Showing 294001 words to 297000 words out of 304363 words
bawan Allah akwai saukin kai sosai wallahi ni kafin yazo yadda na dauka wani mai zafine shi ai yadda ake bada labarinsa .
Kai yana da zafi amma sai ka tabashi gashi kuma da ka ganshi nan kana masa kallon yaro ashe babbane wallahi ni shedace don akwai shegun a boye wallahi nunawa kawai baiyi.
Ina daki kwance a inda na idar da sallah nabi sanyin ties nakai kwance a kasan don na danji saukin yadda nake jin kaina a lokacin Bannah ta saman gadona tana tsalle tsalenta ita kadai Amir kuma ya haye jikina yana doki hakana dole na kyalesu duk da sun dameni ina son hutu.
Amma gudun kada su fita su Asmau na gidan yasa na barsu a nan wajena suna wasan su a lokacin har hannatu na kirani muka buge da wayana muna zancen jikin Abba da ita a cikin wayan.
Kamahin turaren sa daya daki hancina tun kafin ya karaso yasa na furta daddy har yaran sukaji suka dauki ihun daddy a cikin murna ya turo kofa ya shigo yana cabesu ya bini da kallo.
Kokarin mikewa nakeyi zaune da kyar daga inda yake tsugune ya rungume yaran ya zubo min ido yana fadin yayane madam na ganki a kasa kwance haka ?
Ko yau kuma kwanciyan kasan ne ya taso maku kuka zube a nan din murmushi na dan sake nakai zaune tare da jawo gyalen rigan dake jikina dana daura a kaina yake zamewa na gyara ina fadin na kwantane ko zanji dadin jikin nawa nan.
Ai naga alama ya fada yana mikewa tare da yi min wani irin kallo a lokacin nace ka dawo lafiya na fada ina dan murmushi don irin kallon da yai min din a lokacin ni kadai nasan fassaranshi a zuciyana.
Zama yayi bakin gado saidai ya mayar da hankalinshi ga yaran lokacin hakan ya bani daman samu na mike tsaye fita nayi don in dauko mashi ruwa a falon na samu har su Asmau sun wuce ashe.
Dakin Dije na leka ina fadin dije maigida ya dawofa tana kishigide da casbaha a hannunta tana ja tana gyangyadi ta zabura tana fadin Alhamdullahi ya iso lafiya ko ?
Na amsa mata sama sama na dauki ruwa da cup a kitchen na nufi daki dashi na kai masa muka hade dasu zasu fito hakan yasa na juya falo na bisu ya zauna a doguwar kujera yaran suka dane jikinshi suna manne dashi har na tsiyayya masu ruwa da kyar suka barshi yasha wai suma zasu sha ruwan yana kokarin basu na hanna ya dago min hannu .
Haka yasa na koma gefe daya ina kallonsu a raina nace mugun gado son diya kamar rayuwa shiyasa inna take da matsala ai mutun ya dinga nuna son dansa kamar rai.
Yes rainane aiku don wa nake wahala yanzu ba don kuba ya bani amsa yana miko min kofin ganin yadda na hade raina kicin kicin a lokacin.
Nasan me nakeyi zahra kada ki dauka ina son yarana da yawa idan ban kulaku ba kema abin bai maki dadi ai ya fada yana kai jikin shi a makarin kujera ta baya ya lumshe idanunshi a hankali.
Nace yanzu ni mena fada kuma don Allah bai bude idanun nasaba yace nasan tunanen da kikeyi ai ashe ka iso dije ta fada suna fitowa da Aisha dake masa sannu da zuwa ya amsa da na iso dije kuna lafiya tace Alhamdullahi yaya hanya ya kuma mai jikin can da wurin mahaifin naka koda yake munyi waya ma da ita maman naku tace jiki da sauki ai sosai akwai cigaba yanzu sosai.
Dije ai dama rashi kesa a bar mutum har ya halaka a gida amma in kwana bai kareba inda hali magani ai yana inda yake har yanzu ai suna kan masa gwajine su gano ainihin abinda ke damunsa yanzu.
Ai an godewa Allah tunda akwai kudin yanzu da haka zai hallaka a banza cikin kasan nan ana masa canfe canfen ciwarwutan banza a kansa da zai kara dagawa mutum hankali.
Ke baki koma ba ashe yake tambayan Aisha da take kaiwa zaune tace ina nan ai tare da dije muna kwasa nace Asma ashe sun tafine ina daki ban sani ba ?
