Showing 42001 words to 45000 words out of 304363 words

Chapter 15 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33301

ke na ko kai musa gobe ka fita da ita sai ka sayo mata duk abinda take so a nan.
Ai kafin Abba ya rufe baki mama tayi cikin shi tana fadin na fadama banson hakana wani sayayya za ai mata kome ta rasa yanzu da za aje kashe mata kudi kuma?
Can inda suke zaune da uwarta ba a sai masu abune halan tunda duk zuwa ina ganinta da sabbin kaya ai kai haba maimuna yanzu yarinya tazo maki hutu tayi wata daya amma ki bari ta koma haka ba komai daga nan.
Mikewa nayi na bar wurin don ganin kaina ana son samun matsala ga ya musa ya fara fadin haba mama su wa yan nan da ake sayawa fa da cewa su Aisha.
Sai ita datazo maku hutu dan sayayyan da za ai mata kuma shine zai zama matsala yanzu kuma haba dai mama idan hakane ai sai ta bar zuwa hutun tunda zuwan ta duk zata tafi sai an samu matsala irin haka.
Fada sosai mama ta fara yiwa ya musa din yasa na tashi daga wurin cin abincin zuwa sakin kwanan amma ina jin muryoyin su cikin fada sosai daga dakin.
Karshe shine naga mami Dele tazo gidan sun dade da mama kuma suka fita saya tsaraban da Abba bai mun ba ke nan haka na dawo tun wanan karon naji zancen mama ya fara fita min zuciya.
Na shiga part din mu da sallama ummah tana zaune ita kadai a afalo nayi sallama na shigo ina gaida ita da gida ta amsa min kamar a cikin damuwa.
Yadda nake mata kallon tuhuma yasa tace dani ki shiga ki cire kayan nan kifito kici abinci na amsa da to ummah na nufi hanyar shiga dakunan kwanan mu.
Muryan umma din ya
dakatar dani na tsaya tana fadin kinga su Kabir a waje ne nace eh umma suna waje tace ai tun karfe daya suna nan sun shigo su gaidani suke tambayanki nace kin tafi school.
Shine suka zauna nan din abincin safema a nan suka karya saidai na ranane gashi nan na aje masu basu dawoba ko sunci a can ne ban sani ba ?
Suna waje ummah yanzun muka gaisa dasu na fada nasa kai na shige dakina dogon riga na saka baka a jikina sai dan kwalinshi dana daura a kaina nasaka plat shoes dina na zaman gida wanda iya cikin part din mu nake yawo dashi na fito zuwa falo.
Dining na nufa don ban samu ummah inda na barta ba da zan shiga abinci na bude naga sallon girkin na bakine wanan ke nan ko yau din ummah ce ta girka masu abincin na fada a raina.
Abincin na fara zubawa a cikin plate a daidai lokacin kuma naji sallaman Dele cikin muryan nan nasa mai sanyi haka yasani dagowa ina amsawa.
Yana gaba kabir yana bayan shi kai tsaye dining din suka nufo yaja kujera daya ya zauna a sanyaye shima dan uwan nasa yaja yakai zaune kamar wanda ke a galabance dashi.
Kallo juna mukayi nida kabir din muka sakewa juna murmushi lokaci guda yace miko masa wanan ya fara cin wanan da kika zuba sai ki zubo muci tareni .
Ido na fito dashi nace naci abinci da kai kato da kai ai sai kasa a dakeni yau ya dago fuska a daure yana fadin nine kato ko wanan yana nuna dan uwanshi gareni.
Kaidaine kato amma ai shi yayanane don haka nake girmamashi ko yaushe saboda ya dauki girma na kuma sayar mai oh really nace yes ina aje plate din abincin dana sa komai a gaban Dele din.
Na juya na fara zubawa a cikkn wani inda nakesa komai a wadace don nasan yana da ci sosai a baya ina ajewa yace oya zauna tare zamuci ba wasa nakeyi ba.
Dole na zauna muka soma ci tare sai santi yake zubawa wai gaskiya ummah ta iya girki sosai yayin da nake kara lodamai abinci dana sha sai fira yake zuba muna dan uwan nasa na shiru.
