Showing 63001 words to 66000 words out of 304363 words

Chapter 22 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33313

din nan.
Me ke faruwa agidan ne Dije ya sake tambayanta a gagauce, Dije ta dubeshi tace huta dai mayi maganan daga baya barin dan fita in samo muna dan wani abu inciwa cikina ta fada tana jawo tsunman gyalenta daga kofa a rataye.
Tasa kai da sauri ta fice gidan ko kallon inda dabbobin suke batayi ba ta fita da sauri ya bita da kallon mamaki don yadda take jan kafanta mai mata ciwo kamar na dole takeyi lokacin da sauri.
Juyawa yayi wurin dabbobin yana kallon su kafin yabi ko ina na gidan da kallo yasan duk da tsohuwar nada ciwon kafa amma idan yai irin tafiyan nan na sammako ya fita bata barin gida haka da datti saita gyara shi.
Cikin dan lokaci yayi tunane kardai yawan maganan akan uwargarke da tsohuwan keyi ya zamo gaskiya fa shi bai kula ba har wani abu yazo ya samu kakar nashi saidaga baya yayi daya sani akan hakan .
Bin bayan Djje din yayi wace ya samu a tsaye kofan gidan nasu kamar tana tunane Dije ya ambata daga bayan ta cikin murya mai nuna yanayi.
Ta juyo a firgice taga shine ya karsso dab da inda take tsaye yana fadin Dije meye damuwan kine wai ki fada min don naga kamar a firgice kike yau a gidan.
Duban bayan shi tayi kamar tana duba idan wani na biye dashi lokacin kafin taja hannun shi su taka dan nisa kadan da gidan nasu kafin tace yau uwargarke taso kasheni Amadi.
Kasheki Dije tace kwarai nan ta kwashe komai yadda ya faru ta labarta mashi tare da fadin don haka dole ka sayar da akuyan nan ko mu saketa tabi gari kawai taje duk inda zata.
Dan shiru yayi yana kallon tsohuwar kafin yace baki ganin in muyi hakan munyi ganganci Dije akuya nan fa ba zamun takeyi a gidan nan ba yanzun.
Tana zama na amanane a wurin mu yanzu yau idan mun saida ita maishi yazo muce dashi me ke nan ta dawo mun koreta ko ta dawo mun sayar da ita ?
Kiyi hakkuri kizo mu shiga gida zan san abinyi kan hakan me zakayi ta tambayeshi a dan tsorace tana kallon shi don jin me zai fada.
Yace bari dai yanzu koma ciki bari na gangara na sayo maki abinda zakici kafin motan kayana ya iso nan da dan lokaci in zama busy ya fada yana kokarin wucewa.
Ta jawo hannun shi ba zaka barni da wanan abin ba a gida ni kadai kai subbahanallahi ya fada kafin ya dan daga kai yana tunane a wurin na dan lokaci.
Yanzun zo ki zauna ga wuri naje in dawo yanzun nan yana jan hannun ta zuwa wurin dan dutsen dake kofan gidansu a kafe inda wani lokaci suke zama ko masu tafiya su zauna asama su huta akai.
Zama tayi kamar yadda yace din shi ya wuce can inda yan mata ke saida abinci ya sayo mata shimkafa da salad da miya da nama yanka hudu sai ruwa mai sanyi daya riko mata a leda lokacin tare da fantan kwalba.
Ya dawo suka shiga gida tare ya kaita har dakinta ta zauna ya fito ya diban mata ruwan wanke hannu don yasan ba zata ci da cibi ba saida hannu.
Saida ya tabbatar da ta fara cin abincin a galabaice ya mike ya fito sai wurin dabbobin nasu ya tsaya a gaban uwar garke daga daki inda dije take ta iya hangoshi wurin yana gyara masu wuri.
Ya zubar da ruwan ya dauke roban ya wanke ya share wuri ya zuba masu abinci da ruwa duk a cikin zafin nama da alama yana saurine a lokacin.
Haba uwargarke keda Dije ba hakan tsakani ku ai karki manta Dije itace farin ciki gidan nan dani daku duka baki dayan mu gidan ai Dijece gatan mu kin ture ta idan wani abu ya sameta yau duk ya samemu ke na ai.
