Showing 237001 words to 240000 words out of 304363 words
Haka suka koma ciki zugun zugun dasu ga takaicin miji gana danta dake damun zuciyan ta sai sha biyu yunwa ya sauko dashi ya fito yana hamma a lokacin buko digon kunya a idanunshi.
Wurin abinci ya nufa kai tsaye ya fara budewa baiga abinda ke masa ba don kunun gyada suka dama sai kuma irish da kwai da aka soyo sune aje a kan dinning table din.
Kwai da dankalin ya jawo ya zuba ya somaci saida ya fara koshi ya dago kai ya kalli inda suke zaune sun zuba mashi ido suna kallon shi cikin takaici.
Kafin ya cire hannu ya kallesu ya ware hannayen nasa ya nuna alaman tambaya zuwa garesu din kan irin kallon da suke mai a lokaci.
Yasir dama haka ka koma ban sani ba ashe shine dalilin dayasa Alh ya karawa gidansa security har da yansanda a yanzu don yasan ya haifi dan iska.
Bai taba cewa zaiyi tafiya tare da murja ba amma yau tare yace zasuyi tafiyan sai yanzu nagano ko don saboda menene ya tafi da ita tafiya yau din nan har yar aikinta bai bari a cikin gidan nan ba ashe saboda kaine.
Fuska ya dago ya kalli mahaifiyan cikin mamaki yace saboda dani zaiyi tafiya da ita why sabodani haka zai kasance nace zan mata wani abune ko me ?
Ko baka furta cewa zakayi ba nasan Alh ya rigada yasan kome kakeyi acan France shiyasa ya dauki wanan matakan yanzu haka.
Idan ko har hakane zuwanka turai dana zabama ya zama min dana sani haka wanan zuwan nakama bai mun rana ba wallahi a yanzu.
Na kiraku don kuzo ku zauna da mahaifinku amma kai badala kawai kasaka a gabanka shiyasa yayi min habaicin cewa dagani sai diyanane a gidan nan yanzu saiko yan aikin mu dake gidan kafin ya tafi.
Ke nan haka na nufin akwai wani mugun aiki daya san kana aikatawa a can ke nan yanzu yasa da zai tafi ya kwashe iyalansa da yake so ya barni daku a gidan.
Kai ya jijoga ya taso zuwa inda uwar take tsaye saida ya dan zagayata kafin yace gaskiya tsohon nan yanada wayau sosai da yayi dabaran hakan shima ya dauka kashe ta zanyi idan ya barta nan kome ?
Gargadi kawai zan mata idan nataji ba sai nayi mata fewwwww ya nuna hanunshi a saman wuyan shi yana lumshe idanuwanshi lokaci guda.
Dama haka ka koma yasir Alh ya sani bai sanar dani ba hakan ko wanan yasa Alh yake kina daku yanzu ko kuma dai shima a yanzu yai nazarin hakan gareka ?
Kasan wanan abin kunyam da kake shirin shuka muna mu fulani abin kunyana da fade a wajen mu don ba wanda zaiba mai irin halin ka mata yasir.
Ina tufafin da nake aika maka dasu ko wani lokaci ta fada tana kallon idon dan nata kafin ya amsa saida ya juya yace sayarwa nakeyi a can kuma suna sonsa sosai wlh don guy din ya iya dinki sosai.
Zubewa tayi a wurin ta rike hannun kujera ta dora kanta akai ta fara rera wani irin kuka gwanin ban tsusayi ganin hakan yasa salima mikewa tana dakawa wan nata tsawa akan ya fita daga falon ga baki daya.
Ya juyo yana mata wani irin kallo kafin yace idan taji naki nawa mai saukin saurara ne a kunnuwanta yanzu amma zan fita din sai mun hadu kisan nasan komai akanki.
Friday ne yasa ban dadeba na dawo gida don ranan da safe kawai nake lacture kodana dawo na samu ya dora muna abinci yana dafa shinkafa.
Naji dadin hakan don haka na canza kayan jikina na fara aikin miyan da zan dora muna din don kada in makara dan dabi,anshine sai ya dawo daga sallah jumma,a yake cin abincinsa na rana a ranan jumma,a.
Don haka na karasa aikina a tsanake na gyara wuri na dauki nasu Dije nakai masu part din su babu kowa a tsakar gidan don haka na shige dakin Dije din kai tsaye ba tare da wani ya ganni ba.
