Showing 261001 words to 264000 words out of 304363 words

Chapter 88 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33327

na kuma shafa a jikina ko ina sannan na samu sauki har dan barci ya zo min a lokacin.
A nan nayi mafalki da akuyan nan uwar garke tana fada min wai haba dai godiya kin dauki jinjiri mai karfi kuma ki zauna kina sakaci haka bayan kinsan kina da makiya ta ko ina.
Zakuje asibiti yau kada ki yarda kiyi allura haka kuma innan ku zata kawo maki magani a yau din kada ki yarda kisha maganin nan ki daitayin wanan hayakin kina fasa kwan tumfafiya kina shaka sai kin kai wata takwasa ki daina hakan Allah ya raba lafiya ta bace a cikin wani irin haske dana gani.
Zubur na falka tare da mikewa lokaci guda ina dan waige waige a dakin ranan kuma dagani sai Aisha muka kwana don Asmau tace gaskiya bata iyawa ita.
Hakan yasa na mike cikin karfin hali na nufi bandaki na kewaya duk nayi zuba don haka na watsawa jikina ruwa na hado da alwala na fito.
Har aka kira sallah ina zaune a inda na samu nayi nafila a cikin karfin hali na dan jingina kaina a saman gadona don in samu sa ida aka kira sallah asuba nayi na kwanta a wurin.
Kwalon tumfafiyan da tace na samu na dinga mafalki dashi yana min yawo a sama zubur na sake mikewa dije zaune a kaina take min sannu ganin na falka tace mijinki ya bugo waya yace zakuje asibiti yau da mahaifiyar ki tana nan tafe ku tafi.
Dije ki debo min kwallon tumfafiya don Allah na fada a wahalace cikin mamaki tace kwallon tumfafiya kuma nace eh dije don Allah yanzun nan tace amma dai kinsan ba a cinsa ko ?
Eh na sani a debo min dai tana fita inna na shigowa da ruwan magani a kofi yana tururi da gani lokacin ta sauke shi a wuta ta debo min tace gashi ance da yayi sanyi ki kafa kai kisha da dan duminshi .
Gabanane ya fadi don tunawa da zancen mafalkin da nayi da asuba din na karba na aje a gefena sai naji tace kawo dai na fifita yayi sanyi lokacin dije ta shigo da kwallon tumdafiyan a hannunta zasu kai biyar da sauri na karba daga hannunta .
Jikina rawa na bare na fara ina dagawa a zatonsu ci zanyi kada kiyi gangancin cinsa fa matar Amadi dije ta fada shakawa zanyi na bata amsa ina kaiwa a hancina sosai na shaka naji wani irin abu ya doki kaina lokaci guda.
Amma yana kaiwa kamar minti biyu na fara jin kasala a jikina yana rufeni lokacin inna ta miko min maganin nasha na karba kada kisha idan ta baki kalman daya fado min a raina ke nan ajewa nayi gefena tace ki sha mana nace zan wanke bakinane na mike zuwa bandaki.
Allah ya taimaka koda na fito sun koma bandaki nayi saurin daukan cup din maganin zuwa bandaki na watsar na zuba ruwa na dawo da kofin na zauna a bakin gadona kamar nasha.
Aisha ta leko take fadin ashe kin fito zubur inna ta mike tana fadin dauki maganin kisha tun baiyi sanyi ba Aisha tace ai tasha ta shanye tace eh ta shigo tace aiko abu yayi tunda tana shan maganin.
Ai kinsan saukin kaine da ita bata gudun magani ita dije ta fada ga mijinki Aisha ta fada ta miko min wayan na karba muryan shi cikin damuwa yake magana tambayana yake ya jikin nace da sauki yace ance ciwon ya matsa ummah zatazo kuje asibiti nace toh yanzu ina kike ji nace kaina da kirjina ke min suya.
Barin karanto maki Al jinn don dashi Annabi sulaiman ya yaki shedanun lokacinsa a hankali ya fara karanto min a hankali kuma barci ke daukana ban kara sanin a inda nake ba kuma tun wanan lokacin.
Ina tashi naganni a gadon asibiti kwance gasu ummah da yan gidansu Ahmed a kaina sannu suka fara yi min ina amsawa da kyat daga bayan su nurse ke fadin na fada maku tun dazun ku rage a dakin nan.
Likitane ya shigo tare da nurse biyu mata zai dubani yasa suka rage a dakin aka bar Tani da ummah sai wata tsohuwa dake zaune itama yar tanice don na santa dama.