Tace ai dama gulma ya kawota koma ya akayi ta gano gidan nan oho ni nayi mamaki dana gansu wallahi don ban dauka tasan gidan bama.
Au na zata kece kikayi masu kwatance ai tace a a wallahi ban fadawa kowa ba koda naje kwasan kayana inna kamar gaba takeyi dani ma don ko magana batayi min ba har na fito.
Ai naji Asmau ta fara sakin magana yasa na koma daki don ban iya magana yanzu ta lauye mutum baida wuya taje tacewa inna ga abinda akai mata kuma yasa na koma daki na kwanta.
Wayanshi ta dauki kara ya ciro daga aljihun wandon shi yana fadin ya salisu kaga wurin ko sai wanda ya kira da salisu din ya tsaya yana masa bayanin yadda suka kwasa dasu inna din a lokacin mundai ji yana fadin a,a a,a har ya kashe wayan bai iya magana ba.
Sai cewa damu yayi dije yar iskan yarinyar nan Asmau saina karkaryata kita koma gidan ubanta yau wall, , , kai kai kai kada ka rantse don Allah don kasan ba abu bane mai yuyuwa don inna bata bari kadaiyi mata fada kawai idan tayi ma laifine na fada.
Dije tace tayi wani tsiyan kuma ko ya dago ido ja yanacewa Dije din wana tura masu aiki suje gidan su duba gyaran da za ayiwa gidan shine Asmau ta fito take gaya masu maganan banza wai su dawo wurin wanda ya turosu suce dashi ba gidan bane don su basu da labarin aiki kijifa dije wai Asmau zata kawo shegan takanta gareni yanzu.
Wanan yar iskan yarinyar ai tafi da nan barni da shegiya mai gadon tsiya inba tsiya ba yaya cigaba zai sameki har ki nuna halin tsiya a wurin ga yar banza da son kakale idan an gyara gidan ta samu na karya dashi ke nan.
Sai mamaki yakeyi yana fadin a,a yaushe renin nata ya kawo gareni haka niko ina zaune sai mutmushi nakeyi don nasan Asmau zata aika naji Aisha tace.
Yaya kaine baka san yadda ta koma yanzu ba kamar kada tayi shegen auren nan nata take ganin a yanzu ita tafi kowa ita wata babbace inna kuma na kamata.
Da ita da uwar naku duk sai su bar gidan tunda basu da gadon shi gida na Amadine kowa ya sheda hakan a unguwan nan don ladan a masallaci ya fada in ya mutu gidan sa ya mallakawa jikanshi Amadi gona biyu kuma su yaranshi biyu su raba a tsakanin su sai yan tarkaceshi a bani.
Kowa yasan da wanan zancen idan bata sani bane ta sani ni kuma zan tunawa uwarta wanan zancen kuma malam bai bayar dashi gareshi ga banza ba kudin da mahaifinsa ya bar masane da malam din ke juyawa suka karye a kansa ya sadaukar masa da wanan gidan a matsayin kudinshi abu da yake baiyane .
Yar banza koba haka zancen yake ba ina take da gadon gidan mu ita da zata kawo muna iyayi a cikin harkan mu yanzu ta koma gidan ubanta na wanzamai tayi iko dashi in ubanta nada daki gidan.
Haba dije abar gori mana ai abin baikai na tone tone ba haka itama dai sallontane da shiga maganan manya ko shi aidon ya shafeshine yanzu zai shiga balle ita.
Barta yar banza daga ita har uwan nata in karanto masu suji idan sun mantane da zasu kawo muna iko a cikin zance ko yan uwan malam ai sunso suja lokacin aka taka masu burki bayan mutuwan malam din balle ita.
Mikewa yayi rai bace ya shige daki saidana dan dade a zaune kafin in mike inbi bayansa na samu yana ban daki dakin kuma ba wani gyara amma na kwashe kayan daya cire na zuba a inda muke tara kayan dauda na juya zan fita dakin ya fito yana fadin ki shirya Amir muje jam,i nan kasan mu kadan na amsa da to na fita alwala nayiwa yaron da kaina na saka mashi jallabiya da hula fara uban ya fito ya daukeshi suka fita sun dade a can din nasan isha,i suka jira koda suka dawo yaron yayi barci a lokacin.
