Showing 96001 words to 99000 words out of 304363 words
wani gari can inda ake samun hatsi da sauki mu dauko don haka zamu kwana daya ko biyu a can din saidai idan Allah ya dawo damu lafiya ga wanan ki rike a hannunki ya ciro hannunshi dake cikin aljihu da kudi yana mika mata.
Karba tayi tana saka mashi albarka ya amsa da amin tare da fadin na tafi a gafarce mu yasa kai ya fice daga gidan dije bata daga daga inda ya barta ba aikai sallama a gidan ta amsa.
Wani yarone ya shigo yake fadin ance anawa Amadi sallama Dije ta amsa da fadin Amadi yanzu ya fita daga gidan nan yayi balaguro.
Yaron ya juya ya fita bai dade ba ya sake shigowa yace wai ance ina yaje dan nan ina zan sani ina nan zaune ta fada da alaman fada.
Ta zata zai dawo a lokacin saidai shiru bataji dawowan yaron gidan ba kuma sai yamma ta fito kayan data gani a jingine cikin buhu ajeyine ta tsaya tana kallo a cikin mamaki.
Kafin tace yanzu meye wanan Amadi ya aje min nan kuma ta nufi wurin kayan tana duba cikin mamaki takai hannunta taushi taji hakan yasa tayi zaton kayan gwajon shine ya aje a wurin ya manta kafin ya fita.
Abinda zataci ta fita nema a waje ta sayo tuwo da miyan taushe irin na sayarwa da ake samu a layi ta sayo don taci don ba zata girka komai ba don Amadin baya gari.
La,asarne lis lokacin amma ina kwance na kifa ciki ina tunane a dakin ni kadai naji wayana ya dauki kara lokaci guda ban dago ba don naso na share kiran a lokacin.
Hannu na mika na dauko wayan na duba lamban kasan waje nagani yana kirana lokacin mamaki ya kamani tare da tsoron waye wanan din ke kirana.
Kodai ya Jafar ne dake can na fada a raina nakai hannuna da sauri na dauki wayan muryan namijin bature ne naji yana fadin hey na amsa da hello.
Yace young lady kina magana da Jerry daga Paris ko zaki tuna da mutumin da kika taba kira da wanan number shekara daya daya wuce akan wani wallet da kuka tsunta a cikin gwanjo.
Cikin mamaki nace da wanan layin kuwa yace kwarai kuwa kun kirani kuna a Nigeria kun sayi kaya kuka samu wallet dina da kudi da katina nan dai ya tuno min da duk yadda mukayi dashi a ranan.
Ohh i remember na fada yace don Allah idan son samune ko zan duba bayan wanan katin na fado mai wasu number dake rubuce a jikin takardan number guda ashirin ne.
Kayi hakkuri na fada ka dan bani lokaci don yanzun katin baya tare dani don nayi tafiya amma zanyi kokari naga na turoma da number insha Allah.
Koda na kashe wayan sai mamaki ya kamani don lokacin da muka gama magana da Baturen a ranan yace zamu iya amfani da kudin sai ya watsar da takardun na duka na tattarosu na na watsa jakkata ina ganin su kuma ban zubat ba.
Haka kawai nake jin takardan zasuyi amfani wata rana son haka banyi gigin zubarwa na aje sai gashi yau wajen shekara daya da rabi ke nan saiga kiran shi ya shigo min a wayana da wata bukata kuma.
Tambayan kaina nakeyi da yanzu na watsar da wa yanan tarkacen nasa yaya zanyi anya kuwama wanan dan katin yana nan kuwa a hannuna .
Kallo lokaci nayi na mike da sauri zuwa bandaki na dauro alwala na fito nayi sallah a nan inda na sallame sallah na dauko wayana na kira ummah nace taba kanina waya muyi magana dashi.
Ya amsa a hannun ummah din nan na fara masa bayanin abinda zai mun har dakina yaje da kyar na samu ya gano jakkar da nake nufi ya dauko yace min yaga katin a ciki naji wani irin dadi a lokacin.
Nan nasashi ya katanto min number da mutumin ke nema a jikin katin ya turo min da komai yai mi kuma photo n katin ya turo duk a wayan ummah.
Ba bata lokaci na turawa mutumin sako ban kira ba duk ni kadai a dakin nake bidirina nagama bayan nayi sallah na kwanta ban fito ba sai safe kodana fito babu kowa a gidan duk sun fita.
