Showing 225001 words to 228000 words out of 304363 words

Chapter 76 - TUMFAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAWA   

26 Aug 2024

33295

kamar zai karbo duk da a lokacin wallahi ban ra,ayin a dawo maki dashi kamar yadda ummah ma bata son a dawo dashi tace.
Tsohon magana ke nan ni yanzu ba motana ba komai da zai fito hannun Abba a yanzu irin haka bana so don na fahinci ba a bani sai ran ummah ya baci a lokacin kaga gara dai a zauna lafiya zaifi sauki na fita na dauraho cup din na aje a kitchen na dawo na dauki jakkata ina mashi saina dawo ya amsa min haka kawai naki shiga cikin gida in gaidasu na wuce a bina.
Kamar yadda na zata na makara sosai haka din ne ranam don ban samu darasin safe ba ya wuceni a ranan don haka na jira saida malamin ya fita nashiga ajin.
Kan hannatu na duke na aje jakata saman desk ina kawai zaune ta daga tana fadin Zahra har kin daga min hanlali wallahi lafiya yau kika kai wanan lokacin
Lafiya kalau master ya dawo jiya cikin dare yasa na makara yau don ban shirya zuwanshi dole na tsaya hada mashi breakfast kafin in fito.
Kai haba don Allah amma kinyi kokari ma da kika fito mutum yayi irin wanan tafiyam ya dawo kuma ki fito da kawai ki zauna gida abinki na kwana biyu.
Zaune nake daga gefenta ina hararanta kafin nace idan na zauna gida shine zai min marking din pepper na ya bani A ko kece zaki maka min ki bani gara dashi ya gama ya huta yanzu.
Niko karatuna da kike gani hannatu zakice nice na fara karatun boko a gidan mu don yanzu idon kowa a kaina yake tunda su har yanzu basuyi making ba duk da karatun da sukayi a lagos da illorin.
Nafa sani nasan komai nima dai fadi nakeyi ai ina zaki zauna gida har na kwana biyu sai kace baki san ciwon kanki ba dai nace ai shiyasa kikaga na dake kodan na fitar da kaina da ummah kunyan hakan.
Sai yanzu tunane yazo mai na rashin kyautawan da baiyi ba da bai tsaya ya tambayi Rashida ba a lokacin akala dai rabuwan arziki sukayi a lokacin don haka bai kamata ace yaje har gusau din ba bai tambayeta ba.
Sai yanzune wanan tunanen ya tsaya mashi a zuciyarshi yake ganin rashin kyautawan don idonshi ya rufe da son ganin dan nasa a lokacin amma kuma ai bai kamata ace ya manta da ita ba gaskiya.
Shigowan hjy Yabi dakin yasa shi katse tunanen da yakeyi din a lokacin ya bita da kallo har ta iso inda yake kwance takai zaune a bakin gadon tana kallonshi.
Sun shirya tun bayan da yaransu suka shirya tsakaninsu suka lalashi mahaifin nasu akan kome matar nasa tayi masa suna rokonshi daya yafe mata don Allah sabodasu .
Don basu jin dadin yadda abubuwa yake faruwa yanzu a tsakanin su gashi har abin yakai ga barin gida duk da basu san me yafaru ba daddy munsan kai mutum ne mai hakkuri don haka kayi hakkuri da mommy ku karasa saboda mu da rayuwan mu.
Ire iren wana kalaman da diyan suke ta kirashi suna masu yasa dole taji kawai ya hakkura din da ita su zauna tare amma fa wanan abin ba wai zai fita ranshi bane.
Don haka dole a yanzu takon zamansu ya canza sallo shi ya koma miji ita ta koma matsayinta na mata a gidan ki banza ai yanzu ba ita kadai bace a cikin gidan.
Wanan ne dalilin sauyawan shi ya sauko suka fara shiri a tsakaninsu sama sama duk da hakan bata gamsu ba yanzuma tazo mai da korafine dalilin kwace bata kudin ma,aikatan gidan da yayi ga hannunta yake basushi direct ta wurinsa.
Don haka ba karamin kara zubar mata da girma hakan yayi ba kawai dai tana dakewa kamar yadda yan uwanta da yayanta suke bata shawara ko yaushe gashi har yanzu ba zatace ita ga laifin da tasan tayi masaba.
Kawai dai ta tsunci kansune a cikin wanan hakin da lokaci guda ya ricibe mata komai yana batun gagaranta a gidan kamar yadda ta saba yi a baya can.
