Showing 120001 words to 123000 words out of 304363 words
KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Washegari an kare buki a zatona su gwaggo zasu kara kwana garin don naji suna fadin suna son shiga kasuwa su danyi sayayya don haka al,adan mata yake idan anje wuri buki bayan an hada buki zasu dan shiga kasuwa su yawata su sai abubuwan amdanin mata a garin.
Amma ina shiga don gaidasu da kwana sai na samu suna hada kayan su wai zasu koma gida a ranan cikin mamaki nake fadin gwaggo ba kunce kuna son shiga kasuwa ba ?
Bar wanan zancen bari dai mu tafi gida asirin mu rufe gwaggo shafa ta fada do munfi dasawa da ita dama ban daddaraba na sake fadin kasuwa fa kun fasa zuwane gwaggo ?
Maganan kasuwa akai tunda abu ya zama kamar kora mun hwada mata cewa gobene zamu komawa gida amma matan nan tace a,a mu tafi yau don a rage tunda an gama buki.
Duk da nayi masu gwai da hakan ya faru dama ance inda kwadai da wullakanci ai su suna ganin wurin cine sun kwaso jiki zuwa mata karan buki ga irin abinda tayi masu nasan ma wani maganan basu fadi a gabanane.
To nima ko yau zan tafi zan biku mu koma gida bari naje na hada kayana na fada ina juyawa sai naji gwaggo Ai tace ke mukan baki bin mu a dauka mun kitsa maki wani zancena kuma ?
Ki dai jirasu ranan da sunka gama sai ku taho tare awo don walle cewa za ayi wani shirine kuma munka hada ki bimu dauri ki taho da shirin haka kega ba wanda zaiyi zaton wani abuna yanzu matar baffa ta fada.
Waka zaton wani abuna tunda tace gida zata yau itama mi da baku barin ta tahiyata gida tunda ankare bukin ga gwaggo shafa ta fada a hasale.
A,a shafa walle hakan na iya jawo wani tsegumi kuma wadda naga kan matan ga na rawa tana iya kiran office ta kulla muna sheri kesan shiko namijina ba tsayawa bincika zaiyi ba yahaye.
To ya hau din mana ni dai in tace gida zatana walle ban hanata tunda ta tashi mi da baku son gaskiyana wai wanga buki hwa an kareshi mi zata tsayayi nanan ga ?
Shafa an ba hakana bane in munyi hakan bamu kyauta ba gaskiya tunda dai ba tare da ita munka taho ba shigowan mommy dake magana sama sama yasa sukai shiru a lokacin.
Tana gaba wata mace na bayanta dauke da bukitan robobi na bukin ta shigo tana fadin kinga Ai ga kayan bukin ku nan takai zaune ta fara masu bayani.
Suka don kitihi sai godiya suke mata suna yabawa banda gwaggo shafa data fake da shirin kayanta a lokacin saida taji mommy din ta gama lissafi bata amci su mama ba da ummah ta dago tana fadin.
Ina na kishiyotin ki sai tayi wani kwalkwal da idanu tace ai basuzo min buki ba kinga ke nan ko ban basu ba banyi laifi ba ko ?
A,a wagga maganan ba gaskiya bana yadda kinka bada na kowa haka zaki bayar akai masu nasu din basu taho ba mugashi mun taho ba har ita hjy salma da yarta ttataho ?
Gara ita ina iya badawa akai mata din hjy salma bata taba nuna min komai ba koda kuwa tana dani a zuciyar ta wani kallo nayiwa mommy din dayasa ta farga da sakin layin da take shirin yi a lokacin.
Yarki hwa bin mu zatayi tace gwaggo Ai ta fada wace zahra wai mommy din ta fada ita hwa shina muka magana kinka shigo ai.
Munkace ai ba tare munkazo da ita ba ta bari dauri ta biku in kun tashi zaifi sauki tunda tahiyan mu ba gudana ba.
Ina ma motar zai isheku da ita ina ku biyar ne a ina zata zauna din sai naji gwaggo shafa tace matsa mata zamuyi har nawa salma take da bai daukan mu.
Kai shafa na gaya maki ki barta a nan tunda nan munka taho munka sameta balle ba inda zata tafi gaskiyane bata so shine nayi mata fada take wanan fushin.
