Showing 48001 words to 51000 words out of 304363 words

Chapter 17 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33315

fadin meye sunanta kafin in fadi ta amsa mai da yusurah ya dan rage tsawo yana fadin sunan ki nada dadi sosai.
Kafin ya dago yana kallona tare da fadin nice name naso su yarda muyi aure amma saboda maman jafar hakan ba zai samu ba a tsakanin mu.
They are telling me now wai na zabi Aisha ko Rukkaiya na aure mamadin ke ni kuma zuciyana ke yake so zarah ba suba don su din ba zabina bane zabin su mami ne hakan.
Gobe zan koma da safe in sha Allahu ina son ki dauki layina a wayan ki don ina son muyi zumuci a tsakanin mu har yayan mu nidake saboda kada alakanmu dake ya yanke.
Duk wani abinda ya sameki don Allah zarah na rokeki kirani zarah muddin ina raye ba zan taba barin ki wahala ba yadda suke nufi a duniyan.
Idan sun hanani auren ki ba zasu hani zumunci dake ba na sani don ba zasu taba sanin ina taimakoki ba wanan alkwari haka nayi maki zarah.
Ki natsu kimaida hankali ga karatun ki don ki zama wani abu a cikin rayuwan ki yadda zaki taimaki mahaifiyar ki da yan uwanki nan gaba ina maki fatan alheri a rayuwan ki don sun rabani dake yanzu.
Ki mi alkawarin zaki cika min burina na taimakonki a kaina nan gaba don ba karamin shiri akewa rayuwan ki ba zarah shine dalilin da basu son kasancewana tare dake a yanzu na gama fahintar komai daga garesu.
Saidai basu san cewa kedin kinci sunan ki na Zarah ba kin daga sama fiye da diyan da suke son su dago din na barki lafiya sai in Allah ya kaddari haduwan mu ya miko min katin wayan shi da address din shi na dago ido da hawayen daya fara sauko min a idona ina kallon shi.
Suka zubo lokaci daya dan murmushin yake da baikai ciki ba ya sauke a fuskanshi yana fadin don't worry take care kada ki bari su san muna tare ina taimakon ki.
Daga haka ya sake hannun yusura yana fadin bye ya tafi na bishi da kallon mamaki har ya shige inda dakunan samarin gidan suke inda a can ne aka saukesu suma.
Cikin wani irin yanayi na shiga gida Allah ya taimaka ummah bata falo na samu daman shigewa ciki na fada saman gado ina sake hawaye masu yawa.
Ban taba soba ban kuma fara ba saidai kalama brother Dele din sun tsaya min a raina sosai don na kasa raba dayan biyun kan abinda yake kokarin son in fahinta daga zancen shi din .
Washegari hargowan su mamane ya tayat damu daga barci wai Dele ya bace tun asubahi an nemeshi a rasa kuma ya tafi da kayan shi bai fadawa kowa inda zai tafi ba.
Dole ba shiri suka shirya tafiya suma a ranan da cewa zasubi bayanshi don me yuyuwa ya koma lagosne ya barsu nan su zaman me zata zauna yi a garin mutane bata san halinda dan yake ciki ba .
Dole muka fito wajen nasu da zasu tafi ita da drivern su da danta kabir mama sai waya take faman yi da Abba tana sanar mashi halinda ake ciki.
Abbah din a karshe yace su tafi da mama suzo nan sokoto subi jirgi zuwa lagos inyaso sai driver ya koma da motarsu shi a nan mama ke zage zage tana fadin akan wata yarinyar banza can yaro yana neman halaka kanshi.
Duk wanda ke wajen zai fahinci a fakaice mama ke sake magana da wani a wurin duk da bata fito fili ta ambaci sunan wanda takeyi dashi ba wurin amma kowa ya gane hakan.
Kara lafewa nayi jikin motan danake tsaye kusa da ummah da itama ido ta zubawa mama dake faman sakin magana a cikin habaici irin na kwararu iya habaici.
Cikin gida suka kwasa suka koma suka barmu a tsaye waje yayin da yaranta ma suka mara mata baya lokacin guda kabir ne daga inda yake tsaye yana magana da drivern su ya tako zuwa inda nake tsaye ina rike da hannun yusura.
