Showing 129001 words to 132000 words out of 304363 words

Chapter 44 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33330

yau din zan mayar da ita gida na fada mata ta shirya ko.
Shiru sukayi ba wanda yai magana a cikin su saida ya fice take fadin abinda yaron kan nan ke mun bana son shi ina ruwanshi da zahra tunda ba wurin shi tazo ba.
Amma ai kinsan halin musa tunda yace zai mayar da ita gida yau ba fashi ke nan ki kyalesu ya mayar da ita din tunda sun kitsa hakan a tsakanin su.
Duk ina labe ina jin abinda suke fadi a lokacin hakan yasa na koma nayi kamar ban san da zancen tafiyan ba sai gata tashigo min dakin a fusace ta sameni nayi kwance ina karatun wani littafina.
Ta turo kofan a fusace tana fadin Zahra wai me haka ke nufi ne nifa da alheri na daukoki ba don sheri ba amma naga ana son a munafunce ni kuma ?
Na dan kalleta cikon mamaki ina fadin Mommy meya faru tace naji wai yau din nan zaki koma gida yayan ki na fadawa Abban ku nace yau mommy ?
Kamar ban san da zancen ba ina dan dagowa ehmana yanzu yake fadawa Abban ku hakan nace gashi ban ko shirya ba ban hada kayana ba ai.
Au kema baki san da zancen tafiyan bane ko me na girgiza kai tace shirmen banza toba inda zaki don naga shi a gadarance yake abinsa ni ba irin iyayyen sa bane don ya sani.
Nace a a mommy ki bari in tafi tunda yace hakan ina jin tsoron ya musa sosao kada yai min fada kawai na tashi na fara hada kayana dake watse a cikon dakin da sauri .
Ta tsaya tana min kallon mamaki kafinta juya ta fice a fusace kamar yadda ta shigo dakin da farko a hasale na kara hada kayana wanan ne silar barina abuja a ranan sai ganin mu kwatsam akayi mun dawo gusau baki a laikum.
Ga ya musa yasa Abba ya bada kudin da za a sai mun tsaraba Abban ya bashi shi kuma ya miko min su duk da muka bar gidan ya biya dani wani tsore nayi sayayya sosai a store din.
Ummah tayi mamakin ganina tunda na shigo ban zauna ba na nufi part din mama na gaida ita mun gaisa sama sama tayi min an dawo lafiya na fito.
Nan ta fara sake magana cewa ai ido ta saka muna dagani har ummah ita zamuyiwa munafucin mu nuna muna tare da amarya don a hade mata kai aga bayanta a gari ko ?
Kai haba mama yarinyar da Abba ya tilastawa da zuwa Abuja dole wai a can yanzu zata rika hutu don kawai an mata sherin cewa wani saurayi na zuwa wurin ta suma fa bada son ransu bane tatafi abujan hutu.
Aiba sheri bane don nina fadawa Alh komai na sanar dashi kada yaji yace an munafuceshi daga baya don tana ganin yaron da zubin fulani take wani dagawa mutane kai don rainin wayau.
Haba mama hakan ai bai dace ba tunda abinda takeso shi za a bata ta aura ai don baida kudi ai ita ta ganshi tace tana sonsa sai a barta da abinta ta aura.
Nima saidana fada maki mama ki kyalesu suyi abinsu ba ruwanki ba ita zata sha wuyanta ba ita kadai ina ruwan wani ya musa din ya dan harari Aishan yace .
Shi auren ne wuya ko auren wanda baida zarahi haramun ne akace ai shike nan taje ta aureshi din meya damu maimuna mama din ta fada sai ya jafar yace shine ai mama ki kyalesu please tunda tace shi take so.
Bayan fitan diya mazan daga gidan suka zauna nan da Aisha suna magana suna dariya tace ai barsu na fisu iskanci zasu raina kansu daga ita har uwar nata.
Ba mayana zai shigo wani sati ba ku fadawa masu neman ku cewa suzo suga Alh din nasan idan ya matsesu babu wani shi zasu fitar hakana din ai kinga ta fita zakka a cikin ku ke nan.
Shina so ki gane tuntuni mama baki gane hakan ba ai wanan zaifi masu zafi da ciwo ace kowan mu ya auri abin kwarai ita ko ta buge ga wanan tallakan karshe.
Kai Allah ya rabamu da kishiyar uwa mara imani macen da bata kaunan ganin diyan kishiyanta su karu da alheri ko wani iri amin.