Wai ki duba dan gidan Tahir manir mai kudin gaske a garin nan shi yazo yace yana son zahra amma yarinyar nan taki bashi hankalin ta tafi ganewa tsamayen samarin ta na zamfara dake hure mata kunne.
Wallahi haram koh hwada maki Zahra na kula samari yayi karya yarinyar da kullun tana gida kulle kamar macen aure har fadan haka mukeyi ko buki ake a cikin dangi baki ganin Zahra.
Eh kwarai inda wanan kan zahra haka take kamar me tsoron mutane bata fa zuwa ko ina ita gwaggo Ai ta fada nidai ina jinsu.
Wai kuna wanan maganan kamar baku san dan yau ba kuna ina da take kula wani fakirin yaro a gusau saida Alh tayi mata iyaka dashi don Allah kuyi shiru don ku baku san komai ba.
Wani irin malolon bakin ciki na hade a makogorona don ganin irin sherin da mommy ke kokarin azamin don haka bansan lokacin da nace Allah shine shadata kan kazafin da ake kokarin dora min wanda banji bangani ba.
Zahra ashe haka kike sululun boni cuta zalla nice zan maki kazafin ko wa abinda na sani shina fada yanzu yaro kuma in bakya son shi shike nan gari da yawa maye bayacin kansa ai .
A,a kada ki dakata tata ai don ita har yanzu yarinya ce yo ke kuwa ana son ki da arzikine ai yan mata nawa ke zaman jiranshi koke albarkacin hjy dake tare da uwarshine ai.
Wanan matar da suka shigo tare da mommy don dakin ta dauko abin bukin data kawowa su gwaggo ke wanan maganan .
In bataso ai sai a barta din wani bai auren matar wani haka wata bata haihuwan dan wani sai da busurun ta gwaggo shafa ta fada sai naga mommy din ta mike tanacewa wanan matar su tafi ta sallami mutanen Abuja.
Ni walle ban yarda da wanga cin fuska a,a za,a tura yarinya wurin maza kamar maamah aka hwadama haka har yaushe maamah takena ?
To gaskiyan Allah bamu zuwa da ita gida don in munyi hakan kamar mun nunawa hjy karima wani abune gwaggo Ai ke fadi ke mama hakuri zakiyi har randa kunka koma abuja kega daga can sai ki dawo gida.
Don ko yaya fada zaiyi in yajiya mun taho dake gida kesan mazan ga wadda suke in suna borin aure gaba daya lissahinsu karewa yakai.
Tsayawan ki da kun koma Abuja ki tahowanki gida ni dama kada mu barki anan ta canza maki huska nakawa don yanzu tsoro matan ga ka bani mace ko yan uwanta basu mata shedan kwarai ai kega akwai matsala.
Ina kallo suka tafi tunda na juya na koma cikin gida ban sake fitowa ba ina kuryan dakin hjyn su mommy din har bayan la,asar saidai in tashi inyi sallah in koma in kwanta.
Mahaifiyar maryam ce ta shigo dakin jin muryan ta da nayi na mike ina gaida ita don dan zaman mu dasu na fahinci muryan matar.
Ta gama daukan abinda zata dauka a cikin kayan su ta juya zata fita sai kuma ta juyo gareni tana fadin waiko kinci abinci zahra ?
Tun dazun idan na shigo kwance nake samun ki daga falon tsohuwar tace yanzu nake zancen yar nan a raina ashe kema kin kula da hakan.
Bana cin abincin ne na fada haba dai yata tashi kici koda kadan ne ko kisha tea ga kayan tea nan ai kinsan inda maryam ta ajesu dacewa yarta da muke tare.
Idan zansha zan diba mama nagode na fada ba komai keko ai an zama daya yanzun kuma nadai kulane cewa duk na shigo dakin nan tun safe kina nan kwance su maryam kuma suna can gidan da uwayen su basu dawo ba.
Bansan irin karima ba bata da lokacin kula yarinyar nan yaya zakazo da mutum gari ka dinga barinshi shi kadai ai dole yarinya ta shiga damuwa.
Hjy ai kinsan halin karima wurin hutsanci tun jiya nake jin tana complain kan yarinyar nan abu ne ba daman kayi magana yanzu ta hauka da sababi kuma.
Azuciyana nace Abba ashe ya kwaso muna bakar ashanace kona gari kowa bai maganan dadi a kanta wanan wata irin mace ce wai na tambayi kaina ?
