Showing 267001 words to 270000 words out of 304363 words

Chapter 90 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33368

da nasa iyalin yanzu daddy yafada don me zaki tsaya bata lokaci kuma akansa yanzu ?
Au bata lokaci mane kake gani ko to bari kaji idan har ya shigo cikin mu yau Alh ya fadi ya mutu dole a raba dukiyan Alh dashi shine zakace na barsu nabarsu don me zan barsu su yaudaremu.
Mutumin da yake aiki yanzu under UNICEF wani dukiyan daddy zai dameshi yanzu kai da bakasan ciwon kanka ba kake ganin hakana amma ko kwandalace sai ya karbi kasonshi.
Don haka ba zan zuba ido har a kai ga hakan ba sai dolene in dauki mataki a kansa kafin lokaci ya kure min inzo ina dana sani daga baya.
I am out of dis mission don badani za ai wanan ba all what i know shine idan har yazo din yana zaman dan uwane a gareni koma din baizo ba shidin dai dan uwanane tunda mahaifinmu daya dashi.
Idan kinbita tawa kawai ki barsu don banga wani abin tsayawa yin jayayya akai ba na fada maku i am out dis ya mike ya fita tace mahaukacin banza kawai wanda baida tunane.
Ta kallo inda Salima take zaune ta ishishire kafa saman dogon kujera tana dakalan wayarta tace ana magana kinyi shiru tun dazun ke.
Mum me zance ni wanan ba zance na bane ai don haka ba matsalata bace ta mayar da kanta ga waya taci gaba da dakilan wayanta da takeyi din.
Ran hjy yabi din ya baci lokaci guda takaicin diyan nata ya rufeta ta rasa me zatace dasu a lokacin maganganu ta farayi kamar zararra ganin hakan yasa salima din ta bar mata dakin.
Takaicine ya cika hjyn don ganin bata samu goyon bayan diyanta ba yadda take son samu a wurinsu su hade kai su yaki daddy nasu akan basu yarda wanan yaron da yake ikirarin cewa dansa bane ya shigo cikinsu yanzu don ba dan uwan daya san dashi a baya.
Tunane yakai tunane gareta sai batan basira ya shigo mata azuciyar ta aje shawara kan zata nemi hadin kan hjy murja kishiyarta su jajirce mijin nasu akan basu yarda da hakan ba su.
A karo na farko da zatayi amfani da murja din ke nan don a ganinta a baya murjan ba a bakin komai take a gidan ba balle ta nemi wani abu a wajenta.
Sai gashi a yanzu bukatan hakan ya taso mata ya zama dole tayi amfani da murja din wajen cika burin ta ga mijin nata idan tana son abubuwa suje mata daidai a lokacin.
Don haka ta shirya yadda zata tunkari murja din da zancen cikin daure zuciyan ta don sai ta danne zuciyar ta akan hakan zata iya cinwa manufarta akanta in yaso daga baya bayan bukata ya biya sai ta koma kanta itama ta gama da ita.
Kwana biyu faran faran takewa hjy murja din wanda yasa har murja din ta fahinta da akwai wani kulli da matar keson mata a lokacin saidai bata san ta inda kullin zai fito ba akanta don haka.
Take shan jininta da matar tana dan kame kanta taki yarda su sake jiki da juna kamar yadda hjy din take nuna mata a lokacin na ita yar uwane ai a gareta.
Yauma kamar kullun girkin hjy yabice don haka da kanta ta fito tana ba yan aiki umurni ga abinda zasuyi hjy murja data fito daga dakinta zata shan iska waje ta samu hjyn gidan da kanta a falon tana ba masu aiki umurni.
Bata tsaya ba amma ta gayar dasu da aiki zata wuce taji muryan hjy din na fadin wai murja dama ashe haka kuke wahala da aikin nan gashi banice keyi ba amma duk na wahala a wurin magana kawai.
Ay,yah Allah sarki ako son baki saba bane aikin aiba wani wahalane dashi ba hjy ta fada cikin muryanta mai taushi tare da yanayin irin na kamala kamar yadda take ko yaushe.
Tana fadin hakan tasa kai zata shige ta kara jin muryan hjy din na fadin af kingako tun dazun na fito da niyar aika maki anjima mu shirya zuwa gaida dan abokin Alh dake asibiti.