Nikan tunda na shiga dakina na fara gyara duk da baida wani datti a cikinsa na gama komai nayi wanka na dawo na kwanta ina tunanem irin makircin mommy da abubuwan da suka faru a tsakanin mu a tafiyana.
Tare dashi akai sallah asuba don haka wasu suka sanda dawowan shi garin sai binshi mutane keyi da kallon mamaki har ya koma gida duk yana kule da hakan da mutane keyi mashi.
Kwanciya yayi don yana tare da gajiya sosai lokacin barci ya dan fara diban shine yaji muryan malam Tanimu da labarin dawowanshi ya sama ya garzayo ya ji labarin komai daga bakin shi kafin wani ya bashi labarin yadda akayi.
Sama sama ya dinga jiyo sallamanshi kafin yaji muryan Dije ta fito suna gaisawa dashi yaji yana fadin ace Amadi ya dawo shina niishigo taro nai.
Badai lahiya ya iso ba ya yunkura a lokacin zai tashi yaji amsan da Dijen ta bashi yasa ya koma ya kwanta yana sauraren su dije din na fadin .
Allah ya dawo dashi lahiya kasan dan yanzu da wayau shi yana wurin neman shi ana nan ana masa sheri da kazzalaha a cikin gari har wanda baka zata da zai maka sheri ba sai kaji mugun zance da mugun nufi a bakin shi.
Hakane kan Dije kesan in abu yazo sai mutum ya dinga tunane har ya fita cikin lissafinai adaiyi hakkuri abinda ya wuce a barshi ya wuce a yafewa juna tunda ana tare wuri daya.
Shikan amma abin ne da mamaki wai wanda ka dauka jigo shikama zagon kasa a boye yana hwadin maganan da bai dace ba a kanka dolena rai ya baci.
Yanzu dai kiyi hakkuri ina shi Amadin yake shina zaka in gaisai in ya tashi ina hwada mashi ka shigo naji ya koma ya kwanta dazun don hakane malam tanimu din bai samu ganin Amadin ba wanda baiso hakan ba a lokacin.
Sai bayan tafiyan shi an dan dade ya fito ya samu dije zaune bakin murhunta tana hasa wuta suka gaisa yake fadin yaji muryan malam tanimune ai.
Bar munafukin banza da wofi watau yaji labarin dawowankana shina ya taho ya samu na karaswa aini malam Tanimu ya bani kunya a garin nan .
Wai ace shi da kansa ke yawon bata muna suna yana aibanta maka sana ,anka da wani manufanai watau dama ashe dariyan hakori da jinine a tsakanin mu dashiya.
Saida haka ya kasance na gane masoyan mu na gaskiya da wa yanda basu son mu da alheri a garin nan kai Amadi naga abu a cikin garin nan bayan tafiyan ka nan ta dan bashi labarin irin abubuwn da suka faru shidai murmushi yayi kawai bai samu abin fadi ba lokacin.
Can ya mike ya shiga dakin dije din ya kwaso kayan daya shiga dashi jiya cikin dare nan ya dinga fitarwa yana mata bayanin komai a tsanake.
Ya kwashe ya mayar daki Dije sai faman saka mai albarka da takeyi tana mashi adduan gamawa da duniya lafiya yana amsawa son shi kadai yasan abinda yake ji a zuciyarshi lokacin kan komai.
Dakinshi ya nufa duk da ba wani kayan kirki a ciki hakaya gyara ya kakabe dan kuran dake ciki saida ya fitar da komai ya kakabe ya mayar ya koma gyaran gida ya gyara ko ina don duk gidan ya yamutse kamar ba wani mahalukin dake rayuwa a cikin gidan.
Hakama dabbonin duk sun rame da alaman basu samun kiwon daya dace a bayanshi nan ma ya gyaro ya zuba masu dan abincin daya gani a wurin.
Yana kule da kallon da uwar garke ke mashi tun safe amma addua ni a zuciyan shi sam bai nuna ya gane hakan ba gareta saima nunawan da yayi bai damu da itaba..
Baiyi aune ba yaji takai mai irin tunkudan data taba mai a baya a mambilla hakan yasashi juyowa gareta yana dan tsura mata ido na dan lokaci kafin ya mika mata sauran abincin daya rage a hannun shi din.
