Showing 18001 words to 21000 words out of 304363 words

Chapter 7 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33279

sai sallon rayuwan ya canza a wurin mu gaba daya har Abban namu din a yanzu.
Don ko bu za a bamu saidai mama ce zata sayo ita Abba zaibawa kudi ko kuma ta saya idan yazo ta karbi kudinta a hannunshi.
Irin abubuwan da dai ke tauyewa dan adam hakkinsa da rashin
yanci a gida shi muke gani a zamam mu nan zamfaradin daga mu har mahaifiyar mu muna a tauyene muna zama na rashin gata a cikin mama da yaranta wanda muke ganin su suna komai nasu a cikin gata da walwala na jin dadin nuna halin akwashi a gidan mu din.
Don ko motan da nake hawa yanzu wanda anty Aisha tayi amfani dashine mama tace ta barmin shi a ka sayo mata wani na mata mai kyau na yayi ni kuma don zuwa school aka ban wanan din don shima baiji jiki ba.
Gyara akai ta kara komawa sabuwa nake hawa har mutane na ganin aimu a cikin gata da jin dadi muke koda yaushe don basu gane gaskiya idan ba wa yanda suka zamo na jikin mu ba sunsan komai.
Kaina girgizawa Abba din alaman ya barshi murmushi naga ya sake a fuskanshi yana fadin uwata idan ban bakiba wa zai baki ki karba karbi ki aje a wuri ki.
Hannu bibiyu na mika na karba ina godiya kafin na tashi na mike na bar falon saida ya dan jima da yaran kafin ya fito yal nufi part din mama data riga ta samu labarin cewa Abbn yana part din mu kusan minti ashirin a ciki tare da mu.
Don haka yana shigo tana zaune ta hakince saman kujera sai commad da take bayarwa daga inda take zaune din don ita mama tana da yan aiki har uku part dinta.
Bayan diyan yan uwa maza da mata dake zaune tare da ita don har yan aikinta biyu a nan suke kwana a gidan namu don aikin mama.
Abba ya shigo da sallaman shi fuska mama ta hade mai nan wanda suke falon suka shiga gaida Abba din yana amsawa ya kai zaune a gefen mama din ta dan jaye tana gyara zama.
Lafiya naga kin hade rai haka ta kallo shi tana fadin duniya na hada haka kawai za a ce wai na hade rai a kan me kan wa yancan banzan iyalin naka kome zan hade raina.
Murmushi yayi yana fadin sune kuma banza yau da bakin ki ke fadawa iyalina haka maimuna wai meke damun kine haka wai ?
Lokacin su Aymana da Aisha suka fito daga dakunan su jin muryan Abba din a part din nasu suka fara gaidashi kafin su fara zuba mai shagwaba yana biye masu.
Daddy sai ka ban kudin gaskiya don in katafi saidai muji cewa ka bar gari kila Aisha ta fada tana wani shagwaba kamar karamar yarinya.
Dole Abban yasa hannunshi a aljihun shi ya ciro kudi masu yawa suma ya mika masu har lokacin mama na zaune sai busan iska takeyi tana jan kamshi ita a dole an mata ba daidai ba.
Yayin da shikuma Abban yake kokarin ganin cewa ya daidaita tsakanin shi da mama din ita kuma tana bultsewa.
Ranan ya kamata ya juya don wayan daya samu amma dole ya daure ya kara kwana don mama suka daidaita kansu suka koma daidai.
Shi kanshi Abba din a lokacin ba zaice ga dalilin dayasa yaji lokaci guda ummah ta tsaya mai a rai haka ba har yake dan jin tausayinta ita da iyalanta a wanan zuwan.
Don baibar gari ba saida yayi dabaran ganin ya kyautatawa kowa don ya cikawa ummah account dinta da kudi har saida tayi mamakin ganin hakan wanda da dane saidai mama ta bata idan yatafi tace Alh ya basu su rike.
Lokaci guda itama ummah din tana jin wani son mijinta yana taso mata dan lokaci lokaci a ranta wanda yasa Abba yana isa Abuja ummah ta kirashi tana mashi godiya tare da addua mai inganci a gareshi wanda hakan yasa shi lumshe ido a cikin wani yanayi.
Yau kwana biyu ke nan yana zuwa school yana dawowa hannu sake ba kamar yadda ya saba rikowa Dije dan ledan abinda ya samo a wurin aikin shi ba.