Jikin nasa ya danyi dama sosai zuwa safe hakan yasa ya fito har jam,in asuba ya samu yaje saidai bai dade ba ya dawo dakin shi ya shiga yana karatun kur,ani ko zai rage jin abinda yake ji a lokacin.
Suratul Yusuf yake karantawa a lokacin a cikin daga murya har wa yanda ke gidan suna iya jiwoshi kadan kadan daga inda tsohon nan yake ya kada kanshi yai murmushi jin yadda yaron matashin yake karatun nasa.
Bayan shattu ta gama abin karyawa ta hada ta kai mashi har dakin yayi mata godiya ta fito ya tashi zaici ko malam musa ya tambayeta yana kallonta yaji amsan da za ta bashi.
Eh to yana dai zaune yana tulawa nadai aje masa na fito saidai naga kamar yaji sauki sosai yau din ta bashi amsa.
Sai zuwa karfe tara na safe rana ya haska ko ina ya fito daga dakin inda ya samu malam musa a zaune a dan rumfarshi yana rubutu a allon shi da bakin tawadiya.
Sannu da hutawa Ahmed din ya fada lokacin daya kawo kusa da dan rumfar malam musa din ya dago kai yana fadin yarona anfito ya karfin jikin naka.
Da sauki baba Alhamdullahi sai ya kai zaune malam musa din na fadin masha Allahu na dauka yau zakaje asibiti amma tunda kaji sauki Alhamdullahi.
Ya jawo wani tasa da ruwan tawada yasa shi baki ya tara wanke rubutun da yayi din ga mamakin Ahmed sai yaga tsohon ya miko mashi ruwan rubutun yana fadin yi bissimillah ka kurbe wanan tsarine da kariya daga ko wani irin abin tsoro ga bawa.
Baiyi mussu ba ya karba ya kafa kai ya kwankwade ya daureye tasa ya kube ya aje a gefen malam musa din sai dan shiru ya biyo baya kafin can Ahmed din yace baba dama naso fadama ranan laraba insha Allahu zan koma gida.
Cikin bazata da tarin mamaki a fuskanshi malam musa din ya dago kai ya kalli bakon saurayin nasa yana fadin yarona wani abu akai ma da bai maka dadi ba ko yanayin muhalin namune bai maka ba ?
Kai Ahmed din ya kada yana kokarin kakaro murmushi a fuskanshi kafin ya iya fadin wallahi ko daya baba baku min komai banda Allah ya saka da alheri banda abinda zance a kanku yanzu kuma.
In bashi ba yaushe zaka kawo maganan gida yanzu kai da ka baro wuri mai nisa kazo nan neman magaifin ka ana tsaka da nema kuma kace kai ka tashi gida zaka.
Komawa gidan a yanzu ai baida amfani a gareka ba tare da kasan waye mahaifinka ba har in kana ganin cewa neman da muke masa bai maka bane sai mukai cigiya gurin magabata dama haka shine tsarina na gaba.
A,a baba ba sai kaje ba don na gano mahaifina da kaina wanan fitan da mukayi da dan bayaro jiya kuma har nayi magana dashi a jiyan don hakane nake sin komawa gidan ma.
Tsaye Shattu take tana sauraren su tun soma maganan su da taji malam din na fadin ko sun mashi ba daidai bane a nan din yasata dan tsarguwa.
Sai kuma taji saurayin na fadin ai ya samu ganin mahaifinshi ya gano ko waye shi din haka a cikin ruwan sanyi anya ba dai fadi yayi ba don ya kwantar masu da hankalinsu kada su zargi komai ga tafiyan shi ?
Dana kace ka sadu da mahaifinka a garin nan yace kwarai baba don hakanema nake son komaw gida yanzu don na fahinci yabarni da gangan bawai wani matsala aka samu ba.
Azoto da talauci ko rashin lafiya ko rashin zarahi yasa ya kasa waiwayana amma yanzun na fahinci cewa hakan ra,ayinshine kawai ya wofintar dani haka cikin duniya.
Subbahanallahi duk meyasa kake wanan tunanen ko zato akan abinda baka tabbatar dashi ba gareshi kada ka manta cewa koma yaya yake shine dai mahaifin ka daya kawo ka duniya.
Wani malolon bakin ciki Ahmed din ya hade kafin yace duk nasan da hakan baba nasan kuma abinda yasa nace haka baba.
