Showing 198001 words to 201000 words out of 304363 words

Chapter 67 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33361

barambaram suka koma kowa da tasa tafiyan jin hakan tani tace kin gani ba haka take ta kokarin yi gareki amma hakkurin ki ya hana tayi nasara akanki shiya take kara kaimi ga aniyarta din.
Kiyi hakkuri hjy a kullun shi muke baki kinga kar yar nan ta falka ta sameki a cikin yanayin bacin rai haka kuma ba zataji dadin ganin ki hakana ba gaskiya .
Ni yanzu zan koma kada yaran su dawo su samu ba kowa a gidan kuma su shiga damuwa don ba wani kulawa zasu samu a wurinta ba.
Mummy kizo wai inji daddy yana falonsa zaune Salima ta fada daga kofa inda take tsaye hanbayenta na cikin aljihun rigan dake jikinta lokacin.
Ta dago cikin takaici tana kallon yar nata tare da fadi sai yace idan kinzo ki mun kerere a kai ki fada min ko wai Salima meyasa baki da tunane ke kullun kina abin yara ?
Mummy shiyasa na kiraki ba nina fadi hakan ba ta fada cikin shagwaba tana junawa zata bar dakin a lokacin tace kaji sakarai ina magana kina kokarin wucewa.
To kiji da kyau duk wanan sakarcin yanzu ya kamata ki daina shi ki nuna kin girma kinsan ciwon kanki don bamu kadai bane a gidan nan yanzu don kinga ya kwaso muna wa yancan mutanen duk da nasan anyi hakan ne da wani manufa a garemu.
No mummy ba matarsa bace don haka yana da right din da zai kawota nan mana ta zauna damu saidai abinda ban yarda ba shine tace zata rainamu.
Wani kallon ashe kina da wayau uwar tayi mata ta kawar da kanta gefe daya tana fadin zamuyi maganan hakan anjima yanzu kice masa kin samu ina bayine amma kin fada min.
Koda ta je fadawa mahaifin nasa saita samu hjy murja a falon zaune zakace bata taba sanin taba a duniya sai cewa da tayi daddy na samu tana bayi amma na fada mata yace is alright zaki iya tafiya.
Ta juya zata tafi a lokacin hjy murja tayi karfin halin fadin salima mun sameku lafiya ya karatu ?
Lafiya kawai ta amsa dashi tana ficewa suka kalli juna da mijin tayi wani irin guntun murmushi mai nuna cewa dama na fada maka ai.
Sai ji tayi yace dama wai baka ga juna bane tun jiya din tace ga alama ka gani kuwa irin abinda nakewa gudu ke nan tun farko nace ka barni gida can din yafi min rufin asiri don nasan halin hjy da yaranta sarai.
Zasu iya komaiwa mutum idan sunyi niya balle a yanzu gidansu nazo na samesu don haka zasu shiryawa hakan baiyi magana ba sai zuwa can da yace nasan da hakan amma wanan shine tsarina a yanzu naga na hada kan iyalina a wuri daya.
Sun kai wani lokaci a zaune wurin kafin ya kalleta yace zaki iya tafiya ki barni da ita nan gaba zamu zauna zan fita yanzu zuwa office tayi mai Allah ya tsare ta mike ta fita.
Shima bai dade a zaune ba ya mike ya shige ya shiryo zai fita suka hade ko kallonta baiyi ba yasa kai zai fice take fadin salima tace kana kirana ?
Banda wanan time a yanzu ya fada yasa kai ya fita taja tsoki itama ta fice daga falon zuwa part din ta har ta zauna wani zuciya ya debeta ta mike zuwa part din da bakin nasu suke.
Zaune suke dukkansu a falo suna hira saigata ji sukayi kawai an fado dakin ba sallama hakan bai hana dayan tace a, a hjy Yabi ce yanzun muke maganan ko kun tashi muje mu gaisheki ai.
Hannu ta daga alaman tayi mata shiru a lokacin kafin ta bisu da kallo daya bayan daya ta sauke idonta akan hjy Murja din tana fadin murja meya kawoki gidana a wanan lokacin?
Hjy murjan ta dago ta kalleta tayi dan murmushi kafin tace amma dai musulmai kika samu a dakin akala kyayi sallama ko zamu san damu kike zancen a yanzu ?