Saidai Dije din ta amsa gaisuwan shi sannan tayi mai sannu kafin tace da alaman dai kunyi fada da shugaban aikin kuce kwana biyun nan ko ?
A cikin mamaki ya juyo yace tun wancan ranan ban koma wurinta ba don na samu labarin cewa tace idan nazo korata zatayi yasa nayiwa kaina kiyamalleni da ita.
Ka kyauta gara da baka tafi ba ina amfanin wullakacin Allah daya bata bai manta damuna muma idan da rabo namu yana tafe a wurin Allah.
In sha Allahu ya fada tare da jingina jikinshi da bangon ginansu ya shiga tunane don yasan abinda tsohuwar keyiwa dan abincin daya saba shigowa dashi gidan da yanzu ya daina yasa ta kai ga magana har ta fahinci akwai magana.
Itama dijen shiru tayi na dan lokaci kafin taji muryanshi yana fadin sana,a nake son in nema in fara yi saidai jari shine matsalata a yanzu don sana,a saida jari mai dan tsoka a hannun ka.
Tau Amadi kace kayi sana,a babu wani kudi ko abin sayar a hannun ka indai ba wa yan nan dabbobin da su kawai muka mallaka a yanzu ba.
Saidai idan su din zaka kama ka sayar saika rike dan kudi a hannunka kai ya girgiza mata tare da fadin mu daiyi addua Allah zai kawo muna mafita ga komai.
Allah ya nufa ta fada a sanyaye sai kuma ta dora da fadin dadai kabi shawarana sai ka dauki ita uwar garken kakai kasuwa kudin sai kayi amfani dashi Allah yasa akbarka kaga saura kwara hudun in Allah ya raya muna su sai a more masu kuma gaba.
Dije ki bari na kara addua a kai insha Allahu Allah ba zai barmu haka ba da yardan ubangiji da fadin haka yai shiru yana tunane ba komai yake tunane ba sai halin rayuwan daya tsunci kanshi a ciki .
Yau ace mahaifinshi da mahaifiyar shi suna raye amma yana zaman kunci irin na marayu don dan wani dalili mara tushe da mahaifin nasa ke takama dashi a zuciyar shi.
Har yakai dije na magana dashi lokacin bai jiba yayi imani da abinda zuciyar shi ta yanke mashi akan mahaifin nasa.
Dago kai yayi da idanuwan shi da suka kade sukai ja kallonshi tayi lokaci daya sai taji jikinta yayi sanyi ta fasa fadin abinda tayi niyar fada mashi din a lokacin .
Shirun dayayi yawa yasa ta dauko mai zance makwacinsu da maciji ya sara a daji jin hakan yasashi dago kai da sauri yana fadin subbahanallahi shi malam Abashe din ?
Tace kwarai taci gaba da fadin dazun nan aka dawo dashi daga gona inda abi
n ya sameshi suje noma gonan su a can ya tabashi aka daukoshi zuwa gida.
Yanzun dai suna asibiti dashi ance magani dubu sittin da biyar na shiga masu tanzango abin ba dadi gaskiya saisai Allah ya gyara kawai.
Bari inyi sallah sai in leka gidan in yakama har asibitin sai in tafi jn gaidashi can tunda yau naga babu hadari a garin ya mike ya nufi inda suke aje buta.
Washegari na tashi da sauki sosai don haka na shirya zuwa school lafiya lau na shiga mukayi darasin farko bamu fito ba sai sha biyu da rabi.
Wurin motana na nufa na bude shiga na zauna nafito da goran ruwa tulawa cikina saida nayi rabin ruwan na daga goran na cire a bakina.
Kainane ya sara lokaci guda hakan yasa na dora kaina saman sitiyarjn motana na dukar da kaina lokaci guda motar ta fara horn hakan ya jawo hankalin mutanen dake dan sintiri a wajen.
Wai yarinyar can tana da hankali kuwa tun dazun take duke mota na horn haka wasu gugun matasa dake zaune suke fadi daga bayan su Amadine zaune yana karatu saye yake a cikin wani dogon wandon jeans
Pdayo kode sai wata shirt fara mai zanen kanana kana tsaye jikin rigan duk da farine shima rigan ya kode saboda tsufan da yayi shima.
Dan juyowa yayi inda yake jin horn din yanatashi ya hango mace ta kifa kai saman sitiyari mikewa yayi da sauri ya nufi wajen kamar wanda ake ingizawa zuwa wajen.