Bayan ya gama saurarenta ne ya dago yana dan murmushi kafin ya kalleta da kyau yace Yabi waiko kina tuna mutuwa a zuciyar ki Alh don me zaka tambayeni hakan kuma ?
Yace yes dole in tambayeki hakan mana ace mace kullun ita kokatinta dai taga ta danne namiji tana juyashi yadda take so mutane na min kallon sha,sha wanda baida right ga mace.
Akwai wani hakkinkine da ban sauke maki ba a gidan nan ne na matsayinki mace a gareni ko wanan bai maki ba dai saina koma mace kin koma miji yadda kike so ?
Alh kada ka fassara min zancena da wani manufa don muna zaune kallo muna kula da junan mu na cikin farin cikin da makiyana basu son ganimu hakan tun farko shine kuma laifi.
Su waye makiyan naki ki fada min yana mai tsureta da idanunshi yace dasu makiyan kine aida da kika shiga matsala kin nemesu ba ban tabo tsanmani zaki canza halinki yabi.
Saidai ki sani daga yanzu zuwa ranan da Allah zai dauki rayuwata matukar muna tare da ke na daina yarda dake insha Allahu a rayuwana tunda ba imani ke gareki ba ke.
Wani irin kallo take mashi hankali a tashe kafin tace ba mamaki zaka iya fadan komai a kaina yanzu tunda an riga da an shiga tsakanina dakai ana son ala tilas sai anga an raba tsakanin mu a yanzu.
Wanan kuma jahilcinkineki kina ganin kowa kamar irinkine da har zai iya shiga tsakanin mu dake don rashin imani nidai nasan ba wanda ya shiga tsakanin mu Allah ubangijine da kanshi yayi nasa ikon ya kwatoni daga makircin da aka dade anayiwa rayuwata.
Au zargina kakeyi da yima wani sheri ke nan ashe yanzu zaka dauki alhakina kuwa a kanka idan ka dauka hakane ashe.
Yabi kiyi abindaya kawoki dakin nan ki bani wuri banson damuwa da yawa yanzu don kuskuren da kikasani na tafka a baya shi nake kokarin in gyara yanzu.
Shiru tayi tana mashi wani irin kallon mamaki ganin yadda ya rikede kamar baahi ba lokaci guda idanuwanshi sun kada sunyi ja sosai dasu.
Mikewa tayi tana fadin Allah ya sauwaka shi kadai ta iya fadi tasa kai ta fice daga dakin shi kuma ya bita da kallo cikin takaicin ta har ta bacewa ganin shi a dakin.
Ya sauke ajiyan zuciya yana jan tsuki tare da jawo wayanshi dake gefe ya fara neman layin aminjn nasa yana son ya tambayeshi game da dansa Ahmed ko ya dawo a yanzu daga tafiyan nasa.
Abbane a kwance da tun safe bai iya fitowa waje ba ga abin karyawa masu aikinshi sun aje mashi bai fito ba har shadayan rana ya buga yana kwance yana faman tunanen duniya.
Ba komai yake tunane ba sai yadda wai ace matarka ta suna take kokarin son halaka da karfi da yaji taga ta mayar dakai baya ta gina kanta ita.
Bai debe tsamani a yanzu idan akace hjy karimace ta turo barayin da suka shigo masu gida suka kwace kudin da aka kawo mai daga can garinsu gusau kudin kuma na wasu filayenshine daya sayar da sunan zai fada harkan siyasa a lokacin .
Ba wanda yasan da zancen kudin amma kwatsam matasan bariyi suka dira masu a gida da sunan sukawo kudin nan da aka kawo mai su in cash a gida.
Hjy karima dake bayan shi tana nuna tsoro sai fadin take Alh ka dauko masu kawai ka basu su tafi su barmu shiyafi kagansu da bindigogi a hannayensu.
Yace wani kudi kudin da ba a shigo dashi gidan nan ba suna hannun wanda zai kawo min shi yana kokarin nuna cewa babu su a gidan ita kuma tana nuna cewa ai akwai kudin don sai fadi takeyi Alh ka dauko masu kawai su tafi su barmu.
Jin hakan shine dalilin buga mashi gindin bindiga da sukayi ba shiri Abba ya nuna kudin suka kwashe suka tafi.
Sai gashi kuma a yanzu ansace masa takardan babban filinshi haka kawai ranan yaje zagayen filin shine ya samu ana gina a ciki wai ansayarwa wani iyamuri da filin yana gina gidan mai a wajen.
