Showing 255001 words to 258000 words out of 304363 words
haka inna har da laluran ciwo ya kama yarinyar nan amma baki leko kin mata ya jiki ba sai kizo kuma yanzu kina fadin wanan maganan don Allah.
Yarinyar nan fa da ace itama mai halin yan zamanin nan ne bata samu tarbiya irin hakaba ba za ayi abu mai kyawo a tsakani n kubafa don ko waye baida lafiya baka dubashi ba kuma ka kama fadin magana mara didi a kanshi lokacin dole yaji zafi gaskiya.
Don ni banga inda ta kasa daku ba a gidan nan duk yadda ake son a samu mace mai hakkuri nasan zahra tana hakkuri da kowan mu gidan nan don bata taba nuna abinda kike mata yana sosa ranta ba.
Ikon Allah dan Dije duk akan matarka don na hanaku kwanciyan lalaci ka fito kana fada min magana haka son ranka don raini dake tsakaninmu ko ?
In babu raini zaka fito don nayima fada ka jaye mashin tun safe ya tarewa mutane wuri kana cikjn daki kwance shine jin haushin ka dani har zaka nemi mayar min da magana kan wata mata taka can.
Koma dai meye inna ni nasan darajan mata ta don ba zaman banza nakeyi da ita ba a gidan nan aure mukeyi don kuma naga ai bake ba kosu Aisha ke ciwo gidan nan ta fara zariya ke nan tana dubansu amma ke baki leko ba suma hakan.
Fisabilillahi anyi adalci ke nan inna ga hakan yanzun kuma kinzo kina fadin maganan da bai dace ba gareta ai hakan sai ya jawo rainima a gareku wata rana.
Inna yanzu dije ke fadin fa ashe bata da lafiya tun safene fa muma yanzun mukaji dije na fadin hakan da kike magana .
Tana fadin hakan ni waya fada min ai ina gidan da zai tareni da maganan banzanshi can tunda ya samu diyar shi ko ta fada a hasale wucewa yayi zuwa wurin mashin din yana kokarin jayeta a inda tace ya tare masu hanya dashi.
A lokacin still akuyan ta dauki kukan nan nata ba wanda yabi ta kan hakan wanan ranan anyi sa,a dije bata fito ta saye fadan ba shi ta bari da abinsa.
Har ya dawo ciki ya kwanta a falo ina dai jin jukan har cikin raina na daure na fito mm ace a duba akuyan can mana kukan nata yayi yawa fa tun dazun take wanan kukan haka .
Barta kila muryana da take ji yau a gida yasa take kuka haka ya fita batun nima na koma na kara kwanciya zuwa azahar yayi wanka ya fita don yaje yayi sallah.
Sai gashi ya dawo a gigice yana fadin zahra na amsa har lokacin ina kwance yace wallahi an dauke min mashi dana fita dashi waje dazun da inna ta matsa min.
Ai bansan lokacin dana mike ba ina fadin subbahanallahi an dauke fa kace yace wallahi don bata a inda na barta dazun din bari naje nayi sallah in dawo kada in biyu babu kuma.
Haka na lalaba zuwa wurin dije nake fada mata abindake faruwa nan ta saka salati har su Aisha suka fito muke fada masu muka kwasa muka nufi wajen don dubawa babu mashin din a wajen.
Kin gani ko kunga abinda son kan uwarku yajawa yayan ku hasara yanzu ko mutum shi baida tunane baisan ya kamata ba sai bin zuciyan shi saboda hauka da batar basira irin na Rashida.
Wallahi kan inna ta taja mashi haka mashin din nan na ciki aje tasashi a gaba wai sai ya jaye yaba mutane hanya ga abinda ya faru yanzu ai muna samu ana kaimu school da ita yanzu kuma shike nan dada an sace kuma.
Haka ya dawo ya samemu tare da wasu mutanen unguwa ana jajantawa Dije sai gashi tun daga nisa dije ke tambaya ba a gani ba ko yace wallahi dije ban gani an daukene ai shiyasa nake ajeta a ciki ai.
Ko yau din fitan rabone don tun da safe na fita na sayo kosai da zansha kunu dashi shine na dawo na samu zahra bata da lafiya na shagala har na barta nan don na ajetane da niyar in nayi wanka in fita zuwa kasuwa dama idan na sauke zahra gidansu.
Yanzu ai dada shike nan taja maka wanga hasaran ai kowa yaji a jikjnshi don ba kai kadai kai hasara ba ai ni halin rashida yana damuna wallahi.
