Showing 276001 words to 279000 words out of 304363 words
yanzu don ba kyau yaro kan ya dauki abinci ya zubar waishi yayi fushi yana turje turje a kasa yadda kikayin yayi.
Amma yadda ya taso yana fada da sai ki kyaleshi yayi ya gama yarki daice ba zaice sam ba zaki mata fada ba shima zan zauna dashi zan fada mai gaskiya.
Da baki da tarbiya kina zama dashi hakan ko yar naku a gidan nan zata tabbata daku zaune don haka kiyi hakkuri don Allah.
Bai dakyau idan namiji ya taso mace ta taso a karshe ba a maikyau a tsakaninsu don haka ake son mace tayi shiru ba don tsoro ba.
MAMBILA su Abban Ahmed ne zazzaune a gaban manyan shi ana sasantasu shi da iyalan sa don hjy yabi data kai karanshi cewa a kwato mata hakkinta na son dauko shegen dansa ya cusa mata a cikin yayanta yanzu.
Wanan ya hasala Alh har yayi barazanan sakinta a wanan karon ranan hjy murja ce ta hana hakan badon Allah ya gyara ba shine kuma bata dadara ba ta dauki zancen zuwa gida wurin magabatansu takai maganan.
Wanan dalilin yasa suka halarta a gida aka zauna inda yazo da dukkan iyalanshi don zaman ya fadi abinda yake son fadi gaban kowa.
Bayan adduan bude taro da yan jawa bai babban wasune ya fara magana yana kallon kanin nasa cikin kulawa yace to Alh mun gaiyato ku nan ne kai da iyalan ka don maganan da matarka yabi tazo muna dashi.
Saboda ta zo nan garin ta kawo karanka a wurin mu kan wani zance da ita bata da labarinshi tun a farko sai yanzu kake kokarin cusa mata ra,ayin hakan .
Don tace ita bata san labarin zancen yaronka da a yanzu kake kokarin dawo dashi cikin ku son haka ita bata yarda da hakan ba kome zaka fada ?
Don nan wasun mu sunso su fahintar da ita bata yarda da hakan ba shine dalilin dayasa muka nemeku nan muji na bakin kowa don mutuwa akewa gudu.
Ya dan gyara zama yana girgiza kai kafin ya dago yana murmushi yace aiko da na mutu din a yanzu yabi bata da gadona saidai diyanta su gajeni don na dade da yanke alakan da zaisa taci gadona a tsakanin mu.
Lokaci daya kowa ke fadin subbahanallahi meya kawo wanan zancen yace kwarai in dai don gadon dukiyana suke mi haka tsawon shekarun nan ita da su magajiya na yanke wanan alakan da zaisa suci gadon nawa .
Amma a yau Alhamdullahi na fada a gaban kowa ba aure tsakanina da ita a yanzu da na barta gidanane ta zauna a zaman diyanta amma yanzu naga abin bai yuyuwa don haka daga nan ta nemi wani wurin da zata ba gidana ba.
Kowan ku nan yasan abinda ya faru dani a baya duk a dalilin sherin magajiya dasune hakan ya faru har kaddaran rabon yaron nan ya gitta a tsakanina da uwarshi har nayi aure mukai zaman shekara uku da uwarshi.
A lokacin kuma suka karya asirin suka dawo dani gida a haukace tun lokacin dana dawo din ban fada maku nabar iyalina a can ba.
Yayi shiru yana binsu da kallo sai wani yayansu daga gefe ya amsa yace kwarai ka fadawa hardo a lokacin amma akace wuri yayi nisa don haka kabar zancensu wata rana za abi bayansu har hardo ya kwanta dama ba a kara wanan zance ba.
Kai kuma ka shere baka ko taba tunawa da hakan ba sai a yan shekarun nan maganan ya dawo sabo kake yinshi a yanzu da yaron ya girma ya kawo kansa gareka don haka nan duk ba zamuce bamu da wanan labarin ba gaskiya.
Magajiya gaki kin sani na sani shiru nayi nasan duk abin da ake kullawa tun ina yaro a gidan nan ina dai kawar da kainane don kina zaman uwa a gareni ko banza akwai alaka ta zumuci tsakanin mahaifinki damu don haka ko baki auri baffa ba kedin jininane.
A lokacin tsohuwar tayi magana tun zaman ta a zauren da suka taru din a ciki tace kana son kaga laifina a yanzu nasan dama a yadda ka dauke mu don kawai kana ganin arziki a hannunka har kake kokarin kula muna sheri ka wullakantani da iyalina.
