Showing 171001 words to 174000 words out of 304363 words
yace badasu nasayo ba kina iya basu inna ta raina gobe dai zan sayo masu nasu idan na fita.
Ganin baici ba yasana zage ina ci ina mika mashi hakan yasa ya danci sosai yasha yought din muka kwanta.
Na fahinci dan raman da yayi a jikin shi amma naja bakina nayi shiru ban furta hakan ba a lokacin saidai ina tunanen meya sameshi haka cikin dan lokaci har yayi rama hakane ?
Can cikin barcin mu nake jin kamar ana hayaniya a kaina da kyar na iya bude idona shine ke wani irin mafalki a gefena lokacin da ganin kasan yana cikin wani irin mawuyacin hali a mafalkin da yakeyi din.
A hankali nakai hannuna saman jikin shi ina dan bugawa tare da kiran sunan shi ya amsa a firgice nace ka kwanta da kyau kana wani irin mafalkin da ban tsoro.
A daidai wanan lokacin ne bakar akuyan nan nasu mai kukan tsiya ta dauki kuka da bata daina ba har gari ya waye tana faman abu daya gashi ya fita zuwa wurinta tunda asuba amma hakan baisa ta daina kukan da takeyi ba aranan.
Ni kaina kukan nata yakai min ko ina ballesu da na kula hankalinsu ya tashi da hakan can nake jin muryoyinsu na jiyo muryan inna na fadin .
Ai na fada maku ku sayar da bakar akuyan nan tunda ba haihuwa takeyi yanzu ba anki meye amfanin aje akuya hakane sai kudi ake kashe mata.
Ba za,a sayar ba nace ba za,a sayar ba tunda yaron nan ya fahintar damu illan sayar da dukiyan daba namu ba a yanzu.
Gara mu barta nan muna kallonta ko shekara nawa zatayi a nan din kamar yadda ya fada sai inna din tace wahala ko bai kare maku ba ashe don mu ta ishemu gidan nan gaskiya.
Ta shigesu tana fadan bakar magana kan akuyan da dan nata ke kokarin dura mata magani a baki amma akuyar tana bin inna da kallo zakace mutum ne ita lokacin.
Aiko haka aka wuni da ita yana faman kula da wanan akuyar tasa mai abin al,ajabin sai zuwa rana takai kwance ta bar wanan kukan da takeyi din.
Shima din sai wanan lokacin yayi wanka ya fita bayan nayi sallah na samu na kwanta don akwai barci a idona sosai a ranan.
Bayan la,asar ya dawo da cafamen shi kamar yadda ya saba kashi biyu nasu da namu bayan nayi sallah na dora muna girki kamar yadda na saba.
Har lokacin banji duriyan inna ba na dauka ta fitane a lokacin ashe tana daki ba lafiya tun wanan lokacin datayi wanan maganan ta shiga ta kwanta shine zazzabi ya rufeta zuwa yamma kuma sai ga zawo ya biyo bayan hakan .
Ni bansan abin dake faruwa ba har lokacin ina tsaka da aiki a kitchen naji ihun Asmau hakanne ya dauki hankalina da sauri na fito kitchen din hankali tashe.
Sai muka hade dashi ya shigo part din da sauri ashe kudi zai dauka su tafi asibiti da ita lokacin nake tambayan shi ko lafiya a gurguje ya bani amsa da innace ba lafiya.
Salati na saka na fita da sauri tun dana nufi part din na hangota a yashe kasa tana kakarin amai gwanin ban tausayi na karaso ina mata sannu sai gashi ya iso wurin yana fadin ku kamata a fito da ita.
Nan suka kasa kamata din gashi shi kuma ya rigada ya fice a lokacinko ganin yadda suka kasa kamata din dole yasa na yunkura zuwa wurin ina fadin Aisha ta tallaba gefe mu cicibata.
Amma kuma sun kasa hakan don inna ba karamar mace bace gaskiya don tana da jikinta ba laifi gashi kuma ta sabe babu lakka a jikinta saita kara nauyi.
Ganin shiru ba a fito da ita ba har lokacin yasashi shigiwa yana fadin ku kamata mana sai ya ganni da ita na tallabota a firgice.
A cikin tsawa yana kallon kannen nasa yake fadin ba zaku kama mata itaba kun barta da ita haka ina zata iya daukanta ita, , ,
Aman da inna din ta sharo min a jikina ya dakatar dashi ga fadan da yakeyi da kannen nasa yana fadin subbahanallahi da sauri ya karaso ya kamata daga hannuna ya fita da ita daga gidan.
