Showing 90001 words to 93000 words out of 304363 words
da wofi ansan munafuncin da aka kula da zai kaini can din wurin su Abba din.
Mama saude ce tace anya ba da wani manufa yarinyar nan zata Abujan nan ba nifa tun farko shiyasa nace a barta da zancen yaron nan data nacewa.
Amma kin nace sai kin kula mata wanan sherin son kamal yanzu ga kamal din shima ba ganin shi kikeyi ba akai akai.
Anty tunda kamal ya yarda yana sonta ai gara in hadata dashi shegiya inga bayanta har uwarta don dole su zauna a karkashina innuwana sai yadda nayi dasu har kamal din.
Kina ganin ubanta ko uwarta zasu yarda da wanan zabin naki kuwa idan sun gano kudurin ki akan yarsu mama din ta tare da fadin ta yama zasu gane cewa ina hada wanan plan din.
Idan hakan ya faru aishi kamal yafi kowa cin riban harkan dan iska zai samu zukekiyar yarinya irin haka a bagas.
Murmushin gefen fuska mama ta sauke don tasan irin mugunta data shirya min wanda ba lalai bane ta fada a fili sai gurinta ya gama cika za a san manufarta akai.
Mun iso Abuja lafiya wani sabon driver ya turo ya daukeni airport muka isa gidan babu kowa a gidan lokacin wai suna wurin aiki dukkansu lokacin.
Sai yan aiki ke sintiri a cikin gidan falon gidan da yanzu ya sauya sosai nabi da kallo ina jin wani abu na taso min a kasan raina.
Dakin da yake mallakin ummahna a da yana kulle shina kalla na lumshe idanuna ina jin wani zafi a zuciyana yana kuna min rai.
Wanan dakin da ada muke sauke baki a cikin shi naga an bude min waina shiga shine masaukina banyi kasa a gwiwa ba nace.
Wanan ba shine dakina ba ai don ina da daki a gidan nan dama shi Abba ya sani wai waye ne me take fadane wai wata murya dake fitowa ta fada a bayana.
Dan juyowa nayi ina kallon inda nake jin muryan wata mace ce da ba zan iya fadin ajin da take ba ko budurwace ko bazawara waye ita me take fadane wai ?
A,a bakuwar da Alh ya tura na dauko airport ne dama shine take fadin wai ba zata shiga wanan dakin ba dama tana da daki a gidan nan.
A,a to ta fada taba ashe zakisha zama a nan to inane ma dakin naki a cikin gidan nan dama shiru nayi ban kalleta ba ta juya tana tsuki ta tafice gidan tana fadin kaga ka barta a nan harsu dawo idan ba zata shiga ba.
Komawa nayi saman kujera na zauna ganin hakan ya fice daga falon sai yan aikin dake sintiri suke gaidani jefi jefi ina amsawa har barci ya daukeni a wurin.
Ban falka ba sai da la,asar tashi nayi ina son inyi sallah kitchen na nufa wurin yan aikin nasan komai nagidan namu don haka mike nufin baya naso shiga bandakin dake baya din amma yana rufe shima a nan wurin su nayi alwala nadawo falon nayi sallah.
Bandaga ba daga wurin hjy karima din ta shigo tana fadin ina daughter na din take sai ta hangoni a zaune ina addua ga akwatina a gefena aje .
Ya haka naga kayan ki a nan bayan na fada masu dakin da zasu saukeki a ciki idan sun iso saida na shafa nake ce mata sannu da dawowa mummy ta amsa min ta sake fadin wai basu kaiki dakin danace bane ?
Dakin baki suka kaini nikuma nace masu bashine dakina ba don haka ban shiga wanan din na fada kai tsaye a daidai lokacin da Abba shima ya shigo falon ke nan.
Kallon mu yakeyi tunkan ya karaso lafiya bata shiga daki ba ya fada nace Abba ba dakina aka kaini ba ni kuma ban iya kwana ko wani daki gidan nan idan ba nawa ba kasani.
Mama meke damun kine da zuwan ki ko wani daki aka kaiki yanzu ai shine naki tunda ba ummah ki bace a gidan nan yanzu.
Ba zan iya kwana ba Abba na fada cikin rashin damuwa zaiyi magana tace kaga Alh dama wanine dakin nata wacan dayan da kike zama shine nata dayan kuma na uwarta sai wancan dasu hafsat ke ciki yanzu kannenta ke zaune a ciki dayan na mai aikinsuce.