Murja watau har kin dauka wuyan ki ya isa yanka a gidan don dan wanan asirin naki da ayanzu kike ganin yana aiki akan Alh ke nan to barin fada maki kiji kuma ki rike idan kina tafiya da rana tsaye ni yabi dare da ranan duk a tsaye nake indai akan gidanane kece kika fara yanzu.
Lalai kuma kinyi sa,a malamin ki ya iya aiki harda ya iya karya dokana yasaka Alh ya dauko ki daga kauye zuwa wanan gidan a yanzu saidai kinyi kuskure babba na yin hakan .
Don in kishigone ta gaba ta birkice zaki koma wata kilama wanan karon ba inda kika fito zaki koma ba sai wani bakon waien.
Kowa na dakin sai binta sukeyi da kallon mamaki daga can inda yan matasan yan matan ke zaune da sauri dayan ta kunna waya tana daukan komai dake faruwa a dakin lokacin saboda yarinta.
Hjy yabi ke nan ban kara tabbatar da cewa ke din jahila bace sai yau din nan da kike wanan ikirarin haka a gaba saidai ki sani .
Ni murja ba yar matsafa band ba kuma jikansu bace a gidanmu musan Allah da Annabinsa tsagwaron su haka kuma da shi na dogara a rayuwana don shine boka da malam din gidan mu kinga tunda har Allah ya amsa min addua na akanki saina kara gode mashi.
Karya kikeyi munafukan Allah duk inda kike zuwa ai munsani don abin duniya ba boye yake a kasan nan indai indai bera bai daina yawon dare ba wata rana su hade da mage wurin yawon ai.
Ta jiya a fusace ta bar dakin cikin kunan rai tare da mamakin canzawan hjy murjan don bata taba tsamanin irin haka ba gareta wanan abin ya bata mamaki matuka.
Abin mamaki baya karewa sai ga hjy yabi din na fadawa Alh wai yayiwa hjy murja iyaka da ita don ta nuna ba zaman lafiya tazo yiba a nan don tana ganin kamar ka daure mata yanzu.
Har tana nema taci min a mutunci a gaban yan uwanta har tana fadin zataga iyakanta yanzu a gidan ke nan dama da wani manufa tazo nan ke nan.
Ya juyo ya bar abinda yakeyi din gaban mirror dinshi yana fuskantar ta abinda ya dade bai faru tsakaninsu ba ya dan murmusa yace.
Cikin kada kai Yabi kada ki manta da cewa ni din nan ni na aje kowan ku a gidan nan haka kuma nasan halin ko wacen ku.
Don haka ke me kikaje nema a part din ta don naga ni kaina na nemi kizo nan kika bata min lokaci ki kaki zuwa don ki nuna mata koni ban isa dake a gidan nan.
Don haka kina tsanmanin yanzu zaki samu wani girma a wurin murjan ke nan a gabanta fa kika nuna banda daraja ko kima har a idon yayan ki ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
6️⃣9️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Tani data hadu dashi zai shigo asibitin ya tsaya suka kara gaisa nan kwarmaton ta ya debe wurin dadin hira har take labarta mashi abubuwan da suke faruwa kafin tayi mai sallama zataje taron yarane ya biya mata kudin mashin ta dane zuwa gida.
Da sallama ya shigo dakin sai ga su Hannatu suma sun shigo tare da Dije da kanwarshi Aisha dauke da ledan pure water a hannun Aisha din.
Gaida ummah yake jin hakan yasa na juyo ina masa kallon mamaki lokacin hannatu ta gani take fadin masha Allah kintashi matar master ?
Duk suka juyo suna kallona to keyi kwana na rigaki karban jakkan tun dazun ai har na banye na bar maki ragowa jin hakan ya dan sani murmushi kadan ina kokarin juyowa.
Sai ya mike ya nufo bakin gadon yana fadin kin tashi Zahra ya jikin naki yana kokarin taba jikina lokacin Dije ke fadin kai danga ga idon uwarku kana kokarin taba matar ka gaba mu ?
In bakaji kunyan idona ba aikaji na uwarku ummah ta mike tana fadin mama ki barsu sallah zan tafi yanzu inyi ni to Dije ki bita kada ki zauna ki saka muna ido Aisha kai masu ruwan nan sai suyi alwala dashi.
Babu Faro ne hannatu kuka sayo wanan ga ummah da ledan Faro kuka dauko ai da sauri ummah tace a a kai wanan din ma ai muna amfani dashi sosai ko a gida.
