Showing 126001 words to 129000 words out of 304363 words
jikan magabatan mu kasa Aljanna ce makomar duk kan musulmai albarkacin kalman La,illah ha,illah Muhammadan rasulunlillah ya cece mu Amin.
Allah ya taimaka tafiyan dare yayi koda ya biyo layin su ba mutane sosai a lolacin don haka ba wanda ya ganshi dan abinda suke rufe gida dashi ya tura gidan ya bude ya shigo.
Ya samu Dije ta kwanta a lokacin yayi shawaran ya kwankwasa mata kofa sai kuma yaga kada ya tashe ta daga barci don haka yayi shawaran ya aje kayan tsaraban daya sayo din a kofan ta kawai.
Bayan ya aje ya juyane ba tare daya kulaba yayi karo da kwanon data kife daga gefen dakin daga cikin dakin yaji muryan ta tana fadin wani na nan ?
Ido ya dan lumshe kafin yace nine Dije Amadina ya bata amsa daga inda yake tsaye Dije da taji muryan Amadin a bazata tayi wani tsale ta mike zaune tana sake fadin wanena shin ?
Amadi kaina kamin gizo ko kunuwana na ka min karya haba Dije ga muryana kina ji zakice karya kuma ko barci kika farane wai ?
Ji yayi tana kokarin bude kofan nata daga ciki yasa shi tsayawa ya jira ta bude tako bude din tana fadin Amadi ina ka shiga haka kabar gida lokaci mai tsawo haka ne ?
Missa kayi tahiyar ka cikin duniya kabbanni nan ni kadai shin baka tunanen halin da nii shiga bayan tafiyan ka ?
A lokacim ta karasa bude kofan ta fito don ta tabbatar inshi dine sukai arba yana tsaye daga kofan saye da taguwan shi da wando baki kaida ganin shi kasan yayo tafiya mai nisa a lokacin.
Ina kakshigane danga tahiya haka mai tsawo baka fadawa kowa inda kakje ba abinda baka tabayi ba a ruwanka barin gida haka danisa.
Buhun tsaraban shi ya nufa ya dauka yana kokarin shiga dashi daki ta jaye ta bashi hanya ya shiga da kayan cikin daki ya aje kafin ya dago ya fito yana kokarin juyawa don kayan daya bari waje ya dauko sauran yaji muryan dije din na fadin.
Shin ina kak shiga hakane ina magana kayi shiru daniya haba Dije kin san dai bani zuwa wurin banza ko don ban taba abin banza ba a rayuwana.
Allah baka hakkuri amma ka dau alhakin mu dakka daga muna hankali kwanciya asibitina kawai a banyi ba kowa gari ya dauka wani mugun abuna yassameka.
Dauri ka fada muna inda zakana kaga sai mu sani da kyar ya iya budan bakinshi yace kuyi hakkuri ban dauka zan dade bane haka nima don tafiyan da niyar kwana biyu niyishi ko uku sai ya kasance haka.
Awo dama tahiya ita tagaji haka kafin kayitana kake da ita da zaran kayita ko ita addakai badai an dawo lafiya ba ta sake tambayan jikan nata don ganin rashi babu dadi a lokacin.
Bai bata amsa ba ya kara shiga da kayan ciki tana yada mai haske yaga inda zai aje kayan ta kara fadin dauri ka bugo wanga abin zamanin ko a makwabtana mu sani.
Ki kwanta saida safe zanyi sallahna yanzu Dije ya fada yana daukan buta ya nufi bandaki bayan yaji akwai ruwan da zai isheshi amfani a lokacin.
Saida ya kewaya ya fito har lokacin Dije ta kasa shiga daki ta kwanta kamar yadda yace din da ita ya duka ya fara alwala yaji tace kaci wani abuna ko a hanya gashi yau ban dahwa komai ba a gidan .
Jin hakan yasa ya dago kai da sauri yana fadin saboda me dije babu abinda zaki dahwane ko me ya tambayeta cikin son jin abinda zatace din dashi lokacin.
Sai yaji tace kona dahwa ma baci zanyi ba shiyasa na hutar da kaina da dahuwan saidai in kai dan kwano in sayo in dawo gida wani kuka yaji dayasa ya firgita.
Ba kuma bakon kuka bane sai sauti muryan uwar garke haka yasashi kaduwa har yaji gaba shi ya fadi lokaci guda da sauri ya karasa alwalan ya mike yana lalubo yar wayan shi daga cikin aljihunshi.