Allah ya gani nikan ba zance naji dadin zuwa wanan hutun da nayi zuwa gidan Abba don irin sabin rayuwan da nake gani a gidan yanzu kuma Abbane mai yarda da hakan wai.
Gudu sosai motan keyi don haka karfe shidda na safe suna kano suna karyawa inda daga nan zaiyi furfuren mota da zai shiga motan zuwa yola daga kano
ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
3️⃣1️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Jin yawan kudin motar yasa ya fara budan ido yasan dole gari da nisa sosai da nan din don sai a lokacin yaga kasadanshi na kamo hanya shi kadai zuwa wanan waje.
Yanzu yake daya sani ya sanarwa Dije zancen tafiyan shi din duk da yasan cewa ba yarda da hakan Dijen zatayi ba.
Amma a wanan tafiyan haka mai nisa ya kamata ace ya sanarwa Dije din kafin yazo ba wai ya kamo hanya haka shi kadai yazo ba yadda yayi din a yanzu.
Sai Ido yake faman rarabawa yana kallon gari da ikon Allah gashi tunda ya bargida baiga wani idon sani daya sani ba a nan hakan yasakashi fara daya sani da ya hakkura ya zauna inda yafi wayau.
Saidai a take wani zuciya yace dashi haba kamar kai ba namiji ba dai Ahmed haka zaka zauna ana ma gorin iyayye a cikin gari alhalin kana dasu raye.
Waya sani ko mahaifin nawa baya raye yaba kanshi tambaya to ko baya raye dai zanga wasu nasan su su nasani suka tabbatar da ya haifeni a duniya.
Duk da gajiyan dake jikin shi bai hanashi sakawa da kullawa ba a lokacin yana zaune a karshen mazaunin passengers ya kama haban shi da hannu guda .
Wana fitowan ba gudu baja da baya gareshi ko ta halin kaka so yake yaiwa kanshi gata a idon mutanen da yake rayuwa a cikin su duk da mutane da yawa sun sha sheda shiba shege bane.
Da ubansa sabani ra,ayi kawai aka samu yai fushin zuciya bai juyo ga danshi ire iren haka kowa ke tofa albarkacin bakin shi a kai suna fadin iya sanin su kan matsalan nashi dashi yake ganin shi kadai ya shafa.
Don hakane ya yanke wanan shawaran a zuciyan shi cewa zai tafi har garin ya binciko mahaifin nasa ko yan uwanshi bisa taimakon wani mutum da akace tare sukazo dashi mahaifin Amadi din garin suna yara.
Duk da mutumin ya nuna cewa shima baisan shi ba haduwa duniyace kawai sukayi a ibadan dashi har suka zama abokai har yakai sin sami ubangida dan zamfara da suke sana,an dabbobi tare har yakai sunji dadin mutumin sun biyoshi nan zamfara sun zama kamar yan uwa dashi.
Amma shidai ainihin dan kanone kuma yasan shi mahaifin Amadi din yana fada mai cewa shi dan Mambila ne kuma ainihi iyayyenshi sanan nune a garin da kace gidan hardo Dume za a akai ka.
Wanan zance Amadin ya rike a matsayin makami a gareshi yaji yana da karfin tafiya a zuciyar shi koba komai zaiyi kokarin kai kanshi garin ya binciko waye ainihin mahaifin nasa a nan.
Haka yasa yai amfani da daman shi daya samu yanzu tunda ya gama karatun shi kafin ya fara wani abinda zai samu na dogaro da kanshi ya hada yan kudaden dake gareshi ya kulla wanan tafiyan a asirce ba tare da sanin kowa ba a cikin dangin shi.
Tun yana kallon garuruwa har yayi barci ya falka driver sai faman sharara gudu yake dasu a mota saidai sun tsaya a wani gari sunyi sallah sunci abinci a garin.
Dan samakon da akasarin passinger mutanen motan sukayi a lokacin yasa suka sauka akaci abinci suka kara daukan hanya kuma.
Kwance nake ina barci ni kadai a dakin nawa sai faman juyi nakeyi a gado don mafalkin da naketayi marasa kyau daya shafeni gudu nake faman yi ina neman ceto.
Don wani iska mai kama da guguwa dake bina a guje ina gudun ceto kada ya lailayeni a lokacin wani gidane a gabana na gani aka miko min hannu kamar an fisgeni da karfi alaman wani ya ceceni na falka a tsorace.