Bari dai a je a sayo makushi wanan din sai a aje don wani amfani zauna abinka don Allah wanan ya wadatar ai lalurane ya kawo hakan.
Jin hakan ya koma ya zauna yana fadin hannatu ko zaki zuba mata abinci ko zataci wai to Allah yasa tunda kana kusa amma rabon zahra da abinci ni har na manta ta fada tana mikewa da kyat na daga mata hannu alaman ta barshi.
In serious voice yake fadin don me zaki zauna da yunwa a cikin ki haka kina gani yunwama ai yana iya kara maki ciwon na girgiza kai alaman a a.
Naji yace haba princess ko yunwa na kara maki ciwo ai ki daure ko ba yawa kici ko kadan ne haka nake fada mata amma da takai baki zata dawo dashi.
Wani kallo naga yayiwa hannatu dake bayanin hakan gareshi kun fadawa likitocin haka duk mun fada masu yadda take ji din sun dauki bayani.
Tun kan a kawo abin na kawar da kai ya karba wai ya bani da sauri na rufe bakina kamar wanda yaga mugun abu a lokacin guda yayi yayi na juyo na karba na kasa.
Haka ya hakkura ya mike tsaye ya fita ya dan jima sai gashi ya dawo da leda da kayan sanyi a cikinsa ya samu sun shigo dakin ummah tana min fadan cewa na don me ba zan daure koba dadi inci abincin nan ba.
Ummah ku barta ko zata sha wannan yana kokarin budan ledan ya zaro goran fresh milk ya miko min yana kokarin budewa tare da fadin ki daure ga wanan ki dansha ko kadan ne.
Yadda na karba a hannun shi hakan ya tayar mai da hankalinshi karkareni daya ga yadda na fitar da idannuna waje saida gaban shi ya fadi don tsoro.
Wani iri yake ji lokaci guda kanshi na wani irin juyawa hankalinshi na neman gushewa gare shi Allah ya taimaka yayi dabaran mikewa zuwa wajen dakin da sauri zakace ya tuna da wani abune a lokacin.
Ruwa ya saya ya tsiyayya a kanshi tun wanan lokacin ya koma wani sukuku dashi kamar wanda ke ciwo ko dakin baya son shigowa sai dole in ma ya shigo can kofa zai tsaya yai maganan da zaiyi ya koma.
Ummah ce ta farga da hakan ta farawa dije bayanin amma taga Dijen bata gano komai data gano ba sai bayan sallah magariba ta dawo daga sallah ta sameshi zaune yayi tagumi shi kadai a wurin zaune.
Har zata wuce ta gano shine tace Ahmed ne wai ya dago kai da sauri yana mikewa tare da fadin barka da fitowa ummah Allah ya karba tace amin.
Lafiya dai na ganka haka tun dazun nake lura da sauyi gareka saidai ban san me ya jawo maka hakan ba lokaci daya ta fada tare da tsureshi da idanunta.
Eh wallahi dama ba komai bane saidai ban san ya za a fahinci magana taba yanzu idan na fada don gaskiya na fahinci ciwon nan na zahra kamar dai bana asibiti bane kawai kamar ya dan surku da harkan jinnu haka.
Wani kallo na tsab ta aika mai dashi lokaci guda kafin ta sauke ajiyan zuciya tace eh zai yuyu hakan ne don nima nayi wanan tunanen amma yanzu tunda munzo saimu dakata muji abinda sakamako zai bada kafim mu san abin yi nima dai hankalina bai kwanta ba a yadda nake ganin ta din nan.
To shike nan ya fada tare da dan sunkuyar da kai katsa tace Allah ya kyauta ya amsa da amin ta nufi hanyar shiga dakin da nake kwance.
Sai kuma taja ta tsaya tare da dan juyowa ta kalleshi tace da badon akwai gajiya a tare da kaiba dakayi sakkon zuwa zuwa funtuwa gobe kaje kaga wani kawuna a can da ake kira malam Idi mai rafannan acan.
Da sauri yace ba matsala sai inje din ko yanzu badon dare yayi ba aida zan tafine tace a,a ka bari zuwa gobe din nan tayi mai kwantace yace ya gane insha Allahu kuma zai tafi din in Allah ya kaimu da safe sukai sallama take fada mai tunda jjkin nawa da sauki zata koma gida tunda ga Djje da hannaty har da Aisha.