Son kawai Allah ya zabeka a cikin mu kaje can ita data kawo wanan maganan kuyishi da ita haka zaifi amma ba yanzu kazo nan kana fadin wasu zance a kaina ba.
Murmushi yayi ya dago kai ya kalli magajiyan yace magajiya harda in na kira Bande a nan zaki iya musa wasa hakan da kikeyi yanzu ?
Wani Bande banden da yake lahira ko wani banden ka samu a yanzu da zaka kawo muna yanzu yace bande wanda kika sani har kika nemi halakashi a baya kaina da uwata don yaki biya maki bukatan ki.
Shi Bande din sherin da zai mun ke nan kuma don anga kasa ya rufe masa idanu baya duniyan yanzu indai akan kana bakin ciki har yanzu da dukiyan naku daya gudu dashine ka fito fili ka fadawa mutane hakan kawai zaifi.
In kuma don ka kulla min sheri a gaban diyan cikinane suna kallona yanzu za ka iya don kaga kana da kudi da iko zaka iya mulkan mu ke nan a yanzu.
Zancen matar ka kuma koni yabi yanzun bata barni ba don a makiyiyarta ta daukeni yanzu ba gimana ko kimata take gani ba don haka bansan komai akanta ba.
Inna inkin fadi hakan akan yabi kinwa Allah karya tun farko waya kawo shawaran hakan ya cusawa yabi wanan akidar ta dukiyan dan gaske duk kece tun muna yara kika saka muna hakan a zukatan mu ai.
Kin koya muna yadda zamu dinga cin karen mu ba babbaka a cikin jikinahi kuma a mallakeshi ta hanyar da ba zai iya motsin komai daga shi har kowa nasa kuwa yanzu don haka ta kasance a gareta zaki zame jikinki a kanta ?
Duk wanan abin inna ke kika jawoshi don da baki nunawa Yabi wanan hanyar ba da tana zaune lafiya da mijinta a cikin diyanta yar hjy yabi da sukazo tarene ke wanan maganan a hasale.
Alh an gama ina iya tafiya yanzu Abba ya fada ina zaka tafi ba akai ga matsayan zance ba don wasu sabbin magana biyu sun shigo a ciki yanzu na farko kace ba alakan aure a tsakanin ka da matarka yanzu.
Sai na biyu daka kawo muna zancen Bande da muka dade da mantawa a nan yanzu maganan ka ya nuna kamar kasan inda yake ayanzu bai mutu ba.
Kome maganan haka ke nufi don har hardo ya kwanta dama akan binciken wanan lamari ya tafi ya barmu dashi yanzu gashi kazo muna da wani zance kuma akanshi.
Ku tambayeta yana nuna magajiya da tsohuwan take zaune tayi tsuru tsuru da idanun cin mutumci a garesu lokacin don duk diya suke a gareta wurin itace uwargidan hardo mahaifinsu Abba din.
Magajiya zan yakeki da Allah da manzonsa me kika sani akan wanan zancen tsohuwar ta dago kai tana tafi da salalami tare da fadin yau Allah ka gwadamin ranan da yayan hardo zasu tsureni a cikin gidan nan.
Bai kai can ba ya dauki waya ya danna kira Alh jauro ya dauka yace Alh kazo min nan da hardo Bande yanzu lokaci daya kowa ya kalloshi jin abinda ya fada din a lokacin.
Ba a dauki lokaci ba suka iso da sallama tsohon a duduke yake a yanzu amma da karfinsu kuma yana gane kowa dake wurin ta fuskokin su don kamanin su ba a boye yake basu yan gidan nasu.
Amma ka cika munafukin Allah ta,ala dama kana raye baka mutu ba ashe yayin da sauran mazan suka mike suna ambantan sunansa da Bande kaine ko kamane dai ?
Ku tambayi magajiya tasan komai akan batana gashi a gaban ka hardo duk da shima hardone a yanzu a can nahiyar da yake zaune a kasan benen republic dake makwabtaga da kasan nan ta yamma damu maso kudu.
Wanan dan nawa na cikina da yabi take kokarin aibantashi a yanzu shine silar gano muna Bande a yanzu don shi Banden yai amfani da sani da iliminsa ya ganoshi a can wurin kasuwancinsa donshi yaron bai zauna duk da baida gata a lokacin bai yarda ya zamo raggo ba a cikin maza.
Lalai Amo tantiriyan matsafiyace dama kin fada min da sannu cikin hankali komai nawa zai tonu a bainan jama, a kafin na mutu yau gashi kuwa komai din yakai karshe .