Hankalina duk a tashe yake duk da kyakyamina lokacin ban damu da aman dake jikin nawa ba sai binsuma da nayi zuwa kofa ina kallo suka wuce da ita dukan su zuwa asibitin.
Sai lokacin na tuna na koma na gyara jikina a lokacin jin kazanta yazo min Allah yasa dan rigan shan iskane a jikina lokacin don haka na daure na wankeshi na fito ina shanyawa dije ke fadin.
Duk ta bata dakin nasu gaau su kuma sun kwasa sun bisu asibitin ba wanda ya tsaya ya gyara dole nice na shiga na gyara dakin nasu na saka kamshi a ciki don ya canza kamshin zuwa najasan datake fitar wa lokacin na fito na koma part dina don karasa aikin dake gabana na girkin dana dora .
Basu dawo gidan ba don an bata gado dole abincin da nayi na saka aka kai asibitin tare da wasu kayan bukatu muka rufe gidan har dije muka tafi dubanta.
Gaskiya taji jiki sosai zakace ciwon kwana biyu tayi ta zabge haka da zamu dawone muka dawo da Asmau muka bar Aisha can zata kwana a wurin mahaifiyar tasu.
Kwanan ta biyu aka sallamota ta dawo gida dole aiki yai min yawa din zatace wanan take so ko wancan haka nayi ta fama da dawainiyar su sai hakan yasa ban samu komawa asibitin dubanta ba wai ashe kuma nayi laifin nan kuma ga hakan.
Shine naji yana fada tsakar gida yana fadin in ba,a godewa kokarun yatinyar gaba ai abin ya zama ganin iyaka kuma ?
Tana gida tana girki ga wasu aiyukan za ace zuwa dayan da tayi dubuta hakan bai wadatar ba kuma kashe kanta ake son tayine ina part dina ina jiyo abinda suke fadi.
Koda ya shigo banyi magana ba don nagama sharan hawayena ke nan ya shigo shima bai dadeba ya fita na karasa abincin rana nakai masu nasu a part dinsu.
Tana wani shan kamshi dani nidai na kara mata ya jiki na fito abina ashe wasa sabon girki sai cikin dare bayan kowa ya kwanta ta fara kantara ihun azo a ceceta wata bakar mace zata kashe ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
5️⃣9️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Kusan lokaci daya muka mike zaune muna kallon juna wani ihun ta sake sakewa wanda yafi na farkon da sauri ya sauka saman gadon yana fadin innace fa .
Yana kokarin laluban riganshi dake gefe a falo ya karasa sakawa lokacin nida ya bari a ciki tsorone ya kamani nima riga na dauka nasaka nabi bayan shi zuwa waje da sauri.
Tun daga nisa na hango inna tana faman nuna wajen da hannu tare da fadin gata nan tazo min a wani halitta zata zane ni ku taimakeni tana faman nuna wajen kofansu da hannunta.
Ahmed ne ya karasa wajen yana fadin ku jaye nan ya rike hannun uwar shima a kidime yake lokacin ya fara fadin inna ba kowa wurin nan fa don Allah ki natsu ki daina hakan darene yanzu.
Saiga inna na sambatu tana fadin to to zan bari amma ku rokan min ita don Allah ta rabu dani tunda ban mata komai ba.
Inna ba kowa fa wajen nan killa mafalki kikayi haka kike ganin kamar mutum ne a wurin wallahi ba mafalki bane itace ta tayar dani daga barci tana fadin in tashi ciwon da nayi kadan ne bai isheni ba tunda banda tausayi .
Ina jin hakan a cikin tsoro don ina ganin kamar abinda take gani din muma zamu ganshine lokacin nace to inna ki bar fadi kiyi ta addua a bakinki shine makarin bawa.
To naji zanyi tace dani kamar wata yarinya karama Aisha za a samu garwashin wuta yanzu gidan nan Ahmed din ya fada yana kallon kanwar tashi.
A,a yaya yau bamu hasa wuta ba a nan na karba da fadin saidai a jona Bonner idan zaiyi tunda akwai wuta yace a dauko a gwada mu gani.
Saidai na kaaa motsawa zuwa dauko abin a dakina sai can ya juyo yana fadin ina abin baki dauko ba nace wa zai rakani part din mu din kuje da Aisha mana idan kina jin tsorone.