Da kyat na bude idona sai naganin a wani daki na daban sai daga baya na tuna da inda nake na dade a hakana kafin na mike zuwa bandaki na kewa na fito.
Duk da ummah ta fada min na dinga kokarin yin sallah dare amma sai nakejin kasalan yin hakan a gareni saida kyat nake samun daren da nake rayewa ina tsayuwan daren .
Hakana koma wani barcin ya kara daukana wani mafalkin nakeyi saidai wanan karon ganin kaina a wani waje dake da yawan tumfafiya gasu nan birjit a wurin ba iyaka.
Na rasa me zanyi a lokacin in ceci kaina a wurin ina nan tsaye ina tunane sai na kai zaune ga wirin ba motsin komai ina nan zaune ne na kurawa wasu halita a jikin wani iccen tumfafiya dake kusa dani ido ina kallo gashi ni ban san me nake a wurin ba, sai can naji motsin a bayana na juya .
Wani mutum naga yana nufoni dattijone sosai mutumin yana cikin fararen kaya yana min murmushi tare da sallama.
Kaman nin mutumin yayi min kama da wanda na taba sani ko naga fuskan a wani wuri kafin ya karaso nake faman tunanen hakan.
Na amsa sallaman da sauri cikin damuwa yace zaman ki a nan shine alherin a rayuwan don zaki kubuta daga sherinsu har abada.
Don kina tare dasu ta ko ina baiyanan ki a nan shine alheri a gareki ya zama hanyar kubutanki daga hannun makiyanki don suna son saka rayuwanki a ukuban su a yanzu na har abada.
Saidai kuma zasuyi ta wahalan cin maki amma ba zasu taba samun nasaran iya hakan ba gareki don ke din da tsari a jikin ki wanda ba kowa Allah kewa wanan irin baiwan ba a rayuwa.
Don ke din kina tare da tsarin Allah ko yanzunma suna kan neman ki ba zasu hakkura dake ba sai sunga abinda zai faru ya faru dake zasu dauka sun gama da rayuwan ki gaba daya.
Basu san cewa kin riga da kin masu nisa ba a hakan sai daga baya zasu gano hakan gareji lokacin da basu iya komai a kanki zasu san suyi sake har kinfi karfinsu.
Kinga hanya nan ya nuna barin gabas da hannun shi yace ki bishi zai kaiki gidan ku ba abinda zai sameki in kin shiga gidan in sha Allahu.
Nuna min hanyar da yayi yasa na dago kaina ina kallon hanyar daya nuna min din babu komai a wurin sai yawan tumfafiya gasu nan kore dasu sunyiwa wani irin luf luf a wurin gwanin ban sha,awa.
Na dawo da kallona ga tsohon saidai babu kowa a wurin kamar ba wani mahalukin da ya taba tsayawa bayan ni har nayi magana dashi a wurin na yunkura na mike haka naja kafata da kyar na nufi wurin daya nuna min din.
A cikin ganyayen tumfafiyan masu tsawo da tsayin duhu nake tafiya da sauri sauri gudu gudu ina sauri in bar wurin amma bancin ma iyakar wurin ba a lokacin.
Ban kuma fasa kutsa kaina ciki duhun ganyen tumfafiyan ba sai ganin kaina nayi a gidan kakan Ahmed tsaye ina dan waige waige a tsakar gidan su din daga haka.
Har na falka daga barcin don alam din wayana dake kara a lokacin alaman shidda na safe yayi ke nan a gurguje na mike na shige bandaki na dauro alwala don na gama makara ga sallah asuba ranan.
Wanan mafalkin yasa ni jin wani yanayi na daban a jikina don tun tashina nake jin kasala a jikina ko ina yana min ciwo zakice a fili nayi wanan gudun ba a cikin mafalkina ba.
Ranan ban iya fitowa ko falo ba har su mommy suka fice wurin aikinsu ni kuma ina kwance a dakina a galabaice sai wajajen sha biyun ranane Tabitha ta leko dakina tana fadin.
Anty Anty yau lafiya kuwa baki fito ba barci nake sosai a lokacin a galabaice nake jin muryanta sama sama a kunnuwa na hakan yasa ni bude idona da sukai min nauyi a lokacin ina kallon ta bushi bushi tsaye dan nesa kadan dani.