Hankalin Abba din ya tashi sosai ya tambaya sukace a hannun wani suka saya shima yace wata mace baka ta sayar masa ga takardunsu kuma ya duba tabbas takardun filinne hakan ya jawo masu matsala a tsakaninsu suka dinga rikici har ya kira mata yan sanda .
Shine tace ba zata zauna ba tunda ya fara zarginta yace sai ta fito mashi da takardun nasa nan rikici ya tashi ta kwashe dama tana da gida ta koma ciki.
Sai daga baya yake jin irin halinta hankalinshi ya tashi har ya kaishi da kwanciya asibiti yanzu kuma sai abubuwa suke son su tsaya mashi duk lokaci guda yayi hasara mai karfi haka mai yawa.
Gashi iyalansa yanzu yasan suna cikin bukatu don sunyi waya da mama tana lissafo masa lissafi irin yadda ta sabayi mai abaya shine ya bata amsa cewa baida halin hakan a yanzu sai fitina ya tashi a tsakanin su.
A gajiye na dawo daga school jakata kawai na aje nayi sallah saina shiga cikin gida mu gaisa dasu kafin na dora girki ya dauke min hankalina don da safe ban shiga ba.
Koda na shiga Inna na zaune bakin kofanta Dije kuma tana dan sharo dakinta da kanta a hankali nayi sallama dije din ta dago kai tana fadin Amarya kin dawo ashe ?
Nace eh dije yanzu na dawo da safe na fita ban samu shigowa ba shine yanzu nazo in gaida ku tace nasan kin makarane ai tunda naga hakan.
Ina kokarin karban tsintsiyan a hannunta tana fadin haba barshi jeki huta abinki ai ina iyawa yau mai mun sharan ta fita zuwa gidan kawartane tunda ra dawo daga boko.
Nagane Aisha take nufi nadai karbi tsintsiyan ban duka yin sharan ba sai na nufi wurin inna ina gaida ita da ina wuni inna da kyar ta dago kai tana amsawa kamar ba zata tanka min ba sai naji tace.
A yi abinki yarinya tunda kin samu an kama maki in bashi ba inhar muna da muhinmanci a wurin ki aiba zaki fita gidan nan baki gaishemu ba.
Yanzu baga umma na wani tarewa ba shima dabaki sauki uwarshi da kakanshi da muhinmanci ba aigashi cewa yayi bai bude kaya sai kin dawo daga bokon ki kinzo ya bude a gabanki.
Da uwarki ne aiba zaki fita haka zikau zuwa wai bokon daba riba kawai baki nuna kulawa a garemu ba bokon banza bokon badala in bashiba macen aure da boko don lalacewan zamani aiko ga bokon nan muna girba a gidan nan yanzu.
Ke Rashida idan danki yai maki laifi kada ki sauke ga diyan mutane don bataji bata gani ba ita daya sauka a dankinta bata saka rai ga abinda yazo dashi ba saikece uwarshi zaki saka rai kinace tun dare kan magana daya.
Wai in tambayeki Rashida ke haka iyayyen mazanki sukai makine da kikai aure nan uban yaronga a lokacin dan isa ubangidanshine kawai amma nan ya dinga nuna ina aka saka dake don kawai mijnki yana aiki a karkashin shi a lokacin kuma baida kowa.
Nan dai ta fara gaya mata maganganu masu zafi ina jin hakan na shige dakin Dije nayi saurin sharowa na fice daga part din na barsu suna magana ina shiga na samu Ahmed ya shigo yana tsaye ya dafa baranda yana sauraresu.
Yana ganina yake fadin meya farune naji dije na fada da inna haka nace ban sani ba ya kara kallona yace baki sani ba ba daga can kike ba sai kawai na shige daki abina na kyaleshi.
Yaji zafin hakan da nayi sai naji ya kuta yasa kai zuwa sashen nasu nan naji muryanshi yana tambaya wai me ya farune haka don Allah haba inna ko yaushe a dinga jin muryanki da Dije kamar wanda yake zaune da kishiyarshi hakan baiyi ba wallahi gaskiya ki sake ina haka ai abin kunya kike jawo muna a gidan nan yanzu.
Kazo kai min fadane ubana ko ni bansan abinda ya dace ba ko da ace uwarta nake zata fita gidan nan bata gaida mu ba can dije ta amsa tace ba gashi yanzu tazo tace wallahi makara tayi da safen ba ta fita.
