matan da ummah ke ma,amula dasu makwabtan mu su kadaine ga mazajen su suna kuma zaman lafiya dasu hakama yayayen su suna jin dadin su.
Amma mu ke nan yau ace wancan gobe ace wancan ke nan mu bamu da wanan gatan to don me na nasa don umma bata da iyayye masu karfine ko ?
Na dawo nace aiko mama ba wani karfi a gidan su da taimakonta suke kuri kaf din su kuwa kodai don tana uwargidane kuma to ai ba wani ragaman uwargidancin da take samu a gidan namu.
Tunda komai mama ke gudanarwa tun komawan mu gida din na gani tomeye hakan dama haka maza masu kudi sukene wai kome ?
In hakane kuwa gara mutum ya auri wanda baida komai su zauna lafiya da miji yafi anty nace kawo na dora maki ruwan Tabitha ta fada na dawo daga dogon tunanen da nakeyi nace .
No barshi kawai in dora nagode tace da kin kawo aikin mu ke nan ai yanzu mu nace ba komai ki huta abin ki na fara daureye jugdin saida na wankeshi tas don kyaman da nakeji.
Sannan na tara ruwa ya cika na aje ya dan sha iska ina tsaye ina kara bin kitchen din da kallo naji muryan Tabitha na fadin anty nace abinci yana falo hjy yace kitchen in kin tashi .
No bana cin abinci da safe na fada ku dauka kuci kawai ku wanke kayan na fada sai naga sun kalli juna sunyi yarensu kafin Jenet ta juya zuwa falo ta dauko kayan ta shigo dasu ta koma ta kwaso saura.
Wanan miyan naga sun bude sun kalla nayi kamar bansan me sukeyi ba sai naji sunyi yare a tsakanin su can naga sun fara tsame abin cikin miyan kifine manyan yanka zai kai biyar.
Sun tsame daga cikin ruwan miyan suka aje a cikin plate sai nagata juye ruwan miya ya wuce a sink ta tara kifin ta daure sai lokacin ta dago taga ina kallonta tace.
Miyar ne idan mun barshi ciki zai iya bata kifin shiyasa muka zubar dashi ai murmushin yake na sake a gefen fuskana lokaci guda na juya ina kallon abinda nakeyi suko sunata yare a tsakanin su.
Hjy don Allah kada ki fada ma Ajiya cewa mun zubar da miya zata iya koran mu gidan nan yau din nan basai gobe ba don Allah kada ki she ba kaine kaci ba fada zatayi muna sosai idan tasan hakan.
Murmushi nayi kadan nace kada ku damu ba maiji idan ta tambaya ku fada mata naci sosai kadan na rage kukaci ok anty mun gode dayan na aika ta hado min kayan tea na aje a dakina harsu complaints da goldenmore sugar da sauran ajewa daki don bukata sai gata tadawo min da canji nace suje su rike.
Wanan sayayya su na mayar abincina a gidan sai kuma indomei nakan bude fridge na dibi nama in girka muna a sayo bread mu zauna muci dasu ko Sydney kifin gwagwani.
A wanan karon na kara godewa Allah cewa ni din na kasance ba mai yawan cin abinci bane sosai sai hakan yai min dadi don idan mommy ta dawo nakance na koshi da abincin dare bana cin abinci da dare ni.
Hankalin mommy a kwance don tasan wasu dama haka suke a rayuwa basu damu da abinci ba ranan weekend kuma tare muke ci da ita indan tsakwara duk abinda naga taci a cikin jerin abincin.
Ranan zata fita nake fada mata cewa zan shiga gidan makwabta dana sani na gaidasu naga sauyin fuska sosai a wurin hjy din saidai ta daure tace min kada ki jima a can din.
In sha Allahu mommy ba zan tsaya don ummah ta fada masu zuwanane kada suga ban shiga ba tace is OK kamar na sani na dauki kayan shayin da sauran abubuwan da nakeci na boye inda bata gani.
Don bayan fitana mommy ta shiga dakin nawa ta bincika kayana saidai ba wani abin assha da tagani a cikin kayan nawa.
Tafito can ma ta tsure su Tabitha da tambayoyi a kaina sukace basu san komai ba a game dani don idan na fita bana fitowa barci nakan yi ko karatu a falo.
Ban magana da kowansu abincifa ta tambaya sukace ina ci amma sai rana yayi sosai nake fitowa in karya saita washe baki tana fadin shiyasa nakejin dadin aiki daku Tabitha.
Ban jima ba na dawo muka hade da mommy zasu fita take fadin har na dawo nace mommy sannu da gida ta amsa min tana faldin zata fita sai ta dawo nayi mata adawo lafiya na wuce zuwa dakina.
Ina shiga dakin nabi dakin da kallon don na fahinci an shigo min dakin lokacin sarkokina da wasu abubuwa na duba suna nan yadda na barsu ba a tabasu ba.
To me ake nema a cikin kayana na tambayi kaina ni daya a dakin saidai ban nuna nagane haka ba ga kowa don kosu Tabitha baki na rufe masu ina basu kayan kwalan da dan kudin kashi da wanan na saye su a gidan.
Dije zanyi tafiya saina dawo ya fada daga kofan Dije din Amadi sai ina kuma yau tau zamu diba dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login