Yana haskawa ga dabbobin su biyarne a wurin yagani a daure kuma tabbas uwargarkene wanan a madaurin ta ta mike tana kiwo.
Dije yaushe akuyan nan ta dawo gidan nan daga daki dije ta amsa mai da fadin kaidai bari dan albarka aini akuyan nan ta wuce sanina yanzu saidai ido da addu,a kawai.
Akuya sai ta kwasa ta tafi sai lokacin da taga dama ta dawo ni na kasa gane me wanan yake nufi da hakan ko wani gidane ta samu take labewa ko wani ke kamata idan taga sarari ta gudu oho ?
Bai iya cewa komai ba sai addua da yakeyi a zuciyan shi lokacin don baima san abinda zai fada ba game da uwar garke din data zama mai waibuwa a garesu yanzu.
Haka ya ja kafa ya shige dakinshi da a yanzu yaji shi daban sai zafin daya doki fuskanshi haka ya daure ya tayar da sallah bayan ya dan kakkabe wurin yayi shafa,i da wuturi ya samu wuri ya kwanta zuciyan shi cike da tunane kala kala.
Ban samu ganin su yaya musa ba don tun dana shige daki ban fito ba sai washe gari inda na tashi na samu su yaya din a falo tare da Abba suna magana.
Suna ganina ko wanin su ya washe baki a cikkn mamaki da sauri na nufesu na durkusa ina gaidasu ya musa ke fadin dama kina garin nan ne yan mata ?
Tana nan tazo hutu kasan mama da son zaman abuja dama dolene ya kaita gusau ta zauna dama don rashin mace ce a gidan yasa ban daukota duk hutu don tafi sabawa da nan din.
Nima nashayin wanan tunanen cewa na samu lokaci in daukosu dukan su har ummah suzo nan su dan kwana biyu ko din makwabtan dasuke damuwana da tanbayan su idan sun gani.
Ai yanzu tana jin dadin garin tunda ta hadu da wani dan iskan yaro daya fara hure mata kunne a yanzu Abba ya fada daga inda yake zaune.
Gaba dayansu suka kalloni sai ya jafarne yayi saurin magana yace haba dai Abba dama ace su Aisha ka fada zan yarda don sune rawan kansu yai yawa.
Gata dai wanan din yana nunani da cokalin dake hannunshi lokacin yace shiyasa naga gara da anyi hutu ta dinga zuwa nan kusa dani zaifi.
Ya musane ya kalleni yace wai hakane kanwata da sauri na girgiza kaina alaman ba hakana bane daga inda Abban yake yai min wani irin tsawa yana fadin.
Karya zan maki kome ku diba yarinyar nan wai har zataje ta dauko min wani fakirin yaro mara asali har yana zo min har kofan gidana don uwarta ta daure mata gindi yin haka.
Abba be cool don nasan haka kawai Zahra ba zatayi abinda bai dace ba kuma ummah ta sa mata ido kila dai wani abin ne ya hadasu daban ko ?
Ya juyo yana ajiye cibin dake hannunshi da yake shan tea yace zan zauna da ita inji abinda ke gudana Abba no ai basai ka zauna da itaba don naga tana son ja dani akan wanan yaron dam matsiyatan.
Ko zuwa kanon nan da sukayi ace wani dan mutunci yazo neman ta amma yarinyar nan ta rufe ido taci masu mutunci dagashi har ita hjy karima din karshe ma taso hadata da yan uwanta a kan maganan fada.
Wani irin dagowa nayi na kalli inda Abban yake cikin mamakin jin abinda ya fada din lokacin kafin nayi kasa da kaina hawaye yana zuba min a idona mai nuna alaman kazafi akaimin ga hakan.
Abba yaci gaba da fada inda yake shiga ba nan yake fita ba sai ya musa ne ya mike ya kama hannuna zuwa dakina don nan yaga na fito lokacin.
Har ciki ya shiga dani ya zaunar dani saman gado yana fadin ya akai hakanga zahra a sanina kedai ba mai rigima bace zahra ga kuma Abba yanzu yana fadin zance mara dadi a kanki ?
Da kyar na iya dago kaina don jin ya sake maimaita min tambayan nace wallahi Allah yaya ba hakana bane nan na kwashe komai na fada mai har da zancen mommy din ban boye mai komai ba.
