Showing 75001 words to 78000 words out of 304363 words

Chapter 26 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33306

da suka tayar mai da mikin dake damun zuciyar shi a kullun yana tausan kanshi da hakan yana jajircewa don gudun irin hakan gareshi na tozartawa.
Muryan Abbane daya kira sunan shi ya katseshi Abban ke fadin Ahmed daga yau din nan ina son ka nisanci yata zarah a ko ina don yanzu dai nasan kasan cewa zarah ba sa,arka bace ita.
Karatune kuma kagama kai yanzu din haka banson jin wani mu,amula kuma kota mutunci ya sake shiga tsakaninka da ita nan gaba zaka iya tafiya yanzu.
Kuma kada naji ance ka sake kawo wani abu nan gidan da sunan alheri niko yaushe ina tsaye kan Iyalina ga komai don haka ka nisancesu .
Ga wanan dubu hamsin ne ka kara a jarin ka ka kiyaye don ka zauna lafiya Abban ya fada yana kawar da kanshi gefe cikkn takaici.
Kai Ahmed ya girgiza tare da fadin a,a Abba ka bar kudin ka nagode aikai mahaifine a gareni ko yanzu ka fadakar dani ga abndana manta cewa nidin mai raunine bai kamata na dinga kai kaina inda Allah bai kaini ba.
Ya mike ya tsugunna tare da fadin zan koma nagode kwairai ga hakan yana fadin haka ya mike ya fice daga falon suka bishi da kallo kowa da abinda yake sakawa a zuciyan shi lokacin.
Baba Salihu ne yace yaron yaron kirkine alama ya nuna hakan gareshi cewa zaiyi mutumci sosai wallahi saidai dan matsalan nan da aka samu kawai shine cikas din.
Kirkin shi bai dameni ba ya rabu min da yata kawai shi nake so a yanzu itama zanyi warning din ta da kakausan murya kan hakan idan ba hakaba ranta zai baci dani sosai a gidan nan kaji na fada maka.
Banso ka da hakan ba ana cizawa a hura don bamu san me Allah zaiyi nan gaba ba gara ka bita da addua kawai shine mafita nake gani.
Shiru Abban yayi don takaici ya hashi yin magana sai can yace ita kuma shashan daya Aisha wai yaron nan dan kawar uwarta dake Lagos ta lakewa gashi sunja min zubar da mutuncina.
Yau nayiwa uwarshi waya take fada min wai yaron bai yarda da hakan ba yace a barshi ya nemo matarshi idan ya tashi kaga ke nan dama a tsakanin uwayen nasu ne sukeson hadin shi kuma yaki.
Ai kaji matsalan shiyasa nace ko wanan din kabisu sannu don alama ya nuna cewa suna son junan su saida sun kasa gane hakan suka tsaya a mutunci .
Nan dai sukaita tataunawa kan yayan nasu har tsawon wani lokaci kafin Abba din suyi sallama da abokin haihuwan nasa yatafi shi kuma ya fara ganawa da mutanen shi yan maula.
Ahmed ko da kyar yaga ya isa gida dakin shi ya shige ya kwanta don bacin rai don ko Djje bata sanda dawowan shi gidan ba lokacin.
Ba abinda ke masa yawo a rai sai irin maganganun da Abba ya fada mai masu zafi daba wanda ya taba fada mai su a duniya sai yau saidai baiga laifin iyayyen nawa ba don shima yasa yakai kanshi inda Allah bai kaishi ba lokacin.
Wayan shi yai kara ya dauko yana dubawa sunan zarah mayana ya gani a screen din wayan yaji kamar ya share wayan kada ya dauko don shara din Abban daya kidanya mashi.
Saidai kuma ya kai hannu da zumar dauka wayan ya katse baikai ga dauka ba haka yasa ya juya ya barta da haskenta na kira kafin can ya sake jin kiran ya koma shigowa again.
Wanan karon bai bari kiran ya katse ba ya daga yana fadin Zarah ya akayine daga bangarena nace bakazo gun Abba din bane halan naji banji komai ba.
Dan murmushi yayi kafin yace nazo mana me kike son ji halan nace abinda yasa yake neman ka din mana brother don bansan me aka fada mashi ba akan mu.
Yace nazo tayi min warning akan kada in kara tsayawa dake ko yaji an gamu tare duk abinda ya biyo baya nina ja yace min.