Ganin ya nufi wajen ya kara jawo hankalin sauran matasan dake zirga zirga a wajen da sauri ya karaso yana dan magana daga inda yake boyar Allah lafiya kike kuwa ?
Shiru yaji ga goran ruwan da nasha ya zube a jikina rabi a kasan motar yana tsiyayaya kasan motar kai ya fada yana matsawa wurin ke boyan Allah lafiya kike kuwa ?
Karan horn din ya isheshi yakai hannu ya dafa kafadata da sauri ya jaye hannun nasa yana fadin kai don Allah ku taimaka wanan suma tayi ko bata da rai ?
Sai suka fara dan ja da baya kowa yana gudun jefa kanshi cikin wahala don haka basuga abinda zasu tsaya sujawa kansu matsala ba a nan.
Don Allah ba wanda yasan ko wzcece ita ya fada da dan karfi mayanace fa yar gidan mayanace wanan ai ga lamban gidansu nan a jikin motan wata ta fada a dan tsorace tana ja baya.
Kai ya fada kafin yayi kundun bala ya dagoni daga jikin sitiyarin motan na sauke wani ajiyan zuciya lokaci guda kafin na kara lumshe idanuwana.
Meke damun ki hakane ya fada cikin son yasan ko meye matsalana a lokacin kaina nace cikin wani irin kasalalen murya mai wahala.
Bai fahinci me nake fadi ba sai ya kawo kunnen shi kusa ya kara maimaita tambayanshi gareni nace dago hannu da kyar na nuna kaina.
Kanki ke ciwo ya fada yana mai zuba idon shi a kaina na dan bude idona da sukai ja kamar garwashi lokacin na dan gyada kai da sauri ya fara lalaban aljihun wandonshi.
Kokarin shaka min yayi ba tare da shakkun komai ba ya turmuza min a hancina baikai second ba na sauke wani uban atishawa lokaci guda.🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
7️⃣
AL MUHAYMIN,,,,,,,,,,

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA.

A hankali nake jin muryanshi dake dawo dani cikin hankalina da har nasan inda nake a lokacin yana fadin this unfair ace komai sai kin dauka a waya haka kuna yadawa duniya.
Riban me zaka samu a cikin yin hakan yanzu da kake daukanta din a haka ciwone fa ya kuma san kofan kowa anan da ace kanwance ko wata taka zaka iya yada vedio ta a haka ?
Maishi yaso yaja dashi naji yace dashi kajinan wallahi duk wanan vedio din yayi link nasanka na kuma sheda fuskan ka sai mun makaka kotu.
Jin hakan yasa maishi fadin kan wanan din gashi kaga a gaban ka na gogeshi ban iya wahala yace ka iya tunda baka da tauhidi kun dauki dabi,un yahudawa kun dorawa kanku don gulma.
Ciwon kai din shine abinda zaka tsaya kana dauka makin kai mata addua akan hakan kowa nan yasan yadda ciwon kai mai tsanani yake ai.
Ganin yadda yake fada da yadda ya tsaya ya kula dani sai yawanci suka dauka ai yasanin ne muna da wani alaka dashi dama sai gasu suna watsewa daga wurin daya bayan daya aka barmu dagani sai shi a wurin.
Watace tazo wuce naji tace a, a Ahmad kana ganuwa kuwa kwana biyu kabar lekomu shago banji mai yace mata ba sai tayi dariya kawai zata wuce takallo inda nake zaune a cikin mota naji tace dashi OK ka hadu da ita ashe ?
Sai a lokacin ya juyo inda nake din ya dan kalleni farine sol dashi saidai wahala ya boye hakan na gane hakane kawai don farin bai dishe duka ba gareshi yace wake nan yana kallona.
Tace yarinyar ranan data saya ma abinci ta baka canji ai wanan dince itace gata tana nunoni daga inda nake zaune a cikin motan nawa ina maida numfashin wahala.
Bani ruwa daya ya fada don ta dauko katon din ruwane saidai an fara taba ledan an diba yana kokarin ciro kudi a cikin aljihunshi ta miko mai tare da fadin barshi kawai lokacin daya mika mata tsohuwar dari biyun datasha takura cikin aljihunshi.
Kai ya girgiza mata yana fadin ki karba kema ba naki bane ai tace bani nace ka barshi ba zan jefa mata kudin ciki ai kadai barmu ke nan yanzu gashi madam ta fara nadaman rashinka wurin mu ko jiya saida tayi maganan ka.