Bari a sauketa a nata din tunda ban faye shigan shi ba dama ta fada kai tsaye ta kira yar aikinsu Tabitha tazo tace takai mun kaya a dakin tana fadin dama tun da kika iso kina nan falo zaune ?
Mummu ban iya zama ko wani daki sai wancan din na fada ina mikewa nabi bayan yarinyar da taja min kauyan zuwa ciki komai nawa an kwashe a dakin saina mummy din akwai gado da mirro da kujera.
Na aje jakar hannuna a kujeran dakin na shiga bandaki wanka nayi na fito na bude jakata na dauko riga na saka na shafa mai ina shirin naji an turo kofa mummy dince ta shigo dakin.
Yanzun hankalin ki ya kwanta ko ni har kin tayar min da hankali wallahi kan hakan zakiki shiga daki ki zauna a falo yanzu tunda naga kinyi wanka taso muje falo kici abinci.
Mommy banjin yunwa na fada tace me kikaci nace nasha cock da snack da muka iso sokoto dama haka kike wasa da abinci daughter a, a nace tace taso muje ki danci wani abu.
Banyi musu ba na mike nabi bayanta muka fito falon zuwa lokacin itama ta sauya kayan jikinta zuwa rigan shan iska.
Baya na dan tsankwara ne na koma daki ban sake fitowa ba don haka a ranan ban tantace iya mazauna gidan ba a lokacin har na kwanta wayana ya dauki kara na duba Ahmed ne ke kirana na dauka muka gaisa.
Yayi min ya hanya na bashi amsa da lafiya kalau nace yasu kaka Dije tana nan kalau sai nace aff wai kasan naga akuyarka kuwa a cikin mamaki yace a ina ?
A cikin mafalkina wallahi na bashi amsa nan na kwashe yadda mukayi na fada mai komai shiru naji yayi kafin yace ke nan uwargarke tana raye a wani wajen ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA.🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
2️⃣9️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Tafe suke ba wanda ya iya magana a cikin su don kowasu zuciyar shi a jagule yake lokacin don abinda malamin ya fada masu game da tafiyan nasu.
Wani unguwa mai nisan tsiya can suntubawa fita gari wurin wani tsohon bafilace suka fito wanda akace ya shahara da asirin mata ko wani iri mace ke so idan taje wurin shi tagama samun bukatanta don mutumin ya iya aiki sosai a cewan manyan matan gari.
Saidai su tafiyan nasu ya daure masu kai sosai matuka don kusan amsan shi daya da babalawon data taba zuwa wurin shine lagos a baya ita da kawarta dan sanyin da taji shine zancen hjy karima daya fada mata cewa ba zata taba haihuwa a gidan Abba ba asalima dai baiga zama a tsakanin su ba nai tsawo a duban shi din.
Wanan ya dan sa ta rage jin tafasan zuciyar ta a lokacin saidai tunawa da zancen zahra din yasa kuma taja tsuki a lokacin da bata shirya jan hakan ba a bakinta.
Kallon ta yar nata dake gefen mai zaman baza tayi tana fadin mekuma kika tuna kike jan tsoki nifa dama damuwa kan wanan tsohuwar da Alh ya kwasone don sam ban damu da zancen yar nan taku ba.
Don nasan bata taba kai diyan ki kaf dinsu a duniyan nan don me zaki saka damuwa haka akan yarinyar nan ne wai maimuna ?
Yarinyar da duk inda kikaje akece maki akwai matsala a rayuwan ta tome ya rage kuma ki mata yanzu ki barta can suji da matsalansu ita da uwarta su hakan ya shafa ai.
Watau ya saude baki ganewa ne tunda nasa ido ga yarinyar nan zahra naji Allah ya saka min tsanarta tun tana karamar ta kwata kwata na tsani yar a raina wallahi.
To ya zakiyi tunda mai hadawa ya hada zaman ku a innuwa daya saiki kawar da idonki a kanta ki mayar da ita da banza duk daya a gareki kiba kanki lafiya zaifi.
Ko nace zanyi hakan na kwatanta yadda uwarta ke taushe zuciyar ta wurin nunawa nawa diyan kauna sai naji na kasa hakan ga duk yaran salma din .
