Showing 123001 words to 126000 words out of 304363 words

Chapter 42 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33342

cewa bai kara waiwayo wanan garin na mambilla a rayuwan shi ya sadakar da zancen zai kara haduwa da mahaifinshi.
Yasan cewa babu zancen shi a zuciyan wanan mutumin yanzu duba ga yadda yaji labarin harda da wanda sukai kama dashi sosai yadda mutane suke fada din kuma suke ganin kamar tasu.
Yana jin kiran sallah ya fito yayi alwala don har ya riga malam musa tashi shidake tayar dasu a kulun suyi sallah jam,i sai gashi yau shi ya riga dattijon tashi.
Daga nan daki ya koma ya fara gabatar da nafila bai dade da tayar da sallah ba yaji fitowan tsohon daga dakinsu shima har ya gama abinda zaiyi yana jin motsin shi kafin yazo yana bugamai kofa yayi gyaran murya dake nuna yana falke a lokacin shima.
Tare sukaje sallah sun dan dade basu dawo gidan ba kafin su dauki hanya su dawo gida bayan su gama zikirin safe kamar yadda suka sabayi din.
Sai bayan sun dawone ya dibi ruwa da sanyin nan yaje bandaki ya watsa ya fito ya shiga dakinshi ya shirya tsab ya fito a cikin shirin shi ya samu shattu na kashe kuna shi kuma malam musa yana zaune a dan rufar shi yana tulawa.
Shattun ya fara gaiyarwa kafin ta dago kai ta sauke ido a kanshi yana rataye da yar jakarshi ta tafiya da yazo dashi garin.
Kallon mamaki take mashi ta amsa ya mike zuwa wurin malam musa ya duka yana masa ina kwana ya dago kai yana amsawa tare da fadin yau ba zaka zauna tulawan ba ke nan ?
Sai idon shi yai arba da jakar tafiyan shi a bayanshi don haka ya kasa boye mamakinshi a lokacin saboda tuhumar da zuciyan shi ya fara mai zai tafi ke nan kome matashin yake nufi dayin hakan.
Ya naganka haka dattijon ya tambayeshi ba tare daya iya amsa gaisuwan daya fara mashi ba tare da kura mai ido cikin son jin amsan da zai bashi din.
Baba zan tafi gidane yau din nan insha Allahu don yanzu kuma hankalina gaba daya ya koma gun kakata dana baro gida saboda nasan tana can cikin wani hali na rashin sanin idan na shiga a yan kwanakin nan.
Nasan kuma zamana a wanan gari a yanzu haka zai iya haifar da barazana a gareni a yadda na fahinta don haka nake son inyi gagawan barin garin nan a yau din nan.
Amadu ya kira sunan shi na yanka kamar yadda ya fada mai din sunan shi tun farko yace nasan kana da ilimin addini dana boko.
Don haka zaka iya hango abinda ni ban hango makashi ba a yanzu to amma dai komawan nakane a yanzu tun kan ai wani abu gameda mahaifinka din shine ya daure min kai a yanzu.
Babu komai baba saidai zuciyana ta kasu biyu a kan matsayina a zuciyar shine don bansan a wani rukinin nake a wurin shi har in bai fadawa yan uwanshi komai game dani ba kaga hakan zai iya haifar da wani matsala mai karfi kuma a tsakanin mu.
Don haka gara in bar garin nan kasan masu kudi yadda suke a yanzu zai iya gano gidan nan ya turo a halakani ko ai maku wani abin da bai dace ba.
Indon wanan ne zaka tafi kayi kuskure kuwa koma me zaiyi maka yayi din ka dai tabbata a dansa har in mun zauna dashi din nake gani.
Kayi hakkuri baba ka barni in tafi a yau din don nasan daga baya zaka fahinci manufata da abinda yasa na yankewa kaina wanan hukuncin a yanzu.
Saidai taimako daya da nake son kai min baba shine duk sanda na tashi nunawa wani ahalina zan nemoka a matsayin dan uwan mahaifina din don girman Allah.
Shiru dan dattijon yayi na dan lokaci kafin yace wanan yafi komai a wurina yanzu da zaka yardama ni har gida sai in kai ka amma ko yanzu ma hakan bai baci ba garemu zanyi kokari nan gaba inzo har garin naku na ganka a matsayin dan uwa a gareka ni da wasu.