Baby kema kin damune don nasan ya fada maki komai jiya ai don na fito na biyo bayan shi na sameku tare saina koma ciki.
Amma kada ki damu fa ban fadawa kowa hakan ba do kada na jefaki cikin matsala irin nasu maman jafar gaskiya zan fada maki matan nan bata son ki keda maman ki.
Ta sani sarai brother Dele ke yakeso kamar yayi hauka amma yanzu munzo kan zancen ku ta dauko zancen hadi da yarta ta kawo mashi shine dalilin da yayi fushi ya tafi ya barmu nan.
Amma kinsa da ace nine yau da sun gane basu da wayau a garin nan amma shi yana da sanyin hali sosai kinga ya tafi ya barmu a na ita mami tasan halinshi idan yai zuciya zai iya barin kasa nan ga baki daya yanzu haka shiyasa kikaga sun tayar da hankalinsu haka.
Ummah ce ta juyo inda nake tana fadin dauki Yusura mu koma ciki ta kalli kabir tana fadin Allah ya kaisu lafiya ya amsa da amin nima kallonshi nayi ya rigani fadin ban layinki sai mu djnga gaisawa.
Na karanto mai number na yayi serving mukayi sai watarana na juya na shiga vida don ummah har ta shige ko a lokacin ita.
A falo na samu ummah zaune ranta a bace sai hankalina ya tashi sosai ganin yanayin ta kallona tayi tana fadin maamah zoki zauna kuma ki fada min gaskiya don banson karya kin sani.
Wallahi umma zan fada idan abinda na sanine zaki tambayeni a kanshi tace dakyau me kika sani game da tafiyan yaron nan kuma meye hadin ki dasu ?
Ummah ni babu komai a tsakanin mu ku ban san komai a kantafiyan shi ba sai jiya daine yake ce min na kawo duk yadda mukayi dasu tundaga farko har wanan maganan da kabir ya fada min a waje na fada mata komai.
Oh wanan dama take kullawa naso in fahinci hakan amma sai na dauka kawai hakan shakuwane a tsakanin ku amma ai ita hjy mama din tayi kuskure tunda ta mata da Allah ke komai ga bawanshi.
Idan shi Dele din ya kasance mijinki ita bata isa ta hana hakan ba sai anyi balle ban fatan hakan a gareki a samu abin fadi cewa kin kwaso bare kabila kin kawowa yan uwa.
Ita zata hada ita kuma zata dawo tana kulla sheri a cikin dangin ki don a samu abin zagi da barnan suna a garemu ni fatana kullun shine ubangiji Allah ya baki miji mai albarka mai mutunci da sanin ya kamata ba tarana arziki ko kwadayin duniya ba maamah.
A, a ki natsu kiyi karatun ki don gaskiya Dale ya fada maki nan gaba dakene zan fara alfahari a cikin gidan nan shine dalilin maman ku nason dakushe rayuwan ki kota halin kaka.
Ummah me nayiwa mama haka yanzu take jin haushina ba yanzu ba kawai tun haihuwan ki take jin haushin ki maamah bado komai ba kuma don kawai kin kasace yar kishiyanta da bata kauna wace tafi tsana yanzu a duniya.
Ummah kin mata wani abune haka me kuwa nayi mata idan ma yine itace tayi mun tunda a gidan nan tazo ta sameni ban daki zafi da ita ba akan mijina sai itace zata dauki zafi dani daku har yakai yanzun bata kaunar taga mun rabi Alh ko kadan.
Tanice ta shigo falon jiki a sanyaye tana fadin sun tafi har da hjy maimuna wai tare zasu haka ya dace dama ummah ta fada kafin tani din ta sake fadin amma hjy ta fada maki zasu tafine ?
Allah dai ya tsare hanya yasa su ganshi a can din shine fatan mu yanzu mu don hakan ba karamin tashin hankali bane tunda ba a san halinda yaron ke ciki ba yanzu duk inda yake.