A haka Rukkaiya ta shigo ta sameni dasu take fadin wai ana kiransu Dele din gasu nan zuwa idan sun gama cin abinci ta juya ta koma part din su.
Tana fita kabir yace kinsan me na tsani wanan yarinyar wallahi sjn faye gulma da sa ido yanzu wanan fita da tayi zataje tayi amebo akanshine.
Dariya nayi yace gaskiya nake fada nace yan uwana ba haka suke ba kaima ka sani kawai dai baka ra,ayjnsune kawai yasa ka fadi hakan.
Mikewa Dele yayi wanda shima yasa shi mikewan yana bin bayan dan uwan nasa a kofa suka hade da Aisha data biyosu ranta bace.
Duk yadda yaso ranan mu hadu bai samu hakan ba don bubuwa gaba daya sun rikemai a ranan saboda test din da suka shiga mai zafi kodaya fito ya samu motana baya wajen yasa shi komawa ciki.
Zuciyar shi ta bashi shawaran ya nemi number na ya kirani haka kawai zaiyi ya samuyin magana dani yadda yake so son so yake yaja min kunnem yin hakan saidai yasan a fili ba zai iya yin hakan ba gareni don yana kallon narkankun idanuna yasan zasu rikitar dashine lokaci guda.
Zai iya cewa yana hanin mata kyawawa da zarra irina mata amma bai taba haduwa da macen data rikitashi ba lokaci daya irin hakan.
Yasan dai bai isa ya nuna so ko shakuwa a inda Allah bai kaishi ba haka kuma shi bai isa yakai ko matsayin drivern gidan su ba ko mai ban ruwa gidansu ba yadda yaji mutane suna fadan irin arzikin gidan mayana din a gari.
Shawaran zuwa department din mu yayi ko zai ga abokan karatuna hakan yasa ya juya da sauri zuwa hanyar shiga building din suka hade da hannatu a kofan wace ke fitowa don zuwa gidan lokacin.
Tana ganin shi ta fara sake murmushi a fuskanta lokaci guda tare da fara gaidashi tana fadin master kayi wuyan gani fa ashe ka shigo yau bamu sani ba gashi harsu zarah sun wuce gida tunda muka fito dazun tace yau suna da baki a gidansu don haka ta koma gida da wuri yau din.
Don Allah ko kina da lambata ki kira min ita akwai sakon da zan batane eh to nima dai na dauki lambatane a wayan ta bata sani ba amma dai gashi tasa hannu tana ciro wayan nata daga cikin jakkarta na hannu ta fara duba wayan can ta miko mai tana fadin ga layin nata akwai kudi a ciki dazun ta saya min kati.
Kai wanan ta faye surutun tsiya wallahi haka ya nasa a zuciyar shi yana karban wayan a hannunta sunan ZARAH MAYANA yagani da manyan harufa.
Danna kira yayi sunan ya shiga saiga wayan na ringing a daidai lokacin ina kwashe kayan da mukaci abincin dashi da sauri na aje tarim plates din dana dauka zankai kitchen.
Bakon number nagani na tsaya ina mamaki ciki tsoro nakai kunnena a lokacin naji muryan namiji yana kwada min sallama.
Daga wayan nayi ina mamaki naji muryan hannatu na fadin zarah nice coursemate din ki master ke son magana dake na kiraki master na fada cikin mamaki sai naji sallaman namiji.
Amsawa nayi yace OK dama naso ganjn ki yau ashe kin shigo har kin fita ban sani ba muna ciki munayin test bamu fito da wuri ba.
Saisai dama akan wanan sakon da kika ban jiyane a cikin envelope naso muyi magana dake don ban san ko kudin meye haka kika bani ba ?
No kayi amfani dashi kawai na bakane kawai nagode sai anjima zaiyi magana nace kaba hannatu na fada a karshe na hana dama yin magana a gaban hannutu din ko godiya.
Hello Zarah kina lafiya kalau na fada a gajerce har yanzu kina school ke nan ashe tace yanzun nan fitowana daga class ke nan zantafi.