Nan falo ya shimfideshi shima ya zauna jin ya shigo yasa dije fitowa suka gaisa har lokacin tana masa korafin akan zancen Asmau yace ta barta dashi ai batace ita fitsarara bace ai zasu hadu dashi din.
Mama jummai ta gama abinci ta jera muna na fito ina gabatar mashi da abincin ya amsa da gani tafe dama a nan ai ta aje muna aci gaba daya barin dauko mana na fada na kama kwaso kayan yace shi wanan da yayi barci yaya ke nan kuma ?
Zai tashi yaci ai nasani barin gama inzo na fada nabada baya naji yana fadin wai dije kinsan tumfafiya ya kara fitowa gidan nan kuma ?
Ikon Allah a gidan nan kuma tumfafiya uwar kwankwanmai tumfafiya baki fita a wurin banza dibanki sai da sallama wanan kuma wani baiwane na ubangiji gareku.
Tsaya nayi na juyo ina kallonshi cikin mamaki nace wai a gidan nan tumfafiyan ya fito kuma yace nan fa can ta waje idan ka shigo get yana nan a barin gabas ya fito.
Zaune nakai ina fadin wai kasan master ina yawan mafalki da wanan itacen kuwa wallahi yana da wuyane ayi sati daya banyi mafalki dashi ba har uwar garke muyi hira sosai kuma da ita kamar mutum.
Murmushi yayi yana dan kawar da kai don yaga alaman tsoro a fuskana nace wallahi Allah ko jiyan nan take fada min wai inna zata zo da fada gidan mu Amma mu barta da dije kawai .
Naji daje tace ni kubura har dani take ambatowa ya kwashe da dariya yana fadin dije in uwar garke bata ambaceki ba ta ambaci wa abokiyar zaman kice kuma abokiyar fadan ki ko kin mata lokacin data saki zaman daki.
Duk aka kwashe da dariya tace bari akuyan nan ai ta gwada min boni a gidan nan Allah dai ya rabani da ita lafiya batayi min illa ba ko sanadin kafan nan nawa fa itace tayi min sanadin shi.
Ta bangaje sai yanzu nake tunawa akan nayiwa Amadi fada harda duka ranan ina shigowa tayi baya baya ta kwasheni ta zubar kasa na fadi a baude kashina ya amsa tun lokacin nake fama da kafan nan a rayuwata.
Muka kwashe da dariya har Aisha da ta fito ina dariyan nake fadin yanzu nake batun na kiraki muci abinci muka tsaya hiran uwar garke.
Amma dije baki fada min ba cewa kikayi kawai an kin fadi kinyi tarmashe tace ina zan fadi ta kara min wani sanadin aidai gashi mun rabu lafiya da ita yanzu ko ?
Allah yasa kun rabu din don al,amarin wanan akuyan ai sai ita ni kawai zuciyana na ban cewa wallahi zata dawo wata rana kuma ku bari ku gani din Allah dai ya sauwaka kawai.
Aisha ke dube duben tsoro nace aiko gatama tazo duk suka duba a tsorace muka kwashe da dariya munci abinci mun gama nida Aisha muka kwashe kayan don su mama jummai su huta don mutanene suma a ka zauna zaman hira ana rage dare dijece ta fara tashi taje ta kwanta Aisha ta mike ta kwashi yaran zuwa dakina don nan suke kwana tare dasu da master yayi tafiyane nake kwana dasu daki daya a kasa don nafi jin dadin kwanci kasa din.
Ranan kuma yana gari yasa zata kwana dasu ita kadai gaskiya Aisha ta dabance ita don halinsu daya da master basu shiga abinda ba a sakasu ciki ba .
Washe gari kuma tunda nayi sallah na koma na kwanta don gajiya shima daya dawo jam,i yabi sahuna muka kwanta barcin safe don ana sanyi a lokacin can cikin barci nake jin ana nocking din kofa na bude idona shi naji yana fadin waye muryan Aishace take fadin su innace sukazo yaya tashe in tasheku.
Naji yace inna yana daukan wayan shi yana duban lokaci yace basuga hadarin nan bane da wanan sanyin da akeyi suka fito da safen nan haka tashi nayi na zauna ina tunanen meya kawo inna kuma amsa zuciyata ta bani ai gidan dantane .
Saida ya shiga bandaki ya kewa ya fito ya zura riganshi dogo a jikinshi ya bude kofan ya fita har lokacin ina zaune jikina ya mutu a inda nake zaune kafin na zuro kafana zan sauko a gadon .