Godiya sosai ya karawa dattijon kafin shatu ta iso wurin da kwanon kunnunta tana fadi a cikin yarensu naga kamar yaron mu zai tafi ko ?
Mijin yace haka ya kuduratawa zuciyan shi duk da banji dadin hakan ba don baso ya tafi hakan cikin bacin raiba gashi ni kaina bai fada min komai game da haduwan nasu da mutumin wanda yake zaton mahaifinshine shiba mu sani.
Ban rike sunan shiba nadai san cewa shidinne ta maganan dana fada mai duk da bai ban amsana daga bakin shi ba amma yanayinshi gaba daya ya gama nuna min shi din ne.
Duk yadda malam musa uaso ya dakatar da matashin yaki yarda da hakan karshe dai malam musa din yace ba zaka bi hanya ba batare daka karya kumallo a gida ba .
Wanan ya dan tsayar dashi ya tsaya yasha kunun sama sama malam musa din ya kalloshi yace kana da guzurin da zai kaika har gidane ya dago kai yace insha Allah kudin dake wurina zasu kaini har gida baba.
Bayan ya dan kara kurba kunun ya mike yana masu godiya ya sallami shatu ta nuna mai damuwanta a fili kan rabuwan su dashi a lokacin.
Tare suka fito da malam musa din sai dai ba mutane don safiyane sosai kowa na gidanshi lokacin yana rage hantsin safe da iyalanshi agida.
Malam musa din baiyi aune ba yaga ya nufi wurin garken shi ya dan tsaya kadan kafin ya juyo su kama hanya saiga mai mashin suka tare yayi jinga ya kaishi tasha nan malam musa din ya mikowa Ahmed din wasu kudi masu yawa yana fadin ka karbi wanan ka kara kayi amfani dashi .
Ahmed din ya durkusa kasa yana kada kai alaman bazai karba yace ashe baka daukeni ubaba a wurin ka ka karba kuma ina rokon ka idan kaje ka kirani muji saukan ka yace insha Allahu baba.
Ya mike yana dan goge hawaye a fuskanshi ya tafi yana dagawa malam musa din dake jin wani abu a cikin zuciyar shi game dasshi lokacin hannu.
Yayi sa,a yana zuwa mota mota mutum daya ake jira ys biya ya shiga ba bata lokaci suka bar garin mambilla din suka dauki hanya bin garin yake da kallo kafin ya mayar da idanunshi ya lumshesu.
Fada takeyi sosai a wayan kafin ta mike tana fadin gida zata koma mambilla don maigidanta baida lafiya hankalin kowa ya tashi da jin haka.
Anzo dadi dadi ana buki gashi yanzu kuma mumunan sako ya risketa kowa da abinda yake fada a wurin ita kan jinsu takeyi kawai don ita kadai tasan abinda take ji a zuciyar ta lokacin.
Don hankalinta yayi kololuwar tashi sosai ga abinda yaronta aminta kuma hadimin maigidan nata ya fada mata a safiyan ranan suna kama hanya tadauko wayan ta daga cikin jakar ta tana neman wani layi.
Ba adauka ba saida ta kara kira aka dauka yaren su takeyi na mambillawa tana fadin su hadu da mai wayan gata nan ta kamo hanya zata dawo mambilla din yanzu .
Ta dan jima tana waya da wace ta kira din a wayan kafin ta kashe wayan tana han tsuki duk a zatonta driver su din baya jin me take fada don bata taba sanin ya iya yaren nasu ba saboda bai taba yi a gabanta ba taji.
Tafiya sukayi sosai a ranan karfe daya suna cikkn garin mambilla din suka karasa gida direct part din mijin nasu ta nufa tana son sanin halinda yake ciki.
Zaune ta sameshi shi kadai yana tunane gabantane ya fadi ras ras don dan canjin yanayin data ganshi a ciki don a cikin kwana daya ya fada yayi dan duhu sosai a lokacin.
Jin an shigo yasa shi dago kai yana kallon kofan itace ta shigo yake binta da kallo kamar yana son ya tuno da wani abu lokacin amma ya kasa hakan.
Kofan aka sake turuwa lokacin duk suka juya don ganin ko waye ya shigo dayan kishiyar tace tashigo dauke da kayan abinci a hannunta tana sallama.
Saidai tana ganin ta tadan shiga rudu tana fadin au ashe kun dawo sannuku da zuwa ta dan tsuke fuska kafin ta amsa tana fadin eh mun dawo yanzun nan.