Haba dai nasan Abba ba zai taba fadin hakan ba ai yace yako fada wallahi don iyakan gaskiyata ke nan na fada maki kinsan ban magana biyu ni ai.
Yanzu Abba din ya fadama hakan don Allah yace kwarai kuwa don Abba yau yai min tuni ga abinda nina manta a rayuwana duk da ba soyayya mukeyi ba naji dadin maganan wani gefe kuma naji zafi.
Don Abba ya fada min jarin hannuna ko sabulun wankanki ba zai saya ba don haka ya yanke duk wani alaka tsakanina dake daga yau kuma ya kafa shedan hakan ga dan uwanshi da muka zauna tare mu uku a falo naku.
Kashe wayan nawa nayi domn kada yaji sautin kukan da yazo min a lokacin saidai abinda ban sani ba ya riga da yaji ko hakan yasa yai ta kiran layin nawa ban dauka ba.
Don kukan dana rufe kaina a daki ni kadai a ciki inayi lokacin ina maijin zafin abinda Abba din ya fadawa Ahmed don ma bai fada min duka ba ke nan iya wanan din daya fada min ke nan.
Twelve misscal nasa na daga waya na gani bayan sallah isha,i danayi na dauko wayan ina duba kiran inda na samu sakonshi cewa don Allah in kirashi idan naga sakon shi.
Ban kiba na danna kiran rayin shi ya shiga ya daga ya dauka yana fadin yanzun kin sauko ke nan ko kada wanan maganan ya bata maki rai don Allah.
Ni nasan ke din ko Abba bai fada ba keba sa,ata bace zarah don haka muyi hakkuri mu guji abinda zai iya kai ya komo daga hakan.
Dama ashe ba sona kakeyi da gaskiya ba nafada a cikin wani murya ina sake kuka lokaci guda naci gaba da fadin ni tunda ummah tayi muna adduan daidaituwa a tsakanin mu naji zuciyana ya kwanta da hakan.
Zarah dama kema kina sona ashe kamar yadda nima nake son ki ashe bansan da son juna mukeyi ba sai yau da Abba din yake furta kalman raba tsakanin mu dake.


ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAW
2️⃣4️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Wanan labarin na sayar dashi don alredy don haka kada wani yai kasadan juya min shi zuwa audiovisual yin hakan gangancine ga maishi.
Dari biyar ne ki biya don Allah ki karanta a cikin sallama yar uwa don Allah ki biya ki gujewa daukan alhaki a kanki yar uwa.
Kuka nakeyi sosai kamar raina zai fita din maganganun da yake fada min masu tayar da hankali yana kuma kara kashe min jiki da kalaman shi da sunan ban hakkuri a garemu.
Kunnuwana ba zasu iya daukan kalaman shi tun lokacin daya furta zarah dole hakkuri zamuyi da juna don gudun birewa iyayyen ki a kaina dan zaman mu tare zai iya jawo maki matsala da rayuwaka zasu baci.
Don gaskiya Abba ya fadi ni daya nake da maraya ko wani mara uba dayazo duniya don haka kinga banda asalin da zamu iya zama a tare dake har iyayyenki suyi suyi alfahari da hakan don tabon da iyayyena suka shafawa rayuwata.
Dif na kashe wayan saboda cigaba da saurarenshi zai iyasa zuciyana bugawa a lokacin don yadda nake jin kaina haka shima baiyi gigin sake kiran layin nawa ba a lokacin don kukan da yazo mashi.
Kuka yake saboda abu biyu na farko gorin da yasan zan biyo bayanshi dama ako gidanwa yaje neman aure balle irin gidan mu babban gida irin haka da kaddara takaishi ciki.
Shi kanshi yasan duk wanda yaji hakan ba za,a taba bashi gaskiyan hakan daya faru ba don ko driver ya samu a gidan mu yaci a kalleshi a daga mashi hannu.
Balle wai aji yar gidan mune yake nema da aure a lokacin idan ba kaddara ba waya isa yai hakan saiko kaddara din da yanzu aka fake a gareta.
Ya dade a kwance yana kuka shi kadai a dakin kukan nasa yasha bambam danawa domin shi kukan abu biyu yakeyi a lokacin niko ina kukane kan kalaman Abba garemu kadai.
Yayin da shi kuma yake kuka kan irin rayuwan da mahaifan shi suka sakashi cikine don abin fade baiwa mutune kadan yanzu koda abin na a taru a tausayawa mutum ne sai an koma baya ayin gulman mutum a karshe.