Ok saida safe na fada na kashe wayan lokaci guda na mika hannuna na kwashi plates din abincin zuwa kitchen daga nan na koma dakina.
Ba matsala ko Hannatu dake kallon shi ta tambayeshi ganin yadda yanayin fuskanshi ya sauya lokaci daya a wurin duk da bataji ko akan me mukai magana ba a lokacin.
Hostel din maza ya nufa bayan sun rabu da Hannatu din don ya yawata ko kayan zasu shiga nan aka kewayeshi sai gashi kayan sun samu shiga har wasu basu samu ba a wurin.
Haka yasa yai masu alkawarin zai kawo masu in sha Allah, kudin shi mina mina ya kirga sai bakin titi ya hau mashin zuwa kasuwa inda zai kara saro wasu ya kuma cika alkawarin daya dauka din wa mai kaya .
Tun kan ya sauka mai kayan ya hangoshi ya fara washe baki don lokacin daya bashi ma bai karasa cika ba ya dawo suka gaisa dashi yace har sun shiga ke nan yace kaya sunyi kasuwa sosai wallahi.
Nan ya mike ya jawo wanda ya boye mai da farko yana fadin kaga wasu yau aka kawosu sai ka hada dasu zasu shiga sosai wanan mata da maza duk zasuyi saya sosai idan sin gani.
Zuciyar shice ta bashi shawara yayi amfani da wanan kudin kawai tunda nace na bashi su koda daga baya zai zauna dani muyi magana a kansu.
A take ya biya kudin kayan gabaki daya yana gyaran kayan mutumin ke fadin daukan kayan nan yayima yawa da zaka daure ka samu tsohuwar mashin ka saya sai kaji dadin yawatawa da kayan nan zaifima sauki sosai.
In,sha Allahu ina da niyar yin hakan nan gaba amma ba yanzu ba sai kudin sun kara kauri nan zuwa gaba dai sai nasa cigiya in saye don kayan sun fara min nauyi a kai haka.
Ya baro kasuwa zuwa gida da kayansa niki niki yana hanyane ya tuna da alkawarin da tayi na sayowa dabbobin su abinci kaya kawai ya aje daga kofan yace mai mashi din ya koma dashi .
Jin motsin shi da uwargarke tayine yasa ta mike ta fara kuka sosai lokaci guda kuna na tashin hankali har saida Dije dake daki ta fito hankali a tashe zuwa wurim garken nasu tana duban su.
Kofan shigowa gidan uwar garke ke kallo tana kuka sosai sai hakan ya dagawa Dije hankali ta nufi hanyar fita wajen gidan sai kuma taci karo da kumshin kayan shi a ta cikim gidan .
Mamakine ya kama Dijen lokaci guda ita daya take magana dama Amadi ya dawone ashe ko kuwa kayan a nan ya barsu ya tafi ?
Lekawa tayi ba kowa wajen gidan sai yan mutanen dake gittaya jefi jefi a layin can ta hangoshi tafe ya sayowa dabbobin haki da dusa yana sauka saman mashin yana tambayanta ko lafiya ?

ZAINAB IDRIS MAKAWAAHH, HAYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃👠👜💍👡👛 🥿👘👗🧤

INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION.
ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M A C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝
TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI.
YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,,,,,
1️⃣5️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

DARI BIYAR DARI BIYAR KACAL YAR UWA 👌KADA KI BARI RASHIN BIYA YAJA MAKI WAHALA, , , ,

Suna fita part din mu suka hade da Aisha wace ta kara biyo sawun su kabir ne yace waitin you come do here amebo ?
Stop calling me that yeye name i tell you say i no want that name amebo you na de call me with it!
Nobe amebo you come do ? why you de follow us like small kids any where we go har suka shiga part din mama suna fada haka dashi.
Mama wace bata son ran diyanta ya baci ta kasa boye bacin ranta a zuciyarta ta hau Aisha da fada haka yaja ran hjy Rafat baci don tasan halin mama irin wanan wajen don bata kaunan ran yaranta ya baci sam.