Bandade da shiga ba naji muryan inna tana fadin Asmau kizo ki leko muna yarinyar can yau me take dafawa haka kamshi duk ya gaure gidan da tashin da alama wani abin dadin ne suke girkawa yanzu tana iya gamawa ta boyeshi a daki su cinye su kadai.
Daga dakin Dije na amsa masu ina fadin Asmau ki dawo ga naku nan na kawo maku nan na dauka ba kowa a dakin ne na aje a nan dakin Dije bakomai bane miyar kan shanune daya sayo jiya na dafa yau.
Duk abinda na girka ban taba boyewa a daki ban ba wani a gidan nan idan ba idomie da nakan dan sulala da dare ba inci koshi dasu Aisha mukecinsa don ban iya cinye guda daya ni.
shiru naji inna din tayi Asmau kuma bata shigo ba don haka na duka na dauka na nufi dakin nasu dashi na shiga ina fadin ga abincin inna tayi shiru bata ban amsa ba tana kokarin shimfida dadumar sallah a lokacin.
Na fito ban koma dakin dije ba na nufi part dina kai tsaye cike da bakin ciki da bacin rai na irin abubuwan da ina ke mun a gidan nan.
Gara na bar mata gida zaifi don kada tazovta illantani nan gaba don kiyayyan nata gareni yayi yawa tunda harda kazafin abinci take iya min duk da tasan kome na dafa saina diban masu ita da yaranta bayan wanda zan sakaqa dije din kuma subi suci.
In kin debe indomei danakan dafa wani lokacin da dare idan baya gari koshi tare da yaranta mukeci din bana iya cinye idomie daya idan na dafa.
Haka kuma Allah ya gani Ahmed yana da kokari wurin fitar da hakkin iyayye akan shi don haka zai sayo masu abin miya bai sawo min ba saidai inya dawo ya ban hakkuri cewa baida kudine yaga ni ina da saura da banyi amfani dashi ba.
Haka dangin sabulu da omo da man shafawa zai saya masu kusan sau biyu saigana uku zai sayo dani duk wanan bai taba damuna in tambayeshi meyasa hakan ?
Amma duk wanan baiwa inna ba sai takai da yimin shedan rowa wai harda fadin zan iya boye abinci sai kawai naji abincin ya fita min a raina lokaci guda.
Koda ya dawo ina kwance inda na idar da sallah ya shigo yana fadin wallahi kin kyauta ina Allah Allah na dawo na samu kin gama girki dama taso muci yunwa nake ji sosai yau.
Kaci kawai nace dashi ba tare dana dago kaina kalleshi ba kincine ko ya fada yana kaiwa zaune tare da jawo kulan abincin gaban shi banci ba bandai cine na fada a sanyaye.
Sai ya dago kai ya kalleni bazakici ba kuma bakici komai ba nace kaci kawai idan na tashi zanci ai ya zuba ya soma ci har yayi rabi naga ya mike ya fita daga dakin din yace ina zuwa.
Kitchen ya shiga ya duba babu komai har na wanke tukunya na kife sai gashi ya dawo wanan karon ba wasa a fuskanshi yace ki taso kibar wayan nan kizo muci abinci zahra.
Kaci in na tashi zan dafa indomie naci na bashi amsa ga abinci zakije cin indomie kuma nace eh shinake so naci na kara gyara kwanciyana ina game.
Naji ya gama ya fita ashe wurin Dije ya nufa yana tambaya zahra tayi fada da wanine bayan fitana sai dije din tace dashi matarka tana da abokin fadane a gidan nan bayan uwarku dake zubar da girmanta gareta.
Ai tayi arziki baka dauko mata mai ido bude ba kayi dace da Allah ya baka matar kirki da ko tana sonka kana sonta halin uwarku zaisa ta bargidan nan.
Ko kuma a dunga shigowa kullun ana rabasu fada a tsakanin nan ta kwashe komai ta fada mai yayi shiru kafin yaja tsuki ya fita daga dakin yana adduan Allah ya buda mashi ya bar masu gidansu.
Zai shiga cikin part din mu yaro yayi sallama yace ance ana sallama da Ahmed idan yana gida yaja ya tsaya tare da tambayan waye yace wasu masu babban motane suke sallama akofa.
Cikin mamaki ya juya ya fita zuwa ganin wanda ke sallama mashi a lokacin baiga kowa ba sai motoci guda biyu masu kyau da tsada zai juya yaga an bude kofan motan malam bala driver ya fito yana mashi sallama.