Daga haka ya juya ya bar wurun bai sake juyowa inda dabbobin suke ba ruwa ya diba ya watsa a jikin shi ya fito ya shige dakin shi ya shirya lokacin ya nufi dakin Dije don ya karya.
Bayan ya zauna ya fara cin abincin ne ya dago yace mata kinji labarin Rashida dacewa mahaifiyarshi don haka yake kiranta da sunanta.
Mamaki Dije taji jin ya tambayeta mahaifiyar nasa da bai damu da yin hakan ba garesu tace dashi ta bugo waya tana tafe don an kirata an sheda mata batan ka .
Wai mijin natane maciji ya taba ashe muka jisu kwana biyun nan shiru amma tace da sauki yanzu zata zo nan bada dadewa ba idan ta samu sararin hakan.
Allah ya kyauta yace da ita yaci gaba da cin abincin shi yana nazari kafin ya sake dago kai yana fadin lokacin da ta rabu da mahaifina ina da shekara nawa ne Dije ?
Kai Dije ta dago tana mashi kallon mamaki kafin tace dashi missa ka faye tambaya akan mahaifinka yanzu mutumin da yai tafiyan shi ba kara waigo inda kake ba .
Ko bai taho nan don kowa ba ai zai taho don kai amma tsawon shekarun nan ya kwashe ba tare da yasan ya bar wani halittaba a nan
Koma meye shidin dai mahaifinane ko Dije banda wanda zanyi tunkaho dashi a duniyan nan bayan shi banda wanda zai tsaya min ya zama min gatana a al,umma bayadashi.
To wai miya kawo wanan maganan yanzu kuma ina kule da cewa tunda ka fara girma ka dauki ranka ka dora akan shi ka daina tuna wanan mutumin.
Dole in tunashi Dije tunda an fara shegantani cikin garin nan ana kirana da mara asali mara gata a idon mutane duk da nasan ina da gata gatan da ba kowane keda shiba garin nan.
A kul akul naji ka kara fadin wanan haukan waya isa ya sheganta min kai duk garin nan in maka na mahaukaci bayan kowa yasan da auren sunna ma,aikin Allah aka haifeka.
In hakan yasa ka fara haukan hasashen maihaifin ka nada gata ko wani abu gara ka daina tun wuri don wanan kan ba gaskiya bane haka yazo garin nan fakirin shi.
Wanda na tabbatar da sanadin haihuwankane ma ya kawoshi garin nan ya biyo yan zuwa kudu yazo nan ya zauna tare dasu a karkashin Alh Akilu mai shanu.
Har Allah ya taimaka don darajan Alh da uwarka ta nace saishi aka dauketa aka bayar da ita amma kamar mai bakin uwa ana zaune kalau haka kawai da rana tsaka ya bijiro da barin garin nan kamar mai aljannu a kanshi ko kurciya ba yadda malam baiyi ba amma ya kyankyashe yace shi tafiya zaiyi.
Allah ya kyauta ya fada ya mike ya fice daga gidab lokaci guda kai tsaye waje ya nufa duk wanda ya ganshi sai ya tsaya yana kallonshi don labarin shi daya karade garin na batashi da kowa ya sani.
Ya dai sha tambaya da kallo kafin ya isa kasuwa ya sayowa dabbobin su haki ya hauwo mashin ya dawo gida zakace yadda yai wani haske ya murje yayi kyau kamar inda ya fito a cikin AC yake kwana yake wuni yadda yai kyau din.
Haka yasa mutane ke kara mashi kallon mamaki inda duk yabi bayan ya kawo masu abincin ya sake fita zuwa wurin oganshi na kasuwa suka dan tatauna dashi din a can.
Wallahi na gaji Yabi wanan tafiyan ma da kyar nakeyin shi a yanzu duk katarana ya zoje wurin hawan tsaunin nan dafata tayi ba tare data iya bata amsa ba ga magananta ta dan taka wani dutse ta haya tana mayar da numfashi da sauri sauri ta fara fadi.
Adda Wuro da badon bukatana bane ba yadda za ayi ace na hawo wanan wurin amma ba yadda na iya tunda ina son bukatana ya biya .
A rayuwana na tsani in bude ido inga anyiwa diyana yan uba a duniyan nan dubama ga yanzu yadda dukiyan Alh ke kara bunkasa sosai yanzu.
Ba zan zauna ina gani ba wata ko wani yazo daga sama yace zai cudanya damu da sunan inuwa daya a karkashin Alh ko ita wanan jakar na bartane ta zauna kamar yadda mai allon karfe ya umurceni dayi a kanta.