Budan kofan da yayi ne na fara jiyo muryan inna sama sama a cikin fada tana maganava hasale nace to fa yau kuma meya faru inna tazo haka cikin fada tunda safen nan haka ?
Ban fito ba saida na shiga nayi brush na kewa na fito ina saye da rigan barci na saka hula da cusha gashina a cikin hulan sai zanin atamfa danayi sallah na daure saman rigan barcin.
Na bude kofa na fito lokacin na fara jin muryan inna da kyau tana fadin ni gani shasha watau na haifawa wasu da suna cin dadin su suda sukai kudin nasu dawa sukaci ?
Don Allah dai inna ki bar fadin hakan ba kyau gaskiya Aisha ce ke fadin hakan cikin damuwa tana tausa muryanta ga mahaifiyan nasu tace rufa min baki kada yanzu in saba maki gidan nan .
Karya nafada basu yakewa karyan arziki ba saiko umma dake tare dasu ina jin haka na dan ja natsaya taci gaba da fadin banda umma yanzu wakecin arzikin shi sai ita saiko yan uwan matarshi.
Saukin abindai ba fakiriya ya daukoni gidan muba inna inma naci arzikin shi shima daku kunci nawa a baya jin hakan yasa ta juyo tana kallona sai kallon ya koma mata biyu don wai zuwan ranan batama ga ciki a jikina ba haka tsoho sai yanzu din dana fito da zani daure sama rigata tagane.
Oh lalai kiyi abinki issasa don yanzu kan mage yaji magi to sai ki sauke rashin kunyar nan naki garesu don ni ban neman komai a wurin uban yarinya.
Ai dole yanzu kiga kin isa tunda kina cika masa gida da yayan kwara ba dadin gani ba dole shiko idonsa ya rufe ba ganin kamar gwanewa ne hakan kike nai bai san sallon yaudara kuke masa ba.
Hannu master ya daga min ya juya gareta yana fadin lafiya haka inna kika fito gida da wanan uban hadarin da aka hada zuwa gidan nan fada wani abu matata tayi maki ko Dije ko Aisha dake nan ?
Ko wanine ya je ya fada maki wani abin don ni ban garin jiya na dawo da yamma na kuma fada maki zanyi tafiya kafin in tafi.
Kai rabani da dadin bakin banza sai wani yaje ya fada min zan sani tunda ka daukeni wawuya yar kauye ban san abinda akeyi ba kai shike nan na haifawa duniya kai saidai wasu suci gajiyan ka bani ba.
Mena rageki dashi duniya kudin abinci ina turuwa kudin ruwa ina turowa kudin kashi ina turo maki naki dana yayanki ko wani karshen wata hakama sutura inna ki fadi a ina na rageki harda kudin goro kika lissafa min kuma ina baki kince Asmau aure nama kayan daki bayan haka na turo maki da milayan biyu don sha,anin buki a ina na rageki inna ?
Amma inna ai kince rabin miliyan ya baki lokacin shegiya yar iska ki rufa muna baki duk waya turota yanzu bake ba ke har kin isa in tura masu aiki gida aimin aiki ki koresu ?
Yau din nan basai gobe ba ki tattara ki bar min gidana ba sai gobe ba ki koma gidan ubanki Asmau na gaji nagaji hakana wallahi, , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/17, 7:01 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
1️⃣0️⃣0️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Kai jinan bashi ya kawo ni ba kasani nidai din da kake gudu yanzu nice na haifeka da cikina don haka ban haifarwa kowa daba a duniya.
Kuka dije ta saka tana fadin shike nan aida ki fito fili Rashida kice na kwace maki da yanzu ba kizo ki fake kina zagin dan mutane ba .
Lai Rashida kin nuna min ke yar dije yi hakkuri don Allah kada ki karasa saboda Allah badake inna take ba danine dana auri danta shine kiyayyan mu da inna amma ke take nufi ba.
Itama inna din kuka tasa lokaci guda tana fadin umma ko kin min baki a kan wanan maganan ba zai kamani ba tunda ban ambaci sunan ki ba.
Yanzu dai dada bukatanki Asma ya biya tunda kin hada wanga fadan duk kece mai wanan hadin in anyi magana kice wai ba a son inna gashi yanzu abinda kika haddasa a tsakaninsu ai.
Tunda kuka fara irin zancen nan nake fadin ki bari