Saidai duk abinda sukai maka kayi hakkuri amma idan kace zaka rama a gabanta zaku samu matsala da ita duk yadda kuke kuwa da ita.
Don mama irin matan nan ne masu ririta diyan cikin su fiye da komai a duniya kema uban wa yace ki bisune bayan kinsan halin kabir sarai ba kyaleki zaiyi ba.
Hjy Rafat tace kabir kasan uwarsu bata son a taba mata yara don gudun irin hakane fa banso ka biyomu ba kanace sai kazo arewa kaima ka gani.
Gashi ance kunje part dincan kun tare har kuna cin abinci tare da zarah a plate daya da ita kallon Rukkaiya yayi yace mama shiyasa nace yaran nan naku munafukaine wallahi.
Ni sun sani sun san halina idan yarinya ta kawo min raini yanzun za ajimu da ita ba ruwana da wai maman jafar bata son ayi masu mussu yanzu zanwa yarinya one below seven die.
Ganin abin zai iya kawo masu matsala don tasan halin kabir sosai baida kunya ko tsoro irin roget din lagos dinan ne shi don ko kallon shi kayi zaka fahinci koshi waye don kanshi ya tara wani irin suma hakama kayan jikin shi irin na shegun Lagos ne yake sakawa.
Sabanin dan uwanshi da ba ruwan shi shiru shiru yake shi ko halin irin na yayan farine ke binshi oho mama din ne tace mai ai ina ganin kaikan kabir wurin damben kokuwa zamu kaika kawai turai mu huta da haka suka wasance wanan zancen.
Da suka kebe da uwar tasuce take kara masu fada take fadin kai Dele ka cire ranka ga yarsu don komai ya kara rikicewa yanzu gidan nan ga baki daya don dukkan ku nan kunsan halin mami jafar ta tsani wa yan nan mutane sosai.
Ba zata taba yarda a hada ka da zarah ba yanzu ma kokarin hadaka da yarta Aisha naga tanayi bayan ta sani sarai zarah din kakeso ba Aisha ba.
Duban uwar yayi ya nuna kanshi yace wani mama na auri wanan yaran da basu da tarbiya ko kadan nerve kada ki soma wanan zancen dani don ni zarah nace ina so tun tana karamar ta.
Ba zaka auri zarah ba na fadama kada ka bata min zumuncina da kawata kan wanan bukatab naka don haka ka duba tsakanin Aisha da Rukkaiya ka zabi daya.
Ohh really mum da baki kinki ke fada min haka yau baya kinsan iri son da nakewa yarinyar nan zarah a raina ?
So so suma zaka so su ai idan ka zabi daya daga cikin su OK ya fada ya mike ya fito daga dakin kai tsaye haraban gidan namu ya nufa tsaye yayi wuri daya idanun shi a rufe kafin yaji motsi ya bude idanun nasa.
Nice a duke wurin motana ina daukan abu sai kanwata karama dake gefena tsaye tana surutu kusan kamarmu daya da yarinyar na dago ina rufe motar tare da riko hannun yarinyar muna shirin barin wurin da takardun dana dauko a hannuna daga cikin motar.
Takowa yayi zuwa inda naken ganin shi ya dan sani kaduwa lokaci guda zan iya cewa wanan ne ganin murmushi a fuskanshivtun zuwan su gusau din na da sukayi.
Hannun yarinyar ya riko yana fadin meye sunanta kafin in fadi ta amsa mai da yusurah ya dan rage tsawo yana fadin sunan ki nada dadi sosai.
Kafin ya dago yana kallona tare da fadin nice name naso su yarda muyi aure amma saboda maman jafar hakan ba zai samu ba a tsakanin mu.
They are telling me now wai na zabi Aisha ko Rukkaiya na aure mamadin ke ni kuma zuciyana ke yake so zarah ba suba don su din ba zabina bane zabin su mami ne hakan.
Gobe zan koma da safe in sha Allahu ina son ki dauki layina a wayan ki don ina son muyi zumuci a tsakanin mu har yayan mu nidake saboda kada alakanmu dake ya yanke.
Duk wani abinda ya sameki don Allah zarah na rokeki kirani zarah muddin ina raye ba zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login