Nabar wurin ku kenan har abada bana son harka da wullakanci gara naje na nemi wani sana,a zaifi min da cin fuskan madam kullun a kanmu.
Kakafa ta tambayeshi tana nan lafiya ya bata amsa yana balle marfin ruwan daya karba a hannun ta tare da cuna mata matattan dari biyu lokaci guda da karban goran ruwan ya nufoni yana fadin.
Dan sauke kafanki ki wanke fuskanki zai kara lafa maki In sha Allahu wai dama ashe kasantane haba nayi mamaki ranan nan data mika min kudi da abinci in baka ai ?
Veronica please excuse us bata da lafiyane ta kalloni tana fadin ayyah sannu ko Allah ya sauka Ahmed sai gani na biyu ke nan ko duk lokacin ina jin abinda suke fada saidai surutun yarinyar yana shiga min har kasan raina a lokacin don natsuwa kawai nake son samu.
Miko hannu nayi da niyar ya ban sai yace miko hannu na zuba maki ki wanke fuskanki dashi kara miko mai hannu nayi tare da kwatancen zansha.
No ba zaki sha ruwa yanzu ba wanke fuskanki kawai zaki samu relief kadan ko a zuba maki a kafanki zaifi kice zakisha.
Na sake kada mashi kai alaman naji da kyat na sauko da kafana kasa ina gyara gyalen dana dora a kaina lokacin don Allah ya taimakeni na yafa gyalen da kyau yana rufe min jikina.
Haka bujen dake jikina ya sauka min har kasa dadin saka suturan kwarai a jiki ke nan don baka san me zai faru da kai ba tunda rayuwan mu ba a hannun mu yake ba.
Taro hannun ki ya fada a cikin sound din command a gareni na tara ya zuba min ruwan tare da fadin wanke fuskanki dashi nayi yadda yace din sai ya zuba min a kafa lokaci guda na sauke ajiyan zuciya a wurin.
Shi kuma yana fadin sannu yanzu ya kikejin kanki ya lafa ko har yanzu yana sarawa ya lafa na fada a kasalance har lokacin kuma akwai wasu da suka zubawa abinda mukeyi ido daga nisa suna magana saidai sunki suzo su taimaka minne su don kowa na gudun shiga wahala yanzu.
A wahalce na dago kai tare da fadin na gode dan uwa bai amsa min ba sai cewan da yayi zaki iya zuwa gida da kanki kai na kada alaman eh ok shiga motan mu gani ya fada yana tsureni da idanu.
Ganin yadda na koma ciki ina kokarin tayar da motan yasa shi fadin fito ki koma baya ki kwanta har kan ya dan sakeki don tuki a gareki yanzu gangancine.
Yadda yake ban umurni zaki rantse shidin dan uwanane na jini ba lkkacin muka hadu dashi ba don yadda yake nuna min kulawa sosai da damuwa.
Fita nayi idanuwa a kaina ya bude bayan motan na shiga ya rufe ya dawo yayi tsaye a gefe window din motan yana mazurai da idanu ga masu kallon mu lokacin.
Yan mintina kadan ya duko yana fadin zaki gane gida kuwa a haka dana lalaba nakaiki gida yanzu kai na dan gyada masa dama key na jikin motan bawai sosai ya iya mota ba koshi lokacin da yayi wankin mota da yana secondary a lokacin ya koya bawai ya wani gwane bane da tukin.
Haka ya lalaba ina nuna mashi hanya saida muka kusa shiga layin mu na dan jawo jakkana da kyat wayana na lalabo a ciki na dannawa ummah kira ringing uku ta dauka.
Nace ummah banda lafiya gani nan wani zai kawoni gida yanzu salati ta saka tana mikewa tsaye wurin mama ta nufa ta fada mata abinda ke faruwa.
Saidai tana kai kofan shiga part din taji muryan mama da yar uwanta suna zagin ta haka yasa ta juyo bata shiga ba ta nufo waje lokacin har Tani mai aikin ummah ta fita wajen.
Zuwan ummah yayi daidai da isowan mu gidan an bude get din gida muna shigowa lokacin suka nufo inda motan ya tsaya sannu da kokari suke mashi ya fito yana gaidasu.
Nan Tani ta bude bayan motan ta fito dani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login