Wani irin dagowa hjy murja din tayi lokaci guda tana kallon hjy yabi din a cikin mamakin dake baiyane a fuskanta a lokacin don maganan haka yazo mata a bazata.
Yau itace wai hjy yabi da kanta take son fita da ita a mota daya har take taya mata fita a tare da ita da bakinta lalai duniya me juyi ga bawan daya gane hakan.
To hjy tarene zamu tafi bakinta ya tambaya a cikin mamaki lokaci guda eh karfe biyu sai mu tafi mu lekoshi kafin mu isa an budewa yan ziyara kofa ina ganin haka zaifi ta amsa da to hjy.
Ta juya ta wuce cike da mamakin hakan zuciyarta yana faman saka mata maganganu iri daban dabam dama ba kowa a wurinne zaman kadaici ya isheta shine tafito waje tasha iska don yan matanta sun tafi school a lokacin.
Itako hjy yabi harara tabi bayanta dashi cikin kulewa kai kace ba ita bace ke sheka dariya yan mintunan da suka shege ta mayar da fuska tayi murtuk da ita a yanzu don jin da takeyi zuciyanta na mata suya.
Karfe biyu da yan mintuna suka fito suka bar haraban gidan don dauriya harda hira take jan hjy murja din tana fadin kinga idan mukai wurin masu kayan fruit sai mu tsaya a saya mashi kada muje hannu sake a raina muna wayau.
Hakan akayi don irin ledojin da hjy ta makare da kayan fruits din sai dai Allah ya taimaka don suna tayar da mota take fadin kinga wana namune ni daya ke daya wanan kuma sai mu kaiwa maishi.
Sun samu mai jikin da sauki sun fito don basu tsaya ba saboda ba lokaci a hanya sun dan bar asibitin kamar ta tuno da wani abu tace uhumm, ummm a cikin mamaki.
Hjy murja din tayi saurin juyowa tana kallonta tace bari ke dai murja zancen Alh na kwanaki na tuna dashi haka kawai ana zaune kalau zaka jajibo dan shege ka shigo muna dashi gida da sunan da.
Wani Alh ke nan hjy murja dake zaune a takure ta tambaya tace keko murja Alh mu mana wanan dan nasa da yake son lakakawa kansa a yanzu mana.
Ai,wanan zancen ne to amma hjy ai Alh ba jahili bane da zaiyi hakan da kike tunane tunda yace danshine dansane ke nan na sunna ko baya ai an taba maganan danko tunda har su yaya sunsan da zancen agida sunema ai sukaje wurin daurin auren shi wani lokaci.
Au dama ke kinsan da zancen ke nan tun a gida itama kallota tayi kamar yadda ta kalleta tace hjy aiko kekin sani nima nasanda zancen balle ke.
Dansane kawai don ko kamansu ai ya raba gardama amma kuma ni ban yarda cewa dan sunna bane kamar sauran yaya ta fada tana jan tsoki.
Gashi ya fadi yadda sukai aure da mahaifiyar yaron a gaban ki kuma kowa yasanda haka toni ban yarda ba dama nasan bakin ku daya ai dasu .
Meye nawa a ciki hjy banyi bakin ciki da dan kowa ba balle wanan da yake shi kadai a uwarshi don haka ni duk daya na daukesu ga baki dayansu yayan Alh ne.
Bakaken magana sosai ta fadawa murja din haka suka kawo gida ran kowa a bace bata ko karasa fita daga motan ba ta figi motan ta juya ta bar gidan a fusace.
Zaune nake ina rike da kwallon tumfafiyan dake hannuna ina dan juyashi a zahiri zaki dauka dan kwallon iccen nake kallo saidai a kasan zuciyana tunane nakeyi a lokacin.
Ba komai nake tunane ba sai yan uwana da mahaifiyata tare da sauran yan uwa ina duban yadda zan haihu a nan babu kowa nawa a kusa dani duk da dije na tare damu amma ai dije bangaren miji take gareni.
Cikin irin wanan yanayin na fado kan inna da yan matan ta zancensu da danta na tuna na tambayi kaina wai me inna take nufi danine haka ?
A gaskiya dole in fito mata a mutum sak idan ba hakan ba tarihine zai maimaita kasan a iyalina yadda hjy tsohuwa bata kaunar mu haka abinda zan haifa zai taso inna na gwada masa bambaci a gaban kowa.