Muryan Asmauce ke fadin hello inna ki dawo gida an sace mashin din yaya da kikasa ya fita da ita dazun ya fito yanzu bai gani ba an dauke.
Sallati ta saka ba a dade ba sai gata saman mashin tayi wani urin hawa yana ganinta shi kan ya shige gida nima na mara masa baya a can suka kwasa da dije.
Tana sauka tace kodai yaran nan ne dake zaunen innuwar can na malam tanimu don na gansu dama ban yarda dasu ba don bansan fuskansu a unguwar nan ba gaskiya ashe dama barayi ne.
Ke rufa muna baki duk wa ya jawo hakan in bake ba tana ciki aje kika saka masifan ya fito ya jaye maki mashin ke zaki fita da kaya ya tare maki wuri ai gashi yanzun abjnda kikaja masa.
Babu kowa a falon amma duk da hakan bai hana falon yin kamshin dadi ba a lokacin ko bai tambaya ba yasan aikin hjy murjace don ita din ma,abociyar son kamshine sosai.
Balle yau da yake ranan girkintane yasan duk cikin aikintabe wanan don ta farauta mashi rai idan ya shigo abinda hjy yabi bata da lokacin yi ke nan gareshi da sunan farauta mashi zuciya.
Maimakon ya wuce fata din shi sai kawai ya nufi wajen hjy murja din kai tsaye uwa uba wani kamshinne na daban ya kara dakan hancin nasa yayi masu sallama ya shiga.
Lokaci daya duk suka gyara natsuwan su cikin girmamawa har kasa yan matan suka kai suna fasin sannu da zuwa Abba lokaci guda ya amsa masu fuskanshi yana kan matar tasa da a yanzu yake jinta a zuciyar shi.
Itace karshen fadin sannu da dawowa tana mikewa don karba jakar data gani a hannunshi din lokacin ya mika mata yana amsawa ta karba tare da dan rusunnawa gareshi.
Juyawa yayi itama tabi bayansa zuwa part din shi inda suka hade da hjy yabi wace ta fito tana mamakin rashin ganin shi a part din nasa bayan ta tabbatar da shigowanshi cikin gidan daga window dakinta lokacin daya dawo din.
Ba sannu da zuwa sai cewa tayi ina ka tsayane naga shigowan ka tundazun gidan dama nazo fadamane yasir ya samu accident dazun bayan fitan ka.
Amma da sauki muje asibiti an dubashi a kafane ya dan samu targade yana daki kwance ta dauka zai gigice yadda ya saba ga mamakinta sai taji yace.
Oh Allah sarki halan yasha giysrshine daya saba sha yaje ya bugu indai bai bugawa mutane mota ba ya dauko min magana kuma a garin nan ?
Kallon mamaki tayi mai jin abinda ya fada game da dan nasu dayafi so fiye da komai a rayuwanshi ta bude baki tayi magana lokacin ta farga da hjy murja dake bayanshi dauke da yar brief case dinshi ta zuwa office.
ZAINAB IDRID MAKAWA[6/29, 8:15 PM] Zainab Idris Makawa Writer: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
8️⃣7️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Abu kamar wasa sai ga magana ya tabbata gaskiya mashin ko kasa ko sama ba a ganshi ba kuwa nan inna tayi ta babatunta a cikin gida tagaji dai ta kyale dole tunda babu dai yadda za,ayi.
A cikin hakan kuma Ahmed din ya shiga Abujan daya yace din don yin wasu takardu a can a gidan iyayyen wani abokinshi ya sauka wanda suke karatu tare a zaria.
Ya kaishi wurin iyayyenshi su gaisa duk da karatune ya hadasu amma ya girmi Ahmed din a shekaru gaskiya suna dai abotane kawai irin na karatu ana tare.
Suna gaban iyayyen nasa shi abokin yace to mummy kinga dan school din namu da nake fada maku dan zamfara wanda nace maku karami dashi yana da mata .
Amma ni kunce wai nayi karami da neman budurwa yanzu balle aure kai Ahmed din ya dukar kasa don kunyan abinda abokin nasa ya fada game dashi a gaban iyayyen nasa.
Salati mahaifiyar nasa ta saka yayin da mahaifin shi ya danyi murmushi yace ka kalleshi mana ka kalli kanka ai kasan ya fika natsuwa da sanin ya kamata.