Ya mika hannu cikin mamare duk lokacin ranshi yana bace da zancen da Dije din ta fada mashi ya faru tsakanin mu da inna din akai masa sallaman yafito don haka ya fito masu rai a bace lokacin.
Mahaifinkane yazo yana mota ya bashi amsa da hakan banda mahaifi ya fada yana juyawa a daidai lokacin da dogon bafulatanin mutumin ya fito daga motan shima.
Wayan shi dake ringin ya dauka sunan mama ya gani saida yaja tsuki ya daga wayan tayi sallama ya amsa suka gaisa ba wani damuwa da yanayin canjin muryan shi a lokacin tace dama zancen kudin nan ne naga baka turo ba yasa nakiraka yanzu din.
Wai meyasa ku mata baku da hankaline meyasa duk halinku dayane komai shekarunku to banda kudi ki zo ki daukeni ki min wanka kikai kasuwa idan kin sayar dani sai ki dauki kudin.
Alh daga tambayan kudi zaka hauni da fadan bakar magana haka inma wata ta bata maka rai ai bani bace na bata ma saikayi da maishi bani ba.
An fada maki nace an fada maki zancen banza zancen wofi baku da wani zance ga mutum saina kudi kullun cikin turo maki kudi nake har yanzun baki gode ba to banda su kinji na fada maki ya kashe wayan yana huci.
Ya dan dade a kwance kafin ya mike zuwa wanka don ranan jumma,a ce ranan yana son shiga sallah a lokacin yagama shiri zai fita wayan ta sake kara a zatonshi mamace ya bar wayan har ta katse.
Andan dauki lokaci yana cikin mota ta sake kiranshi ya daga yana tsuki ba tare daya duba wake kiran nasa ba yaji muryan ummah tana fadin Alh ina kwana tun dazun nake kira baka daga ba.
Ya amsa mata a darare suka gaisa tace baka jin dadine halan tun jiya ina jin muryanka wani iri yace kwana biyun nan bana jin dadin jikin ayyah Allah ya dada sauki na kirane dama mu gaisa Allah ya bamu Alheri ya kara lafiya yace amin yana kallon wayan.
Tayi mai sallama ta kashe wayan yabi wayan da kallo yana sauke ajiyan zuciya tare da jin natsuwa yana shigan shi lokaci guda ya lumshe idanunshi har suka kai masalacin driver ya samu wuri yayi parking suka kulle motan zuwa cikin haraban masallacin.
Mamako fada ta dinga yi dashi sosai tana fadin wai mata haka muke yanzun haka kilakiyar matarshi ce ta bata masa rai yake son fashe haushin hakan a kaina.
Tayi fada sosai kafin yarta ta kirata tana fada mata angama aikin da suka bawa wani ba,are yayi masu akan yaranta dama ita mama din tace zata turo da kudin gobe.
Zuwa yamma bata daddara ba ta sake neman layin Abba din kamar yadda suka saba kiranshi a kullun kirane ko yaushe zuwan hjy karima ce ma suka daina waya kamar yadda sukeyi dashi din.
Bai daga wayan ba sai abin ya kara batawa mama din rai sosai ta hakeshi kan zai sauko zasu kwasa dashi idan ya kira ai ta jefar da wayan tana huci .
Shigowan wayan Aisha ce yasaka ta dan bar zancen bawai abin ya fita ranta ba a lokacin Aisha din ke fada mata yadda sukayi da dangin mijinta taci masu mutunci don haka tasan manya na tafe zata shiryawa zuwan nasu suma.
Kiri kiri yaki tsayi ya shige gida ya barsu da mamaki a kofan gidan don shi kanshi dan gaske bai taba tunanen zuciyan yaron yakai haka ba sai lokacin.
Malam Tanimu aka sallamo masu ya zo yayi masu sannu da zuwa ya shiga gidan yana fadawa Dije zuwan nasu zo kaga kame kame a wurin su dije din lokacin.
Na bar labari baya don wancan lokacin na fada maku da mahaifin master yazo yayi rabon kudi ga duk wanda rabon shi ya tsaga a lokacin .
Bayan wuce wansu ne inna ta dinga cewa na ranto mata kudin duk ta karbe a hannu na da sunan aro har yanzu babu wanan zancen gareni.
Ko Aishace don tafi Asmau dama sosai halinsu akwai babbaci don Aisha tafita sanin ya kama inaga itace ta fadawa Dije abinda inna din tayi min harda take fadin ai mahaifina bai taba ba ko Ahmed din wani abuba nima.