Tabbas kin nuna min aljanni kuwa gaskiyane kince zaki hada ruhi da ruhi suyi aiki biyu a lokaci daya gashi naga sakon naki ya baiyana gareni duk abinda nake boyewa tsawon shekaru a yau ya baina ya bainan jamma,a.
Lawali dauki magajiya kukai ta ciki hakan ma ya isheta iahara ita da yan baya in zaka gina ramim mugunta ginasa ya zan gajere .
Dan nata da aka kira da Lawali ya dago a ciki takaici yana fadin inna kin shu,shemu kin batawa ahalinki suna na har abada kan rashin godiyan ki mm a fada maki tun baya Allah bai raba daya ba.
A ina dan uwanmu dan gaske ya rago muna munaci muna sha daga cikin jikinshi muda iyalin mu a kulun yana muna komai inna ashe hakan bai isa a gode mm ashi ba sai anbishi da wanan sakaiyan na sheri.
Yau ga yabi din da kikasaka gaba nan ta watsar maki da duk wani manufa taki ta fara gina kanta akan huduban ki ke yabi banda batan basira don da daya ya shigo cikin ku yau me zai rageku dashi don Allah.
Uhumm,humm ai baka sani ba yanzu zamu zauna mu lissafa ko nawa na kashewa yasir tun daga ranan haihuwanshi har kawo yau sai a cire wa wanan yaron nasa kason don nasan akwai hakkinsa a kaina banson na mutu da wanan nauyin nasa.
Duk ya nuna bai kaunar kwandala a cikin dukiyana don nasa ya isheshi a yanzu shi da iyalinsa amma ni hakan bai mun ba don hakkin zai yi yawa a kainane.
Ga Bande nan ya dawo min da dukiyan mahaifiyata dake hannunsa na yanke shawaran barmasa su ya dauka halak malak idan bayan ancire duk abinda addini ya tanada ayi a dukiya sai ku mallaka masa don kune shedun hakan iya abinda zan iya masa ke nan a yanzu.
Wani irin kururuwa Hjy yabi ta sake tana fadin bata yarda ba wanan zaluncine da cin amananta da yayanta akayi ai Hardo yace a jata zuwa ciki shike da dukiyansa shi kuma ya kyautar da abinsa don haka babu yadda za ayi gaskiya saidai shima din ya dai kwatanta yadda ya kamata.
Yace iya adalcin da zanwa wanan yaron ke nan a yanzu gara na fitar dashi cikinsu tun ina raye zaifi don wanan macen da kuke gani yabi ba karamar azzaluman mace bace
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/9, 7:59 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
9️⃣4️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Bamu samu shigo Nigeria ba a takaice sai da muka share shekara biyar acan a cikin na shidda ya shirya muna zuwa gida koshi zuwan da dalili.
Don Abbana da baida lafiya sosai a lokacin yasa muka shirya a gagauce zuwa gida saidai zamu sauka a karo na farkone a gidan mahaifinshi yadda ya bukata.
Lokacin yarana biyu ina dauke da cikin na ukku a jikina saukan dare mukayi don haka a part din da aka shirya muna muka sauka mun samu an hada muna abincin taro da komai a ciki.
Saidai kafin mu shiga na kula master baiyi gagawan shiga ciki ba a bakin get yasa driver ya tsaya ya fito mun dan dade tsaye a wurin kafin yaba driver umurnin shiga damu cikin haraban gida shiko ya tako da kafa zuwa cikin haraban gidan.
Tun lokacin nasan shima hatsabibin kanshine ashe gidane mai kyau wanda ban taba tsamani ba gaskiya ashe Abban ya tambayeni waye ubana a lokacin dana fara ganin shi.
Da gajiya a jikin mu sosai abincin ma shida kansa yaba yaran sukaci shida Dije wanka na shiga na fito na nemi abincina fresh milk na kinkima nasha tare da dan cake na kwanta.
Koda matar gidan ta shigo ta samu na kwanta a lokacin don haka bamu samu ganin juna da ita ba saida safe shidai kan ba zance yayi barci ba a ranan.
Don zaune ya kwana yana lazumi bandai san abinda yakewa ba amma naga hakan gareshi don duk falkowa nayi zan gashi a tsaye yana sallah ko zaune ya daga hannayenshi sama yana rokon Allah.