Bana son naga Alh yana nuna masu kulawa ko wani nuna kaunan suma diyane a gareshi don Allah ya gani banso ace wai salma ta haihu da Alh ba a gidan nan.
Haka da yawa suke ji kan yayan mijinsu saidai kowa na taushe zuciyar shine a zauna lafiya bakiji manya sunce dan kishiya rikon mai hakkuri ba .
Duk wacce kikagani tana ji da dan kishiya dole akwai tabon haka a zuciyan ta yan kadan ne keyi tsakani da Allah to ita taki mun kasa gane ko a wani ajin take do komai wayaun ka baka taba fahintar salma.
Munafuskace ta gaske don baka taba ganin bacin ranta kome kuwa zakai mata zata iya hadewa ta shanyewa cikin ta ta boye abin yai mata zafi koda kuwa mijin ne yai mata hakan.
Ai taci sunan ta kuwa salama son sunan ya dace da halinta mama saude ta fada a hankali taga yar uwan na rage gudun motarsu taga tayi parking a wajen masu kayan marmari zata saya.
Tana tsayawa masu kayan marmarin suka taso suna fadin hjy a sai kankana asai abarba wani kuma na fadin hjy Apple ne ko kai don Allah wancan nake so na tsaya ta fada a dan tsawace masu tallan suka fara ja da baya mai table din lemun ya taso yana dauko leda tare da fadin na nawa za a zubane ?
Zuba na dubu daya sai Ayaba shima na dubu daya ta duka tana dauko kudi a jakkan kayanta tana dagowa idonta ya sarke cikin na wani makaho dake zaune rike da sandanshi baiwa kowa a wurin magana sai dai mika roba da yakeyi.
Da sauri ta kawar da kanta gareshi don sai halittan mutumin taga ya bata tsoro kafin ta dago kai da niyar bawa mai kayan marmarin kudi sai ganin shi tayi bakin window motan tsaye yana fadin.
A taimaka saboda Allah da Annabi matafiya Allah ya sauke lafiya tafiyan da akayi Allah ya mayar da aniya ga mai ita sarkin da akayiwa ya sani.
Masu mugun nufi ya koma masu masu hassada halinsu ya bisu masu, , , haba malam muba tafiya muka fito ba nan cikin gari muke mama saude ta fada a hasale don irin adduan da taji yana fita a bakin shi.
Mai sayar da kaya marmarin yace dasu ai malam mamman kalar baranshi ke nan shi hjy ai fata na gari yai maku yanzu din Allah ya kaiku gida lafiya.
Motar mama data fara jan motan tayi yasa ya kauce yana masu Allah ya tsare ya bar wurin yana binsu da kallo har suka bacewa ganin shi ya koma bakin sana,arshi.
Mama saude ta fara magana tana fadin kinji mun mutumi wazai baka sadaka da wanan baran nasa wai nufin mutum ya bishi kamar wanda yasan abinda muka fitoyi.
Nima shinake tunane mama ta fada irin mutanen nan ina tsaron haduwa dasu don wata kawata a lagas ta taba yin gamo irin haka da kyat ta sha daga sherin su.
Sai yamma sosai suka isa gida suna magana daya sun shiga gida ana kiran magariba direct part dinsu suka nufa mai wanki yana biye dasu da kayan tsaraban da suka sayo a hanya.
A sabule ya shigo gidan Dije dake zaune a baki murhu ta dago ta dan kalleshi tana fadin yau da wuri haka ka dawo yace eh Dije yau munje kauyene na dauko hatsi a can .
Ledan da ya shigo dashi a hannun shi ya aje a gaban ta yana fadin wanan naman na gani a can yai min araha na sayo muna shi kinsan kauye suna da arahan komai su.
Ledan ta jawo zuwa gabanta ta fara buda tana fadin kace min dai yau dadine a gidan mun huta da cin yan yama yama kwana biyu gata nan dai ki zuba ma,ishi kowa ya wadata yaci .
Mikewa yayi ya nufi wurin garke yana gyara masu dauri kafin daga can din yace Dije uwargarke dai ta barmu da kewan ta kullun nazo wurin nan saina tuna da ita wallahi.
Dole a tuna da uwargarke sabo ba karamin abu bane don kusan shekara nawa ana tare da ita ba zan manta ba a daren da mahaifinka zai tafine yazo gidan nan sallaman ka shine ya bani fam biyar nayi ta boyonsu har suka kara taruwa.