To wai ina zashine ko ya taba zuwa arewane dama ni shi nakewa mamakin inda yaje ga hjy kuma sai wani zance takeyi a dunkule wai daman haka akeso dasu aga bayansu, towa ke son ganin bayan nasu take nufi ?
Wai Amadi kasan dabbobin nan ganinka yasa suke wanan kukan haka toke Dije ba kuna wuni gida dasu ba ko wani lokaci suna ganin ki ni kuma sai wanan lokacin idan na shigo.
Haba dai wani sabon abu dai suka samu hakan gashi uwargarke gabadaya tun dawowanta gidan nan sam ban gane mata abubuwa takeyi yanzu dabo dabo kamar , , , ,
Shiru tayi domin idon ta daya sauka kan uwargarke irin kallon mutum uwar garken kemata a take taji tsikan jikinta ya tashi lokaci guda sai gabata ya dinga faduwa.
Mikewa tayi tana fadin innahu sulaimana wa innahu bissimillahi rahamanin rahim Amadi nikan nayi nan idan ka gama ka sameni a daki ta fada ta wuce sa sauri zuwa dakin nata tana sake labulen kofan da sauri.
Ranan abinda bai taba faruwa ga Dije ba shine ya faru don Dije ta kwana a wahalce tana mugun mafalki da tsoro a zuciyar ta har gari ya waye kiran sallah asalatu a kunnenta tafito tayi alwala ta koma daki don sai ya kasance tana jin tsoron gidan nata a ranan.
Tana jin fitowa jikan nata dafa dakin shi sai dai batayi yunkurin ta sake fitowa ba a lokacin a inda tayi sallah ne barci ya dan dauke ta bata falkaba sai da gari ya haska ko ina rana ya fara fitowa lokacin take jin motsin mutum a cikin gidan.
A hankali ta mike zuwa wajen bata yarda ta fito gaba daya daga dakin ba lekowa tayi daga ciki sai ta gango Amadi ne ke faman wanke kayan sana,anshi yana shanyawa a rana.
Hakan yasa ta fito tana fadin a, a yau ba bokon ne ko ka daga kafan ga zuwane yau din yana buga kayan dake hannunshi don su mike yake fadin .
Akwai Dije kawai na tsayane in wanke wa yan nan kayan daga nan sai in dan fita da wa yancan dana kulle amma lafiya kika kwanta haka har wanan lokacin.
Kai dai bari saita daga ido ta kalli garken dabbonin ta kuri idon uwar garke a kanta hakan yasa tace munaga rasulu Annabi sidi farin gani mazon Allah.
Shiru tayi har yaje yayi shanyi ya dawo yanayin da yaga Dije din acikine ya daga mai hankali yake tambayan ta wai kuwa yau lafiya kike Dije ?
Lafiyata kalau barin dan je nan makwanbta tunda kana gida na samo muna dan kamu nazo in kashe muna kunu yau a gidan mu karya dashi.
Idan da saura ki gyara kawai Dije ba sai kin wahalal da kanki ba ai kayyah yau ban jin cin tuwon kunun dai nafi son insha yau tana fadin hakan ya tura hannu cikin wandon dake jikin shi yana lalubo kudi ya dauko dari biyu ya mika mata.
Tace barshi akwai canjin jiya daka ban suna nan banyi komai dashi ba zan sayo dasu ta fice da sauri daga gidan yaci gaba da wankin shi.
Wandunan daya dauko zai tsoma a ruwa a daidai lokacin uwar garke ta aza wani kuka dayasa ya kallota inda take din ya tsame hannun shi ya nufi wuri su yana jaye masu igiyar da suka harde dashi ya kara masu abinci da ruwa duk lokaci guda ya juya ya koma wurin wankin nasa wandon ya kara dauko wa ta sake wanan kukan nata irin na farko.
Zai aje wandon hannun shi yakai daidai aljihun wandon yaji abu da dan karfi a ciki ya tura hannu a cikin wallet irin na maza mai kyau ya zaro a cikin wandon .
Cikin mamaki yake kallon wallet din kuka sosai uwar garken tayi ya juya ya kalleta sai yaga ta koma ta kwanta lokaci guda hankalin shi ya mayar kan wallet din ya dauraye hannayen shi ya fara budan wallet din.