Ba zance yadda uwana ke shan wuyan gidan miji ita da yayanta nima hakan zan iya fuskanta ba don irin kalaman da nakejin master na fadi a kaina duk da hannatu ta ban shawara da kada inyarda da dadin bakin namiji .
Lokacin da namiji baida kudi komai yana iya fadi akan matarsa amma da zaran ya fara rike yan canji a lokacin ne wasa zai canza zai fito da kalanshi na gaskiya don haka kada ki sake ga baki daya zahra ki rike kimar ki a cikin tako don mace mataayi gareta.
Nakan tsaya nayi tunane wanan maganan in kuma duba shawaran data bani a lokacin inda tace dani abu na farko zahra shine ki rike Allah fiye da komai kada ki yarda da hanyan masu bata.
Don kina zagaye dasu ta ko ina zaki iya cewa kema sai kinyi abinda sukai maki kada ki yarda shedan ya rinjayi zuciyar ki ga hakan.
Ki zamo mace mai kula da hakkin mijinki ako yaushe ta yarda zaki zamo mowar zuciyarsa bata gida ba kawai don akasari mowar gida na karfi da yajine wasu suke zama hakan.
Nan ina nufin ki zamo mai son abinda yake so mai kaunan yan uwansa fiye dashi maj kula da arzikinshi fiye dashi mai damuwa da damuwarshi koda bada saninsa ba duk ki wanan.
Sai kin hada da kula da hakkin makwabtaka dana abokansa da ma naduk yan uwa ko yana nan ko bayanan yazamo daya a wurin yan uwasa don watarana zasu fada masa alherin ki ko akasin hakan duk dai wanda kikai masu din.
Ki kasa ki tsare gaba da baya na komai nasa ta inda zai rasa gaba ya rasa baya babu wani hanya da kike da rauni dai a gidan nasan kina da tsabta basai na tabo maki nan ba zaki iya wanan fannin amma dai ki kara kulawa kada ki gaza da hakan.
Zahra zaki iya nasan zaki iya don ba yawan surutune dake ba amma ki kara kama bakinki akan sirim mijinki da kika sani da wanda kika gani harsai idan kinga zai kaucewa Allah nan kan kina da daman neman sharawa akan haka.
Hannatu duk wanan a ina kika sansu ta kwashe da dariya kafin tace kin manta yawan gidajen dana zaunane zahra ina fa ganin komai kuma ina ji don ni yar garice na fiki shiga mutane sosai don haka nasan hakan.
Zama na gyara tare da ajiyan zuciya ina lumshe idanuwana nace lalai hannatu tayi gaskiya ya zama dole in dauki shawaranki in fara nuna kaina a cikin dangin miji da nawa yan uwan yanzu.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/4, 10:05 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
9️⃣1️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Dije ce ke zaune saman kujera mai zaman mutum daya sai ni kuma da nake zaune din na ishishire kafata don inji dadin zama a lokacin ga diyan icce tatacce a hannuna ina sha a hankali.
Amma yanzu ina ganin kin rage shaka abin naki ko dijece ke min wanan tambayan don sai mu zauna ba hira don ni din ba gwana bace a wurin hira hakana muna dai dan tabawa wani lokaci.
Duk da dije din ma bawai tana shiga mutane bane sosai kuma wai tayi irin tsufan nan na sosai bane don innace yarta ta fari shi kuma Ahmed jikanta na farko so batayi irin tsufan gigicewa din nan ba a yanzu.
Illa kafa dake damun ta da rashin gata yasata dan mokade a yanzu kuma da take cikin hutu ta dan fara dawowa hayacinta don tana dan murmurewa saboda abincin da take samu yanzu duk da wani bata iya cinsa sosai tunda bata saba dashi ba.
Haka yasa nake dagewa ina dan sarafa shinkafa irin namu na gida da muka saba dashi don ita na neme hanyan tuka tuwo a can ba ita kadai ba harshi yana ci sosai sai shimkafa da miya da nakan muna ban damu da nayi abincin su na can ba.
Don haka a fannin dije kan nagama kamota sosai don na saye zuciyar dijen fiye da tsamanin ki mai karatu tun a gida na kafa gwaunatina a zuciyanta uwa uba kuma zuwan mu wanan kasan yanzu.
Saura inna da wasu yan uwa nasa dake min kallon mai wayau a cikin su don su a daukansu wayau kawai nakewa Ahmed a zaman mu dashi tunda suna ganin ni idona ya bude ko.