Zuwa lokacin ya jafar ma ya shigo dakin yace shi yaron Abba ya fada min wai baida baba ke nan shegene kome zahra ?
Kai na girgiza mashi nace ba gaskiya bane yaya last da mukai waya dashi ya fada min yana taraba zaije gun mahaifin shi ne.
Da baida baba aiba zai fadi hakan ba kuwa ya musa ya amsa daga inda yake zaune is OK ya jafar ya fada ki bari zanje Zamfara yau zan zauna da ummah akan zancen.
Da sauri na dago kai ina fadin don Allah ya jafar ka wuce dani wanan matar makirace sosai bana jin dadin zaman gidan nan sam wallahi.
Idan nayi hakan Abba zai dauka wani abune no kaje kawai zanzo da ita zuwa jibi don na fahinci wani abu cikin zancen zahra din ni zanzo da ita gida ka wuce kawai zamuzo tare ya musa ya fada.
Sai safa da marwa takeyi a cikin dakin nata kafin can wayanta ya dauki kara kobata duba ba tasan me kiran nata don shi ta sakawa irin ringing tone din wani wakan larabawa ne da akewa habibi.
Ta dauka cikin saita muryanta yake fadi daga bangaren shi kizo ga sakon yasir an kawo ta karba da gani fitowa saida ta dan bata lokaci ta nufi falon.
Mijin nasu ne a zaune tare da amininshi Jabbi sai tellan yaranta maza dake gefe daya a takure ta shigo falon cikin isa da izza da takama kamar bataga jabbi din ba ta fara fadin.
Yau Isah tellane gidan eh hjy naji ance kunzo shine nace barin sheko in kawo dinkin nan nasu oga yasir don yace akwai wanda zaikai mashi can idan na kawo maku.
Eh nima yayi min waya kwanaki idan nazo na karbo mashi dinkin yana cirowa yake fadin kai hjy ashe ana kama a duniya haka ?
Wallahi shekaran jiyan nan wani matashi yazo shegona sai ka rantse da Allah yasir din gidan nan ne sai dai idan yai magana zaka gane bashi bane.
Wani kallo jabbi dake gefe yayi mashi amma ya basar don maigidan ya dan daga a lokacin ya shiga ciki zai daukowa aminim nasa sako tellan ke fadin haka.
Mikewa tayi tana daukan kayan tare da fadin jeka zakaji alert tayi tsaye har saida taga fitanshi daga gidan ta juya ta shige ciki sai jin wani abu takeyi a zuciyanta na tashin hankali da fargaba.
Kayan ta jefa a gefen gado ta jawo waya ta fara neman layin wata yar uwanta dake Gembo cikin tashin hankali take fada mata abinda ke shirin faruwa dasu.
Mikewa tayi kamar a gaban yar uwan nata take ta soma fadin wanan karyane wallahi irin abinda mukayi muka bizzine za ace yanzu wai yaron nan yazo ya baiyana.
Wanan ma karyane wallahi in ko har haka sai mu canza mu koma wani hanya me zamu tsaya jira dama kin daiji abinda ake fada cewa muddin ya baiya zai doke duk zatin da taurarin diyan ki ga baki daya zai dushe.
Shi nakewa tsoro ya Lantana idan ina kaunan mutuwana ina kaunan yau in bude ido inga wani da a gidan nan da sunan dan Alh ne shima koda kuwa diya macece ita bana kaunan hakan.
To kingani inda mukaje aka bawa kare mahaifar wanan gajan kishiyar taki aka daureta can zamu koma mu kara matsesu a saka masu duhu a tsakanin su har abada.
Don haka kiyi dubaran da zakiyi ki fito gobe mu sanu muje wanan kauyen don kinsan wuyan zuwa ke dajin arnan nan don hawan dutsen nan dake wajajen .
Na sani idan ba dole ba wallahi ban son zuwa wanan wajen saidai ba yadda na iya tunda ina son biyan bukata in sha Allahu gobe din dai zansan yadda nayi nafito muje wurin.
Allah ya kaimu ta fada suka dan taba hira aka kashe wayan kowa ya zauna yana cicika a zuciyan shi tare da tuna irin kudin da suka kashe a baya.
Yallabai ina zuwa zanje in dawo yanzu jabbi ya fada yana saurin tashi daga inda yake zaune Alh ya bishi da kallon mamaki yana tunanen inda zaije haka da sauri har yana tunanen ko lalura ya kamashi.