Don baya cikin yanayin rashi ko damuwa saima falalan da ko irin mu goma ya watsar zai iya neman mu cikin duniyan nan.
Amma babu tunanena a zuciyan shi yadda naga rayuwan shi na tafiya ya samu wasu diyan yanzu ya manta da zancena ga baki daya.
Murmushi malam musa din ya sauke a fuskan shi kafin yace kana ganin haka daine baka san meke zuciyarshi ba game dakai ai don haka karka yanke hukunci akan abinda baka sani ba ko kayi zato.
Waima waye mahaifin naka dake masa wanan hukuncin hakane don har yanzu ban fahinci inda zancen ka ya dosa ba ta yaya kayi ka ganoshi kuma ina ka ganshi har kasan shine din .
Zuwan da wata mace tayi gidan suka tsaya gaisawa da malam din yasa Ahmed din tashi ya bar dattijon a wurin ba tare da dattijon ya farga da hakan ba .
Dakinshi ya shiga ya soma hada kayan shi a cikin fushi da bacin rai ya mike ya dago sai kuma ya fita waje ya rasa me zaiyi a lokacin don haka ya nufi inda garken gidan yake yaja ya tsaya yana kallon su.
Idon shi ya sauka kan akuyan nan me zubin uwar garke sai yaga kamar akuyan na hawaye lokacin dan kara kura mata ido yayi sisai.
Tabbas hawayen takeyi ba karya idonshi yai mashi ba hawayen take sakewa a idonta to hawayen meye ya tabayi kanshi tare da nufar inda take kiwo din.
Yana zuwa kusa da ita tayo kanshi tana zagayenshi tana dan tuma kafin ta wani ja baya ta dawo ta kwanta a gaban shi tana cigaba da tuka tare da dan rufe idanunta.
Tsugunawa ya samu kanshi a gabata yayi yakai hannunshi saman bayanta yana dan shafata a hankali yana fadin .
Allah kadai yasan dalilin hakan a garemu nasan akwai wani sirin dake boye ga hakan koma maye ubangiji Allah ya mayar muna dashi alheri a tsakanin mu.,
Haka yai ta shafan akuya yana jin wani iri a zuciyarshi wanda shi kadai zai iya fassara irin abinda yake ji a rayuwan shi lokacin sai can ya kalli akuyan yace.
Uwargarke kokece ko bake bace in Allah ya kaimu gobe in sha Allahu zan koma gida sai kuma in Allah ya sadamu da alheri sa ke nan.
ZAINAB IDRIS MAKAWAP🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
4️⃣1️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Bamu hadu da mommy ba har wajajen goman dare kafin naji muryoyin su kaf diyan dakin su suna magana akan abinda ya shafi rayuwan su.
Saidai zancen ya shafi wani rikicin daya tasone a tsakanin su lokacin bukin uwartake kolatin sasanta tsakanin su a lokacin.
Saidai duk laifin akan mommy suka dorashi inda ita kuma bata yarda da hakan ba inda nake jin muryan mommy na fada da karfi da alama bata yarda da korafinsu a kanta bane.
Kafin naji wace ke biwa babban yar nasu ta sako zancen na a cikin maganan su tana fadin irin abubuwan da mommy din tayi ta nuna mata rashin jin dadin hakan da tayi.
Nan ta sake daga murya garesu tana fadin ina dai wanan kuma ba matsalan daya shafeku bane ko kuma ita din ma zaku saka min idone a kanta yanzu kuma.
Duk abinda nakeyi sai a zauna ana sakawa mutum ido don kawai ayi mashi sheri ace ga abinda mutum yayi in bashi ba meya kawo zancen yar mijina a bakim ku yanzu ko ita ta fada maku hakan kum ?
Bata fada muna komaiba wallshi uaarsu ta fada sai naji tace kada tayi mana ni dama ai don ibanta nake son na taimaka mata tunda taki ai shike nan gata ga fakirin nata da take so ai sai tayi ta kaya.
Daga haka na daina jin muryan su ina nan wurin ina tunane har barci yazo ya daukeni na manta da zancensu .
Komai nasa ya gama hadawa a lokacin ya shirya tsab don gari yake jira ya waye yayi sallama da masu gidan yatafi don alkawari ya daukarwa kanshi cewa ba zai kara kwana wanan garin ba kuma.
Haka kuma yayi alkawarin