Saidai ni din ma dana samu barci mafalkaiya nake faman yi a lokacin da na samu barci zan gani a cikin iccen tumfafiya masu yawa wani lokaci suyi min haske wani lokaci kuma kore shar nake ganin su.
Idan kuma fitsari ya tayar dani don maganin da nake sha yana yawan sakani fitsari sosai haka kuma banda abinci sai abu mai dan ruwa zansha ya zauna a ciki idan na yashi na kewaya na dawo na kwanta zaci gaba da irin mafalki gudane na wanan iccen na tumfafiyar masu yawa a wuri.
Sai a karshene gabanin asubahi na ganmu dukkan mu har yaran zaune saman wani dadduma mai kyau a cikin zugun tumfafiyan wani mutum daya bamu baya yana fadin ai na fada maku zaku shigo ku zauna kamar kowa.
Danan da can a yanzu kun wuce kaidin kowa a cikinsu hankalinku da natsuwanku da rike Allah da kukaiyine ya kaiku ga nasara a yanzu din don haka.
Babu wani mahalukin daya isa ya taba lafiyan ku face wanan abinda yai maku kwatankwancin shi bai sameshi ba kudai kada kuyiwa kowa sheri a rayuwan ku shine cikar imanin bawa sai dai idan ku kuka canza rayuwan ku nan gaba zakuga akasin hakan.
Master yace dashi bamu fatan mu canza akullun muna kawo Allah a gaban komai da zamuyi don haka ubangiji ba zai yarda mu halaka ba insha Allah kai waye wai da kazo muna nan yanzu
Mutumin yace ni nine mahadin kaddaranku na asalin don nine sanadiyar haduwan ruhin ku a nan baki daya.
Da mutumin ya juyo sai naga tsohone kuma na taba ganin fuskashi a baya na nunashi da yatsa ina fadin dama baba kaine ashe yayi min murmushi yace nice diyana .
Na bishi da kallon mamaki naga ya juya ba tare daya kara magana ba ya shige cikin duhun wanan itatuwan na tumfafiyan yana saye da dogon jallabiya fara da dan buhunshi saman kafadanshi yana dogara sandan shi kamar ranan dana fara haduwa dashi a hanyar makarantarmu.
Na bude baki zanyi magana lokacin ya kusa lumewa nace baba din Allah ka dawo ka karbi sadaka yau ban baka ba ka wuce daga inda yake ya tsaya ya miko min hannunshi.
Abin mamaki sai naga hannun sun kawo har inda muke zaune duk da dan nisan dake tsakanin mu dashi a lokacin na bude jakkata na debe kudi na basa yadda yai min addua a ranan irinsa ya maimaita mun a lokacin na dago kai ince amin sai naga ya bace bangasa ba na fara fadin innalillahi da hakan na farka ina ambata innalillahi a bakina.
Naga master ya kalloni daga inda yake zaune ya bude Alkur,ani yana karatu yace ke zahra lafiya meke faruwa dakene haka tun dazun kike suraitai fa.
Bin dakin nayi da kallo na tuna a inda nake zaune nakai ina fadin mafalki kila nakeyi na bashi amsa da hakan kafin na mike na shiga bandaki.
Washegari bayan munyi wanka mun shirya gaba dayan mu muka dunguma zuwa falo inda mutanen gidan suke jiran mu muci abinci.
Shine gaba yana dauke da dansa Amir mai sunan Abbanshi Abubakar ke nan ya riko Bananh da dayan hannun shi nida Dije muna daga bayansu.
Yayin da yan gidan gaba dayansu suke zaune saman kujera sun zubo muna idanu tun lokacin da sukaji sallamanmu din suka dago suna kallon mu inka debe salima dake duke da kai tana dakilan wayanta a yangance a lokacin.
Muka shigo wurin Abba din muka nufa inda yake zaune muka zube kasa har Dije da sauri Abban ke fadin haba haba mama kizo ki zauna ga wuri nan a tanada maku ku tashi ku zauna ga kujera nan.
Shiya mike ya gyarawa Dije wurin ta zauna ya dawo kasan inda yake yana gaida mahaifinshi a cikin ladabi ya amsa yana mika hannu ya dauki takwaranshi yaron yaki zuwa ya kara makewa a jikin ubanshi.
Yace mai sunan ne kuwa dakin takwaransa a cikin hausansu irin ta fulani da yakeyi a harshenshi kafin yace idan shi bai zuwa ke mata kizo yana mikawa yarinyar hannu ta sone kai a jikin babanta.
Abban yayi dariya yace watau baku san kowa ba sai iyayyen ku ko kaina duk yana duke a