Tare muka tafi na dauko mashi muka jona a dakin sai ya zagaya baya zuwa can ya dawo dauke da bawan tumfafiya a hannunshi irin wanda ke bushewa a jikin iccen ya dan barbasa a cikin abin.
Dakin ya dauki hayakin maganin daya turara mata din lokaci guda Asmau banda kuka ita da Aisha babu abinda takeyi lokacina.
Ita kuma inna din sai wuri wuri takeyi da idanuwanta kamar me ganin wani abin tsoro a lokacin gabanta ya rike mata kai yana addua .
Muna tsaye cirko cirko muna kallonsu zuwa can mukaji kamar motsin tafiya a wajen gidan muka kalli juna da Aisha kowa na signal da idanu a tsorace .
Ya kara mika hannu ya kara zuba hayakin a wuta kowa dake dakin yaji tsoki kamar a fusace an nufi baya inda dabbobin gidan suke hanyar makewayin su.
Sai ga inna din ta mike shambal a jikin dan nata sai kuma wani barci mai nauyi ya dauketa lokaci guda haka bai hanashi karanto mata adduan da yake karanta mata ba lokacin.
Ku dan kama min ita mu kaita a shimfidanta ya fada nida Aisha muka kama kafafuwanta zuwa saman katifan da take kwana a sama.
Aka kwantar da ita saman katifan tana barci sai lokacin muka dan zauna gefen katifan su Aisha din muna mai kurawa inna din dake kwance idanu.
Ganin ta samu barci sosai a lokacin yasashi dago kai ya nisa yana fadin fadin Djje ina ganin inna gamo tayi tunda har maganin nan yai mata amfani yanzu don bayan iccen tumfafiya na debo na turara mata.
A dan firgice Dije din tace dashi gamo kuma na dauka zafin ciwon ne haka yace bashi bane saidai idan dama haraswan da gudawan nada nasaba da hakan ne.
Kowa dakin yayi shiru karfe uku saura yacewa kowa ya kwanta tunda ta samu barci abari aga abinda Allah zaiyi zuwa safen kuma.
Mu zamu kwana da ita ke nan Aisha tayi saurin tambayan yayan nata a dan rude lokaci guda tana kallonshi.
Kai ya girgiza cikon takaici yace to menene tunda abin ya lafa a yanzu yana da wuya ta tashi ai kuma ciki wanan daren.
Saidai mu kwana da Dije hakan zai danfi muna sauki da a barmu da ita a nan haka yace dama aida Dije din zaku kwana a nan dakin.
Ba zance tunda muka dawo dakin ba ya kara runtsawa har zuwa safe don ko masallaci da yatafi ban tsanmani ya tsaya yin addu,a ba ya dawo gida ranan kai tsaye part din su ya nufa yana duba mahaifiyan nasa wace a dan lokaci guda kamaninta gaba daya ya sauya a yanzu.
Abin duniya baya boyowa kafin ace haka labarin ciwon inna ya karade gari musanman unguwar namu nan mutane suka fara shige da fice a gidan namu wurin gaida ita tare da ba idonsu abinci su samu na karaswa gaba wurin bada labari.
Sai da Ahmed ya fahinci hakan ya dauketa a dakin nasu ya dawo da ita part din mu koda mutane sun shigo sai ace dasu ai sun tafi wurin magani bata nan don abin ya zama mata kamar tabin hankali.
Don saita fara kokarin cewa zata bada labarin yadda matar tazo mata tace ke dai bari kawai ina kwanche sai ji nayi an tayar dani ina bude ido naga wata bakar mace da tunda nake duniya ban taba ganin mutum mai bakinta ba sai ranan.
Kaiwai tace min tunda baki da tausayi da jin kai zanyi maganin ki gobe baki kara ganin wani rayuwa na ciwo kiki tausaya masa kinyi karshen yin hakan a kaina.
Jin irin maganganun mahaifiyar nasa da in yana kusa sai ya kwaba mata yasashi shiga wani hali don bashi kadai ba koni dake tare dasu yanzu hannu a gaba yake da ita.
Ganin ba shiri ko banza a tsakanin mu yasa nake kara kama kaina da ita yanzu don sai inga kamar tana hararata idan na gilma a inda take zaune.
A rana na biyu da faruwan hakan na dauki waya da safe na kira ummah ina fada mata abinda ke faruwa a gidan namu ta tausayawa inna sosai har tayi min fadan ban fada mata da wuri ba ai ba a haka.