Wanan zai iya rike ko mata hudune yanzu don yana da natsuwa ba sai an fada ba ai don wanan shiyasa fa don ace min hakan nake koyi da halinsa yanzu momi bakiga na canza ba sosai kuma sallah baya wuceni ko yaushe yanzu.
Kai tafi can don Allah ka rabamu da shirmensa ka kaishi daki ya huta yaci abinci ka zaunar dashi kana masa shirme a nan ai kaga irin rashin hankalin naka zakace wai ai maka aure yanzu.
Ka diba yadda ya zauna a kasa da zai gaidamu kakofa ba a tsakiyan mu kake zaune ba yanzu hakama ko gidan matar kaje neman aure zaka haye kujeran ubanta ka zauna.
Duk aka kwashe da dariya harshi a falin suka mike zuwa cikin yaga taro na mutunci da karramawa a wurinsu nan yayi kwanakinshi da taimakon abokim nasa ya samu ya kammala abinda yazo yi abujan sukai sallah jumma,a a Central mosque.
Bayan sun fito daga sallah yake cewa abokin nasa akwai wanda zan gani a nan dama bayan sallah bari na kira naji ko ya samu zuwa a lokacin ne kuma wayanshi ta dauki kara ya ciro daga aljihunsa yana dubawa tare da fadin gashima ya kirani.
Sallama yayi bayan ya dauka yake fadin gamu a mosque din aka amsa mai da fadin amma zaka bari mu gaisa ai ko mahaifin nasa ya fada jin hakane ya dan shake murya yana fadin.
Ina wuni gani nan ta kofan ya juya ya tambayi abokin ya fada masa shima ya fada mai yace muna saurine yau nake son in koma gida.
Kana nufin har kayi abinda ya kawoka garin ke nan yace eh tun rana monday na shigo yau kuma zan koma ok gamu zamuzo wurin ya fada yana kashe wayan.
Mutumin garinkune ko abokin nasa ya tambayeshi saida ya danyi murmushin yake yace mahaifina ne yana kawar da kansa gefe daya.
Da sauri yayi mai wani irin kallon mamaki yace mahaifinka fa kace dama mahaifinka yana garin nan ne baka taba fada min ba kafin ya rufe baki Abban ya tsaya a gaban mu.
Ba sai ka tambaya koshi waye ba gareni saboda yawan kaman mu dashi don sak shi na kwaso a wurin kama shiyasa mutane suke musun cewa wai innace ta haifenshi don basu da kama da ita a ko ina.
Kai ya daga sau daya ya kalleshi ya dukar da nasa da sauri yayin da yakai kasa kuma yana masa gausuwan da hausawa sukewa iyayyen su na girmamawa a garesu.
Ganin hakan yasa abokin nasa shima ya kai kasa da sauri kamar yadda shima din yaga yayi suna gaida mahaifin nasu.
Ku tashi yace dasu yayin daya kai hannuwanshi saman kafadan Ahmed din yana tayar dashi yace yanzu baba karami ka kyauta ke nan kana cikin garin nan amma bakazo gidana ba sai yau da zaka tafine zan ganka ?
Duk da nasan baka son taimakona a yanzu amma ya dace ace munga juna dakai tun zuwanka garin nan ko badon niba ai zakazo don yan uwaka ko uwayeka nagida.
Wani iri Ahmed din yaji ya sonar da kansa kasa saidai yayi alkawari a ransa cewa duk yadda mahaifin nasa yake kokarin nuna masa ba komai a fili bazai yarda ya afka gidan mahaifin nasa ba a yanzu sai nan gaba kamar yadda shi ya daukarwa kanshi alkawarin hakan.
A nan yaja hannun dan nashi suka dan fara takawa a hankali yayin da kowa na wurin yake kallon ikon Allah don ba sai a tambaya ba ko dansane ko kuma wani dan uwansa saboda kamarsu da yai yawa na jini.
Mamakin shi wanan mai kama da Alhajin wayeshi wasu keyi inka don har yafi danshi yin kama dashi sosai saboda shi yasir ya dan debo mahaifiyarshi ga tsayi don baikai uban nasu tsawo ba .
Inka debe bala driver a wurin danshi Alh ya fada ma komai game da dan nasa lokacin da suka bishi zuwa zamfara shikuma bai fadawa kowa komaiba kan hakan.
Malam Ahmed kayi hakkuri ka jaye tafiyan ka a yau din nan muje gidana kaga iyalaina suma su ganka koda kuwa ba zaka kwana a wurina ba idan kayi min ko hakan ne ya datar dani a zuciyana.