Sunzo da itane wai zata zauna dani a dakina saigashi kuma ankaiga bani gado na kwanta asibitin su suka rage a dakin lokacin tare dani .
Likita ya farawa ummah bayanin zasu fara min magani don inji sauki in samu barci za a kuma daura min ruwa a lokacin kai na fara girgizawa a hankali kafin nace a,a , a,a ummah.
Don Allah ku mayar dani gida kada ki bari suyi min komai idan ba magani zasu ban ba nasha idan suyi min zan mutune ummah.
An fada min kuma naga komai zasu halakanine ummah ke don Allah kiyi shiru kin taba ganin wanda aka halaka a asibiti ne ummah ta fada a hasale.
Wallahi ummah ba karya nakeyi ba ki yarda dani komai dana gani a cikin mafalkin yana faruwa daya bayan daya don haka ku barini indai kuna kaunata.
Likita ka bar yarinyar nan tunda ta fadi haka kada kuyi mata wani abu a samu matsala wanan tsohuwar da zata zauna dani ta fada daga inda take zaune.
Shiko likitan bai kulamu ba sai zukam alluran da yake shirin min yakeyi yana murmushi ya gama yayo kaina yana fadin kada ki damu babu zafi ai wanan murmushin nan naga halittanshi ya juye min ya zama wani kamar dodo a lokacin.
Basu ankara ba sai wani irin hankade likitan nayi tare da tsale na sauka a saman gadon nayi waje hakan danayi sai hankali ya tashi dani.
Su a ganinsu na zautune yasa hakan nan suka biyoni hankali tashe na karbi hijjab a hannun dije na saka nake fada masu banson allura na fada gashi kuma wallahi nagani likitan nan yana rikida ba mutum bane shi.
Hakan dana fada a karshe shiya kara daga masu hankali kai hjy kubar yarinyar nan tunda har an gane cewa ba ciwon asibitine ke damunta kada azo ai mata wani abu tunda sun fada sun kuma nuna alaman basa so to in kunbi ta nawa ku barta aci gaba da mata nagida a gani.
Wanan tsohuwar take fadin hakan hankali tashe ga ummah kallonta ummah din tayi tace to iyan jummai haka zamu kyaleta tana wahala ai ba zamu dakatanata ba ko ?
Zafin ciwone kawai ke damunta ba wani abu ba zaki aikata kuskure babba kuwa hjy don wallahi na taba ganin hakan a unguwar mu akaki yarda ya zama sanadinta.
Jikin ummah din ne yayi sanyi haka dai suka rarasheni na koma dakin kowa na fadin na bakinsa saida aka rage ina lafe nayi shiru naji suna maganan lokacin na fara fada masu abinda naji a mafalkin da kuma komai daya faru har maganin da inna ta kawo min da aka hana insha.
Washe gari dai aka ban sallama tunda safe muka kwaso muka dawo gida hakana amma ina yawan shaka kwalon tumfafiyan nan da Dije ke wahalan tsunko min a kai akai.
Na fara jin sauki har ina dan iya cin abinci amma abu mai ruwa ruwa nake samu ya zauna min a cikina wanan tsohuwar dai ita ta fara magana dagani sai ita a daki sai kuma ummah tana shigowa ranan ta gane hakan.
Tace anya iyar jummai wanan kawar taki ita kadaine kuwa don gaskiya akwai sauyi sosai a jikinta wata kawar ummah dince tazo har gida ta aunani ciki wata hudu yake batun shiga lokacin.
Sunyi mamakin hakan sosai ummah da kanta take fadawa Ahmed din sun dade suna magana sai lokacin hankalinshi ya kwanta a karshe da sukai waya da mahaifinshi yake sanar dashi halin da nake ciki.
Mahaifin nasa yace tunda na gama karatu a lokacin me zai hana in bishi kawai mu je can a dubani yadda ya dace don zaman nan ai baida alfanu a yanzu gareni tunda shima hankalinshi ba zai kwanta da hakan ba shima.
Tafiya ya kama da Dije hakan ya dan kawo tsaiko ga tafiyan mu din inna ko hankalinta ya tashi sosai da jin hakan duk dauriyan ta sai data nuna a fili bata son hakan yakai mahaifin Ahmed din ya kira a waya yayi mata magana da murya mai kaushi a gareta.