Abincin ta aje tana kokarin jerawa a gabanta take fadin barshi kawai aiba yanzum ne zaici ba ko tace cikin murmushi shiya umurceni na kawo mashi yaci yanzun din.
Kallon mamaki ta jefi kishiyan dashi na yadda ta bude baki ta iya bata amsa kai tsaye ga mijin a zaune bai iya furta komai ba a lokacin don yanayin da yake ciki.
Meke faruwa da kaine haka Alh ta mayar da tambayanta kan maigidan nasu dake zaune saye da doguwar jallabiya a jikinshi ya zauna ya mike kafafunshi duk da yana cikin wani hali hakan bai hanashi kamshi turare ba sai dan karamin tasbaha daya rike yana ja a cikin zuciyarshi lokacin.
Kai ya dago ya kalleta kafin ya daga mata hannu yana fadi da kyar kije ki huta zaifi ke kuma aje min abincin idan na tashi yanzu zanci.
To matar ta biyu ta amsa dashi kafin ta kwantar da murya tana fadin Dan baro na waje yana sallama dakai shida jabbi a kofan falo OK har sun iso ke nan ya fada yana mikewa da sauri kamar bashi ba a lokacin.
Kowa part dinshi ya nufa zuciyar shi cike da zargi akan halinda mijin nasu ke ciki a lokacin na tashin hankalin da yaki fadawa ko dan dama ita hjy Indo dake gari abin ya faru.
Amma ita hajiya Ni,ima da take wurin tafiyan bata san komai ba a yanzu sai zargin abubuwa da dama da takeyi a zuciyan ta lokacin.
Tunane take waye wanan din da Alh ke tunane akansa haka kardai zancen sanda ya zamo ba daidai ba gareta Alh ya sadu da danshine wurin sakaci irin nasu har hakan ya faru ?
In ko hakane ashe kashinta ya bushe a gidan nan ke nan don tasanda abubuwa da dama zasu iya faruwa a cikin lamarinta ke nan a yanzu tunda anfada mata ka idan abin kuma ta yarda da hakan .
Sam bata taba tunane ko zaton cewa maigidan zai iya sake wanan yaron nasa a ido ba kuma duba ga irin shekarun da aka kwashe babu wanan zancen .
Don har diyansu sun taso sun zama wani abu yanzu a cikin rayuwa tana ganin cewa lokaci yayi da zata gaje gidan ita da yayanta da yan uwanta da suka tsaya mata komai ya tafi daidai.
Amma yanzu zuciyarta yana bata cewa duk wanan abubuwan suna kokarin wuceta idan ba Allah ne ya gyara lamarin nata ba kam.
Alh munyi iya bincken mu mun kasa gano waye wanan yaron kuma daga ina yake wanda ma ya sanshi ko yasan a inda yake zaune bamu sameshi ba gaskiya.
Murmushin kasaita mai kama dana takaici ya sake lokaci guda yana fadin amma Jabbi kasan dai yaron nan dana gani ba aljani bane da zakuce ya bata a cikin garin nan.
Ba haka nake nufi ba Alh Jabbi din ya fada a ladabce yana sone kai kasa yace muna dai kan binciken hakan in sha Allahu zamu gano komai a kanshi da yardan Allah.
Shiru sukayi na dan lokaci kafin Alh ya fara mikewa tsaye saida yaba da baya kamar zai shige ciki yace ina mamaki da jiya zuwa yau za a ce an kasa gano inda wanan yaron yake a cikin garin nan.
Daga haka yasa kai ya shige ciki ya barsu nan a zaune suna mamakin sauyin da suka gani wurin aminin nasu kuma maigidansu abokinsu tuna tasowa da har yanzun basu yada junan su ba suna tare.
Saidai sun san cewa shidin ba mai fushi bane irin haka alama ya nuna ke nan zancem wanan yaron yana da muhinmanci sosai a wurin maigidan nasu.
Nan suka mike kowa ya nufi inda yake tsamanin samun labari akan yaron da sukayi siri da maigidan nasu kan a nemo masa shi kota halin kaka a kawo maishi a gabanshi.
Kukan da akuyoyin keyine ya sa Dijen fitowa daga daki don ta dubasu saidai tsoro da tashin hankalin abinda ta gani yasa ta ja baya da sauri tana fito da ido waje tace .
Uwar garke kene a gidan nan kuma ni Dije naga abinda ya tsoratani akuya kamar mutum saiki tafi sai lokacin da kikaga dama mu ganki kwatsam kin fado muna gida.