Sam bansa zatazo gidan ba don ta kira Ahmed din tayi mai jajen abindake faruwa tare da fatan samun lafiya gareta.
Washe gari sai gasu a gidan namu shine karon farko da har ummah din tazo gidan namu tunda nayi aure a gidan sai wanan zuwan.
Duk yadda ake bata labarin talaucin gidan sam ummah bata ga hakan ba indai muna zaune lafiya hakan ba komai bane a wurinta don ko yawan maganan da mama kan sake mata a gida sharewa takeyi bata amsa mata.
Don su ko yaushe suna gida tare da mama su kwasa zuwa unguwa ko wani wajen ba zakace sunyi aure ba a lokacin.
Mama kance rashin jin dadi ko rashin samun waje da walwala yasa ban fitowa nima aiko yaushe din don ina kunyar agani lokacin.
Ga Aisha da tsohon ciki a jikinta haihuwa ko yau ko gobe itama Rukaiya din nada ciki saidai baikai na Aisha din tsufa ba.
Kamar a mafalki naji sallaman su ummah din duk da naje gida sau biyu da aurena amma hakan bai hanani bin jikin ummah ba ina murnan ganin su.
Haba ki natsu mana mahmah gaida mara lafiya mukazo fa ummah ta fada min da dan rada sai jin hakan yasana natsu na kaisu direct dakin da inna din take ciki.
Ina shiga bata farga da baki a bayana ba tace yarinyar nan bansan me kika daukeni ba tun dazun nake jiran abinci shiriritan ki yasa baki gama ba da uwarkice a wanan halin aiba zaki barta da yunwa ba.
Sallaman su ummahne ya katseta ta fara binsu da idanu tana kallon su har suka karaso cikin dakin suna gaida ita lokacin ne Aisha tace Lah ummah kune tafe ashe inna ga mahaifiyar matar yayan mu nan tazo gaidake.
Sannuku da zuwa ashe kuma kun samu labarin abinda ya sameni din kunzo kedai bari ina tsaka da barcina saiga matar nan ta shigo min ta tayar dani wai kasheni zatayi.
Koda yake sunce wai nabar fadi kingansu nan wai mutane zasu dauka na tabune a hakan don na fadi gaskiya.
Tana fara fadin hakan Aisha ta mike ta fita nima nabi bayanta muka barta dasu tana basu labari kamar yadda takeyi idan wani ya shigo gaida ita din.
Hawaye na samu Aisha nayi tana fadin yanzu matar yaya wanan abinda inna keyi haka za a saka ido abu sai gaba takeyi kafin na bata amsa Ahmed ya shigo fuskan shi a kan mu yana fadin .
Ummah ce tazo da kanta ashe kin fada matane yana don jiyama ta kirani tana min ya mai jikin ya fada yana kallona .
Nace eh jiya na fada masu inna ba lafiya kada taji daga baya taimin fadan hakan yace hakane yana kokarin wucewa zuwa dakin .
Gatacan ta fara zuba masu ai Aisha ta fada a dan kuntace sai ya nufi dakin da sauri yana sallama nan ya samesu suka fara gaisawa bayan sun gama gaisuwanne ummah tace wanan abin sai kun dage da addua sosai a kanshi don kamar bana asibiti bane kawai ?
Eh ummah yanzuma daga can nake na amso rubutu da za a bata tasha da hayaki don sunce ba shiganta sukayi ba sun dai shafatane kawai don ta tabasu suma sukace.
Ai abin ke nan tunda muba ganin su mukeyi ba sai sunyi hakkuri rashin sanine ya kawo hakan Tani mai aikin ummah ta fada tana kallon inna din dake wuri wuri da idanu tana sauraren su.
Kafin tace in na sani aiba zan tabasu ba ko in takasu har wanan bakar macen na barazan daukan raina lokaci guda haka.
Basu jima ba suka fito na zata zasuje dakine sai naga ba haka ba don suna fitowa suka fara muna sallama muka rakasu har kofa suka tafi don haka bamu samu maganan komai ba da ita a lokacin.
A wurin Aisha yaji abinda ya faru shigan mu dakin itin fadan da inna ke min a lokacin gaban mahaifiyata sai ranshi ya baci da hakan har yake fadawa Dije abinda ya kawowa inna din ciwon ta lokacin.
Yace irin wanan halin ne