Ke kanki ina baki girman ki na babba cikin yan uwa duk wani laifi ko wani abu kece babba ke, ke dauka don haka kibar firgita min Djje don Allah ba lafiya ke ga tsohuwar ba kin sani.
Haba uwar garke bai kamata haka ba tsakanin ki da Dije sai mutunci ai yanzu kibar mata abin dabo dabo tana firgita dake haka don Allah.
Zaka ce da mutum dan uwanshi yake magana a lokacin yana taba uwargarke magana sai ta mike ta girgiza jikinta kafin ta dona kai a ruwan shan su tana sha .
Bayan ya gama dasu ya dawo zuwa dakin dije daga kofa ya tsaya yana mata magana Dije zanje na duba na gani ko motar kayan mu ta iso na fake don nan nake son a kawo min su gida tunda banda shago a kasuwa yanzu.
To kayi niyya Amadi Allah ya taimaka nima barim je gidan malam Tanimu harka dawo sai in dawo gidan ta fada tana yunkurin tashi tsaye ya dawo ya tsaya yana fadin .
Dije kardai ki dauki wana zancen ki kaiwa makwabta shi suzo su fassara wanan magana da wani manufa kuma daga baya.
Kinsan yadda mutane suke yanzu balle ana ganin na fara sana,an nan da kudin mutane sai su dauka ai wani hali na daban na farayi yanzu karshe ma sai a camfa gidan nan kiga anzo anki shiga daga karshe azo ana gudun gidan nan kuma.
Hakane fa yanzu lokaci ya canza ai gara daka kwabeni don kan abinda nayi niyar zuwa fadamasu ke nan yanzu inda taimakon da zasuyi min su taimaka min dashi.
Ba abinda zai sake faruwa in sha Allah har inma ta hurhurane Allaj zai muna maganin ta balle yanzu ina batun shigo da kayan nan kinje kin fadi hakan a take zasu camfa min ne kan kudin tsafi nake amfani dasu.
Alhalin kudin mutane ne na aro na kara nake juyawa tace Amadi kudin wa ka anso yace naso maki wanan bayanin kuma sai naga baki cikin hankalin ki yanzu idan na dawo zan fada maki komai in sha Allah.
Nan ya fice ya barta tana zancen zuci ita kadai a gidan har ta dan samu fitowa ta gyara gida saidai tanayi tana kallon inda dabbobin suke har taje ta sakamasu hayaki saboda sanyi a wurin garken nasu.

ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
2️⃣0️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Kamar yadda mukai zaton Abba zai koma ranan monday sai gashi monday din tayi duk Abba yana gari na dawo daga school na samu basu wuce ba ke nan ranan ummah zata basu abincin dare.
Don haka na samu suna aiki amma kuma ga abubuwan rabanan na azumi an kakasa a ko ina na gidan da gani damasu shi na wuce zuwa ciki na kwabe kayan jikina na fito.
A kitchen na samu su umma suna aiki nasa hannu akayi girkin tare dani har aka hada komai muka fito falo nida Tani lokaci guda don ummah ta barmu muna karasa kulin tuwo a leda fara.
A galabaice na zauna kan two seater din mu na falon Tani ta kalleni ta kwashe da dariya tare da fadin yau kan mutumiyar tasha aiki ko ta fada cikin zolaya.
Ummah ta kalleni tace har wani aiki tayi bayan ta samemu mun hada aikin muko kafin tazo nace hai ummah nimafa nayi aikin nan sosai fa.
Tsuki ummah tayi tana fadin kina ji Tani ki dauki wanan kayan sadakan azumin guda goma kije ki raba ga duk wanda ya dace a bangareki amma fa ba naki ciki don haka ki bayar a sadakan yadda na fada.
Na kai kallona gun kayan tare da fadin ummah nima a ban na rabawa kawayena mana a school har sun fara tambayana abin azumin su fa ?
Wani kallo ummah tayi min tare da fadin ji mun yar nan da zance kayan magidanta zaki kaiwa yan mata kuma ?
Hjy ai yan matan suna da iyayye a gida sabasu ai ko tunda ta tambaya in akwai sai a bata irin nasu Tani ta fada gashi can ki diba gobe idan zaki fita don ni duk bayarwa zanyi ga mabukata.
Sukaci gaba da maganan su ina bin kayan da kallo don ganin meye a cikin leda din dana gani ummah ce ta juyo take tambayana har nawa zaki dauka ?