Uwar garken da kanta ke done a cikin kaskon da ake zuba masu ruwanshan su tana zukan ruwa zakace tayi tafiyan mai nisa don yadda take durawa cikinta ruwa a lokacin.
Kururuwa zatayi ko sulalewa zatayi a cikin gidan taje neman taimako a makwabtansu azo a gane mata abin mamakin datake shirin gani kota gani a gidan.
Akuyan da tayi wata nawa bata gidan Amadi kafin shima ya bace yayi neman akuyan bai ganta ba haka ya hakkura da nemanta har shima tashi ibtila,in yazo ya sameshi daga baya.
Tasowan ta ke nan kwana biyun nan ta dan fara jin karfin jikinta har tana da fitowa tsakar gidan nata tadanyi wani abu don rashim jikin nata har damuwan hakan takaita kwance a gidan.
Wazata kira ta sheda mai yanzu malam tanimune da kunnuwanta ba wani ya tsegunta mata zancen shi ba akan jikan nata da yake sakewa a bayan idonta ita da kantane Allah kawota ta tsurashi yana fadin maganganun da basu dace ba ga jikin nata lokacin.
Don haka kuma sai taga ai gara taja bakinta tayi shiru kada kuma a kara chamfa masu sabon zargi bayan wanda take fama acikinsa na batan jikan nata yanzu kuma.
Tuna shawaran makwanciyanta tayi kan ba komai ake fadawa mutane ba yanzu don mutane basu da tabbas a yanzu lalaikan ta sheda hakan ita don bata taba zaton cewa Tanimu zai iya sukan ahalinta a wani wajen ba ai.
Tun safe muka kama hanya kamar yadda mukazo garin iya mu muka dauki hanya nasamu nayi sallama da maryam munyi musayan lamba da ita.
Nan Allah ya taimakeni dana tafi bamu karbi layin juna ba don ba wanda yasan da cewa zamu koma a ranan zaune nake kawai a cikin motan ina tunanen abubuwan da suka faru wanda a yanzu na sani aka mommy din da bansan dasu ba a baya.
Tabbas dakan bata san waye wanan matar ba amma yanzu zuwa gidan su yasa ta kara fahintar cewa bata shigo gidansu da zuciya daya ba ashe.
Ita kan a gobe zata koma gusau wurin mahaifiyata ba zata yarda ta kara wasu kwanaki ba a gidansu na Abuja din kuma.
Ba wanda yai mata magana a motan don kusan duk sun sharetane ma za ace don ba wanda ya nuna ma kulawanshi a kanta kamar yadda itama din suke mata kallon karamar yar iska mai shegen wayau da jin kai da nuna isa da gadara don hakan da take masu sai ya saka wani dan shakunta a zuciyar su.
Don da watace tayi masu wanan iskancin dasun nuna mata cewa bata isa ba amma yanzu a matsayin makami take a wurin su don suna sonyin amfani da daman su yagi mahaifinta ta hanyar ta.
Wai har yanzu Zahra fushin ake da mommy ne kome hjy karima ta fada acan gaban motan inda take zaune din don ta kawar da komai dake tsakaninsu kada su isa Abujan haka da ita.
A bazata zancen yazowa zahran har ta dan juyo tana fadin lah fushi kuma mommy ni bana fushi da kowa wallahi .
Kina fushi mana zahra son tun jiya baki sake jikin ki ba kina faman daure fuska ta dan murmusa tace a,a mommy kawai dai gajiyace yasa kika gani haka don ban faye shiga mutane ba ni haka nake ko a gida.
Jin hakan yasa ta dan kama janta da hira ita kuma zahra din tana da biyewa tana bata amsa bayan kar take kallonta da mamakin halaiyanta fam a zuciyar ta.
Ko ta mata da cewa ya mace tun tana kankanuwa take fara fahintar wasu halaiya na zamantakewa oho.
A haka har suka isa gida inda suka samu cewa yaran Alh sunzo maza daga kasan waje hakan sai yaiwa zahra din dadi sosai ganin yayyen ta musa da Jafar a garin har su biyu.

ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Allah ubangiji ka zaba muna abinda yafi zama alheri garemu ka saka tausayi da imanin duk wanda ka zaba muna ya Allah kada ka bashi ikon cutar da bayin ka ka saka mashi tausayi da jinkan na kasa dashi.
Allah ubangiji ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login