Ni dai naji shigowan shi amma gaskiya bansan fitanshi daga gidan ba sai gashi naji ana sallama na fito baba tanimune a tsaye daga kofan mu yake fadin sallamo muna mijinki don Allah na juya da sauri zuwa ciki.
Sai gashi na fito har kitchen na leka na juyo ina fadin baba baya gidan nan amma ina ciki naji shigowanshi bada dadewan nan ba gaskiya.
Sai ga yayi murmushi yace mahaifinshi ne yazo kuma ya gansa ya boye ne wata kila sai abin ya ban mamaki don yana da karfin hali gaskiya da mace ce aiba sai an tsaya kiranta ba zata kawo kanta wurin.
Wasa wasa har dije da kowa saida suka shigo nemansa suka tabbatar baya gidan lokacin hakan yasa suka san dai ya gudune don kada su gana da mahaifin nasa.
Inda kowa yaji ba dadin hakan da yayi don ba sai ya tsaya yana nuna hakan ba za a san yayi zuciya ai amma hakan daya nuna tozarcine ga mahaifin nasa dama shi kansa ai.
Ku kyaleshi wanan karon kwana zamuyi anan dole dai ya dawo gida ai idan ya dawo ku fada mai yayi hakkuri ya sauko daga fushinshi mu fahinci juna dashi don Allah.
Bani kadai ba duk wanda ke wajen kalamin mutumin yabawa kowa tausayi don yadda a yanzu din ya damu da dan nasa gashi shi kuma ya nuna shi jinin fulanine wurin riko da zuciya.
Ganin haka yasa na kirasa da kyat ya dauki wayan nake fadin kana inane kaiko don Allah bayan kasan muna da baki a gidan.
Yace gani nan zan shiga zaria daga nan kuma gaba nayi kiyi hakkuri ban samu yin sallama dake ba don nasan zaki hanani tafiya a lokacin yasa na tafi ban sallameki ba.
Kiri kiri mutumin nan ya tafi don a karshema kashe wayansa yayi babu mai samun shi don kawai dije ta soma mai fada tana nuna bacin ranta ga yadda yayiwa mahaifin nasa.
Saida ya share sati uku masu kyau baya gida dole ya gaji ya dawo kwatsam da dare ya shigo garin babu alaman wahalan komai a jikinshi ya dawa a daidai lokacin bukin da za ayi a family house namu.
Don haka washe gari nikan na shirya na fita zuwa gida don dama a matse nake da inje gida a lokacin don haka sai bayan fitanane Dije ta sameshi suka kwasa sosai dashi har tana fadin zata bar masa gidan tunda tona masu asiri yake sonyi.
Yace tayi zaman ta dama shi yazo ne ya dauki matarshi su tafi don gab yake daya soma aiki a yanzu don haka zai tafi da matarshine can .
Jin hakan daya fada sai kuma hankalinta ya tashi sosai nan kuma ta shiga lalashin shi tana bashi baki akan ya tsaya ya saurari mahaifin nasa kada Allah ya kamashi da laifin aikata hakan.
Kace zaka dauke matarka ku tafi ni kuma idan kun tafi in zauna dawa Amadi ta fada tana kokarin sake masa kuka nan kuma ya soma magana yana fadin duk inda zani dake zan tafi dije amma sam hankalina bai kwanta da in yarda da mutumin nan ba a yanzu gaskiya.
Kul ma karajin ka kira mahaifinka da sunan mutumi zan saba maka rai yanzu nan wai hankalin ka daya kuwa Ahmed ko kaima asirin ya shafekane wai ba a sani ba.
Kukan akuyan su da kwana biyu kamar bata da lafiyane ya katseshi fadin abinda yayi niyar fada a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/19, 8:05 AM] Mmn Bibo: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
8️⃣1️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
BAMBARAKE garine dake cikin Benin republic dake makwabtaka da kasan Nigeria kamar sauran kasashen da sukeda iyaka da kasan ta Nigeria.
Mutanen cikinsa bakakene yayyen kasan faransa don sune suka yayesu a zaman amsan incin kai daga mulkin mallaka da turawa sukaiwa kakanin mu na bakkaken fata irin mulki na bauta da rasa incin kai.
Akasarin mazauna wanan kasan Dandawane babu addini a tare dasu sai bauta irinna arnanci da ake kira da kafirci a sannu wayen kai har addini yazo ya ziyarcesu yanzun kasan nada mabiya addinin musulunci dana kirstanci sai da yawansu da har yanzu suke bautawa