Gidan mu kuma basu sani ba sai ana saura kwana uku zamu wuce abujan naje na sallamesu nake fadawa mama nace mama nazo inyi maku sallamane ranan Tuesday zamu tafi.
Ina ta tambaya cikin mamaki nace zan sameshi a can ne mahaifinshi yace mu sameshi na haihu a can ikon Allah yanzu shine ba a fada min ba sai yanzu Allah ya kaiku lafiya yasa a sauke lafiya nace amin na daga na fito daga part din zuwa namu.
Tafiyan mu gari ya dauki zance kamar an fasa bom lokaci guda maganan ya yadu a cikin gari kowa da abinda yake fada a kan mu.
Kwanan mu biyu a abuja muka daga zuwa US nida dije da sauran abokan tafiya da muka hadu a filin jirgi ban sha wahala ba don nasan yadda ake fita don haka ban wahala bani.
Saidai Dije da abin take gani kamar a mafarki itace ta dan ban wahala kadan koshi ba sosai ba a lokacin kuma fada sosai mama tayi da ummah wai an munafunce ta an dauketa muguwa ko me ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/1, 7:06 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
8️⃣9️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

A airport muka sameshi yazo taron mu aka dauke mu zuwa gidan da yake zaune akwai gajiya sosai a jikin mu lokacin don haka ba wani zumudi zuwa sai neman wurin hutawa.
Gidane mai kyau a saman bene don lifter zaka hau ya kaika gidajen nasu dakuna hudu da falo kitchen sai stor don ajiya komai na bukata kuma akwai a gidan.
Wanka nayi na bude jakkata na dauko kwallon tumfafiyana na dinga shaka kafin ya shigo har barci ya daukeni baiyi gigin tayar dani ba duk da yana son muci abinci amma ya kyaleni hakana don yasan lalurana.
Idonshi ya sauka a kan kwallon tumfafiyan da aka labarta mashi shine abokin arkalla na a yanzu murmushi yayi ya kai hannu da niyar ya dauke kwallon a hannu na nayi zubur na mike.
Subbahanallahi kin farkane kuma nace eh me zakayi dashi yace zan dauke a wurin nan ne kada ki danneshi wurin barci baki sani ba ya fada.
Wanan shine lafiyata a yanzu shi nake shaka naji daidai a rayuwata shi nake dan jin saukin akan abubuwa idan na shakashi barmin shi a nan komai dare ina amfani dashi.
Ba mamakin abinda nake fada ba yakeyi a lokacin kallon bani bace yake mani don yadda yaga ina magana ba sauke numfashi kamar yadda na saba maganata a tsanake don haka ya gane akwai abu a tare dani.
Dan lokaci yana kallona yana kallon yadda na shaka abin a hancina ina lumshe idanuwana kafin a hankali in mayar da idanun nawa rufe na sani kuna kan zahra amma zan rokeku da kubar jikinta a nan don kadata wahala da yawa.
Har in sone na Allah da Annabi kukewa mutum bai kamata tana cikin lalura ace kuma kuna jikinta zaune ba haka kuna bata wahala da shakan wanan abin .
Nasan da kuna jina don naganku a jikinta saboda ba haka zahrata take ba ina rokon ku don darajan Annabi har in ku musulmai ne kuyiwa Allah da Annabinsa kubar ta haka ta samu lafiya bana son mu kai inda ba a so daku nasan son mu kukeyi kuke tare damu amma ku tuna akwai bambamci rayuwa a tsakanin mu.
Mungode da kariyan da kuke bamu kuma mun sani don munsan kuna tare damu mun gode amma ku bar min matana hakana don Allah.
Wani irin ajiyan zuciya na sauke duk a cikin barcin yana tsaye a kaina saye da farar jallabiya ya kura min idanu shi kadai yasan abinda yake Nazari a cikin zuciyar shi.
Sannu a hankali labulen dakin ke wani dagawa kamar ana iska mai karfi a garin kana ya dan lafa har lokacin yana tsaye yana karanta addua a bakin shi.
Kafin yaji komai yayi tsit ya fito ya kashe komai na gidan yazo ya kwanta zuciyarshi cike da tunanen dalilin wanan abin shi dai a saninsa tun yana yaro haka ya tashi baida tsoro.
Yasha kwana wajen unguwarsu shi kadai daga wajen wasa ko hira barci zai daukeshi kowa ya shige gida a barshi wajen shi kadai don rashin gata ya kwana a nan.