Wai inna dama akan zahra ake duk wanan abin haka akantane mana tunda kun daure mata gindi tayi iya shegen da takesowa mutane don kawai banda komai ko dadin abindai a tsatsona kafito ko mahaukaciya nake kuwa .
Inna zan saki zahra kowa ya huta ba shike nan ba ya fada a fusace yana juyawa nan djje ta shiga kwala mai kira yaki dawowa ya fice daga wurinsu din bata barshi ba ta biyoshi a baya tana fadin karka soma wallahi dama hakan takeso don ta aurama suwaiba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/19, 8:05 AM] Mmn Bibo: .🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
8️⃣2️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,

Zahra ki debo min bayan iccen tumfafiyan nan don Allah yake fada cikin wani irin murya mai nuna rauni a gareshi da alaman jin jiki ga bawa yake magana.
Banji me yake fada ba saida na matso kusa dashi na fahinci me yake fadi hakan yasa na fita da sauri saidai gaskiya nikan ba zan iya zuwa wurin wanan dan itaciyan ba da kullun nake mafalkin haske a cikin sa don na riga na tsorata da wanan wajen ko gaskiya.
Tsaye nayi a kofana ina shawara sai ga dije ta shigo gidan ta fito gidan mlm Tanimu da bata sameshi a gida ba lokacin yasa ta juyo gida hankali a tashe sai mukai kicibis da juna da ita.
Ince dai lafiya na ganki a nan haka hankali tashe na gane me take nufi yasa nace a, a ba komai ba cewa yayi dama a debo mashi bayan wanan dan iccen dake wurin ban dakinku din nan.
Iccen tunfafiya ke nan ko na gyada mata kai da nufin shi din tace ai abu mai saukine wanan bari naje na kakabo masa shi din ta shige ciki da sauri ni kuma na koma ciki.
Bata jima ba sosai sai gata dashi a hannunta tana fadin wanan dai yake nufi ko tana kokarin nuna min abinda ta debo din a lokacin nan nace da ita bari a nuna masa idan wanan yake nufi.
Maimakon in karba daga hannunta sai nayi gaba ta biyoni ciki da kyar ya iya tashi ya gani din don har lokacin yana cikin mawuyacin hali yadda muka barshi.
Idon shi ya kade yayi jawur dashi lokaci guda kamar ba nasa ba daya kallo inda muke din don yaga me aka debo hannu ya mika ya karba yana kokarin murmusawa tace kawo nan a murza maka idan shine da sauri na fita zuwa kitchen na dauko dan karamin turmin karfe da ban amfani dashi na karba na daka yace a barshi hakana in miko masa turmin na bashi.
Ya tura hannu ya debo yana shakawa a hancin sa Dije sai faman yi masa sannu takeyi ya miko min tare da komawa ya kwanta yana fadin Dije akwai garwashin wuta na turara ?
Take fadin na daiga sun dora girki yanzu da zan shigo bari na duba idan yayi sai a debo ma kawai master ka tashi ko chemist ne katafi zaifi.
Zahra ba ko wani ciwo bane na asibiti wanan ciwon na daban ne don, , , , atishawan daya fara sakewa ya hanasa karkare fadin abinda yayi niyar fada a lokacin.
Yayi tayin atishawa babu kakautawa lokaci guda muna masa sannu kan dije ta fita da sauri zuwa debo masa garwashin wutan ta kawo mai ya mike zaune da kyat yana dan dube dube a dakin kallo daya nayi mai a lokacin naji gabana yayi wani irin faduwa.
Saboda yadda naga yanayin tashin hankali karara a cikon idanun shi dagani kuma ciwon ba karamin ciwo bane gaskiya.
Yunkurin sauka daga kan gadon yayi take fadin ina kuma zaka haka bari na zauna a kasa inyi hayakin ya fada cikin murya mai rauni yana sauka a gadon zuwa kasa mika masa abin rufa tace da sauri.
Na dauko wani mai dauda da muka cire na bashi ya rufa nan dai ta taimaka mai yayi hayakin kafin ya bude lokacin yayi wani irin zufa sosai.
Ya dan dafa gefen gadon ya dora kanshi muna tsaye duk mun zuba mai idanu can ya sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi sai kuma atishawan da yake danyi a yanzu jefi jefi kafin ya mike yana hawa gadon tare da tambayan yanzu karfe nawa ake ne ?
Sha biyu saura minti ashirin dije ta fada mai don dai gaskiya ta nuna damuwa sosai a yadda take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login