Basu san zaman miji da mata ba sai Allah a tsakaninsu sai kuma hakkuru duk yadda zance in masa ma wayau Ahmed ya darani in dai dabaran karban kudine a hannunsa abinda basu gane ba ke nan su.
Don shi ya bude idone da neman kudinshi na zufan shi don haka zaiyi wuya a iya karban kudi haka hannunshi wasan dadi shine su kuma basu gane ba suke kallon nice mai hanawa.
Kallonta nayi ina murmushi kafin nace da ita gaskiya yanzu na rage tun bayan zuwan mu nan amma dai ai ina dan shakawa akai akai don dama ance sai cikina ya tsufa sosai zan daina.
Waya fada maki hakan ta tambayeni cikin kureni da idanu tana son ji na danyi murmushi nace a nadai fada maki haka sukace dani tace ni nasan ba banza ba kan wanan abin dole mutanen kankine ke sakaki hakan don wanan abin karfi gareshi sosai.
Ni dai ina ganin mutanen ku dayane da mijinki don shima tun yana yaro haka yake mu,amula da tumfafiya nakan rasa inda yake debowa kona kwashe na zubar gobema zai samo ya aje min a daki.
Ke har wanan ganyen nasa dake fadowa kasa da kansa Amadi daukowa yake ya kawo min daki idan na zubar kuma ya kama jinini ke nan na zubar masa da abu ranan har yajin cin abinci yake min don wanan abin.
Shiyasa a karshe nama daina zubarwa yadda ya kawo haka nake tara masa kayansa a gefe sai ya gaji shida kansa yake zubarwa sai gashi a karshe iccen ma ya fito a cikin gidan mu karewa ke nan.
Kullun fada yake zakiga ya duka yana tsince duk wani abu dayaga an zubar a wurin iccen yanzu kuma gakike da naki saddabarun tumfafiyan .
Allah yasa dai kardan cikin naki ya gado ku din dan gado yafi nagada riko haka nake kallon wanan lamarin tafe maku.
Dije kina nufin abinda ke cikina zai iya hakan shima tace waya san gaibu yar nan Allah dai ya sauwaka amma ni lamarin mijinki kan nasan komai tsarawan ubangijine a kansa gaskiya.
Shiyasa ban faye yarda zuciyana ta amincewa wai mabiya ke gareshi ba yadda mutane ke fadi kansa don rashin mu,amulanshi da mutane.
Don kinga yadda yake din nan fari ga kyau sai dora mai aljannace ta aure shi don da har ina jin tsoron hakan amma tunda ya aureki har kuka zauna lafiya yanzu har ga ciki .
Hankalina ya kwanta sosai wallahi amma a lokacin da naga har shekara biyu da yan kai baki da komai gaskiya ban fada bane amma hankalina ba a kwance yake ba gaskiya.
Shiru nayi ina nazarin maganan ta kafin can ince wai yau me zamucine a gidan dije ta juyo tana fadin ni yar gata ai yau inda tasone ta gida zamu tuna muci shimkafa da mai da yaji.
Lokacin na tuna da akwai yaji ai danazo dashi wanda ummah ta bani idan na haihu wai nayi amfani dashi ni yaji bai dameni ba amma don kawai kada na aje na saka a cikkn kayan tafiyana gashi kuma zai mun amfani yanzu.
Waken su bai kai namu dadi ba a baki amma nasan idan na hadashi itin namu hadin zaiyi dadi don haka na mike kawai na shiga kitchen na dora muna girki.
Shimkafa da waken na dafa sai ganyen kabejin dana yanka na soya mai da albasa da kamshin shi ya karade easthed din namu har saida makwabta suka shigo tambaya me muka dafa haka ke kamshi ?
A lokacin na hada muna a tire don in munci tare da dije din nafi cin abinci sosai in koshi ido matar ta sauke ga abincin tana binshi da kallo na nuna mata.
Ta dan debi cibi daya dan kadan takai bakinta tana wani taunawa a yangance sai naga ta kara turmuza cibi wanan karon da yawa ta dibo takai bakinta.
Munci sosai muna hira yayin da shima ya dawo ya zauna yaci yana ta saka min albarka ni dai ina murmushi kawai don jin dadin yadda suka yaba da girkina din basu ba gashi har makwabta mutum uku suka karba na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login