Kudine a ciki irin na kasan waje da sai a photo yake ganin su sune a hannun shi ya ciro da sauri yana duba kudine masu yawa sun kai guda goma a ciki sai dan katin sheda dake da rubutun wani address din kasan waje sunan maishi da lamban wayan maishi a cikin katin.
Ya karanta wana address din yafi a kirga kafin ya aje wandon a gefe daya tare da mayar da kudin yadda ya gansu ciki yaci gaba da wanke sauran kayan yana dubawa.

ZAINAB IDRIS MAKAWAAHH, HAYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃👠👜💍👡👛 🥿👘👗🧤

INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION.
ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M A C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝
TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI.
YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏

https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,,,,,,,
1️⃣6️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Allah Allah yake ya gama ya fita ya koma wurin maikayan yaji ko yaya zasuyi dashi kan wanan kudin akarshe dole ya maida hankalinshi wurin abinda yakeyi din.
Dije wace ta dawo wurin malam tanimu da dan kullin hayakinta data karbo a wurin shi daki ta shiga ta aje ta fito ta gwama wuta duk abinda takeyi hankalinta na kan uwar garke dake kwance tana binta da kallo ko ina tabi.
Ruwa ya diba ya zaga ban dakin har ya fito yazo ya canza kayan jikin shi lokacin ya fara jin kamshin hayakin da Dije ta buda yana tashi a cikin gidan.
Da farko ya dauka hancinshine ke shako mai kanshin a makwabta kafin ya tun kari kofan Dije din yaji kamshin a nan yafi tashi sosai ya fara dan sunne sunsune.
Mikewa yayi tsaya da kyau yana fadin Dije wai me nake ji yana fitowa ne haka wai kai dan Allah ka faye surutun tsiya wallahi ta fada a hasale sai yabi kakan nasa da kallon mamaki a wurin.
Kayan ya daure yadda ya saba kafin ya leka wurin Dije yana fadin tau Dije ni zan tafi ga wanan sai ki kara yana miko mata dari biyun daya bata da farko.
Amadi shigo daga ciki ta fada a sanyaye ya dago yana mamakin tsohuwar ya fada dakin don ganin bakon yanayi a fuskanta na damuwa daya nuna hakan gareta.
Dije lafiya kike kuwa Amadi ba lau ba gidan ya canza tun dawowan uwargarke gidan nan nake jinshi ba daidai ba sai jiyan kuma na kara tabbatar da hakan.
Dije uwar garke kuma tace kwarai uwargarke dai Amadi daka sani yanzu kamar ta hurhura ba ita bace a gida nan yanzu don wanan halinta ya bambanta da wacan.
Dije don me kikace hakan yanzu tace kwarai don tana bamu alama saidai ganewa ne bamuyi da hakan ba Dije don Allah kada ki firgitani ya fada ya juya yana kallon uwargarke dake kwance tana tuka tana lumshe idonta.
Bayanin komai daya faru ta fara mai yace gaskiya zancen ki dutse nima naso gane hakan Dije don ko yanzu fitan nan naki saida ta ban wani alama ya fadawa wa Dije din komai har kudin daya tsunta din tace kaji ba na fada ma akwai lauje cikin nadi wanan lamarin gaskiya .
Koma dai meye Allah ya gani bamuyi niyar cutar wani ba kada Allah yaba wani ikon cuta muna muma ni zan tafi ya fada a karshe ka kula don Allah yace in sha Allahu.
Ba zaka karya bane yace ki bari zan karya a waje idan na fita don yau kan ba zancen makara bane a wurina don nasan na rasa darasin safe kan.
Har ya fita ya dawo yana fadin Dije ki rike addua kada kiji tsoron komai in sha Allahu inma ta hurhura Allah zai karemu ga ko meye tace ai wanan hayakin dana karbo tunda na turara naji faduwan gaban ya daina.
Ki dai hada da addua shine mafita yafi hayaki kaifi duk kikaji wani abu ki karanto addua tsari a wurin Allah tacw ba komai ai tana kanyin hakan itama.
Amma kadai yi shawara kafin ka koma wurin mutumin ka samu wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login