Abinda Alh ke fadi ke nan ga dan nasa lokacin dayaja hannun nasa suka kebe daga sauran mutanen dake wajen don ganawa da dan nasa dayazo garin ba tare da saninsa ba.
Alkawari na dauka sai wanan asirin na gidan ka a kaina ya karye zan taka kafana zuwa gidan ka Abba idan yau baba musa ya kirani ya fada min cewa naje gareku insha Allahu zan dauka iyalina muzo mu ganku.
Kada kayi amfani da fadan mutum watau camfi ban faye yarda da abinda mutum dan uwana zai fada min ba duk da nasan asiri gaskiyane don anyi min akan rabon samunka naje da kafata har garin mahaifiyar ka na zauna har mukai aure da ita aka sameka.
Amma duk da hakan ban yarda da cewa wani yai min ba na dai dauka cewa rabon kane kawai yasa nabar gida na bar gatana da kowa nawa zuwa wanan garin don haka ka cire fadan mutum dan uwanka a zuciyar ka.
Zan shigo saidai ba yau ba Abba ya fada a dan sanyayye kafin mahaifin yai magana yace dama dalilin haduwan mu yau shine don in tambayeka don Allah ko kasan buba Bande dala ?
Ko hardo Dala Banden a baya can wani irin kallon mamaki mahaifin nasa yai masa don koshi a yanzu ba zai iya bada labarin wanan mutumin ba saidai yasan dan uwansa ne na jini daya bata tun suna yara suma.
Kaiko baba a ina kasan Dala Bande mutumin daya bata ko ya mutu tun muna yara kwarai kuwa na sanshi amma ba sosai ba don shine wanda rabin dukiyan mahaifiyata take hannunsa.
Amma tun bayan rasuwan mahaifiyata muka daina jin labarinsa kwata kwata mutanen garin muma cewa sukayi ya mutu a lokacin baya raye.
Bai mutu ba Abba yana da rai saidai baya cikin kasan nan yanzu yana wani gari a can cikin benin republic zaune shi da iyalinsa ya fada min duk ranan da muka hadu in maka wanan tambayan kuma in fada ma inda yake zaune.
Ya kumace na isar mai da gaisuwana a gareka in a fadama komai na nan yadda yake saidai zuwa gembo ne abu mai wuya gareshi don magajiya ce silar komai.
Babana Dala bande fa kace ka hadu dashi har ya baka wanan sakon yace kwarai kuwa Abba shine ma dalilin dayasa na tsaya na ganka a yanzu don in sanar dakai sakonshi don nayi alkawarin hakan gareshi.
Hulan kanshi yaga ya cire yana fitara dashi yabi mahaifin nasa da kallo mamakin hakan kafin ya dubi lokaci agogon hannunshi yace Abba ni zan koma don motan dare zanbi na koma yau din.
Kai ya dago da idanuwanshi da sukai ja lokaci guda yace zaka koma amma kuma ba yau din da kace ba a matsayina na mahaifinka na bada umurnin hakan gareka.
Zanso mu zauna dakai yau da dare ka fada min komai game da Dala nasan in har dalane ko wani ne yake son yimuna wasa da hankali a matsayin sunan Dala din don ba karamin labarin daya taba min zuciya bane ka kawo min game da wanan mutumin da aka dade ana nemansa an rasashi.
Saboda haka ka koma masaukin ka ba zan matsa maka sai kazo gidana ba tunda baka tashi hakan ba amma ni zanzo har masaukin naka da yamma in sameka idan na taso daga office.
Yana fadin hakan yaiwa security dinsa hannu a take suka shirya da sauri suka shiga mota shima ya shiga nan suka barshi tsaye yana kallonsu.
Nabil ne ya dafashi har lokacin a cikin mamakinsa yake yace wai dama mutumina kai dan wanan mashahurin mutumin ne ko garin ku dayane kawai dashi.
Amma kuma zanfi gaskata idan kace min shi din mahaifinkane don yawan kaman da kukeyi dashi gaskiya ban taba sanin cewa kai din kana da halaka da mai kudi irin haka ba a cikin garin nan.
Muje gida kawai in dauki kayana ka kaini tasha ya fada Nabil din ya kalleshi yace muje sun fara hanya yaji yace alama ya nuna akwai takon saka a tsakaninka da mahaifinka ko ?
Bai bashi amsa ba sai hannu daya dora a gefen glass din motan yana