Lokacin hankalina bai garesu Tani tace dani mamangida dake aike magana fa na juyo idon ummah yana kaina lokacin take kara tambayana mutum nawa zaki baiwa ?
Ummah zasu kai goma fa amma dai a binda aka ban sauran sai na basu wani abu ba zaki samu goma ba nace toh ummah ko nawane a ban na bayar.
Ki dauki shidda don ina son in bayar nan bayan layin mu don akwai masu bukata sosai a wanan layin ummah ko a barshine ki basu tunda kince suna da bukata suma.
Washegari har na manta da zancen na fita saigashi Tani ta biyoni da kayan a ciki katon buhu tana fadin ga kayan nan zan koma na dauko maki sauran.
But na bude ta zuba saura muka saka a bayan mota tayi min sallama nace ida na dawo zan ganta tashige tana min godiya.
Na isa school din na samu ba a shiga ba don har na rigasu hannatu shigowa ajin ina zaune suka sameni tana fadin gobe ne kawai ba zamu tashi da azumi ba don shi na tsaya na dankari abinci na cika cikina.
Ke kan kinji kunya yanzu duk shekara dayan da kikayi kina cin abinci sai yaune zakiyi na kankat ta kwashe da dariya muna haka malami ya shigo class muka natsu.
Bayan mun fito ne break na nufi wurin motana don i dan karya da ruwan zafin da aka hada min sai kwai dana zo dashi wanda Tani ke asubancin zuwa ta dafa muna don yaran dake zuwa makarantan.
A nan su hannatu suka sameni don tare muka fito ta tsaya magana da wasu na wuta bayan ta bude da niyar zama sai tayi tozali da kayan dake baya din aje.
Wanan kuma fa kayan meye zarah ta tambayeni na juyo na kalla tare da fadin sorry fa na manta in fada maki dazun su madam Asma nazowa dasu na azumi.
Meye a ciki ta fada tana kokarin budewa ta gananwa idon ta kwan ina tsiyaya ruwan shayin dake tururi a kofi nace ban sani ba nima wallahi na dai dauko ne na rabo a falon ummah nazo masu dashi.
Kaji manya ke nan ki dauko abu kice baki sani ba ruwan shayin na kurba kafin nace ban duba ciki nasan meye a ciki ba ta shiga budan kayan kafin ta dago tana fadin wasu madam asma gamu ?
Kaya shayine fa a ciki sai shinkafa zaikai mudu biyar nace OK kawai naci gaba da shan shayin da nakeyi abina ta zauna ta dauki flask din shayin ta tsiyaya ta jawo kwai tana ci.
Kamar sun sani saiga su madam din su uku matan auren department din mu sun jero sun dawo daga wurin sallah muka gaisa zasu tafi Hannatu ke fadin aiko mayana tana nema ku fa .
Suka juyo zuwa inda muke muka kara gaisawa dasu tace wai abin azumi ta riko maku shine kuma take jin nauyin da zata baku din don kada ku dauki hakan wani abu.
Haba dai keko mukan mun gode wallahi kaina yana kasa ban dago ba sai ku bari idan an tashi sai ku dauka a, a ki bamu abin mu yanzu abu a hannu shine mutum.
Hannatu ce ta mike ta dauko leda uku ta mika masu suna godiya da addua suka tafi kafin mukai class har wanan zancen ya yadu a class din muna shiga akayo min caaa wai ina nasu ban dai yi magana ba don ba zan iyasu duka ba ai ajin.
Wa yanda nayi niyar bawa sauran mutum hudu na mika masu har hannatu muka shiga mota muka bar school din saida muka dauki hanya na kalleta tare da fadin zaki gane gidan su master kuwa ?
Zan gane mana ai nayi zama a unguwar wurin kakana kafin ya rasu saidai shi yana ta bayan su kadan nace OK ki nuna mi hanya muje.
Akuyar nan fa tana nan saboda Akuyar zanki zuwa mu kai masu wanan kayan su nayi niyar kawai da wana tsohon makwabcinsu daya shigo din nan ok muje zan gane ta fada.
Da kwatance har ta kaimu gidan yana nan kamar yadda muka barshi mun dade a cikin mota muna shawaran shiga kafin mu fito da addua a bakina muka nufi hanyar shiga gidan tare da almajirai a bayan mu dauke da kayan.