Yasan kulba dade dama zai samu irin hakan saidai bai taba tsamanin hakan da wuri ba gareshi sai gashi ya fara fuskantan hakan ga babban mutum kamar Abban mu daya nuna mai kyama ko tsana kan kawai don matsala irin ta iyayyenshi dake binne shekara da shekaru.
Motsinshi da Dije taji na fitowanshi daga dakin ya nufi bandakin yasa ta fitowa tana fadin Amadi kana gidan nan dama ashe ?
Eh kawai ya amsa mata ba tare daya tsaya ba a cikin dakusheshen muryan shi da kuka yasashi narkewa hakan lokaci guda.
Kallon mamaki da zargin ko baida lafiyane ta tsaya take mashi lokaci guda tana tsaye har ya fito ya tsuguna daga can ya samu wuri ya fara alwala a gurguje.
Ya gama ya mike tana fadin abincin ka na nan tun dazun a daki me yuyuwa ma yanzu yayi sanyi don tunda sauran rana nayishi barshi Dije yau banjin yunwa ya fada yana wucewa ba tare daya dan tsaya magana da itaba yadda suka saba idan ya ganta tsaye.
Ya shige dakin shi ya fara sallah komawa Dije tayi dakinta cike da zarginshi a zuciyar ta can taji ya rufo kofan gidan su kafin taji yana rufo kofan dakin nasa kuma haka yasa ta mike ta fito har zuwa kofan shi tana fadin.
Amadi haka zaka kwanta ba tare da kaci wani abu a cikinka ba ka kwana hakana da yunwa ka fito ko shayi ka fita ka samo kasha son babu ruwan zafi a gidan nan yanzu.
Dije bana iya cin komai jeki kwanta kawai dare yayi yanzu karfe tara saura zakace darene yanzu meke damun kane yau din nan wai ?
Dije ta tambaya daga waje duk da yaji muryanta hakan baisa ya bude kofanba bai kuma bata amsa ba yayi shiru kamar bai cikin dakin a lokacin.
Munaga rasul Dije ta fada ta juya tana cigaba da fadin yaron nan kanshi daya kuwa yau din nan yaro haka kamar wanda yai gamo a hanya Allah ka cecemu ta fada ta koma dakinta.
Gidan yai shiru kowa na part din shi tare da yaran shi don ni tun safe ban leko waje ba ina dakina kwance hjy tsohuwa ce ta shigo tare da wasu jikokinta mata biyu da suka rakota.
A ka,ida dakin ummah takan fara shiga kafin ta koma dakin mama ta zauna har zuwa lokacin da zata bar gidan idan tazo gidan mu.
Saidai hakan bai hana ummah hidima da zuwan nata zata girka mata abinci koda batayi niyar yin girki na musanman ba a ranan zatayi hidima sosai wa hjyn akai mata can falon mama inda zasu zube kowa yaci yasha wani lokacin ma bata sanin tafiyan su saidai taji cewa sun wuce.
Ta shigo bata ko zauna bata ko zauna ba a ranan a tsatsaye suka gaisa da ummah din ta juya ta fita zuwa dakin hjy karima tunda yanzu sun zama su uku a gidan .
A can ma din bata tsaya ba ta fito ta zarce dakin hjy mama a can suka zauna kowa yaci gaba da harkokin shi a part dinshi sai zuwa ranane mama ta aiko wai idan ummah ta gama abinci a kawo wa hjy.
Ummah tace abinci yau banyi girki ba don yaran ma basu zauna ba basu gida komai ban girkaba a part din nan saida yamma zanyi abinci.
Ai ana fadi mama tace zancen banza ke nan ki koma kice mata bata sanda cewa a nan hjy zata wuni bane bata girka mata abinci ba.
Yarinyar ta dawo ta fadawa ummah sakon mama tace jeki kicewa maimuna nace ko ta manta itace da girki yau ne ?
Nan mama ta harzuka wai ita ummah zata aikowa maganan banza har ta aiko mata da wani zancen haka ita ummah ta aika mata da zancen zafi.
Har yakai hjy din ta mike wai zata tafi gida tunda ba a san darajanta ba a gidan Abba din dama inda mama keson akai ke nan Aisha ce ta samu Abba a fslon shi hankali tashe take fada mai abinda ke faruwa a cikin gidan namu.