Allah ya taimakeshi ya samu wanda yake son gani din a lokacin har ya tare mashin zai hau ya tare shi don haka ya tsaya .
Ya sanshi farin sani don customer shine a wurin dinki sosai bayan sun kara gaisawa ne ya dan duba baya kafin ya fara fadin.
Ka gafarceni kan maganan da nake son muyi yanzu in har hakan ya zama kamar katsalandan a garejku don zakaji maganar kamar ina son maka kutse a cikkn sa yanzu.
Kan isa tella din ya daure kafin yace Alh lafiya dai ko don ban dahinci inda zancen ka ya dosa ba yanzu yace eh hakane gaskiya ba zaka gane ba sai na fada.
Dama game da maganan nan danaji kana fadawa hjy shine a yanzu na yaron da ka gani sunyi kama da yaron wurin Alh don Allah ko ka san inda zamu sameshi.
Kallon mamaki isa din yai mashi kafin yace dashi Alh wallahi ban sanshi ba nima haka kuma ban san daga ina yake ba illa abinda na sani shine.
Sun kawo dinki shagona munyi dasu su dawo gobe jumma,a su karba da karfe hudu na yamma shine kadai abinda na sani game dasu din.
Amma bayan haka bansan komai a game dashi ba wallahi zaka taimakemu don Allah nan dai ya fada mai abinda yake son yai masu na taimako kuma iya shi yasan da wanan zancen ya kama bakin shi.
Insha Allah in har ya yaimaka masu akwai goron da zai samu kuma ba zasu taba yarda hjy tasan da zancen ba don kada su hana mashi hanyar samu daga gareta da diyanta.
Basu kai ga kare maganan ba kiran hjy ya shigo a wayan isa din ya dauka ba sallama ta fara fada dashi kan baida hankaline ko wayau zai fada mata magana irun haka a gaban wani.
Hakkuri ya fara bata saida kyar ta yarda tayi shiru tare da fadin to ka iya bakin ka don nasan wanan munafukin zai bincike ka akan maganan nan watarana duk daya nuna ba komai a hakan daya nuna a falon dazun yace insha Allahu zaiyi yadda tace din.
Kallon juna sukayi ya kashe waya ya dan murmusa yana fadin aina fadama wanan marar akwai abinda take boyewa wanda bata son asani.
Sun dai gagauta tsayar da zancen sukai sallama ya tafi shi kuma ya juya ya koma ya samu Alh yana fadin ya dan kewayane sukaci gaba da hiransu a wurin.
Hjy ta fito kamar tana neman wani abu a lokacin shi jabbi ya gane me take nufi da haka yai kamar bai fahinci komai da hakan ke nufi ba.
Kamar yadda suka shirya da isa din hakan ya faru bayan dan bayaro yazo yake tambayanshi ina abokin shi yake fadin ai bayanan ya koma garin su ko.
Daya karbi dinkin ne ya hau mashin shima ya hau yabi bayan shi har zuwa unguwar su dan bayaro din yaga gidan da yashiga din.
Ya juyo ya dawo shagon shi ya zauna ya kama bakinshi har zuwa tashi ya samu wuri ya kira wayan Alh Jabbi yai mashi bayanin unguwan da siffan dan bayaro din.
Yai mai godiya ya kashe wayan yana kiyasta yadda zai bullo idan yaje unguwan don wanan lamarin yana son taka tsantsan a cikin sa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
4️⃣3️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Ya musa ne a gaban Abba zaune matarshi tana gefe daya zaune bayan sun gaisa ya kalli Abban yana fadin yau zamubi jirgin sha biyu zuwa sokoto na buga waya a turo mota azo a daukemu.
Kaidawa ke nan naga jafar ya tafi tun jiya dani da zahra zan mayar da ita gidane ya fada kai tsaye ba tare da jin komai ba.
Abban ya kalli hjy karima din yana fadin har ta gama hutun ke nan zata koma kafin tayi magana ya Musa din yace eh zata koma don next monday zasu shiga school.
Abba ya kara kallon hjy karima din sai cewa tayi amma ai naga bashi ya daukota ba ya kamata ko in san cewa zata koma in mata shirin da zan mata din a bangarena.
No ku barshi ba sai kun mata wani shiri ba ai ya mike yana fada fuska daure tare da fadin