Na riga naba kare mahaifanta ya cinye don haka yanzu banda fargaban komai a gareta tunda mahaifanta karnuka sun lashe shi tuni bata da sauran amfani a yanzu.
Kai Yabi baki da kyau kiga yadda matan nan tayi kamar zata mutu lokacin nan kuwa amma kika nuna kina tausaya mata kene har da fita kasan waje da ita.
Saida hakan ne Addah wuro mazan yanzu in kayi sake kaine a baya balle irin nawa mijin da idon shi akan mace har indai yaga mace yana so yanzu zakiji zancen aurene.
Amma yanzu kinji shiru ba wanan zancen tundana hada shi da makulli na kulle na kada wanan tsohon rijiyan baki kara jin wani zancen aure ba kuma gareshi.
Haka suka sukai ta hira tsakanin su har suka isa bakin bukkokin dake tsakiyan amtsaunin da alaman mutanen wajen su dan wayesu nan aka gaisa akai ya kwana biyu.
Basu sha wuya ba wurin ganin bokan don yasan zuwansu wurin shi alherine garesu shida iyalan shi gasu dai fulanine amma kuma arnane su basu ko wani irin addini a rayuwan su sai tsafi.
Zaka kuma samesu da dan walki a jikin su mazansu da matansu ga tarin dukiya da Allah ya basu a tsakiyan dajin sun gabatar mai da abinda ya kawosu duk da yaga abune mai wuya a iya dakatan da hakan .
Amma sai ya nuna masu zaiyi aiki mai wuya ya hana hakan faruwa ya dai dan kwantan masu da hankali tare dayin surukulen jayewa Alh hankali ga barin wanan maganan .
Sukai mai sallama mai tsoka suka dawo a gajiye ace tsafi gaskiyan mai shi saiga Alh na fadi washe gari ta shirya su koma Abuja ya gaji da garin nan shi.
Haka suka tattara suka koma ba wanan zancen nan ya bar Jabbi da dan baro da mamakin yadda akayi lokaci guda Alh yabar zancen yaron daya tasasu a gaba a cikin yan kwanaki biyun nan.
Duk da haka basu share zancen ba a bangaren su don sunci gaba da bincike a tasu bangaren saboda sanin halin hjy Yabi da sukayi don irin hakan yasha faruwa a tsakanin suma ganin haka suka kulla da ita.
Har suke kwato abokin nasu daga halakanta idan tayi wani abin sai subi su warwale ba tare da sanin aminin nasu ba.
Wanan yasa ta tsanesu da duk wani abu daya shafesu duk inda ta buga kuma sunki rabuwa suna manne dashi ko yaushe don har abuja sukan bishi wani lokaci duk da sun san tsanar da take masu din.
Don hakane ma wanan karon basu tsaya bin ta kanshi ba koda ya tafin suka samu isah tella yai masu bayanin unguwar da yaran suke suka bashi sallaman da sukai mai alkawari suka tafi.
Ni dai an wayi gari naga sauyin fuska tsakani na da mama sai hakan yasani shan jinin jikina amma ban yarda na fadawa ummah komai ba.
Haka abinda ya faru dani da mommy ban mata hiran komai da naji ba kona gani saina barwa cikina zancen har muka koma school mukaci gaba da karatun mu kamar yadda muka saba.
Saidai karatun yanzu baija sosai don rashin Ahmed da bai samun shigowa yana muna bita ko yaushe a yanzu busy yake wurin neman kudin shi.
Mun dai hadu dashi sau biyu ya dan taba muna karatu daga nan bamu sake ganin shi ba kuma da mukai waya dashine yake fada min cewa ba zama garin ne yana yawan shiga kauyoka har wasu jahohin suna sayo hatsi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
4️⃣4️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Abubuwa sun faru a rayuwa da dama wanda ba dole saina tsaya fayace maki suba kamar yadda rikicin gida kan auku ko ya faru a wani lokacin.
Haka mukan danyi waya can ba,a rasa ba tsakanina da Ahmed wanda yanzu zumuncin mu dashi yaja baya sosai wata kila don yanzu bamu ganin juna dashine akai akai.
Wata kila kuma ya kama kanshi danice don yasan ba ajin mu dayaba dashi kamar yadda Abba ya fada mai haka haka kuma ko waya zai ai wata dayama ko fiye da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login