Tayi waya azo a dauke karfe goma yayi mata godiya ta juya ziwa dakin ya koma ya zauna nan dije tazo suka zauna suna dan tatataunawa kan zancen matsalan nawa.
Cikin bacin rai ta juya tabar dakin ganin ya dauki waya ya fita batun ta ya nuna baida lokacin ta kamar yadda tayi mai itama ke nan da safen.
Saidai bata dauki nata da sunan wullakaci ba sai nasa don haka ta kulla a ranta cewa ai don hjy murja dince yai mata hakan bako sauran zaman lafiya ke nan a tsakanin su a gidan .
Don haka zata kada masu gangan shedan da sai duk sun raina kan su suyi da sun sani da basuyi mata hakan ba a rayuwan su don ba a takata a wanye lafiya a rayuwan ta.
Ita mace ce dake tsaye da kanta da yayanta a ko wani lokaci tayi a mannan cewa boka da malam suna biyawa mutum duk bukatan sa idan ya nemesu.
Da wanan kudirin takai dakinta ta kwanta tana faman saka yadda zata fara bullowa zancen da hjy murja zata fara koda maigidan yanzu nan tunanen ta ya tsaya akan zata yakesu a lokaci dayane don da zafi zafi ake buga karfe.
Mai aikinta ta nema da sunan bata umurni akan ta san ita dai ta daukota aiki a gidan nan ko daga lokacin aikinta zai tsayane akan ita da yayanta da mijjnta kawai a gidan.
Da sauri Asabe ta dago kai ta kalleta don jin umurnin da tabata a lokacin kafin cikin ladabi tace hjy ki gafarceni jiyan nan Alh ya ban umurnin da a hade girki ga baki daya a gidan nan.
Itama din wani kallo ta jefeta dashi a harzuke take fadin Asabe nina daukoki gidan nan ko shi kece hjy Asaben ta fada cikin rawan murya.
Tace don haka nina baki umurni da haka idan ya tambayeki dalili ki fada masa ninace ai hakan ki tashi ki van wuri Asaben ta mike da sauri zata tafi sai kuma ta dakarta da ita tana kare mata wani mugun kallo tace.
Wai yaushe har kika samu daman yin magana da mijina haka ban sani a gidan nan wani iri Asaben taji sai ta daburce lokaci guda kafin tace da sauri a,a hjy jiyane da ina tsaka da aikin yamma ya shigo kitchen ya fada min.
Wani kallon banza ta bita dashi kafin ta kawar da kanta gefe ta fita batun ta ta dan dade a duke kafin ta mike da sauri ta bar dakin tana watsa mata zagi a zuciya da fadin macuciya karyan ki dai ya kare tunda kishiya ta shigo gida nan da sunan zama.
Har takai kitchen din tana tunanen yadda zata bullowa zancen Allah da ikonshi taji muryan maigidan waje yana magana yan aikin gidan maza.
Nan ta dauraye hannu ta sameshi ta rusunna daga bayan shi tana gaidashi kafin tace dama Alh hjy ce dai ta kirani dazun nan ta ban umurnin dana daina girki da hjy karama da duk wani aikin daya danganta da ita a gidan nan.
Ya juya gareta a cikin mamaki sai daga bayan shi kuma yaji mazan na fadin muma dai Alh munsan hakane zai cika damu gun hjyn .
Don yana da wuya ta barmu muyu wani aiki daya shafi hjyn a gidan nan din ko baki akayi mukai masu wani abu zata zagemu tace zamu bar aiki balle wanan da take ganin kishiya a gareta yanzu.
Innalillahi ya ambata kafin yace duk ku saurareni cikin tsawa shin hjy ce ke biyan ku koni to ku sani daku da ita duk a karkashina kuke har wana din datazo daga baya.
Don haka kowan ku ya tsaya iya matsayin aikin da aka daukeshi a gidan nan wanda bai iya bin umurnina sai nata ya fada min tun yanzu na sallameshi.
Kafin ya bisu da kallo daya bayan daya can kuma ya numfasa tare da fadin bayan hakan tunda aiki ya karu yanzu zanyi doubling din kudin kowa a cikin ku ga wata kai driver mai kai yara school.
Zan kara ma kudin ka ya cike dubu hamsin haka mai wanki daba shuka ruwa kaima kudin ka a yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login