Munyi sallama ba kowa a tsakar gida abin mamaki muna sallama idona na kan wanan akuyan ta mike tsaye tsam a daidai lokacin da zata fara wanan kukan natane tsohuwar gudan ta fito daga daki tana amsa sallaman mu.
Daga inda muke kamar matsorata muka gaida ita tare da tambayan ko Ahmed yana gida tace baya nan kuwa kallona hannatu tayi sai nace ga wanan kaka idan yazo ki bashi meeeeh har cikin raina naji wanan kukan akuyan mai daga min hankali.
Haba uwargarke bakin ma baki barsu bake nan bako fa rahamane a gida balle wa yan nan ai bakin arzikine su a kullun suka zo gidan nan koba kune na ranan nan da kukazo ba ta fada tana dawo da kanta ga kallon mu.
Ganin yadda na rike hannatu gam a jikina yasata dan murmushi tana fadin kai haba ai bata komai itama tana maku godiyane kusan dabba da sabo da mutane ai.
Hanne ko cewa tayi ai akuya kamar mutum take da fahinta wani lokaci sai su dinga abu kamar mutane don sabon su da zama ciki mutane da sukeyi ko yaushe.
Jinsu kawai nakeyi don kiris ya rage min na sake fitsari a lokacin don tsoro da tashin hankaki juyawa nayi da sauri tare da fadin sai anjima ai banyi nisa ba wanan akuyar ta kucce ta biyoni a baya sai ji nayi ana fadin subbahanallahi.
Juyowan nan da zanyi akuyar ce a bayana tana zagayena kace ta saba danine dama idan nayi nan tayi nan tana wani tsale tare da kuka kamar na rike tsaba a hannuna tagani.
Yaran nan da muka shigo dasu suka kama dariyata irin yadda na tsorace don akuya ikon Allah basu kiwone a gidan su ina fa kaka wana kilama sai a ciki mota take hango akuya ai don su din yan gidan masu garin nan ne ai.
A ina Amadi ya hadu da yar masu kudin nan tana fadi hankakinta na kanmu da akuya muna drama yaran nan sai kwasan dariya sukeyi.
Haba uwargarke ba tsaba ta dauko ba ga tsaba can idan yunwa kikeji mana kai ku kamata ku daure min ita a garken ta Dije ta fada jin hakan yasa akuyan ta kara matsowa kusa dani sosai tana dago kanta gareni kamar tana sunsunan kamshin jikina.
A zatona dai cizona akuyan nan zatayj amma sai naga sabanin hakan sai sun sunan jikina kawai takeyi tana dan sake wani gumji a cikin wani sauti da ni kadai nake jin shi wani iri.
Zarah ya ambata a bayan mu idona suna lumshe bansan lokacin dana budesu ba nanufi wurin shi da sauri na tsaya a bayan shi ina sauke numfashin wahala lokaci guda.
Haba uwar garke kada ki kada itama tunda tana tsoron hakan don Allah ki tafi a daure ki abin mamaki sai akuyan ta dago kai ta dan dubeshi kamar mutum ta dukar da kai kasa.
Haba uwargarke kina tsorata farar tumfafiya mai furen albarka baki baiyanan a wurin banza, zuwanta garemu alheri ya kawota wurin mu nasan kema farin ciki kike nunawa kan shigowanta mazaunin mu.
Dijece ke jera wanan kirarin lokaci guda haka kai kuje ku daure ta Ahmed din ya fada cikin bacin rai yaran sukaja akuyan ki suna turata tare da fadin ke ke ke yau sai kinsha daure a hannun mu sosai.
Zarah lafiya kukazo gidan nan ya kara tambayana saidai ya fahinci cewa ba a cikin hankalina nake ba lokacin don na gama tsorata ko lokacin.
Ya juya wurin hannatu yace hannatu ina kuka fitone kuka zo nan wallahi mun kawo wa kaka abin azumi shine ka ganmu nan yanzu.
Kaidai kaji yar arziki abinda ya kawosu ke nan sukazo muna da abin arziki haka na azumi wanan yar ta zamo silan alheri azumin bana zanyi shi da yar gwaunati ka kayan shayi kuma duk an hado muna dasu.
Sai washe baki takeyi tana bayani shi kuma ya daure fuska ganin yanayinda nake ciki yasa hanne fadin zamu tafi sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login