Saina hada na fara sayan karo dashi ina dan kiwatawa sai na sayar nasai wani har kai ga sayo uwargarke daga baya naji bazan iya sayar da ita ba don tana da shigan ciki a jikinta lokacin.
Kai kuma ka dauki son duniya ka dora a kanta ance dabba baya dadewa to nidai kan uwarharke tayi min halarci don ta haifa min diya da yawa inba daga bayan nan da ta zama juya ba ta daina haihuwa nasan kuma tsufane tayi ya jawo hakan.
Yanzun gashi ta barmu don kanta tayi tafiyanta ai mun morewa wanan dabban sosai ko yanzu ta barmu ai munci ribanta ko.
Ballema bata tafi ba duk inda take idan ba yankata maishi yayi ba zata dawo gidan nan in sha Allahu komai daren dadewa kuwa nasan zata dawo garemu.
Sororo Dije tayi da ledan data dauka wanda ya shigo dashi da nama zata ta wanke tace haba dai Amadi har son da kakewa uwargarke yakai haka yau kwana nawa da batan ta inane ba ace min anganka kana nemanta ba ?
Ni kaina na zaga kaf gidajen unguwan nan na duba koda wanda ya ganta amma babu labarin ta ai ya kamata ka hakkura haka ka fitar da rai a zancen ta kuma.
In sha Allahuma zata dawo don na yarda da hakan kuma an fada min hakan ma zai faru daga inda take takemai kallon kanka daya kuwa Amadi ya gane me take nufi yace .
Dije uwargarke da kike gani alherice a garemu rabuwa da ita kinga zai muna jimame din haka kiyi fatan Allah yasa ta dawo gidan nan garemu.
Ta dawo wani gida koka manta cewa a yanzu ita din ba mallakinmu bane wai da me itafa a yanzu don me zaka dauki sin duniya ka dora a kan dabba haka wai ?
Murmushi yayi daga duken da yake yana fadin keba zaki gane hakan ba ai Dije amma nasan abinda nakeyi ni tace to Allah ya kyauta kada ka koma dan bautan akuya na mutanen kasan India.
Suda kiri kiri zasuga ta mutu su nemi wata suna mata bauta kuma daga baya ko su gina gunkita su dinga bauta mata.
Dariya ya kwashe dashi ya gama gyara gida ya koma gyaran wajen gidan su ya dade a can wajen yana gyara kafin ya shigo cikin gidan ya samu harta gama girki tana kokarin gyaran wurin.
Karban aikin yayi daga hannun ta koma kofan dakinta ta zauna tana fadin yaro da iya aikin mata haka matar ka ta huta saika dinga miya ita tana tuwo ke nan.
Daga duke ya bata amsa yana fadin dukama zanyi mata ita ta huta kina ma zancen mata wa zai bani yarsa garin nan an fara fada min cewa banda asali.
Wane dan banzan ya fada ma hakana wani irin zancene haka nake ji a bakinka kai mutane akwai iya sheri garesu kaida ubanka ya bar garin nan yatafi ya barka a saman kafafun ka biyu.
Amma aiku kuka hana inna tabishi yanzu ba gashi ta zauna garin ba da kunka hana tabin mahaifina ai kun yarda tabi wani daga baya kuma.
Kai Amadi shin kanka daya kuwa a gidan nan koka fara shaye shayen zamanine da akeyi yanzu a a zan bar yata zuwa wani nisan uwar duniya da banda kowa a can ni ina nan cikin gusau zaune zama ?
Ashe dama ni kaka zargi da hanaka zama da mahaifin haka kawai nika daukan yata in mikata uwar duniya ni ina nan nan niya gara dai su rabu din yafi min sauki da ace ya tafi da ita can inda ba a sani ba.
Kina fadin wai ba a sani ba baku san garinsu ba kuka yarda yarku ta aureshi dole inga laifin ku a yanzu don na daina jin zafin mahaifina da nakeji a baya yanzu laifin ku nake gani.
Shiru tayi tana bin jikina nata da kallon mamaki kafin tace shiyasa kataho min da zancen shi kwanaki ko ai tun lokacin na fara zargin da akwai wani magana a kasa da kake son fito min dashi.