Haka kuma zai iya raba dare ya biyo hanya ya dawo bai haduwa da kowa a lokacin sai karnuka da akuyoyi a hanya wata rana kuma idan yan uwan kakansa yayi masu laifi kan zuwa gona din sun mayar dashi jakin gonan su a lokaci da duk wani aikin wahala shine maiyi masu suda matayensu.
To haka zai gudu ya kwana cikjn garken awakai don kawai kada a ganshi a dukeshi yasha ganin abubuwa ma bambamta data mutane amma ko Dije dake kula dashi bai taba fada mata komai ba kan hakan.
Dole yasan abubuwan a yanzu sune suke barazana a rayuwanshi dana matarshi in har hakane ita zahra me tayi masu suke kokarin binta haka ji yadda suka sauyata ta koma wata iri kamar dai ba zahran farko daya sani ba yar gayu.
Washe gari da kyar na tashi nayi sallah asuba amma kuma ina mamaki da mamare a zuciyana na yaushe mukazo saidai na bar komai a kasan zuciyana ina wayancewa .
A gurguje ya shirya yayi muna sallama akan zai tafi offoce bayan tafiyanshi ne muka samu zama da Dije da har lokacin tana dunkule wai sanyi take ji sosai ita don haka ya bata wani katon rigan sanyin daya sayo don mu saboda ya shiryawa zuwan namu.
Wai mama yanzu gaskiyane ashe tafiyan zahra kuwa ni abin kallonshi nake kamar almara ana fadin fakiri fakiri muna mata dariya gashi yau fakiri ya kaita wajen da muke fatan zuwa.
Ajiyan zuciya mama din dake zaune tana tunane ta sauke kafin tace gashi ko kinga gaskiyan hakan tunda kinga zahiri ai ba zuwa turaine wani abu ba Aisha.
Zama wani abin shine magana yanzu ni hankalina yanzu bai tashi kamar farko don maganan da mukayi da iya bisi take fada min wasu cleaner's suke zuwa yi wasu kuma wani aikin karfi yake kaisu ke wasu har wanka gawa suke aikin yi acan da daukan gawa.
To kilama shi yakaisu can din don kinga ai shi yarone mai karfi sai duk suka kwashe da dariya lokaci guda nan suka kafe da fadin ai kuwa a nan zamu fake ga duk wanda ya tambayemu sai muce masa ai wankan gawa aka daukeshi yi a can ba sunce iskanci suka iya ba.
Iya bisi ta fada min cewa bisi ya fada mata basu dauki wasu ma,aikata ba a wurin su kinga ke nan ba anan inda yace yana aikin ba suke a wani wajen dai yake ke nan.
Rukkaiya dake gefe tana dariya tace za ai irin na su ya musa ke nan tunda haka muke fadawa mutane cewa suna turai a da ashe suna nan cikin Africa tare damu ta fada tana dariya.
Wani kallo uwar tayi mata kafin Aisha tace kefa Rukky wawuyace da yannan naki zaki kwatantasu kuma kodai ba a turai suke ba ai dai ba a Nigeria suke ba dai ko ?
Sai dai idan ke kikaje kika fada wurin katobaran bakin ki yanzu uwar ta fada a dan hasale a,a wallah me zaisa in fada da ina da niyar fada aida na fada tun baya dana sani.
Amma ai ummah ta sani saidai kawai tana nuna bata sani bane don ranan hjy karima ke fadi a gaban ta sai cewa tayi Allah dai ya tsaresu a duk inda suke.
Kaji wata yar banzan ke nan wanan matar ta shigo gidan nan cike da ahurin ta wullakantani Allah bai yarda ba yar banza ashe macuciyar gaskece ta karshe.
Wai mama shike nan yanzu Abba ya barta da dukiyan shi Aisha ta tambaya dolen shi ai tunda ta lauyeshi tayi mai wayau kuma ta nuna mashi tasan manya tana tare dasu.
Shima Alh kamar kame kame yakeyi yanzu ai ni tsorona kada ace ta kwashe komai a hannunshi shinakewa tsoro wallahi tunda yaki fadawa kowa gaskiya har yanzu.
A tunda kikaji bai fada ba ta kwashe din ke nan amma abin da mamaki yadda har ta iya yiwa Abba wanan dabaran ta kwashe komai duk wayau irin na Abba din.
An fada maki matan birni irin kine da dabara da asiri yadda ta shiga jikinshi akaji aurensu kwatsam haka tayi mai dabara kuma ta kwashe komai ta tafi ina wanan matar zata iya zama a famile

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login