Mamaki sosai Abba yayi da jin hakan a take ya tarasu a falon shi ranshi bace yake sosai jin cewa wai unmade taki girjawa hjy abinci ga kuma fitina da ya biyo baya.
Har hjy din duk suna falo da matanshi ukun suna shigowa daya bayan daya kusan ummah ce ta shigo a karshe yanayinta kawai zaka kalla kasan bata jin dadin jikinta ko tana cikin damuwa a lokacin.
Wuri ta samu ta zauna kamar yadda kowa yake zaune a falon kafin zuwa can Abba din yace ya akayi har hjy tazon gidan nan ace an rasa wanda zai bata abinci a cikin ku.
Falon ya dauki shiru ya kalli mama kafin ya juya aurin su ummah da hjy karima yace tambayan ku nakeyi fa kun min shiru ?
Ai gata nan a tambayeta don ita ta saba girkawa idan tazo wake nan Abba yace wake nan fa ya tanbayi mama din da tayi magana tace.
Hjy salma na aika a kawowa hjy abinci ta aiko min da maganan banza ta karasa cikin niba ruwana fa don idan mutum yana takama da iya shege ne saimu zuba.
Wai tsaya hjy maimuna mu zuba din nan da kike fada hannun ki ya rikene kin kasa zubawan ko kayan nauyi kika dauka da kika kasa ajewa ki zuba din.
Kai hjy maimuna kiji tsoron Allah don raini ai kinsan cewa yau kece da girki don kawai ki hanani kwanciyan hankali zakiyi kokarin hadani da hjy ?
Amma kece ai kika saba girka mata idan tazo gidan nan dama mama ta fada amma kinsan sai idan nike da girki har in tazo gidan nan lalai ya zama wajibi na zubawa hjy girki kan .
Kuka tsohuwar ta saka wai an raina mata wayo ana wullakanta ta a gidan danta sai maganganu take sakewa wanda ke nuna aibanta ummah.
Haba haba mama wanan maganan baikai can ba ai maganace da amsanta a zahiri ga maigirki a yau ta kasa girka abinci ta baki ta ya wata zata dauko ta kawo maki alhalin mama a wurinta fa kika sauka da kikazo gidan nan koda ace ba ita bace ya kamata ace ta girka maki tunda kina side dinta hjy karima ta fada.
Wana naga kina son ki shige mun hanci da kudundune a cikin gidan nan don tun zuwan ki idan zance ya taso sai kiyi kokarin dora min laifin a kaina ?
Eh don gaskiya dayace a fade idan hakan ya taso haba wanan boyar Allah meye laifinta gidan nan kan wanan abubuwan yanzu ?
Kujeku na gode da wanan abinda kukai min din mahaifiyata dani kun nuna min bamu da daraja a idanun ku a, a Alh wanan zance sai idan anso a jashi amma wanan ga gaskiya a fili kowa ya sani .
Akan me zamu bar hjy bamu bata abinci ba don ba wanda zai zata cewa tun shigowanta gidan nan ba a girka mata abinci ba a gin hjy maimuna duk hjy karima ke fadan haka karshe saita mike tsaye tana fadin Allah ya huci zuciyar ku wanan zancen maimunace mai laifin haka ko gaba kuliya akaje.
Zan tafi don wana maganan bai shafeni ba ni yanzu kuma naga ba a son gaskiya a cikin zancen don haka na barku lafiya hjy kiyi hakkuri .
Kowa ya bita da ido don ganin yadda tasa kai ta fice daga falon ba tare da Abba ya basu umurnin yin hakan ko nauyi yadda tayi din Abba yaji ya kira sunan ta da karima karki sake ki kara daga kafa a wurin nan.
Alh dole in tafi don naga fadan rashin gaskiya kakesonyi wurin nan a yanzu don ko gidan kuliya yana son hujja ga sharia ai.
Ta koma ta zauna tana cicika saman kujeran Abba ya kallesu yace ya zama wajibi ga kowan ku daga yanzu duk ranan da hjy tazo gidan nan kowa ya girka mata abinci a kai mata final ku tashi ku ban wuri banson karin wani zance kuma.
Amma mama ta fada ya daga mata hannu yana fadin nace banson wani zance kuma ku fice min zanyi magana da hjy.
Hjy kiyi hakkuri hjy karima ta fada ta fice daga falon sai ummah ta dan zaudo daga saman kujeran da take zaune tace hjy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login