A cikon murya mara sauti nake fadin yau bana jin dadin jikinane nake kwamce ina kokarin son in juya itakuma tana tsaye a inda take idon ta yana kaina tana kallon yanayina tare da fadin ayyah sannu ko .
Na hado maki ruwan zafi ki sha shayi ta fada cikin tausayawa nace barin yi wanka na fito kitchen din tace Allah baki lafiya nagode na fada a daidai lokacin dana samu na mike zaune.
Ta juya ta fita na dan dade a zaune don sanin danayi cewa baida kyau daga rashin ka kace zaka sauko daga kan gado ba tare daka dan dade a zaune ba na wasu yan mintuna kadan.
Don irin hakan yana jawa jikin bawa wani matsala a take attack zai iya kama mutum a wurin yasa na saba da idan na tashi zan danyi minti biyu ko uku zaune kafin na mike na sauko.
Bandaki na nufa na watsa ruwan zafi ko zan samu dan karfi a jikina na fito na murje jikina da manshafina na fito bayan na shirya zuwa kitchen.
Ina shiga Janet ta shiga yimun sannu itama na amsa Tabitha ta fara fadin madam yau ta fita ta kwashe kayan shayi muma ba a bamu shayin munsha ba.
Na danyi murmushi karfin hali ina fadin zakusha shayin ke nan tace in mun samu zamusha mana anty nace barin zo na juya zuwa daki na dauko kudi na kawo masu dubu uku nace su karba su sayi duk abinda suke son suci.
Gadiya suka fara min na dora idomie a wuta na dafa nan na fara jin gulman mommy da irin halinta na samu abubuwa da yawa da nake son ji game da mommy din a bakinsu.
Zaune nake na kasa cin abinci don bakina da nake ji harshi babu test a lokacin wayana na jawo na fara neman layin Ahmed saidai computer na fada min not richarble ..
Kira kusan hudu nayi mai ban sameshi ba yasa nayi mamakin haka don yana ganin kirana yaka dauka ko ya bari sai ya mutu ya kira da layin shi.
Irin haka yasa na kasa fahintar halin shi don shi mutum ne da sam baison aga gazawan shi a al,amari idan ya taso tsakanin shi da mutum din.
Yau kwana biyu ke nan baya gidan ganin cewa yamma ya soma a rana ta biyun a daidai lokacin dashi yake can yana kokarin shiga garin yola Dije kuma a nan zamfara ta tayar da hankalin ta sosai.
Har yakai ta fita ta samu malam tanimu da fitosanshi ke nan a lokacin take labarta mashi rashin dawowan Ahmed din gida da sunan zai shiga kauye ya sayo hatsi kamar yadda ya fada mata din.
Dijeki kwatar da hankalinki duk inda yake in sha Allahu Amadi yana lafiya don ni jikina bai bani cewa wani abu ya sameshi a can ba kinsan tafiya yadda yake.
Mai yuyuwa wanan karon yayi nisane da gida sosai don in kin kula abinci a yanzu yayi nisa sosai ba ako ina ake samun shi ba haka kai tsaye.
Malam Tanimu Amadi bai tafiya irin haka yakan danjene ya dawo gida don haka donle in damu da rashin dawoawan shi haka yaufa kwana biyu ake nema ga tafiyan nasa.
Namiji nefa Dije don Allah kijeki ki kwantar da hankalinki insha Allahu yana nan lafiya ba abinda ya sameshi a can saidai muyi adduan Allah ya dawo dashi lafiya yanzu kan.
Wanan zancen nasu da malam tanimu yasa ta danji hankalinta ya dan kwanta ta ta koma gida da dan kwarin gwiwa ba kamar yadda ta fito ba da farko.
Kowa ya fito a motan ga yamma da yayi sosai a lokacin don har wasu sun fara shirin alwala shima fita yayi da dan jakkarshi na ratayawa kalan ta maza a kafadan shi.
Wurin wani dan Union ya nufa da yake gani dattijone a wurin yace don Allah malam tambaya nakeyi mutumin ya juyo don jin hausan shi yana kallon shi.
Yake fadin mabila nake son zuwa don Allah ko za a samu motan da zata tashi a yanzu zuwa can ?
Malam da yamman nan kuwa gaskiya yana da wuya a samu motan da zai tashi yanzu zuwa can don yanayi hanyan a yanzu.
Amma ka dakata mu gani nan